KUNDINA

24

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*

*NAFISATU ALIYU SASAAL*



24


A ranar da Salim ya bar gidansu Fatima a waccan ranar da Hajiya Babba ta karɓi lambar mahaifiyarsa, a Parlo ya samu Mahaifansa suna hira, kowannensu ya na ɗan taɓa aiki a System..

Hajiya Turai tana ganin shigowarsa ta saki dariya fararen haƙoranta, da tayiwa ado da haƙoran maka biyu dama da hagu suka bayyana gwanin sha'awa..

Bata gama rufe baki ba ta ce;

"Oyoyo Ango, wai ni yaushe zaka kawomin Amaryar tamu na ganta ido da ido ne? don ni ban gamsu da hoto ba.. ko ya ya kace Daddynsu"

Ta ƙarasa faɗa tana kallon Mijinta..

Shima dariya ya yi yace;

"Rabu da shi, duk ya gama wani ɓoye-ɓoyensa, sai tayi sati a gidan nan sannan za'a kai masa ita gidansa"

Dariya suka saka gaba ɗaya har Salim, sai dai shi nashi na yaƙe ne..

A gefen Hajiyarsa ya zauna, yana ganin, kamar wannan ne lokacin da ya dace ya sako musu batun da ya zo da shi duba da yanda suke cikin nishaɗi...

Gyaran murya ya yi, dukkansu suka maido da hankalinsu gaba ɗaya kanshi, cikin ladabi ya fara magana;

"Dama ina so na tattauna da ku, amma inaso dan Allah ku yimin kyakyawar fahimta" cikin taushin harshe da zai sanyaya musu gwiwa su amince da Fatima ya basu labarin ƙaddarar da ya faɗa mata, sannan ya ɗora da;

"Ba na so ku ji a wani waje, a gaya muku ƙarya da gaskiya kuma ina ganin kamar mun dace da juna, duba da irin kuskuren da na aikata a bay..."

Bai ƙarasa ba, Hajiya Turai ta tareshi, Fuskarta a haɗe kamar bata taɓa dariya ba ta ce;

"Kul karka kuskura ka haɗamin kanka da yarinyar da ta kasa riƙe mutuncinta. Kai naka kuskure ne, ita kuma nata son zuciyane da rashin mafaɗi..

Salim idan har kana son farin cikinmu to ka rabu da yarinyar nan, wallahi sai  na ji gaba ɗaya ta fice min, to banda hauka irin naka, kana ganin zata faɗa maka gaskiya ne? waya san iyakacin abubuwan da ta aikata, wato shi waccen ya gudu, kai kuma kaine sokon da zaka aureta ko??

Ba zan yi maka baki ba, amma iyakacin horon da zan yi maka ya isheka"

Ta ƙarasa faɗa tana tattare wayarta da System ɗinta ta barsu a zaune..

Fuska a mairairaice Salim ya kalli Daddynsu kamar zai yi kuka..

Daddynsu bai ce komai ba domin dama can sai abinda Turansa ta ce, ba boka ba Mallam haka Allah Ya jarabceshi da tsananin sonta, zai yi wahala ta yanke hukunci ya ce a'a..

Shiyasa gaba ɗaya danginsa suka tsaneta, don idan ta ce kar ya bayar to fa ba zai bayar ba, har sai tayi niyya...

"Daddy ka ce wani abu dan Allah, wannan karon"

Salim ya faɗa kamar zai yi kuka..

Ɗan jim Daddynsu ya yi sannan ya ce;

"Tuntuni nasa su Alhaji Idris(Abokanansa da suka je neman auren Fatima) sun yimin bincike komai akan gidan da kaje neman aure, kuma sun tabbatar min da ƙaddara ce ta faɗawa ita yarinya, kamar yanda ya faɗa maka, amma iyayenta mutanen ƙwarai ne, shiyasa ban damu ba, amma kasan halin Turai da gardama, Alhaji Baba ne( Mahaifinsa) kawai zai iya taka mata birki"

Kasake Salim ya yi yana binsa da kallo, a karon farko yaji haushin yanda mahaifinsa baya iya motsa ƙwanjinsa a cikin gidansa, da murna suke yi, Hajiyarsu ta ciri tuta sai abinda ya ce.

