Chapter 14&14
*HAƊUWAR DARE*
©️Meenat A. 'Yandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
TALLAH TALLAH TALLAH
Idan Allah ya yarda da kai, to ka ci nasara, ko da mutane sun ƙi ka.
Idan Allah ya ƙi ka, to ka yi asara, ko da mutane duk sun soka.
#ZancenHikima
Assalamu alaikum
🛍️ INA MASU BUƘATAR KAYA MASU KYAU DA INGANCI 🛍️
Lallai nesa ta matso kusa!
Ku gaggauta shiga Group ɗin Hajiya Aisha Mustapha,
👇👇
***
Domin samun kayayyaki masu kyau a farashi mai sauƙi.
📞 Ko ku tuntuɓeta a wannan lambar:
( *** )
Kayayyakin da take siyarwa sun haɗa da:
👗 kayan bacci
👙 Pant & bra
👖 palazzo
🧒 Dilar kayan yara (mix)
👕 Dilar T-shirt
🛏️ Dilar zanin gado
👜 Dilar hand bag
🧕 Dilar Abaya
👘 Jallabiyan maza da na mata
🤝 Muna maraba da:
✔️ Masu siya ɗaya-ɗaya
✔️ Masu siya sari (wholesale)
📦 Ƙari:
Muna kawo kayan yara na 'yan kanti bisa order, kuma duk akan farashin sari.
Ku garzaya yau, ku amfana da kaya masu kyau da inganci.
Page 13&14
...Har magriba tayi Usman na tare da Zainab. Bayan ya yi isha'i ne ta ga ya fesa uban wanka tamkar wanda zai je gasar kyau.
"Wannan wanka haka, ko dai abokiyar zama zaka karo mini ne. Domin wannan gayu dai ya yi kama da na wanda zai je taɗi?"
Ta karasa maganar cikin sigar zolaya. Har ga Allah sai da Usman ya ji zuciyarsa ta karaya gabansa ya yi wata irin mummunar faduwa. Samun kansa ya yi da yin murmushi. "Mahaifiyar abokinmu ce ba lafiya ita za mu je ganowa"
"Allah ya tsare" Zainab ta karasa maganar tare da kwanciyar a kujera.
Mota ya dauka kai tsaye ya nufi gidan su Zulfaida. A wannan karon babban abin da ya ba shi tsoro tun kafin ya karasa ta fito ko kuma dama can tsaye take tana dakon zuwansa.
Hasken motar ya kashe ya na mai fitowa fuskarsa dauke da murmushi ganin yau an samun canje-canje, duhun kofar gidan ma ya rage akwai haske ba laifi amma fa ba wani mai yawa ba. "Angon Zainab! Ya mai jikin?"
Cewar Zulfaida. Hakika Usman ya yi mamaki ko kuma in ce ya kadu da jin abin da ta fada. "Wa ya fada miki wannan sunan? Yaushe kika san bata lafiya?"
Murmushi mai kara narkar da shi tayi. "Duk abin da ya shafe ka ina kokarin saninsa"
"Haka ne yar masani nima yau ya kamata ki barni in Shiga ciki mu gaisa da Hajiya ko in bata hakurin kade mata dita da na kusa yi"
"To shi kenan zaka shiga, amma minti nawa za kayi?"
"Eh to! Ki barmu in ma kwana za muyi ki zuba mana ido"
"Hmm! Ai ramin kura sai 'ya'yanta kai dai ka bari In shiga da farko In sanar mata zaka shigo."
Tana kaiwa nan ta tura kofar ta shige gidan. Ta kusa mintuna biyar kafin ta dawo ta ce mai su shiga. Usman ya yi mamaki ganin da suka shiga gidan shi ma babu hasken kirki. Tamkar masu rowar haske haka gidan ya ke can da haske kadan In kuma kayi dubanka zuwa wani wurin sai ka ganshi durum ba haske. Wani daki ta shigar da shi, wani irin kanshi ne ya daki hancinsa. Zai iya cewa kaf duniya bai taba jin kamshi me dadi da shiga zuciya irinsa ba. Zaune ya hango babbar mace wadda zata yi sa'ar mahaifiyarsa. Ganinsu ya sakata washe baki, bayan sun gaisa nan hira ta barke a tsakaninsu kasancewar Usman irin mutanen nan ne da ke da surutu in suka samu wuri. Abin sha Zulfaida ta kawo masa bai bata lokaci ba wurin shan wani juice daya dauki hankalinsa. Shan shi ke da wuya ya ji ilahirin tsikar jikinsa ta tashi, kansa kuwa kamar an juye masa shi. Sabuwar kaunar Zulfaida ta shiga ilahirin lungu da sako na jikinsa. "Ya kamata ka tafi gida dare na kara yi" Zulfaida ta karasa maganar tare da kwashe kayen data kawo masa. Bankwana suka yi da mahaifiyarta ya mike ya fita. Sai dai a wannan karon a tsakar gidan kananun yara ne birjik suna wasa, abin da ya ba shi mamaki shi ne dazu babu kowa.
