HADUWAR DARE

Chapter 15&16

by @meenatyandoma

*HAƊUWAR DARE*

©️Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

TALLAH TALLAH TALLAH
Idan Allah ya yarda da kai, to ka ci nasara, ko da mutane sun ƙi ka.
Idan Allah ya ƙi ka, to ka yi asara, ko da mutane duk sun soka.

#ZancenHikima


Assalamu alaikum 


🛍️ INA MASU BUƘATAR KAYA MASU KYAU DA INGANCI 🛍️

Lallai nesa ta matso kusa!
Ku gaggauta shiga Group ɗin Hajiya Aisha Mustapha,

👇👇
***

 Domin samun kayayyaki masu kyau a farashi mai sauƙi.

📞 Ko ku tuntuɓeta a wannan lambar:
( *** )

 Kayayyakin da take siyarwa sun haɗa da:

👗  kayan bacci
👙 Pant &  bra
👖 palazzo
🧒 Dilar kayan yara (mix)
👕 Dilar T-shirt
🛏️ Dilar zanin gado
👜 Dilar hand bag
🧕 Dilar Abaya
👘 Jallabiyan maza da na mata

🤝 Muna maraba da:
✔️ Masu siya ɗaya-ɗaya
✔️ Masu siya sari (wholesale)

📦 Ƙari:
Muna kawo kayan yara na 'yan kanti bisa order, kuma duk akan farashin sari.

Ku garzaya yau, ku amfana da kaya masu kyau da inganci.



