KUNDINA

23

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*


SALIM;

Kansa ya sunkuyar ƙasa na sakanni, sannan ya ɗago idonsa cike taf da ƙwalla ya ce;

"Tun daga ranar da na bar gidanku komai ya rikicemin, amma In sha Allahu komai ya kusa zuwa ƙarshe"

Murmushi kawai nayi, amma Allah ne kaɗai yasan abinda nake ji a cikin zuciyata, ban ce mai komai, tunda baya so na sani, idan ma a kaina ne, dole zan ji wata rana..

A ranar Salim bai dawo da ni gida ba, wai zasu shiga meeting..

Bai tafi ba, sai da ya rakani har bakin titi, yana ƙara kwantarmin da hankalin lafiyarsa ƙalau, wasu abubuwa ne kawai suka shige mai gaba.. 


Da kanshi da ya taremin Adaidaita sahu da zai kaini ni har ƙofar gida, ya biya sannan muka yi sallama..

SALIM; yana dawowa cikin makaranta ofishin Abokinsa,  Lawal lecturer su Fatima ya wuce, ba meeting ɗin da zai shiga, ya faɗawa Fatima hakane don ya samu sarari, ya kuma yi sa'ar ba Mace ba ce, mai shishigin son sanin abinda aka nuna ba'a so ta sani..

A zaune ya sameshi, yana aiki, suna yin ido biyu Sir Lawal ya zare gilashinsa, cikin tausayawa ya ce;

"Salim kai ne ka ƙara komawa haka, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"

Ya ƙarasa faɗa yana miƙewa..

Salim bai ce komai ba, ya nemi waje ya zauna.. shima Lawal komawa ya yi ya zauna yana cigaba da kallon Salim...

Sun jima a haka, kafin Salim ya numfasa cikin takaici ya ce;

"Wallahi na rasa ya ya zanyi Lawal, bana so Fatima ta ji wani iri, yanzu haka ina buƙatar kuɗi masu kauri, saboda asarar da na tafka a kasuwancina amma Hajiya tace sam ba zasu bayar ba, akan maganarnan har Bammali na je, amma ina babu wanda ya maramin baya..

Lawal ban saba da kashe iya albashina da kuɗin kasuwancina ba, yanzu haka ma fa abinci sai dai na siya, na rasa ya ya zan yi da Hajiya wallahi, ta komamin kamar ba ita ba, magana ma babu na arziƙi a tsakanina da ita sai dai sai dai faɗa da habaici, tana ganina ina ƙarewa a tsaye amma taƙi tausayamin ta amshi abinda nake so"

"Ta yaya zata amshi abinda ka nuna fifikonsa akansu"

Lawal ya tari Salim muryarsa a kausashe.. 

Shiru Salim ya yi..

Lawal ya ɗora da;

"Wai yarinyar nan ita kaɗaice Mace ne Salim, ban san yaushe ka zama gardamamme irin haka ba, Iyayenka sune ƙashin bayanka, idan babu su bazaka maru ba, ko kana tunanin yarinyar zata cigaba da son ka ne, idan taga ka daina hawa manyan motoci eh? To bari ka ji na gayamaka tun wuri kasan inda dare yayi maka, soyayya ba hauka ba ne, idan zaka yiwa kanka faɗa kayiwa kanka, saboda ko danginku da suka mara maka baya sun shige maka gaba an ɗaura muku aure, ba farin ciki zaku samu ba, ƙarshe abinda kake gudu shi zai faru"

Cikin karyewar murya Salim ya ce;

"Ba zaka gane ba Lawal, mahaifinta fa, har kirana ya yi, ya ce na daina zuwa hira gidan kar step mother ta, ta karɓi numbern Hajiyarmu ta ƙulla wani makircin, da wani ido zan kalleshi na ce na fasa? Ba zan iya ba, Fatima zata cutu, zata yi kuka ƙarshe ma nayi sanadiyyar faɗawarta wani hali, ba zan iya ba"

Lawal a fusace ya ce;

"To ai sai kaje kayi ta yi, ka kashe kanka a banza, ni dai na gama nawa"

Salim wayarsa da ya ajjiye a teburin lawal ya ɗauke ya zura a aljihu tare da barin Ofishin...


*MENENE YA FARU TSAKANIN SALIM DA IYAYENSA BAYAN YA BAR GIDANSU FATIMA A WACCEN LOKACIN DA HAJIYA BABBA TA ƘARBI LAMBAR MAHAIFIYARSA???*✍🏻

In sha Allah anjima ƙarfe 8:00pm zamu ɗora