 Ko da yake ba Mahaifinsa ba ne kaɗai, baya iya motsa ƙwanjinsa ba, shi kansa da ya zaƙe ya motsa ƙwanjinsa ya nemi ƙudi ya tara na kansa bai dogara da nasu ba, da Hajiya bata yi masa barazanar horo ba da dukiyarsu ba..

Ya na can tunanin bai lura da sanda Daddynsu ya bar shi a zaune ba...

Daga wannan dare ya fara rasa kwanciyar hankalinsa, musamman da yaje Bammali ya kai ƙarar Hajiyarsa dangin mahaifinsa suka yi mata chaaa, har da masu kiranta a waya..

Daganan nan ta ƙara tsananta masa kamar ba ita ta haifeshi ba, don bata saba cewa "a'a" a cikin gidanta wani ya ɗaga yatsa ya ce mata "eh" ba..

Duk wani hanya da ta san Salim zai samu walwala daga dukiyarsu duk tabi ta toshe shi, idan aka cire motocin hawa.

Abunka da wanda bai saba da damuwar komai ba, idan ban da waccen ƙaddarar da ta faɗa masa, wannan dalilin yasa ya fara rama, gashi yana tsananin son Fatima ba zai iya rabuwa da ita ba, ga matsi daga gida, Mahaifinsa kuma baya cewa komai, haka ƴan uwansa duk sun bi bayan Hajiyarsu...

Wasu lokutan haka zai wuni yana jin ciwo a ƙirjinsa amma baya gayawa kowa.

A wajen wata Abokiyar  aikinsa Mariya da suke mutunci sosai, matar aure ce da yaranta biyu,  yake haɗa lefen Fatima da kaya masu kyau, da kanshi yake siyo duk abinda yaga zai mata kyau..

Hajiyarsu babu wanda ta gayawa bikin da bakinta, ko da iyayen a can Bammali suka ji labari;

Maganganun son zuciyarta ta faɗa musu, wasu sun goyi bayanta musamman iyayenta, amma a ƴan uwanta ansamu masu sukarta har da yi mata gorin abinda Salim ɗin aikata..

A cikin wata ɗaya saboda rashin kula da tunani aurensa da yake tunkaro shi, kuma babu mai mataimaki, komai  nasa ya fara lalacewa musamman  kasuwancinsa..

Lokaci ɗaya Jarinsa ya yi ƙasa saboda cutar da wani wanda ya yarda dashi ya yi masa..

Har gaban Hajiyarsa ya je ya ɗurƙusa yana roƙonta, tayi biris da shi, ta ce; tunda ya iya zuwa dangin mahaifinsa su shige mai gaba har a saka ranar aurensa ai zai iya zuwa su farfaɗo masa da kasuwancisa..

Akan wannan  har Bammali ya je wajen kakansa, ya saka baki Daddynsu ya ƙara mai jari, to dama Mahaifinsa shine abinda Bature yake kira Breadwinner wanda yafi kowa rufi asiri a dangi, balle ya saka ran a cikin masu bin bayansa a dangin mahaifinsa za'a samu masu taimaka mai..

Alhaji Babba cewa yayi shi ba shi da hurumin tursasawa Daddynsa ya ƙara mai jari, batun auren dai yarinya da yake so ne Turai ba ta isa ta dakatar ba, sai abinda Allah Ya yi da kuma iya inda ƙarfinsa ya ƙare...

Haka ya tattaro ya dawo gida, washe gari ne suka haɗu da Fatima a makaranta...


*DAWOWAR LABARI*✍🏻