BARRISTER SUHAIL
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki,
Mai iko bisa komai, buwayi gagari misali.
Kamar yadda Ya bani ikon farawa lafiya,
Ina roƙonSa Ya bani ikon gamawa lafiya. 🤍
🅿️-----1
Sannu a hankali ya soma buɗe idanunsa daga dogon baccin da ya ɗauke shi
Sakamakon daren jiya da ya kwana yana aiki
Idanunsa suka sauka kan agogon dake manne a bango
ƙarfe tara saura da sauri ya miƙe daga kan gado ya nufi bathroom
Bai wuce mintuna goma ba
ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa
Ruwan da ke diga daga sumar kansa yana sauka a kan faffadan ƙirjinsa.
Tsayawa yayi gaban mirror
yana goge gashin kansa a hankali
Kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar
Suhail ba ƙaramin haɗaɗɗen saurayi bane dogo ne fari sol yana da doguwar fuska idanun sa manya fararare tas hancin nan a mike yana dan karamin baki mai dauke da pink lips mai kama dana jarirai.
cream dinsa ya dauko ya fara shafawa akan farar fatar sa ba bata lokaci ya gama ya nufi closet dinsa ya fito da wata bakar suit ya saka kayan sun yi matukar dacewa da kalar jikin sa exclusive perfumes ya dauko ya feshe jikin sa dasu ya dauki jakar laptop din sa ya fito zuwa compound din gidan part din da yafi ko wanne girma a gidan ya dosa knocking yayi mai aiki ta buɗe masa cike da girmamawa ta gaishe da suhail ba tare da ya amsa mata ba ya shige ciki uptsair ya nufa daidai ɗakin mahaifiyar murda kofar yayi ya shiga wata dattijuwar mata ce zaune bakin gado wanda a kallah bazata wuce shekaru hamshin da haihuwa ba kallo daya zakayi mata ka tabbatar da mahaifiyarsa ce sanye take da wani haɗaɗɗen lace brown colour anyi mata ɗinkin doguwar riga an cika shi da stone sai kyalli yake hannun nan an cika sa da gwala-gwalai zaune take bakin gado tana dan na wayar ta kirar iphone 17 pro max cike da girmamawa suhail ya gaishe ta ta amsa ba yaɓo ba fallasa tashi yayi zai fita ta ce"Akwai breakfast a dinning"
"i'm already late,zan samu wani naci a office"
"fine" kawai ta ce
ya juya ya fita parking space ya nufa ya shiga motar sa kirar mercedes benz CLE black colour,mai gadi ya buɗe masa gate din ya fita cike da natsuwa yake tafiya a haƙa har ya kara bakin babbar koton Shari'ah court dake garin Kaduna parking motar sa yayi ya nufi office din sa mukulli ya amsa a hannu seccterai ya buɗe ya shiga Wani sanyayyen Kamshi ya fito daga ciki office din a share yake tas an ajiye komi inda ya kamata zama yayi kan kujera ya fara duba files din dake ajiye kenan Secretary din sa nadia ta shigo kallon da yayi mata sai da ya sa hantar cikin ta ƙaɗa wa na daya daga cikin Abinda suhail ya tsana daya shigo office a fara damun sa a fusa ce ya ce"What again nadia"
murya na rawa ta ce"yallabai dama wasu mutane suka zo tun dazu suke san Ganin"
dan tunani yayi kadan ya ce"okay let them in"
har ta juya zata fita ya ce"i need coffe"
risinawa tayi ta ce"okay sir"
tana fita ba dadewa ta turo mutanen mata da miji ne wanda duk sun manyan ta iya kayan jikin su ka kallah zai tabbatar basa cikin wadata alamu yayi musu da kujeru biyu dake gaban teberin ya ce"Ku zauna"
Bayan sun zauna Suhail ya kare masu kallo bayan sun gaishe ya ce"baba mi ke tafe daku"
kasa yayi da murya ya ce"Yallabai dama munzo akan maganar ɗiyar mu,da akayi fyade wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar ta yau kwana Goma kenan shine mukaji labarin kana da adalci akan aikin ka kuma an tabbatar mana da zaka ƙwato mana hakkin mu shine mukazo"
jinjina kai suhail yayi cike da tausayin tsohon ya ce"Baba i'm sorry for the loss,Allah ya bada haƙuri rashi Amman kafin mu fara bincike shin kun san wanda ya aika mata hakan?"
sai lokacin Mamar tayi magana ta ce"yallabai ai ba wani boƴaƴƴen mutun bane Tahir ne dan gidan Alhaji Sani Dan kasuwa" kuka yaci karfin ta suhail cike da tausayi Suhail ya ce"Mama kiyi haƙuri kimin bayani"
share hawayen tayi ta ce"Bilkisu tana aiki a gidan Alhaji Sani wanda baso ɗaya tana faɗamin tahir nazo mata da maganganun Banza,har ta ce ita kawai zata bar Masu gidan su na bata haƙuri, Wannan aikin da take shine rufin Asirin mu dashi muke ci muke sha hatta magani na duk a ciki muke siya tunda mahaifinta bashi da karfi wata rana ina zaune aka shigo da bilkisu a wani yanayi wanda bazan taɓa mantawa dashi ba jikin ta duk jini,na tambayi tsohuwar data kawo miya sameta ta ce"Tahir ne yayi mata fyade,itama gidan take aiki daga yau ma zata bar masu gidan nan ta bani duk Labarin abinda ya faru da yadda tahir yasa a fito da bilkisu kofar gida wanda ganin haka yasa ta dauko ta kawo ta gida"
Ban taba shiga tashin hankali irin na ranar nan ba ga Bilkisu kwance a gaba na cikin jini ko magana bata yi da taimakon makwabiciyar mu muka kai ta asibiti, suma suka ƙi amsar ta wai sai munzo da dansanda haka mahaifin yaje police station duk inda yaje yayi masu bayanin Akan dan gidan Alhaji sani dan kasuwa yayi wa diyar da fyade sai suce su ba Ruwan su a haka ya gama zagaye-Zagayen ya dawo ya same su a asibiti a yashe yayi mana bayanin duk abinda ke faru makwabciyar mu tace kawai muyi haƙuri mu tafi gida muyi na Hausa haka muka dawo a samo sassake a rinƙa dawa ana ba Bilkisu kusan kwana biyu ba magana sai kuka kawai cikon kwana na ukku Bilkisu ta ce ga garin ku nan kuka sossai yaci karfin ta sossai Suhail ya tausaya mata tashi yayi ya dauko ruwa a fridge da cup ya bude ya zuba ya miƙa mata amsa tayi ta sha har lokacin kuka take suhail yayi gyaran murya Ya ce"Mama duk naji bayanin ku kuma nayi maku alƙawarin sai na ƙwato maku hakkin Zalincin da akayi maku"
Baba ya ce"Nagode sossai yallabai,Allah yayi maka albarka ya sa ka gama da duniya lafiya"
IDAN HAR BAKUYI LIKE DA COMMENT BA ZAN DAKATAR DA TURO WA GASKIYA COMMENT DINKU KADAI ZAI BANI ƘWARIN CIGABA DA MAKU POSTING
TAKU HAR KULLIN
OFFICIAL KHADEEY