HADUWAR DARE

Chapter 17&18

by @meenatyandoma

*HAƊUWAR DARE*

©️Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

TALLAH TALLAH TALLAH
Idan Allah ya yarda da kai, to ka ci nasara, ko da mutane sun ƙi ka.
Idan Allah ya ƙi ka, to ka yi asara, ko da mutane duk sun soka.

#ZancenHikima


Assalamu alaikum 


🛍️ INA MASU BUƘATAR KAYA MASU KYAU DA INGANCI 🛍️

Lallai nesa ta matso kusa!
Ku gaggauta shiga Group ɗin Hajiya Aisha Mustapha,

👇👇
***

 Domin samun kayayyaki masu kyau a farashi mai sauƙi.

📞 Ko ku tuntuɓeta a wannan lambar:
( *** )

 Kayayyakin da take siyarwa sun haɗa da:

👗  kayan bacci
👙 Pant &  bra
👖 palazzo
🧒 Dilar kayan yara (mix)
👕 Dilar T-shirt
🛏️ Dilar zanin gado
👜 Dilar hand bag
🧕 Dilar Abaya
👘 Jallabiyan maza da na mata

🤝 Muna maraba da:
✔️ Masu siya ɗaya-ɗaya
✔️ Masu siya sari (wholesale)

📦 Ƙari:
Muna kawo kayan yara na 'yan kanti bisa order, kuma duk akan farashin sari.

Ku garzaya yau, ku amfana da kaya masu kyau da inganci.

Page 17&18
...Wata iriyar katsawa cikinta ya yi tamkar zai fito a lokacin. Daga nan sai dai bude ido tayi ta ga Usman a kanta ya na yi mata sannu. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin jikinta ya yi mata matukar nauyi . "Sannu kinji, ya kamata in samo miki 'yar aiki zama ke daya a cikin gidan nan ba zai yiwu ba" ya karasa maganar ya na mai gyara mata kwanciya. Ita kam shuru tayi ta na mayar da numfashi a hankali. "Tashi ki ci wani abu mana" girgiza kai tayi tana mai kara rufe idanunta. "Noo Zainab! A yanzu ba ki da hujjar da zaki ce ba zaki ci abinci ba. Ko kin manta karamin ciki gareki? Ki daure ko yogurt be kisha" ya karasa maganar ya na mai mikewa. Da kyar ya samu tasha. Sallah ma ranar daga zaune ta yi ta domin data mike sai jiri ya kwasheta. Daren ranar ba ita ta runtsa ba, da ta kulle ido zata fara jin tafiyar Dawaki a saman rufin dakin da suke kwance. Zuwa can kuma wata irin hayaniya ta rika jiyowa kamar masu cin kasuwa. Kukan jarirai shi ya biyo baya wanda tilas ya sakata danne kanta da fulo. Yadda ta ga safiya haka ta ga dare. Bata yarda Usman ya fita sallar asuba ba a gida ya yi ta. Gari na wayewa ta faki idon Usman ta shiga daki. Kai tsaye number Kaka ta Kira ta fashe mata da kuka tare da rattaba mata abinda ya faru. "Hadi kuna ina?" Kaka dake zaune a falo ta shiga kwala masu kira. Sanin hali ya fi sanin kam, baccin safe da suka koma katse shi suka yi domin sun san wannan kiran ba na lafiya bane. A falo suka isketa. Durkusawa suka yi har kasa suna gaidata. "Ku mike ba lafiya a gidan Jikalliya? " 
"Subhanallahi! Me ya faru? Ko jikin nata ne ya tashi. " Alhaji hadi ya fada.
"To in ma jikinta ne ai da sauki za a iya kai ta asibiti  a bata magani. Yarinya dai ta na can ana ci gaba da tsorata ta ga karamin ciki ga Usman ya bullo da maganar aure. Ka ga kuwa ai babu lafiya" 
"Hajiya don girman Allah ki bar yarinyar nan ta yi zaman aure a gidanta, karin aure a ba kanta farau ba"
"Rufe mini Baki kinji" Ta dakawa Umma tsawa. "Ke dama har wani abin arziki kika iya, yarinya kamar ba ke kika haifeta ba. Wato kara aure ba kanta farau ba ko? To ke ya aka yi Hadi bai karo miki wata ba ko mallake mini ɗa kika yi ne?"
"Haba Hajiya! Don Allah ki daina wannan maganar yanzu me kike so a yi?" 
"To tunda ka zo da magana ta hankali kai zai iya saurarenka muyi magana. Abin da nake so yanzu da munyi kalaci ka daukeni ka kaini gidan Jikalliya ai na sani hada kadaici ke haddasa mata gane ganen nan"
"To in Shaa Allah za a yi Hajiya"
Ganin Umma za ta yi wata magana alama ya yi mata da ido suka koma daki. Ajiyar zuciya ta sauke "amma kana ganin ya dace ta je gidan Zainab ta zauna?"
"Abin da nake so ki fahimta ko taje ba zata iya zama ba, sannan yin jayayya da Hajiya babu riba kiji fa abinda ta fada miki dazu. Kiyi hakuri kawai a kaita ina mai tabbatar miki da kafafunta zata dawo. Sannan Hajiya da kike gani da hankalinta ba zata tayar da hankalin Usman ba akan zai kara aure kawai na san matsalar Zainab ita ce ke damunta"
Shuru Umma ta yi ilahirin jikinta yayi sanyi da lamarin Hajiya. 
Bayan sun gama kalaci ko hutawa bata yi ba bare ta jira abincin ya fada ta ce ma shi ya mike su tafi. 

