TALES OF THE WAZEERIS

london

by @surayyahms

20...🦋🦋🦋

SURAYYAHMS

Tales of the wazeeris

washegari da safe haka camp din gaba daya ya kaure da wani irin tashin hankali dan ziyada ce data farka ta fara noticing cewa babu duka kayan ushna a dakin ko tsayawa wanka batay ba taje camp clinic nan ma akace mata ushna batazo ba, ta kira layin mr abdl yafi sau talatin amma baya shiga, nan take ta fito takai magana har wajensu matrons aka fara searching gashi wayarta a kashe.

wajajen karfe tara da rabi hanklin kowa yafara tashi can sai ga mr abdul din ya karaso dan dolensa ya shafa concealer a fuskrsa ya rufe bruise marks din kona masa fuska datay da tafassashen tea da make up snn yabi ya saka dark shades dan kar agane hkn sosai. ganin yadda aka taru duka awaje guda ana cece kuce sai yaji gabansa ya dan faɗi

acikin sauri ya taho wajen musmn dayaga duk an juyo yuuu anyo kansa...ganin idon xiyada da hawaye bai barta tay magana ba yace everyone calm down please ushna is fine.

nan take hayaniyar wajen ta dan tsaya kadan, ziyada ta matso gabansa cikin tashin hankali tace thank God but sir where is she, how is her health? naga gabaki daya kayanta baya daki

ya sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya gaji sosai sannan yace “after what happened yestade i just gave her permission to go home sabida she was not emotionally okay kuma ban ga dalilin da zaisa a tilasta mata cigaba da camp ba.

matrons da wasu students suka gyada kai ahankli ganin maganar tashi tabada ma’ana wani instructor yace “thats understandable sir. ziyada kuwa duk da haka sai da taji kamr hankalinta bai gama kwanciya ba dan tasan dai ushna bazata taɓa tafiya gida cikn dare aggagauce batare da ta mata sallama ba

but she was relieved atleast tasan ushna tana lafiya daga gefe taji mr abdul yanakara fhmtr da kowa cewa ushna needs some rest sbd stress nd he had already informed the management.

daga haka komi ya tsaya magananta ya lafa a camp din kamar ba abunda ya faru..

saidai can cikin zuciyar mr abdul shi kadai yasan irin tashin hankalin daya shiga ciki musmn jiya da dare data walakntashi ta gudu cikin ruwa dan har yanzu yana tuna yadda ta falla masa mari ta watsa masa ruwan zafi and for some strange reason abin yana bata masa rai fiye da yadda yake tsammani

abun yana balaeen cinsa arai amma haka ya shanye ya dauki students dinsu long economic lectures kamar babu komi har ma ya tsaya yana musu jokes yana dariya dasu saidai wani lokaci idanunsa yakan tsaya a empty seat din ushna inya tunata sai yadan dauke kai ahankli yana tuna abunda ta masa

da yamman ranar haka yahada ma students dinsa closing dinner inda yay surprising din grp B student maza da mata da boxes na expensive gifts,dsigner perfumes, watches da jewelry dan kawai ya nuna musu cewa yana da kudi sosai

sosai yan mata suka rikice da farin ciki suna ta daukan pictures har ziyada ma saida ya mikawa wani customized package yace takaiwa ushna gida, ziyada ta karba ahankli tanata kallonsa dan wani abu acikin zuciyarta is telling her something is wrong saidai bata ce komi ba.

kusan raba dare sukayi ana shagali ta dauke hotona da yara dayawa wasu yan matan dayake latsawa ya musu alkwari zai nemesu suna haduwa a hotel.

washegari kmr da wasa aka rufe bootcamp din gaba daya kaf students suka fara komawa gida har lokacin kuma wayar ushna a kashe take

can da yamma tayi bayan komi ya lafa ziyada taji bazata iya hakuri ba haka nan ta taho gidan su ushna wanda tunda aka bude mata gate zuciyarta bai dena bugawa ba.

