BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----3 

koda ya bar gidan aunty Aisha hanyar gidan su zeenah ya kama kamar yadda yayi mata alkawari sanin zeenah na matukar kaunar snacks ya biya ta Dalema Supermarket ya mata order na snacks da cakes kofar wani katafaren gate yayi parking wani waje ya ɗan na a jikin gate bayan ya gama mashi scanning ya buɗe a hankali ya fara shiga ciki yan aiki ke ta kai kawo a gidan ko wannen su sanye da kayan aiki wayar sa ya dauko ya kira Zynah bugo ɗaya ta daga ya sheda mata yana cikin compound din ba bata lokaci ta fito sanye take da black abaya wanda ta haska farar fatar ta ƙamshin turaren daya daki hancinsa ya tabbatar masa da zuwan ta duk yadda taso su shiga ciki ƙi yayi a cewar sa sauri yake ba wata magana sukayi mai tsayi ba ya bata ledar snacks din ya wuce zeenah taji dadin abinda suhail ya kawo mata ji tayi duk wani haushin da ke cikin ranta ya wanke sa har bakin motar sa ta raka sa.

Suhail na dawo wa gida ya kaiwa Mahaifiyarsa sakon da ya amso mata ya fito a harabar gidan ya iske aunty Fauziya kishiyar Mami ta raƙo kawar wata irin kunya ta kama shi dan yau kusan sati guda kenan bai sata a idanun sa ba duk da kullin mahaifin sa nayi masa umarnin yaje ya gaishe ta,so sa kansa yayi ya ce"Aunty ina wuni"

kare masa kallo tayi kafin ta ce"lafiya qlau Suhail,kana garin kenan ai duk tunanin ma baka nan"

murmushi yayi ya ce"ina nan aunty kawai ayyuka ne suka dan min yawa shiyasa kwana biyun nan "
"ya Allah taimaka"
har ta juya zata tafi ta ce"Dambun shinkafa na girka idan zaka ci"

"mizai hana naci aunty naji ana kiran sallah Magariba idan nayi isha'i zanzo naci in sha Allah"
"to shikenan ina jiranka"

Bayan yayi sallar magariba da isha'i ya koma part din aunty Fauziya yaci Abincin rabon da yaci abincin da yayi masa dad'i haka har ya manta dan mami yan aiki ke mata komai saɓanin aunty Fauziya da hatta shara ita keyi da kanta duk da tarin dukiyar da mijinta ya mallaka Amman bata yarda ta ajiye yar aiki ba.

yana gamawa ya koma Dakin sa wanka yayi ya saka wasu blue din pajamas mai kyau na bacci ya haye kan gadon ya janyo laptop din sa ya cigaba da  hada Application din da zai tura court akan case din tahir domin ta bada warrant of arrest akan sa.

karar shigowar sakon text message ya shigo wayar sa ya duba yau ma kamar dai ko yaushe Unknown Number da ta saba tura masa sako ce ko wani dare ya fara karantawa kamar haka 

Ban san ko akwai ranar da zaka taba kallona da idon da nake kallon ka ba ,amma wallahi ina sonka Suhail Son da duk lokacin da naji sunanka sai zuciyata ta buga 
ban sani ba Wata rana idan ka gano wacece ni watakila zaka tsaneni amma na gwammace na boye wannan soyayyar a raina fiye da na na bayyana a fili 

Ka kula da kanka Suhail saboda  addu’arta kullum akan ka Allah ya baka nasara da kariya akan aikin i love You so much good night Sweetheart dreams♥️

Tun Abin na bashi haushi idan aka turo sakon har ya soma bashi dariya a farko yayi datunanin sa zeenah ce sai da yayi dogo bincike kafin ya gano ba iya bace dan ita idan zata tura masa sako bata shayin bayyana Number ajiye wayar ya cigaba da abinda yake.

Meerah ce zaune dakin mahaifiyar wanda shigowar ta kenan hannun ta riƙe da waya ta  ta ce"Momy dazu ya Suhail miya zo yi dan nasan baya zuwa gidan nan ba tare da dalili ba"

Aunty Aysha ta ce"yazo amsar wa Ummi maganinta na sugar da aka kawo mata jiya,ni nace ta turo shi ya amsa dan nasan ko aiken ki nayi bazaki je"

taɓe baki tayi ta ce"kamar ko kin sani,ni zuwan ma da yake gidan nan ba san shi nake ba da ina da yadda zanyi da na dakatar da shi daga zuwa"

Aunty ta ce"Eyye sannu rasa kunya to ai ko ubanki yana raye bai isa ya hana suhail zuwa gidan nan ba bare ke" 
turo baki tayi ta ce"gaskiya nidai a daina zagar min ubana akan wani"
tashi tayi ta fita daga ɗakin cike da mamaki ta bita da kalllo lalle ma yarinyar nann suhail din ne wani"

washe garin ranar da Suhail ya tura karar tahir yan sanda suka je har Club din da yake sheƙe ayar sa aka kama sa cikin kumfar ɓaki ya ce Masu"Baku da hankali kun san waye ni kusan waye ubana a garin nan  to wallahi duk sai nayi sanadin da za'a kore ku wajen aiki shasshasshun banza kawai"

cikin yan sandan babu wanda ya kula shi duk zazage-zagen da yake har suka isa babban headquarter ta ƴan sanda dake garin kaduna direct akayi cell dashi.

wasu daga cikin abokan Tahir da abun ya faru a gaban su suka kira mahaifinsa suka faɗa masa a fusa ce ya ce"su waye suka kamasa"
abokin ya ce"ƴan sanda"
tsaki yayi ya kashe wayar dan duk cikin masu aikin kaki babu wanda ya raina sama da yan sanda

yana katse wayar ya fara kiran duk wasu DPO's da yake da lambar su yana tambayar su ko police station dinsu aka kawo Tahir amman duk amsar ɗaya ce "a'a"
anan fa hankalin sa ya fara tashi to ko dai yan kindnapping ne sukayi amfani da kayan yan sanda suka sace masa Tahir .

TO JAMA'A KU BIYO NI DANJIN YADDA ZATA KASANCE GA TAHIR A POLICE STATION KUNA GANIN ZAI FITO KO YA SHIGO HANNU KENAN SUHAIL ZAIYI NASARA A CASE DIN KO KUWA