Bai yi mata musu ba haka suka fita ba zame da ita ko ina ba sai gidan Zainab. Bai yarda ya shiga ba ya na kaita ya juya. Tun daga tsakar gidan take tafka uwar sallama tamkar wadda ta shigo gidan kurame.
Zainab da Ke zaune suna kalaci da Usman Muryar kaka ta sakata mikewa da gudu suka fita. Rungume ta tayi suna dariya. Usman da ke falo ji ya yi gabansa ya fadi. Har ga Allah bai so zuwan Kaka a gidan nan ba, saboda ya san Zainab ta Jima da Sanar da ita halin da ake ciki.
Murmushin dole ya kirkiro ya na gaida Kaka. Ba yabo ba fallasa haka ta amsa tare da jan jikanyarta suka shige daki.
"Jikalliya ya naga jikinki duk ya yi wani iri ko baki lafiya ne?"
"Ke ma kin sani gidan nan ya zame mini rana zafi inuwa ƙuna. Kullum cikin tashin hankali da fargabata abin da zai faru nake"
"Sha kuruminki jikalle. Ai gani na zo in ta kama ma har wurin mai magani sai In Kai ki . Yo ni in banda mahaifinki da ke tankwarar dani ai da tuni mun ziyarci mai magani domin matsalar ki Jinnu ce Bama sai an fada ba."
"Kaka kada ki biye masu ni na sani kin fisu sona" ta karasa maganar ta na mai kwanciya a cinyar kaka. Da sallamarta ya shigo dakin. "Zainab zan fita kasuwa, an jima kadan mai aikin da na daukar miki zata zo sai na dawo. " Ba ta ce masa uffan ba har ya fice. Usman ya ji zafi sosai ganin abin da Zainab ta yi masa. Shi yasa bai so Kaka ta zo gidan nan ba. "Kaka kin gan shi ko? Ko kunya babu wai Usman ne zai kawo mini  kishiya saboda Mamansa ta matsa"
"Ke kam kiyi hakuri! Ai duk abinta ba zata iya fitar da ke daga cikin gidan nan ba. Kuma Usman mu shaida ne akan irin soyayyar da yake yi miki kada ki nuna masa hankalinki ya tashi ko kuma ki ce zaki yi tashin hankali. Shi namiji a wannan gaɓar in dai kasan ya na sonka uzuri zaka yi masa"
Ya mutsa fuskar Zainab ta yi. "Haka ne ko kaka?"
"Kwarai kuwa Jikalliya. Ai shi ya sa na zo gidan nan. Yanzu dai mu je ki zubo Mani sauran abin da kuka yi kalaci kinsan sha'anin mota da ubanki ya daukoni duk ya girgije ni a hanya, abin da na ci ya gudu ji nake cikin nan nawa kamar anyi yakin duniya a cikina."
Dariya Zainab ta babbake da ita suka fito falo. Kaka na cikin cin abinci suka ji sallamar mace. "Kallo ɗaya suka yi mata suka gane ita ce yar aikin da Usman ya ce zai samo. Cikin ladabi da biyayya ta gaida su tare da sanar masu ita ce mai aikin da aka samo tazo ne daga gidansu abokin Usman. Asali can take aiki sakamakon kiran abokin na shi da yayi suna neman mai aiki sai mahaifiyar abokin nasa ta ce a kai masu ita su zasu samu wata. "Yarinya ya sunanki?" Kaka ta fada.
"Sunana Hinde"
"Ma sha Allah Hinde. Kiyi abin da ya kawo ki banda shiga lamarin da ba a saka ki ba. Ki tsaya matsayin ki na mai aiki kinji"
Kaka ta karasa maganar.
"To Hajiya In Shaa Allah yadda kika ce haka za a yi. Da me zan fara?" Dakin da zata zauna Zainab ta kaita. Sannan suka fito ta sanar da ita abin da zata dafa masu da rana, sauƙin kan yarinyar shi ya burge Zainab. Komawa falo ta yi suka ci gaba da hirarsu da Kaka. Bayan sun ci abincin rana Kaka zafi ta ce ta na ji zata shiga ta watsa ruwa. Bayan ta shiga toilet dabi'arta CE sai ta tsaya ta yi ta dammaci kafin ta fara wankan. Kofar ta ɗan tura saboda bata yarda idan za tayi wanka ta kulle kofa ba. Garam ta ji an kulle kofar da karfin tsiya! Fasa cire kaya ta yi ta tsaya sake da baki ta na kallon wannan ikon Allah! "Waye ya kulle ni, ke Jikalliya ki budeni mana" ta karasa maganar da karfi. Juyowar da zatayi suka yi ido hudu da Hinde dake tsaye ta kurwa da kallo. Dafe kirji Kaka ta yi a rikice "na shiga uku! Ke yarinya wace uwar kika shigo yi cikin kewayen nan bayan kinsan ina ciki?" Zare ido Hinde ta ci gaba da yi. Ta tare da fara magana cikin rikitacciyar murya. "Zuwa nayi In wanke ki tas! KO kin manta da aiki aka daukeni a cikin gidan nan?"
"Yau Ni na shiga uku! Cewa za ki yi mahaukaciya ce aka kawo mana matsayin mai aiki. Ni ba yarinya ba, sannan ba mai wannan jego ba ni zaki wanke" 
"Eh ke din, maza ki durkusa"
Ta daka mata uwar tsawar da ta saka Kaka zabura tayi baya. Mahaukaciyar dariya ta babbake da ita, ba shiri Kaka tayi kasa da rarrafe ta samu ta kai ga kofa tana kokarin budewa. Kafarta aka fizgo da karfin tsiya...


Saura Page daya free page ya kare. Zaku biya 400 a maimakon 500 daga yau Bononzar zata kare. Ku turo ta wannan Account din 8133562798 Opay AMINA ABUBAKAR. Ko katin MTN na 400 ta wannan Number ***