yau mai aikin gidan ne yakaita har sama ta kwankwasa kofa after like 3 min ushna ta bude kofar fuskarta yayi fayau manyan idanunta sun dan kumbura kmar wata wacce bata samu bacci ba kwata kwata.

suna hade ido ziyada tace..ush what…kafin ziyada ta karasa furta tambayar ushna ta jawo ta ciki ahnkli ta rungumeta tightly nan take zuciyar ziyada ya karye tajanyota ahnkl suka zauna a bakin gado hannunsu sakale da juna....

ahnkli ushna ta dan sunkuyar dakai kasa hawaye ya cika kwayar idonta tanamai sauke ajiyan zuciya cos she was feeling tired nd so depressed ko abinci bataji shaawar sauka taje taci ba

da tsananin fargaba da tsoro ziyada ta damke hannunta tace ushna dan Allah menene ya sameki is everything okay? did he hurt you?

tun ushna bata amsa ba hawaye suka fara sauka a idon ziyada

daga nan ne ushna ta share nata hawayen itama tafara fada mata komai da ya faru cikin rauni da sanyin murya

yadda ya kaita lodge dinsa. yadda taga bank papers da yadda tajishi yana waya akan wai zaiy sex-drugging dinta da yadda ta gudu cikin ruwan sama wanda lokaci guda fuskar ziyada ya sauya gaba daya cikin shock tace

innalillah wa enna ilaihi rajiun dama kuma sai da kikace mana baki yadda da mutumin nan ba mukata miki musu, you were right abt him he is really a monster!

ushna ta gyada kai hawayenta na sauka ahankli. tace zeeyada he lied to everyone abt his prsonality ashe gaye kam babban dan iska ne, kuma fa da kudin matarsan ma ya saya muku abubuwan nan na designers da ya baku kyauta bana tsmnin ma da saninta yay wnn siyayyar inda ba haka da ba bank bazasu bashi irin wncn form din shaidar yacika ba.

ziyada ta dafe kirjinta cikin tsananin mamaki tace oh my God....ai kuwa gashi ya bani gift pack din wai in kawo miki naki gida

ushna dake share hawayenta ahnkl tace" tanks, but pls take it away i dont want anything from him nide babu ruwana wallah

ziyada tadan kalli perfumes da watches din sannan ta kalli ushna jikinta yayi mtkr sanyi sosai dan sai yanzu ne ta gane cewa kmr duk abunda deeja tay akwai wani darker side din da basu taba ganewa akansa ba...

hira sukay me tsayi tsakaninsu dake ma sauran kawayen su na dacan can da suka taso atare zarah da tasleem duk sun kira waya akan maganan deeja kowa ya bawa ushna hakuri snn suka nema wa deeja yafiya.

bayan sun gama wayar ziyada ta dan babbata shawarwari game da rayuwa kafin nan suka rabu..

washegari da safe kmr yadda ta tsara ranakun ta tay maza ta shirya kanta ta shigo cikin university compound gabanta na mugun faduwa taje admin office dan ta karɓi pass ticket dinta na zuwa dubai program dinta kai tsaye.

dakyar aka bata pass sbd fake report da mr abdul yashigar akanta na cewa kwakwarlta ba daidai ba waitana fama da emotional stress da anxiety

haka ta dinga roko sai da aka bata.

tana fitowa babu bata lokci ta dau uber kai tsaye tanufi gidansu saukarta agate dinsu kenn taga mr abdul tsaye jikin motarsa sanye da black hoodie da wata sunglasses kamar wanda ya jima yana jiranta awajen.

atake ta juya zata wuce kmr bata gansa ba sai taga yayi saurin biyota .“ushna wait., ta kara sauri zata bude gate batare da ta tsaya ba yakara sauri ya riko hannunta da ƙarfi yace haba please ushna just listen to me mana

ta fizge hannunta cikin bacin rai tana kallonsa tun kafin tay magana cikin lowered voice dinshi na mayaudara yace "i know i messed up…okay? but i swear to u wallh ina sonki, i really like you.

ushna tayi tsaki tare da juyawa zata tafi kawai taga yawani hargitso ya sha gabanta yana wani matsowa kusa da ita.

