22
*KUNDINA*
*SASAAL*
***
22
FATIMA; hankalina a kwance, nayi addu'a na shafe jikina, bayan na gama, na kwanta ina tuna kalaman Salim barci mai nauyi ya ɗaukeni...
★washe gari da Asuba, ana kiran assalatu na kira Salim.. bai ɗaga ba kamar yanda ya saba, ya katse ya kirani..
Ya na amsa sallamata ya ce "na gode wifey Allah Ya yi miki albarka"
"Ameen" na ce a hankali sannan ya katse wayar..
Wayar na riƙe a hannuna, ina murmushin jindaɗi, nutsuwa na ƙara ratsa zuciyata da gangar jikina...
Ban jima a zaune ba, bayan na idar da salla, na fara gyangyaɗi don na miƙe na koma kan gado, barci mai daɗi ya ɗaukeni...
*BABA*
kwanan zaune ya yi, yana kaiwa Allah kukansa, har aka kira sallar Asuba ya tafi Masallaci..
Bai shigo gida ba, sai da gari ya yi haske, kai tsaye sashen Hajiya Babba ya nufa..
Ya jima yana ƙwanƙwasawa, ba tare da tambayar ko waye ba Farida ta buɗe, a tunaninta masu yi musu hidima ne..
Yanayin fuskarta ya nuna alamar ko sallah bata yi..
A ɗan firgice bayan ta buɗe ta ce;
"Ina kwana Baba"
Maimakon ya amsa gaisuwarta sai ya tambayeta;
"Maiyasa baki yi sallah ba Farida?"
Cikin kame-kame tace;
"Wallahi Baba nayi tare muka yi da Hajiya"
Bai ce mata komai ba, sai kansa da ya girgiza ya raɓata ya wuce, a ransa ya na yi mata addu'ar shiriya, tunda ba yau ya saba yi mata faɗan Sallah ba..
Kai tsaye ɗakin Hajiya Babba ya murɗa kofa ya shiga, a kan Sallaya ya sameta tana Sallah...
Kai ya jinjina yana kallon agogon hannunsa, da ya nuna ƙarfe bakwai saura...
A doguwar three seater da ke gefen gadonta ya zauna, yana jiranta ta iddar..
idonsa ne ya kai kan wayarta a gefensa, da hanzari ya ɗauka ya zura a aljihunsa haɗe da gyara zamansa.
Hajiya Babba tana idarwa bata tsaya wasu addu'o'i ba, ta tattare sallayan ta kwashe, ta na cewa;
"Barka da Asuba Alhaji, ina kwana"
Ya na binta da kallon takaici ya ce;
"Yanzu Fisabilillahi Saratu haka ake Sallah? Yanzu ƙarfe nawa, kuma daga idarwarki har kin yi zumbur kin miƙe, saurin me kike yi, ina zaki je?"
Hajiya Babba baki ta saki tana kallonsa, tuna ƙudirinta nason tambayarsa fita zuwa gidansu Salim, sai ba ta yi masifa ba ta ce;
"To Alhaji za'a gyara In Sha Allahu. Dama ina so na tambayeka, zan je gidan ƙawata na dubota bata da lafiya, tun shekaran Jiya tana kwance Asibiti, jikin sai a hankali"
Ta ƙarasa faɗa tana marairaice fuskarta da muryarta kamar gaske, don tasan matsawar yasan gidansu Salim zata je, ba zai barta ba..
Mamakinta da tsoronta ne ya kama Baba, sai ya fara tambayar kansa a cikin zuciyarsa, shekarar Saratu nawa, tana shirya irin wannan makircin a gidansa bai taɓa ankara ba?
Gudun karta fahimci ya san da maganar karɓar lambar mahaifiyar Salim da tayi, sai ya yi gyaran murya ya ce;
"Idan kin shirya, kiyimin magana na saukeki, nima na shiga nayi dubiyar, Allah Ya bata lafiya"
Baki ta saki tana kallonsa har ya miƙe ya fice..
Banda tasan halin Fatima da tsoro, ai da sai ta ce ita ta gayawa Alhaji komai..
Babu irin saƙar da bata yi ta kwance ba, amma sam bata samu mafita ba..
