Chapter 19&20
*HAƊUWAR DARE*
©️Meenat A. 'Yandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
TALLAH TALLAH TALLAH
Idan Allah ya yarda da kai, to ka ci nasara, ko da mutane sun ƙi ka.
Idan Allah ya ƙi ka, to ka yi asara, ko da mutane duk sun soka.
#ZancenHikima
Assalamu alaikum
🛍️ INA MASU BUƘATAR KAYA MASU KYAU DA INGANCI 🛍️
Lallai nesa ta matso kusa!
Ku gaggauta shiga Group ɗin Hajiya Aisha Mustapha,
👇👇
***
Domin samun kayayyaki masu kyau a farashi mai sauƙi.
📞 Ko ku tuntuɓeta a wannan lambar:
( *** )
Kayayyakin da take siyarwa sun haɗa da:
👗 kayan bacci
👙 Pant & bra
👖 palazzo
🧒 Dilar kayan yara (mix)
👕 Dilar T-shirt
🛏️ Dilar zanin gado
👜 Dilar hand bag
🧕 Dilar Abaya
👘 Jallabiyan maza da na mata
🤝 Muna maraba da:
✔️ Masu siya ɗaya-ɗaya
✔️ Masu siya sari (wholesale)
📦 Ƙari:
Muna kawo kayan yara na 'yan kanti bisa order, kuma duk akan farashin sari.
Ku garzaya yau, ku amfana da kaya masu kyau da inganci.
Page 19&20
...Ta na ji ta na gani haka a ka fizgi kafarta aka hada da bango ba yadda ta iya. Buguwar da bayanta ya yi ita ta sakata fashewa da kuka ta na ihun neman taimako.
Zainab data biyo ta dakin Kaka ta ga ko ta gama wankan ihun ta data jiyo shi ya sakata shiga dakin da gudu.
"Subhanallah! Kaka me ke faruwa?" Jin bata daina ihun ba ya saka ta tura kofar da karfi. Kwance ta na ta faman ihu ita daya. Cikin hanzarin ta matsa kusa da ita ta na mai tayar da ita. Ji da kaka ta yi an rikota wani sabon ihun ta ci gaba da kwakwa "Jikalliya ki zo ki taimake ni, yau aiki ya biyo ta kaina ashe abin da nake shirin fuskanta kenan hadi ko gardama bai yi mini ba ya kwaso ni ya kawo gidan nan."
"Bude idonki ki ganni nice nan Kaka. " Zainab ta fada. Jin Muryar Jikalliya da tayi ya sakata bude ido ta na fizgar dogon numfashi.
"Mu je daki kaka kamar baki tare da nutsuwar ki." Ganin sun fito daki kin zama kaka ta yi bisa dole falo suka koma. Ruwa mai sanyi ta bata ta sha sai da ta samu nutsuwa take tambayarta yadda aka yi.
"Ke dai bari! Wannan mai aikin taki ba mutuniyar arziki ba ce. Ke Ni na ma fi tunanin mayya ce. Ina cikin kewaye sai ganinta na yi tsulum kamar aljana" kaf abin da faru ta kwashe ta fada mata. Ba karamin mamaki Zainab ta yi ba jin wai Hinde ce ta tsorata kaka. Hinden da suna cikin falon nan da ita ta na goge shi. "Kuma kaka ba idonki bane? Hinde fa ta na cikin falon nan yanzu ta gama goge-goge. "
"Ya za ki ce haka, ai shi munafuki mai fuska biyu ba a taba gane shirinsa kira mini Hinden"
"Hinde! Hinde!!" Zainab ta Shiga kwala mata kira. Da rawar jiki ta karaso tare da zubewa a gabansu. ganin ta da Kaka ta yi sai da gabanta ya yanke ya fadi, dauriya kawai ta ci gaba da yi.
"Me ya saka kika shiga dakin Kaka bayan kinsa ta na cikin kewayen ke ma kika shiga?" Zainab ta jefa mata tambayar. Dafe kirji Hinde ta yi cikin firgici. "Hajiya Ni kuma? Bayan ina nan falon tare da ke lokacin da ta shiga ta yi wanka?"
