26
KUNDINA
26
FATIMA;
Har na isa ƙofar shiga sashen Baba ban daina saƙe-saƙe ba..
Da Hajiya Babba na same shi, suna hira sama-sama.
A raɓe na tsugunna na gaishesu, Hajiya ta amsa ciki-ciki tana ɗauke kai..
Baba cikin fara'a ya amsamin yana tambayata yaya karatu? bayan na gama amsa masa na miƙe nayi musu sai da safe.
Ina zuwa Sashena Salim ya kirani, mun jima muna waya har aka kira sallar Isha'i sannan muka yi sallama..
Ba mu sake yin waya ba, sai da zan kwanta, na kirashi muka ɗan hira sannan nayi barci..
A haka watanni biyu suka shuɗe.. ƴan uwan Salim suka zo aka saka ranar aurenmu watanni biyar masu zuwa...
A cikin watanni biyun da suka shuɗe Salim ya ɗan murje ramarsa ta ragu ba kamar daa ba.. shi yake kaini makaranta ya dawo da ni gida kullum..
Daga Mama har Baba a ɓoye suke shirye-shiryensu, gudun tsegumi daga kowa..
A ɓangare Salim babu abinda ya sauya a tsakaninsa da Hajiyarsa, sai abinda ya yi gaba..
Magana ma sai ta dama take yi masa, ranar dai yayi Sa'a tace ya kaita, wajen taron ƴan makarantarsu, Salim bai kawo komai a ransa ba, bai kuma tambayeta taron wani makaranta ba ne, ya shirya suka fita...
A ɓangaren Hajiya Babba tunda taji za'ayi taron makarantarsu na sakandare jikinta yake rawar Allah Ya sa idan ta je ta haɗu da Turai.
Ba ta taɓa zuwa ba, amma saboda burin ta haɗu da Mahaifiyar Salim yasa ta shirya Driver ya kaita, ko Baba bata gayawa ainihin inda zata je ba, ta dai ce masa zata je biki...
Ta kuwa yi sa'a Driver na ajjiyeta, motar su Salim ta danno kai..
Hango Salim ta farin gilashin motarsa, yasa ta sauke ajiyar zuciya, tsabar masifar da ta ɗorawa zuciyarta, jikinta har tsuma yake yi..
Ƙara matsawa tayi daidai inda taga Salim ya na ƙoƙarin faka motarsa..
Ido ta zubawa motar har sai da Hajiya Turai ta sauko.
Ta kuwa yi sa'a kallon farko Hajiya Turai ta gane ta..
Da wani irin farin ciki Hajiya Turai ta ce;
"Wa nake gani haka kamar Sara"
Hajiya Babba manyan-manyan iduwanta ta juya, ta kwashe da dariya farin ciki, da alama ta tuna baya..
Rungume juna suka yi, cikin so da ƙaunar abotar da ya wanzu tsakaninsu shekarun baya..
Salim ganin komai yake yi kamar a mafarki, tsabar tashin hankali yawun bakinsa har kafewa ya yi..
Cikin kame-kame ya ce;
"Hajiya ina wuni"
A tare Hajiya Babba da Hajiyarsa suka waiwayo suna kallonshi.
Cikin mamaki Hajiyarsa ta ce;
"Ka santa ne"
saboda yanayin gaisuwar tasa ya yi mata kama da wanda yasanta a wani waje..
Maimakon Hajiya Babba ta amsa, sai ta ɓata fuska ta ce;
"Ohhh ni Salim ya ka ji da haƙuri halin Fatima, nasan zuwa yanzu labari yaje maka, kayi haƙuri halin mahaifiyarta ta gado, Allah Ya yi maka zaɓi mafi alkhairi ɗan albarka"
Salim baki ya saki yana kallonta, tunda yake bai taɓa ganin mace mai muguwar zuciyarta ba, ba zama ta haƙura ta bari su nutsu ba, tun anan zata fara kwancewa Fatimarsa zani?
"Ohh Allah" ya faɗa a sarari yana runtse idonsa..
A daidai wannan gaɓar Hajiya Turai ta ƙanƙace idanuwanta cike da masifa tana kallon Hajiya Babba ta ce;
"Sara me naji kin ce? Dama ƴar kishiyarki Salim yake so ya kawomin gida, kuma ya sani amma bai gayamin ba, lallai Salim ka mayar da ni uwar banza"
Ta ƙarasa faɗa tana Kallon Salim da har lokacin idonsa ya ke a rintse..
A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi jaa ya ce;
"Hajiya ni zan koma, idan ku ka gama ki kirani"
"A wacce motar zaka koma Salim? Ba dai a motar gidana ba, ba ni makullina"
Hajiya Turai ta faɗa a gadarance tana miƙamai fararen yatsunta..
Salim ƙara runtse idonsa ya yi, bai taɓa sanin haka halin Hajiyarsa yake ba.
Kamar ya ce mata ai nima motar mahaifina ce, sai kuma ya tuna matsayinta a gareshi ya fi gaban nan..
Yatsunsa suna karkawa ya miƙa mata ya juya a zuciye..
Da ya yi nisa, kasa tafiya yayi ya tsaya a hanya ya fashe da kuka...✍🏻
Kashemin gwiwa kuke yi, ba kwayin like🥺