"waimesa kike taurin kai ne, Abunda kike tunani akai fa ba haka bane, we are already having issues with my wife thats why i kept it private kuma dama im planning to divorce her.

ushna tadan tsaya tana kallonsa cikin tsananin raini, yaci gaba da magana cikin desperate tone " cmn baby girl, camp is over now nobody has to know anything i just want you to be my girl

dawani irin disgust a fuskarta ta kallesa daga sama har kasa tana mamakin yadda yake mata magana kamar yarinya yar karama dayake tunanin bata da brain dan haka zata fada tarkonsa cikin sauki

ta lura dake shi dama arayuwarsa kmr ya gama raina darajar mata ne yana ganin kowace mace is cheap kamar sauran matan da yake yaudara ya kwana da su.

gani yake kmr mata fa in general wawaye ne musmn ma agaban hadadden namiji kamr sa me kyau da kudi.

cikin wani irin harara da kallon bacin rai tace you are actually insane ka raina makanka hnkli how bold of u to come here nd talk to me byan duk abunda kayi jiya? me ka dauke ni??is it bcos i didnt report u for trying to drug me nd raped me hakan ne yasaka kake tunanin zaka iya zuwa gabana harka samu daman yin maganan soyayya da ni ko?

yana kkrn bude baki zai magana abazata yaji wani paahssss ta watsa masa mari mai dan uban karfi dayafi najiya ƙara dazafi saida ya tsaya cak cikin wata iriyar shock baiko iya motsi ba

da tsaurin ido ta matso kusa dashi idanunta cike da tsana cikin rawan murya tace malam rainin ya ishe ka hka, now, listen to me very carefully mr abdul or whatever disgusting name u call urself…ni ba kalar ka bace..u are a cheap ass manipulative liar, a cheating filthy predator nd wallahi ko karshen rayuwata xan kai ban ga namijin da nake so ba bazan taɓa hada kaina da wawan namiji mazinaci kuma kazami kamar ka ba.

atake fuskarsa ta canza kala sosai zai magana da tsawa ta kara cewa “u think every girl is cheap because they fall for ur stupid attention?you are soo pathetic, nafi karfin ka, ni ba ajinka bane nd i wll neva be. snn inka cigaba da bibiyata zan maka abunda har ka mutu bazaka manta ba

yayi yunkurin magana again ta daga masa hannu tace enufff mr' dont ever come near me again or i wll dial 911 on you ryt now useless he goat mtss.

daga haka ta juya ta tafi tabarsa nan tsaye ransa ya mugun baci jikinsa na wani irin rawa wani abu me zafi ya tsaya masa cakk a wuyarsa bawai dan saboda zafin marin data masa ba saidai saboda yadda yaga yarinya karama da yake tunanin zai iya controlling cikin sauki wai ta zage tana kan wakalantashi ..

ransa sosai ya ɓaci har yana kumfan baki yana huci duk dama tuntuni abokinsa faisal ya riga yabashi shawara akan kawai yay threathning inta da hotonanta daya dauka akan gadonsa lkcin datake bacci in taki kulashi ya bazasu a internat ya mata sharri cewa aitana zuwa wajensa suna kwana a camp sai yasaka abun yay kamr kawarta deeje ce ta tona mata asiri

yaso yay hakan amma ganin kalar tsaurin idon ushna sai kuma ya kashe masa kwarin gwiwa, gashi normal pics inta ne kawai dashi lkcin da ya cire mata wet jacket dinta jiya da dare while she was uncounsious nd wet ba nudes bane bare abun yay mata zafi snn yasan koda yakawo mata wnnan karamar barazanar hala asirinsa ne kawai zata tona sbd yaga alama kmr bata da tsoro kmr deeja

der is high chance dake nuna masa cewa ushna bazatay shiru ba kuma zata tona masa asiri sosai.