Page 15&16
...Tuki ya ke amma ji ya ke gefen mararsa ta ɗan daure, haka dai ya ci gaba da tuki har ya karasa gida. Zainab da ke kwance a falo tana bacci ba karamin mamaki tayi ba jin karar motar Usman.
Shigowarsa ita ta kara tabbatar mata da shi din dai ne. "Lafiya kuwa? Ko mantuwa ka yi?" Zainab ta jefa masa tambayar. Har ya bude baki da nufin fada mata daga gidan Mama ya ke sai kuma ya fasa. "Har na fita sai kuma na ga bai kamata in barni ke daya ba tunda jikinki ba kwari ba lafiya ce dake ba. Wancan juice din ma a hanya na ganshi na siyo miki nasan kina kaunarsa. Murmushi Zainab ta yi tare da karbar jug din "wallahi kamar ka sani, tunda na tashi nake ta wawure-wawure ina neman abinda zan ci wani irin kwadayi nake ji ya na damuna matuka" ta karasa maganar tare da karbar jug din, bata dauko cup ba kanta ta daga ta fara sha. "Baby! Wannan kwadayin haka kodai-kodai" ya karasa maganar tare da daga mata gira. Murmushi ta yi "Ni dai kada ka ja mini duka wata shida da yin aure ka fara yi mini jaye-jaye?"
"Eh mana wata shida da aure ai ya kamata a ce kina nan kin kusa zama uwa" Dariya ta yi ta miƙe, jug din ta dauka ta nufi kitchen. Sai dai tun kafin ta karasa kitchen din ta fara ganin wani duhu ya na gifta mata. Tamkar mai ciki haka ta ji cikinta ya yi wani irin motsi, ba shiri ta dafe bango tana cike lips. A hankali cikin ya warware kafarta ta mika da nufin shiga kitchen din sai dai ƙatuwar bakar mage ta hango tsaye da kafafuwanta na baya tana kallonta.
Ja da baya Zainab ta yi tare da murza idanunta ko su ne suke yi mata gizo. Da gaske mage ce ta biyota a guje, bata bata lokaci ba ta zabga da gudu tana kiran sunan Usman. Kicibis suka yi daidai lokacin da ya kawo kofar falon. "Lafiya subhanallah " ya karasa maganar tare da rirriketa. Ta kasa magana sai faman haki take yi ta na nuna masa kitchen da hannu. Kamata ya yi suka shiga falon ya na kara yi mata sannu. Ruwan sanyi ya bata ta sha ajiyar zuciya ta hau saukewa a jere. "Usman mage abin da nafi tsana ita na gani a cikin kitchen ta biyoni Zata ciza" dariya Usman ya hau yi hada buga kafa.
"Baby rigima! yanZu ke fisabilillahi ina muka samu mage a kaf cikin unguwar nan babu mai kiwon mage. Kawai dai kina so kiyi mini rigima ne."
"Wallahi mage ce ni nasan abin da na gani"
"Hmm! Baby MU ajiye wannan maganar a gefe. Wata magana nake so muyi, amma pls ina fatan za ki yi mini kyakkyawar fahimta. Yanzu misali a ce Mama  ta ce in kara aure shin za ki gogamin baya In Kara auren domin kwanciyar hankali da zaman lafiyarmu?" 
Ruwan data kurɓa ne ta feso ta hanci ta baki ba shiri.
A rikice Usman ke jero mata sannu. Numfashi ta mayar idanunta cike da hawaye. "Dama da gaske abin da jikina ke fadamin zai faru? Ashe aure zaka kara innalillahi wa Inna lillahi rajiun!" Ta karasa maganar tare da rushewa da kuka. "Zainab ki fahimceni mana, ban shirya kara auren nan fa sai da na tabbatar da shi ne kaɗai mafitar data rage mana. Ba sai na fada miki ba kin riga da kin sani mahaifiyata baku jituwa, auren nan shi ne hanyar da zamu samu zaman lafiya da ke ba tare da ta sake yunkurin raba mu ba" a fusace ta mike. "Ta raba mu mana in ta rabamu sai me? Tare da kai muka zo duniyar ko kai ɗaya ne Autan maza. Usman sai ka sake ni wallahi na gaji" ta karasa maganar tana kokarin riko shi. "Kada ki bari hankalinki ya bace Mama mahaifiyata ce, babu yadda za ayi in yi mata jayayya muddun ina son haduwata da Allah ta yi kyau…”
Da karfin tsiya Zainab ta fizge hannunta ta na fada cikin karaji. "Uwarka dai kai kadai ta haifa ni bata haifeni ba, matar da ta tsaneni bata kaunata kome zanyi mata bata gani me kake so in tsaya yi kusa da danta. Ya zame maka wajibi ka sakeni inta kama ita sai ka aurota ta zo ku zauna" lafiyayyan marin da Usman ya tsinke ta da shi ba shiri ta kwala uwar kara daga nan ta sulale ƙasa. Fadar tashin hankalin da Usman ya ke ciki ba zai misaltu ba.
Iyakar kokarinsa ya yi amma ina Zainab bata farfaɗo ba. Kwasar ta yayi suka nufi asibiti. Safa da Marwa ya ke zuciyarsa cuskushe da tunani, shi kenan jikinsa ya fara basa kila lokacin mutuwarsa ne ya matso. In Zainab ta bar wannan duniyar ya sani take mata baya zai yi ko tantama babu.
Zancen zucinsa ne ya kawo karshe sakamakon nurse din da ta fara yi mana magana. “Ta farfado amma tana bukatar hutu, zuwa an jima zaka iya shiga mun dibi jininta da fitsarinta domij tabbatar da abin da muke zargi.” hannuwa ya harde cikin matsananciyar damuwa. A daya daga cikin kujerun da ke gefen dakin ya zauna. "Mama duk ke ce sanadin faruwar komai, nayi miki biyayya amma abin ya ci tura na rasa ya zanyi ga shi har rayuwar auren mu ta fara tangal-tangal. Ba shi ya shiga dakin ba sai da aka ɗauki kusan mintuna sha biyar, duk da faduwar da gabansa ke yi haka ya tura kofar dakin. Kwance take saman gadon ta kalli sama hawaye na kwaranya a fuskarta. Kujerar da ke kusa da gadonta ya zauna ya na mata magana a hankali cikin sigar rarrashi. "Ka rabu da ni kada ka sake ka ce zaka taba Ni" ta karasa maganar cikin tsawa. Kwantar da murya ya yi. "Haba Zainab yau ni kike fadar kada In tabaki Usman dinki fa ne nine fa" ya karasa maganar tare da kallonta. Shuru ta yi da alamu maganar ta fara shiga jikinta mata da miji sai Allah.
"Na yi kuskure sannan ke ma kinyi kuskure. Duk yadda mahaifiyata zata gallaza miki ki sani ba Yadda zanyi domin ita ta haifemu, bare kuma maganganun da kike fada a kanta Zainab sunyi muni da yawa ko da a ce ba ita ta haifemu ba." Sallamar da likitan ya yi ce ta katse masa maganar da ya ke yi. Hannun likitan ya miki masa murmushi kwance a fuskarsa. "Congratulations! Madam na dauke da ciki na tsawon wata daya" tsabar farin ciki Usman ji ya yi tamkar ya daka uban tsalle ya rungume likitan. Bakinsa ya kasa rufuwa. Takardar ya kika masa tare da ta sallama Sai faman godiya ya ke har likitan ya fice daga dakin.
"Baby kin gani ko? Kin ga yadda Allah ke lamarinsa mun kusa zama iyaye. Murmushi ta yi duk da ta ji dadin cikin amma bakin cikin da take ciki bata yi irin murna nan sosai ba. Ba su suka koma gida ba sai gaf da magriba bayan Usman ya yi mata uwar siyayya. Da taimakon mai gadi suka sauke kayan ya shigar mata da su ciki. Saman kujerar falo ta zauna ta na mayar da numfashi, duk da ta ji fitar Usman ya ta fi masallaci. So take ta kira Kaka ta sanar mata da batun kara auren nan amma ta kasa sakamon wata iriyar kasala data lullubeta sallar ma ta kasa ta shi ta yi kara gyara kwanciya tayi tana kallon Mbc2 ana haska wani horror film. Mai suna train to busan. Tsoro take ji matuka domin bata manta da tsorata ta da ake yi a cikin gidan ba. Remote ta dauka ta canza tashar ta mayar da ita Mbc3 tare da sakin ajiyar zuciya. Wiƙil tamkar almara ba tare da ta taɓa remote ba aka canza tashar aka mayar da ita Mbc2. Zabura tayi a rikice ta sake mayar da ita Mbc3 sai dai kafin gani tayi an mayar da ita Mbc2. A yanzu kam ta firgita ba kadan ba. Da karfin gaske ta ji an banko kofar dakin tamkar ana shirin karyata. Karfin gwuiwa ta samu ta mike ta kashe kallon, kafin ta zauna ji tayi an sake kunna wa. A yanzu kam hankalinta ya gama tashi ta san wannan lamari ba na lafiya bane. Mikewar da ta yi lokaci guda wutar dakin ta fara fafarniya. Zuwa can kuma ta dauke ɗif! Wasu irin surutai da hayaniya ta ji a kusa da ita tamkar ana fada ko kuma rigima. Damko hannunta aka yi da karfi sai da ta ji hannun ya yi wata kara. Falau wutar dakin ta dawo. Mace ce sanye da bakaken kaya ta rufe fuskarta da bakin mayafi baka iya tantance yadda fuskarta take. "Ki bamu abin da ke cikinki, shi muka zo amsa ki ba mu ko kuma ki mutu!"
Aka karasa maganar cikin rikitacciyar murya, lokaci daya falon ya dauki amsa kuwwa...


Saura Page daya free fage ya kare. Yau kadai mun mayar da shi 400 ga mutane goman farko. Ku turo kudinku ta wannan Account din. 8133562798 Opay AMINA ABUBAKAR