25
*KUNDINA*
25
FATIMA;
muna tafe a Adaidaita sahu ina kallon ababen hawa, haka kawai na ji ƙwalla yana neman tahomin, saboda tuna yanayin da na baro Salim.
"Me Salim yake ɓoyemin"
Na tambayi kaina a cikin zuciyata ina ƙara hasaso irin ramar da ya yi..
Har muka kai bakin gate ɗin gidanmu bai daina tunani ba, jikina a mace bayan mai adaidaita sahu ya faka na sauko, na nufi ciki..
Murya ƙasa-ƙasa na gaishe da Baba mai gadi.. dai-dai lokacin hankalina ya kai kan irin ƙosassun motocin da aka faka a Harabar gidanmu har gudu huɗu.. duk sun cinye har hanyar wucewa..
Ban cika kallon abun duniya ido buɗe ba, gudun wulaƙanci daga masu shi, amma a wannan karon ƙuri nayiwa motocin da ido, ina jinjinawa Ubangiji a cikin raina.. na san ba zai wuce wasu ne suka zo daga ƴan uwan Aunty Amarya ba.. amma da alama waɗannan sun fi ragowar kuɗi.. don ba'a taɓa zuwa da irin waɗannan motocin gidanmu ba...
Ban kawo da mutane ciki ba, na matsa na ɗan shafa wacce nake ganin zata fi tsada a ciki...
"Ohh Allah" na faɗa ina murmushi haɗe da riƙe haɓa.. gaba ɗaya sai na manta da damuwar da nake ciki...
Baya na yi kaɗan, ina kallon lambobin jikin motar, har da star ɗauke da sunan
*"GEN. MUZAFFAR ALEE"*...
ƙara maimaita suna nayi, a raina na ce sunan ma irin na masu kuɗin da suka isa ne...
Tuna abubuwan da suke gabana yasa na ratsa motocin don zuwa Sashena.. Daga nesa na hango mutane, Aunty Amarya da Baba kawai na gane a cikinsu, bakinsu a washe har ina iya gano haƙoransu daga inda nake tsaye, mamaki dariyarsu ne ya kamani, musamman Aunty Amarya da bata saba dariya ba..
Kamar na tsaya na ga wanane suke tare da shi, har suke irin wannan dariyar, mutumin kwanaki da na gani a parlon Hajiya Babba ne ko kuma wani ne daban? sai dai tuna yanayin ƴan uwan Aunty Amarya da wasun su suke masu sauƙin kai wasun su kuma masu shariya balle wannan da na ga motoci na alfarma yasa nayi sauri na shige sashena...
A gajiye na buɗe sashen na shige..
Abunka da zuciya da son abu mai kyau, har na yi wanka nayi girki na yi Sallah ban daina tuna kyan motocin da na gani ɗazun a Harabar gidanmu ba.
Tunanina sai ya fara janyewa daga kan Salim, kawai na fara hasashen na gama karatu na samu aiki na haɗa da business, na siyawa Baba irinsa ɗaya na siyawa Mama itama, sannan na siyawa kaina..
Har ina hasashen yadda zata kasance da irin farin cikin da zan samu idan haka ta kasance..
A haka barci ya ɗaukeni cike da mafarkan motocin da suka yi matuƙar birgeni..
Ban farka ba, sai bayan la'asar, abinda ya fara faɗomin shine Salim, wayata na duba, naga dai bai kirani ba..
A kasalance na tashi nayi alola nayi Sallah, ina idarwa na ɗauki wayata na kira Salim..
SALIM;
Daga ofishin lawal gida ya wuce, zuciyarshi sam babu daɗi.
A parlo ya samu Hajiyarsu tana waya, bata amsa sallamar da ya yi ba, yana yuƙurin gaisheta ta dakatar da shi da hannu..
Ransa ne ya ji ya ƙara ɓaci, maimakon ya yi kwanar da zai kaishi Sashensa, kawai sai ya juya ya bar gidan gaba ɗaya..
Yawo ya yi ta yi a gari, ya rasa wa zai tunkara da matsalarsa ya ji sanyi a ransa.
Fatima ce kawai zai iya gayawa ta mara masa baya, sai dai kuma ita ba zai iya gayamata ba, saboda yasan lamarin ba zai yi mata daɗi ba..
Da ya gama bulayinsa gida ya ƙara komawa, bai nemi Hajiyarsu ba, ya shige Sashensa ya yi wanka ya kwanta, ko abinci bai nema ba, barci ya ɗaukeshi...
Bai farka ba, sai da alarm ɗin sallar La'asar ya tashe shi..
Jiki a mace ya ƙarayin wanka, ya ɗora alola, a gurguje ya shirya ya ɗauki mukullin mota ya fita.
Sai da ya fara biyawa masallaci ya yi sallah, sannan ya wuce Restaurant don neman abincin zai sawa cikinsa..
Ya na ƙoƙarin gyara parking kiran Fatima ya shigo mai..
Murmushi ya saki, bai bari ya gama gyara parking ɗin ba ya katse ya kirata..
Cikin taushin muryarsa na halitta da ya haɗe da yunwar da yake ji, ya ce;
"Assalamu alaikum Wifey, ki yi haƙuri, ban kira na ji ya ya kika je gida ba"
Fatima murmushi tayi ta amsa sallamarsa haɗe da gaisheshi..
"Ba zan amsa gaisuwarki ba, har sai kin ce kin haƙura"
Dariya mai sauti ta yi tace;
"To ai ni baka yi min komai ba"
ta faɗa har cikin zuciyarta..
"Ni dai ban yarda ba, kawai ki ce kin haƙura"
Ba don Fatima ta so ba ta ce; "na haƙura"
Murmushin jindaɗi Salim ya yi ya ce;
"Yauwa Wifey na gode, yanzu yunwa nake ji, ki bani lokaci kaɗan zan kiraki kin ji?"
Cikin ɗan damuwa Fatima ta ce;
"Tohm ka ci da yawa ka ji?"
"Ba ki da matsala Madam"
Salim ya faɗa yana dariya.. da haka suka yi sallama..
Bayan Fatima ta katse kiran, ya jima da wayar a hannunsa, kansa jingine da kujera mota, idanunsa a lumshe, saurin fahimtar Fatimah da sauƙin kanta kaɗai abin so ne, ba zai bari wani kuskure da ta aikata a baya yayi masa shamaki da samun Mace ta gari irinta ba...
Cikin sabon ƙarfin gwiwar da ya ji lokaci ɗaya bayan gama wayarsa da Fatima ya sauko daga Mota, ya shiga cikin Restaurant..
FATIMA;
Na jima a zaune, ina murmushin sauƙin halin Salim...
Ban tashi ba, har sai da aka fara kirayen sallar Magrib.. na tashi na yi.
Bayan na idar nayi addu'o'i na, sannan na miƙe don zuwa gaishe da Baba..
Da na fito na zo daidai inda motocin ɗazun da rana suka faka, sai na na ji a raina, ina ma da zan iya tambayar Baba, su wanene suka zo ɗazun...✍🏻