Yafi minti ashirin yana tsaye yana tunanin abunda zai mata ya rama dan wallh tun da ta maresa har sau biyu bayan bai cita ba bazai taɓa hakura ba sai ya dau fansa akanta wata rana

saidai yay tunanin duniyar nan amma har yanxu dai bai same wata gamsashen hanya ba ganin zai bata makansa lokaci dayawa aknta kawai sai yabar abun aransa.

huci yake tsabar bacin rai da baqin ciki haka idanunsa sunyi jaaa yaja wata arniyar tsaki ya bude motarsa ya shiga tare da kunna music trying to calm himself down abit.

ahnkli yafara danasani bata lkcinsa dayay akn ushna bayan kuma ga abubuwa dayawa dake gabansa

next week dolensa ne yaje shi Abuja wajen sarauniya Areesha sbd zatazo taro na marayu yasan kudi take kawai bukata daga wajensa,

isarsa hotel dinsa bada jimawa ba ya fara harhada kayansa dan ya koma lagos akan lkaci ya samu ya shawo kan matarsa rihanna ta dan bashi isashen kudi da wuri shiyasa ma yasaya mata wani kyauta zai tafi mata dashi.. he cudnt even wait da da dare yabar london yabi jirgi xuwa lagos nigeria kai tsaye.

*****

dagata bangaren ushna kuwa washegari da safe sosai ta tashi tayi shiri cikin nutsuwa duk dama batada wani masaniya akan kalar abunda zataje ta tarar a dubai idan taje duba dan bata taɓa zuwa qasar ba.

karamin beige suitcase guda daya ta hada with few classy outfits inta masu mutunci, some books, laptop dinta da kuma documents nata na schll da ID cards.

duk da zuciyarta babu wta cikakken natsuwa amma akwai wani irin relief data keji aranta na cewa atleast zata bar london din nan na wasu kwanaki cos all her life kulle ake mata daga schl sai gida ne inkaga taje hutu wani location to sanadiyar makaranta ne amma ko gidan kawaye ba'a barinta taje.

bayan tagama shirinta tsaf tajawo karamin trolley inta tana kan saukowa kasa cikin shiri a falonsu nakasa taga dattijuwar matar dake kulawa da ita a zaune akan dining area tana shan hot coffee ata dayan hannunta kuwa wayartane tanata chating da Areesha jin qamshin turare me dadi da alaman ushna na saukowa yasaka tay saurin aje wayar dan bataso ko kdan ushna tasan cewa ita take kai rahoto da gulmanta wa Areesha kowani lkci.

motsin isowarta kasa yasa nan take idanunta suka sauka akan dan karamin suitcase dinta

fuska ba yabo ba fallasa tace ohhh so the dubai trip is finally today?

ushna ta gyada kai ahankli tace “yes maam. matar ta mike tsaye cikin fara’a tace “come nd have some breakfast first mana, da mamaki ushna ta taho tazauna saidai tun kafin nan ta fara shan shayin nan matar tafara mata wasu irin tambayoyi.

tace..wai awajen suwaye zakije ki zauna snn waye ne sponsor din program? nd how long zaki dauka kina wajen dan kindai san yanayin mahaifinki mai martaba bayason wani abu da zai zubda masa mutuncinsa ko?

nan take ushna ta dago idanunta da mamaki tana kallonta lokaci guda kuma sai duka maganganun ziyada suka hau dawo mata aranta sosai.

sometimes not everybody asking you questions genuinely care…

barema matar nan bata taɓa damuwa da wani abun alheri nata ba inbawai kara ko gulmanta zata kai gida ba.