Waje ya fita ya na jiran zuwan Zulfaida.
"Yau dai ka ga mahaifiyarta ka ga yan gidanmu" ta karasa maganar tare da fitowa. "Kwarai kuwa kuma na ga wurin zama, abin da ya rage shi ne a bani damar turo magabatana domin bada wasa na zo ba”
“Ban fahimci abin da kake fada ba.”
“Ina nufin kinyi min naga matar aure ko in ce na wadda zanyi ta biyu da ita"
Sunkuyar da kanta tayi kasa tana wani irin murmushi da ita kadai ta san ma'anarsa.
"Ni dai marainiya ce, amma ka je ka fara sanar da mahaifiyarka, Indai tasan da wannan maganar hakika zan baka duk irin damar da kake nema. Dare ya yi sai da safe" garam ta turo kofa ta kulle.
Har ya karaso gida yana farin ciki da wannan lamari. Rokonsa daya Allah ya wayi gari ya sanar da Mama halin da ake ciki, ko dan tsanar da ta yiwa Zainab yasan zata amince masa. Lokacin da ya koma gida har ta yi bacci, shi ma ruwa ya watsa ya kwanta. Washe gari da kansa ya haɗa masu breakfast Bai fita ba sai wajen tara. Ganin ya karaso kofar gidan ya saka shi ji gabansa ya yanke ya fadi. Allah ya sani ya na tsoron halin mahaifiyarsa, abu daya ya san zai kwace shi shi ne maganar aure daya zo mata da ita"
Kallon banzar da ta aika masa ko gausuwar tasa taki amsawa.
"Sallamamme Me ya kawo ka inda nake ko ita ta baka izini ka zo inda nake ka karasamin rashin mutumcin da bata karasa ba?"
"Kiyi hakuri Mama. Wallahi banzo wurin nan da nufin in bata miki rai ba, zuwa na yi in baki hakuri akan abin da ya faru"
"Kai nan har kasan darajanta da mutumci na? Ai da ace kana daraja ni a matsayin uwa da tuni ka rabu da waccan yarinyar. Ko da ya ke ai dama can bada yawuna ka aureta ba"
"Kiyi hakuri Mama wallahi bana jin dadin fushin da kike yi da Ni, Indai maganar kara aure ce wallahi zan kara yanzu ma maganar data kawoni kenan" ya karasa maganar tare da sunkuyar da kai.
"Me ka ce? Zaka kara aure kake nufi?"
"Kwarai kuwa yanzu haka wadda zan aura ce ta bukaci in sanar da ke halin da ake ciki."
Baki ta washe cike da farin ciki. "Yanzu kazo da maganar da zan iya tsaya in saurarenka. Na amince koma wacece ka aura ni ba damuwata ba ce Indai zaka kara aure alhamdulillah!"
Bai yi mamaki ba ganin yadda ta sauya lokaci daya. "Yawwa ga wancan ruwan juice din cikin jug, ka kaima Zainab Kar kace ni na bata ka ce a hanya ka siyo shi ka kawo mata. Ni ma farin cikin daka sakani ne ya sa na ce bari In BA matarka juice din da na hada duk da ba wani kaunarta nake yi ba"
Godiya yayi ya amshi jug din ya tafi har zai fita Mama ta kara tabbatar masa da cewa na Zainab ne ita daya.
A mota ya saka shi sai dai ji tayi zuciyarsa ta kwadaitu da ya bude ya ga me ke a ciki, lafiyayyan jus din mango NE ya ji kayan kanshi ga shi nan sai uban kanshi ya ke yi. Bai bata lokaci ba wurin dagawa sai da ya sha mai isarwa kafin ya ajiye sauran....
Saura pages Biyu free pages SU kare.
Zaku turo da kudinku ta wannan Account Number 8133562798 Opay AMINA ABUBAKAR