"Karya kike munafuka! Ki fito ki fadi gaskiya ni da kika kusa kashewa a cikin kewayen gidan nan?" Cewar Kaka
"Na rantse miki da Allah ba ni ba ce, Hajiya ki yarda da ni sai dai idan wata mai kama da Ni ce kika gani." Nan hinde ta hau rantsuwa har ta na shirin kuka. "Ta shi ki tafi dakinki" Zainab ta fada. Bayan ta tafi kallon Kaka ta yi.
"Ki yarda da yarinyar nan! Ba ita ba ce. Abin da ake mini ne ke ma da kika shigo gidan ya fara shafarki."
"Aiko ya wajaba a garemu mu je can cikin wani kauye da na sani domin neman magani. Har yanzu a tsorace nake gaskiya jikalliya kinyi matukar kokari wallahi"
"Hmm! Kaka Kenan Ni kadai nasan aZabtuwar da nake yi a cikin gidan nan. Ko me kenan gobe ko jibi ya kamata muke wurin can, ko da wasa bance ki bari mahaifanki su san da maganar nan ba. Saboda tsaf za su yi ruwa su yi tsaki su hana mu zuwa"
"Ni kaka wa ya aike ni? Ai bakina Kanin kafata"
"Yawwa yarinyar arziki haka ya kamata mu yi abin mu a sirrance"
Sakin maganar suka yi suka kama wata...
Usman bayan sun tashi a kasuwa so ya ke ya je gidansu Zulfaida sai dai ya tuna da gargadi da ta yi masa a kan ba a kai mata ziyara ita da duk wani nata sai da dare.
Gidan abokinsa faruq ya nufa kai tsaye, ya kuma yi sa a ya na gida.
Maganar da ya zo masa da ita ba karamin kada Faruq ta yi ba. Duka yaushe Usman ya yi aure matarsa ko haihuwa bata yi ba amma har ya ke maganar kara aure.
"Anya abokina ka dauko hanya mai bullewa kuwa?"
"Faruk ya kake so in yi? Muddun ina so in ci gaba da rayuwa da Zainab ya zame mini tilas in karo auren nan. Sannan ka sani na fada maka juna biyu gareta, ta ya zan bari In rabu da ita babban tashin hankali ne a ce ba gidana aka haifa mini jinina ba. Sannan nan gaba rayuwar yaron zata iya lalacewa"
Kasancewar Bama tare "Kuma haka ne kana da gaskiya, saboda babu wanda ke so a haifar masa jininsa a rariya. Amma fa Ni yarinyar da ka ce mini zaka aura ita ce kwata-kwata bata kwanta mini a zuciya ba. Yarinya kamar aljana ba a ganinta sai da dare kai Usman ka yi dogon nazari kada ka jefa kanka ga halaka."
"ka daina wannan tunanin ka taba ganin mutum da aljanu sunyi soyayya bare har su kai ga maganar aure?"
"Sosai ma kuwa Usman. Nawa aka yi ka ji aljani ya auri wata ko kuma ya auri wani. Kai dai ka dage da addu'a sannan kada kayi saurin kai kudin aure sai ka kara bincike a kan yarinyar nan. Ni fa don kada ka ce na cika kunshe abu da na fada maka wata gaskiya. "
"Hmm! Faruk Kenan! Na yi maka farin sani magana idan ta zo bakinka bata boyuwa. Yi maza ka fadi ta cikinka."
Dariya Faruk ya yi. "Zulfaida fa, kana da masaniyar Zulfaida sunan aljana ne, aljanar ma muguwa mai fuska biyu wadda ke da kyakkyawar fuska da sura ta daukar hankalin maza , amma zuciyarta cike take da mugunta da keta"
"ka ga Faruk sai an jima, na gaji da jin wannan tatsuniya taka ga shi har magriba ta matso. Za ka je gidansu Zulfaida ko kuma in tafi"
"Wa ni? Gaskiya ba zan je ba domin na fada maka ban yarda da ita ba, kai ma din ka fara bani tsoro"
Dariya suka yi a tare suka fice bayan sun taso masallaci Usman ya nufi gidansu Zulfaida. A wannan karon ma tsaye ya tarar da ita kofar gida kamar mai zaman jiransa.