jiya ne kawai tace mata zataje dubai yau yin wani schl progrm shine wai harta zaunar da ita tabata tea tana kkrin mata Q&A tsbr gulma hmmm

nan take tay dan gyaran murya da karamin yake tace “bafa wani abu bane na jimawa bane, is just a short term academic program everything is arranged already daga schll tunda bani kadai ne daliba da zataje ba

matar tay shiru da alaman tana jiran karin jin wasu details amma sai taga ushna tana bata short dismissive answers can dai tagaji kawai sai tay shiru

sama sama taci breakfast din snn ta mike ahankli tace ni zan wuce i dont want to miss my flight

har waje matar ta rakota tana mata addu’a da tunanin ushna zata fayyace mata komi game da zuwa dubai innan amma haka taqi sam saima nuna mata take abun ba serious bane

har driver yazo ya dauketa zuwa airport..

sabd traffic da nisa sai wajen 9am ta isa cikin London Heathrow inda jirgin emirate airways zai sauketa zuwa Dubai International Airport kai tsaye.

tundaga main entrance din airport mutane da yawa suke juyowa suna satar kallon fresh nd smooth kyakkywar fuskrta saboda wani irin calm elegance dake tattare da ita

tay shigar simple clean muslim girly ce amma dake tana mugun son harkan gayu wata iriyar hadaden mocha brown two piece travel set ne ajikinta, loose fitted trousers da wata elegant long sleeve top me laushi, snn ta daura creamy silk hijab dinta cikin tsari me kyau tare da karamar gold wrist watch na catier da nude handbag me tsananin aji da kyau

dressing dinta ba mai hayaniya bane amma duk inda tawuce mutane sai sun juyo suna kallonta saboda akwai wani irin clean rich aura tattare da ita.

gashi ta mugun iyayi wa fuskrta light clean makeup wanda duk inda ta wuce sai kaga mutane dayawa na satar kallonta with deep admiration sbd ushna kyakkwace bana kadan ba kana kallonta kaga jinin kasaita da sarauta

bata wani jima awajen checking ba tana tsaye sai wani airline staff daga upstairs yazo ya sameta yana dab mata murmushi

can yace “miss ushna right? ta gyada kai politely tace yes..

after few minutes of introduction sai ya sanar da ita cewa anyi mata complimentary elevation zuwa first class as a holiday gift frm the emirates airline sponsors.

oh my god, wani dan uban dadi taji cikin mamaki tace“really?”

staff din yayi mrmushi

yace “yes ma’am. its festive time, your beautiful dressing nd elegance fits our first class aesthetics.

murmushi me sanyi ne yakwace mata abazata dan duk dama tasan tana da kyau da tsari but it feels so good to hear it frm strangers

ahankali ta karba first class ticket gift din ta musu godiya sosai

suna mata da wasa cewa tay hotona masu kyau awajen cos they know her face alone can attract them alot of male customers to join first class.

itade bata wani damu ba dan bakaramin dadin samun wann uban darajawar da suka mata taji ba...

wajajen karfe tara da rabi suka fara shiga jirgi hakanan tanemi waje me kyau a first class ta xauna feeling sooo excited 10:am jirgin su ya tashi zuwa 8 na dare dede zata sauka a dubai dan haka ta jawo book dinta tazauna very confotably tana shan fresh orange juice tana karantawa,lkci zuwa lkc intagaji ne sai taje lavotory ta sauya pad ta dan wanke jikinta da ruwan dumi snn ta dawo ta cigaba da karance karance ko kuma taci abinci...

ata daya bangaren kuwa dake tafiyar dare farees yay ya iso lagos ne da safe can wajajen around 8:30am

cikin wani irin yanayin gajiya da sauran bacin ran ushna dayabi ya kunsho aransa yazo dashi

tun daga airport din ransa yake a hade dake home driver aka turo yazo ya daukesa

amma sbd traffic sai basu isa gida ba sai wajen 10am na safe

yana isowa babban wazeeri mansion dinsu dake banana island ya dan tsaya da mamaki yanata kallon yadda gidan ya wani cika da sabbin workers da decorators kowa na kai kawo cikin fara’a an kawata flowers an sake design har wasu security personnels an sauya su.