Ba ta lalubi wayarta ba, ta nufi ɗakin Farida... Tana mitar abinda Baba ya yi mata..
Ba ta tashi neman wayarta ba, sai da suka karya, ita da Farida sukayi shawarar kawai ta kira Hajiya Turai ta haƙura da zuwa, kar Baba ya ganota.. wataƙilama su yi sa'a Hajiya Turan tace zata zo da kanta..
Farida ta aika ta ɗauko mata wayarta, sama ko ƙasa Farisa ta nemi wayar ta rasa, kuma idan suka kira tana shiga amma basa jin ringing..
Hajiya Babba bata kawo komai ba a ranta, sai wataƙila wayar wani wajen ya faɗa...
BABA;
Yana fita daga Sashen Hajiya Babba, ya lalubo lambar Fatima ya danna mata kira..
Da muryar barci Fatima tayi sallama ta gaisheshi, bai amsata ba, ya tambyeta menene sunan mahaifiyar Salim..
Fatima ta ce; "Hajiya Salamatu Turai Bamalli"
"Okay" kawai Baba ya ce ya katse kiran..
Password ɗin Hajiya Babba da ya jima da sani ya cire, ya lalubo lambar Hajiya Turai Bamalli ya goge, ya saka wayar a silent ya gefe a aljihunsa..
Ya na zuwa Sashensa ya kwanta barci, duk kiran da su Hajiya Babba sukai ta yi da wayar Farida bai san suna yi ba.
Sai ƙarfe 10 ya farka, ya yi wanka ya shirya suka karya da Aunty Amarya, sai a lokacin ya ga tarin kira da lambar Farida..
Wayar ya ɗauka ya koma sashen Hajiya Babba..
Ya jima yana ƙwanƙwasawa basu buɗe ba, yasan ba zai wuce wani makircin suke haɗawa..
Farida ce ta buɗemai, ta ƙara gaisheshi haɗe da bashi haƙurin ta shiga wankane, Hajiya Babba kuma tana ɗaki kanta yana ciwo..
Murmushi kawai Baba ya yi, ya wuce ɗakin Hajiya Babba kai tsaye.
A kwance ya sameta hannunta dafe da kanta idonta a runtse, a hankali tana furta
"ciwon kai lokaci ɗaya haka, Allah Ya sa ba lokacin tafiyata ce tayi ba, Allah Ya sa mu cika da kyau da imani"
Baba ƙara tsorata ya yi da lamarinta, bai taɓa sanin Saratu ta iya makirci irin wannan ba...
"Sannu" ya ce mata, kafin ta ɗago ya tura mata wayarta a ƙasan gado, sai ya yi kamar zai durƙusa don jin kanta ko da zafi...
Da sauri tayi baya, Baba bai san sanda ya saki dariya ba, cikin zolaya ya ce;
"Haba ke kuwa, sai ka ce mai iska, irin wannan zabura haka? Allah Ya ƙara sauƙi, Ni zan fita, duk yanda kika ga yanayin jikin kisa Farida ta kirani a waya"
"Toh Alhaji" ta faɗa murya ƙasa-ƙasa..
Juyawa yayi ya fita, a zuciyarsa yana jinjinawa halinta..
Baba yana barin Sashen Farida ta taho ɗakin da gudu, Hajiya Babba ta miƙe zaune tana dariya...
A gaggauce ta ce;
"Farida ki ƙara kiran wayar nan dan Allah, ina so na kira Hajiya Turai mu fara gaisawa, idan ya so ko zuwa gobe ne ko jibi, sai na sako mata zancen waccen mara kunyar da abinda ta aikata"
Farida ranta fari fes da kalaman Hajiya Babba ta fara kiran layin amma basa jin ringing Gashi dai wayan yana shiga amma babu ƙara kuma ba a ɗaga ba, balle su yi zargin wani ne ya ɗauka..
Sai da suka yiwa ɗakin filla-filla suna haki sannan suka ga wayar a ƙarƙashin gefen gado..
Ko ƙarasa gyara ɗakin basu yi ba, Hajiya Babba ta zauna tana haki..