Bayan sun gaisa ya ke sanar da ita gobe za a turo gidansu ta sanar da mahaifiyarta.
"Na sani. Kada su zo da safe, su zo da magriba kamar yadda kake zuwa din nan. "
Bai yi mamaki ba domin zuwa yanzu ya fara sabawa da halinta. Ya na baro wurinta bai zame ko ina ba sai gidan Mama. Bai boye mata komai ba ya sanar da ita ba a zuwa gidansu sai da dare. Saboda rufewar da idanuwan Mama suka yi, ta kasa fahimtar maganar zuwa da dare. Kudi masu yawa ta amsa a hannun Usman suka yi bankwana ya nufi gida.
Kasancewar mahaifin Usman ya jima da rasuwa, Kannen mahaifinsa biyu sai na mahaifiyarsa suka kama hanyar gidansu Zulfaida da magriba. Su dai ba karamin mamaki suka yi ba, neman aure da ake zuwa da safe ko kuma da marece su nasu shi ne suka tafi da dare. Burki da Usman ya taka a kofar gidan shi ya tabbatar masu da sun iso. Ciki suka shiga Usman ya na a mota. Bai san me ya saka ba shi daya cikin motar amma ji ya ke kamar akwai wani ganinsa ne dai baya iya yi. Ba zato ba tsammani sai ganin mutum ya yi tsaye a gaban motarsa. Har cikin zuciyarsa sai da ya tsorata.
Daka-dakan idanun mutumin su suka kara tsoratar da Usman. Alama mutumin ya yi masa da ya sauke glass din motar.
Duk da a tsorace ya ke bai bata lokaci ba ya sauke glass din. "Kai ne Usman?" Mutumin ya jefa masa tambayar fuska a matukar daure.
"Lafiya bawan Allah me ya faru?"
"Ka adana tambayoyi ka kayi abin da ke gabanka. Gargadi ko kuma in ce kashedi na zo in yi maka,Zulfaida da kake kokarin aure ka janye hannunka ko kuma ko me ya biyo baya ka kuka da kanka. Auren nan da kake shirin yi shi ne zai janyo maka duk wata masifa da ɓacin rai da bakayi tsammani ba"
Jin wadannan maganganu ba karamin tayar da hankalin Usman suka yi ba. Har ya bude baki zai yi magana ya ji Muryar Kanin mahaifinsa a bayansa. "To kai Usmanu an yanka ta tashi. Mun zo da niyyar neman aure yanzu haka maganar nan da nake maka sun bukaci mu biya sadaki a daura aure, mun biya Zulfaida dai ta zama matarka ka ga yadda Allah ke lamarinsa ko?"
Wata irin kyarma ce ta kubcewa Usman. Juyawar da zai yi ya nemi mutumin da ke masa gargadi ya rasa, wani gumi ya shiga wanke masa jiki...
...Zainab da Ke zaune a falo ita da Kaka lokaci daya su ka ji an kwala uwar guda a rikice suka kalli juna ita da Kaka...
WACECE ZULFAIDA?
ME TA SHIGO YI A CIKIN RAYUWAR SU USMAN?
INA LABARIN MAGANIN DA MAMA TA BADA A KAWO MA ZAINAB USMAN YA SHA?
YA YA ZAMAN ZULFAIDA DA USMAM ZAI KASANCE?
WAYE WANDA YA YI MA USMAN GARGADI A CIKIN MOTA?
ME YE MAFARIN MATSALAR USMAN DA ZAINAB?
Wanda suka biya kudi ne kadai za su samu cikakkun amsoshin nan.
Ku turo 500 ta wannan Account Number 8133562798 Opay AMINA ABUBAKAR
KO kuma a dauki hoton katin Mtn na 500 a turomin ta wannan Number ***
Meenat A. 'Yandoma
***