yana kallon wokers din ya wani hade rai yace what is going on here?

tun bai samu me bashi amsa ba caraf saiga nan matarsa rihanna wazeeri ta fito daga main hallway sanye da wata elegant silk dress tana murmushi, sosai tay haske dan karamin cikin dake jikinta yadan kara mata kyau sosai

suna hade ido tace “Farees.. finally..

da yanayin sanyin kasaita da girmamen aji dayagama bin jinin jikinta ta taho tadan rungumeshi cikin nuna farin ciki saidai shi ko amsawa sosai baiyi ba

ya kalli workers din yace honey meyasa gidan nan ya koma like an event center ne wai wani hidima zakuyi ne?

rihanna tayi dariya kadan amma mai cike excitement ahnkli tace Oh i forgot, ban gaya maka ba my brother is finally coming to lagos very soon.

nan take zuciyar farees tayi wani irin bugawa muryansa har na rawa yace kina nufin wai yayanki Shamsan din ne xai dawo gida?

cikin farin ciki sosai tace "yes, is the Sultan,

dude... have some respect..

wani irin rolling eyes dinsa yay dayasata tay dariya.

yace "mezai kawosa??

kuma yaushe zai zo din.

tace kasan dai he is curently heading one of the biggest dam projects in africa ynxu kuma ankara masa da wasu manyan project din alongside some real estate firm across lagos, south africa, morocco and egypt.

ta kara da cewa "mahafinmu mai martaba has decided he should temporarily work from our lagos real estate head office for now tunda babban project dinsan a africa ne, dama kuma kaga anfara zancen aurensa uwarjini ta damu akan ace masa yadawo gida yay aure inaga, zuwan san nan zai kai next week haka dan yanxu yana da wasu special meetings dinsa da zai kammalashi a dubai main headqtr.

lokaci guda farees yaji jikinshi tawani irin yin laasar tareda mutuwa wani irin haushi da disgust mai hade da uneasiness suka tsaya masa aransa atare sai yaji ya rasa abunda ke masa dadi a duniyan nan

dan yasan sarai idan har shamsan ya dawo garin nan then his own freedom is over ba zai sake iya manipulating rihanna yadda yakeso ba snn bazai sake iyayin yawonsa yana lalata yan matansa openly ba bare harma ya samu damar juya komai yadda yakeso agidan.

musamman ma ganin yadda shamsan yake tsananin protecting din kanwarsa da family dinsu, yasan kashe kudi anyhow da satan kudin rihanaa zai fara masa wahala kenan

rihanna duk bata lura da canjin yanayinsa ba ta cigaba da magana cikin farin ciki tana cewa bazaka fahimci farin cikin danake ji araina bane farees…its been many years nd im just sooo happy zamu sake zama a gari daya dashi.

farees dake jin jininsa kamar tana tafasa a 100^ kusan ma murmushin dole kawai yake dan binta dashi ya kasa cewa komai.

daga cikin zuciyarsa tsananin baqin ciki da haushin shamsan din ne yake karuwa.

karshe kyaleta yay ya wuce personal room dinsa ya kulle kansa aciki yana huci dan kwata kwata baisan meyasa kwana biyun nan yake cin karo da rashin sa'a ba

first he cundt get dat little brat ushna nd now wai shamsan ne zai dawo nigeria?

dawowar shamsan is like a drop of bomb in his heart dan ko akan areesha ma kadai ya isa ace ya tsane shi bana kadan ba, he just hate that guy with passion....

AYI COMENTS

AYI SHARE

SURAYYAHMS

TALES OF THE WAZEEERIS.

***