Hannunta yana rawa ta cire password, sai dai sama ko ƙasa ta nemi lambar Hajiya Turai ta rasa..
wayar ta miƙawa Farida itama ta duba yafi sau goma amma babu lambar..
Cikin takaici kamar Hajiya Babba zata yi kuka ta ce "wallahi da hannuna nayi saving ɗin lambarta, gaskiya dole Alhaji ya canza min wayar nan, gaba ɗaya naji na tsaneshi"
Farida tsabar takaici kasa magana tayi, ga wahalar nemo waya ga babu lambar da suke zumuɗin kira...
Masu aiki Farida ta kira suka gyara ɗakin..
Hajiya Babba tace Farida ta saka mata ido duk ranar da Salim ya ƙara zuwa ta gayamata da kanta zata fita ta amshi lambar...
FATIMA;
Kiran Baba ne ya tasheni daga barci, ban kawo komai ba a raina dangane da tambayar sunan Hajiyar su Salim da ya yi, sai wataƙila bincike zai yi a kansu...
Abin kari mai sauƙi na samarwa cikina, nayi wanka na saka kaya marasa nauyi, na zura Hijjabi don zuwa gaishe da Baba...
A bakin Mota na sameshi a tsaye, yana ƙoƙarin shiga.
Bayan na gaishe shi ya amsa ya buƙaci na bashi lambar Salim, zasu yi magana.
Ban fito da wayata ba, kuma ban haddace lambarsa ba, don haka na koma na dauko..
A cikin Mota na dawo na sameshi a zaune, da alama ni yake jira, ina gama karanto mai, ya tashi motarsa ya bar gidan... Nima na koma Sashena na kira Mama, bayan mun gaisa har da Kakata tayi min addu'o'i da tambayar yaushe zan zo?
Kafin na bata amsa Mama ta karɓi wayar tace na bari sai aurena ya matso, saboda bata son ƙananan maganganu... Da haka muka yi sallama na kira Salim..
Mun jima muna hira da shi cikin so da ƙauna kafin muyi sallama na ɗora girkin rana...
Da dare yayi kusan raba dare muka yi muna waya da Salim..
Bayan kwanaki;
Daga ranar wata Monday da Salim ya ɗaukoni a makaranta ya dawo da ni gida a motarsa, kullum shi yake zuwa ya ɗaukeni, ya dawo da ni, amma abin mamaki bai ƙara zuwa gidanmu da sunan zance ba, sai dai muyi hira a makaranta, da kuma a kan hanya idan zamu tafi ko idan muna dawowa..
A watanni biyun da suka baya, iyayen Sadik suka kawo kuɗin aure gidanmu.
A wannan gaɓar Hajiya Babba kasa haƙuri tayi ta aiko masu aikinta na bata lambar Salim, ban yi musu ba, na rubuta na basu.
Ban sani ba, ko ta kira be bata samu, sai gashi ta ƙara turo Farida har Sashena na ƙara basu ɗaya layinsa..
Sanin ɓarnar zai iya biyowa baya yasa na sanar da Baba..
Bai ɓata lokaci ba, yaja hannuna har Sashenta, ya yi mata gargaɗi da kakkausar muryar babu ita babu shiga lamarin aurena, idan kuma har aka fasa auren nan ta sanadiyarta to wallahi shima ya gama zama da ita...
Ban san zuciyar Hajiya Babba ba amma nasan cike yake tsanata..
Abinda Ya fara ɗagamin hankali shine ramar Salim, idan na tambayeshi me yake damunsa sai ya yi murmushi ya ce ba komai...
Muna cikin haka ya ce min zai yi tafiyar sati ɗaya...
Ranar da sati ya zagayo muka haɗu a makarantar da na kalleshi kasa jurewa nayi na fashe da kuka saboda irin ramar da ya yi..
Lallashina ya fara yi yana bani haƙurin zazzaɓi ne yake damunsa, bai gayamin ba ne, saboda kar hankalina ya tashi...
Kai na girgiza da salon maganar da ban san na iya ba na ce;
"Ka gayamin menene yake damunka, karka ɓoyemin, ka ji"
Kan sa ya sunkuyar ƙasa na sakanni, sannan ya ɗago idonsa cike taf da hawaye ya ce;......✍🏻