BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖

Wannan page din naku ne ƴan amana Nussey bee🐝 da docter d Allah ya bar zumunci 

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----4

wayar Alhaji sani ta fara Ringing ganin ɓakuwar lamba yasa ya daga cikin rawar  jiki bayan sun gaisa ya ce"mun kiraka  ne mu shaida maka mun kama danka Tahir,kan zargin yiwa yar aiki fyade wanda har ta rasa ranta"

cikin rawar murya ya ce"yana ina yanzu tahir din"
nan wanda ya kirasa ya sheda masa yana headquarter ƴan sanda nan da nan ya tashi ya kira driver din ya gaya masa inda zasu je direct office din DPO ya nufa bayan an masa iso ya shiga kan kujera ya zauna bayan sun gaisa ya ce"nine mahaifin Tahir"

jinjina kai yayi ya ce"okay,kamar yadda na faɗa maka ana zargi sa da aika laifin fyade,already an shigar da kara kotu dan daga chan ne suka saka mu kamo sa zancen da nake maka yanzu ranar monday za'a shiga kotu dashi.

cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta fara tsatstafowa daga goshin Alhaji sani duk girma laifin da Tahir ke aikatawa bai taɓa wuce police station ba ,sai gashi yau ana kiran court to ƴar gidan wa Tahir ya taɓa haka amman yayi wa kansa Alƙawarin ko yar gidan wacece zai shiga ya fita ganin case din ya lalace ko da Dukiyar daya mallaka gaba ɗaya zata kare wajen kare tillon ɗan sa.

gyara zama yayi ya ce" ko zan iya sanin wanda suka shigar da karan?"

"Barrister suhail munnir mahmud"

a ransa yake maimaita sunan suhail munnir mahmud tabbas yasan sunan munnir mahmud dan idan dai a kaduna kake zai yi wuya ace bakasan Alhaji munnir bs babban mutun ne tsohon commisioner ilimi  na jahar kaduna,mutun ne mai matukar kirki ya iya ƙoƙarin sa wajen  taimakawa mabukata,mutane da yawa a Kaduna suna girmama Alhaji Munir Mahmud saboda mutuncin sa da kuma tsoron Allah da yake dashi.

a hankali Alhaji Sani ya sauke numfashi yana kallon DPO ɗin kafin ya ce,

“Kana nufin ɗan Alhaji Munir ne ya shigar min da ƙara?”

“Eh shi  ne.” DPO ya amsa a taƙaice.

Shiru Alhaji Sani yayi yana jin wani irin bugun zuciya. Domin yasan family ɗin Alhaji Munir ba irin mutanen da za’a iya tsorata da kuɗi ba ne

ya ce"DPO ina neman alfarma a bani belin Tahir zuwa ranar Litinin din ka faɗa ko nawa kake da bukata zan baka"
murmushi yayi ya ce"Alhaji, doka bata bada damar yin hakan ba a halin da ake ciki ko ganin sa baza kayi ba"

duk yadda Alhaji sani zaiyi yayi amman yaƙi yarda da bada belin sa haka ya haƙura ya koma gida yana zaune a falon sa ya rasa ma wa zai kira ya fada masa cikin manyan da yake dasu a garin Kaduna,Hajiya saudat ce ta shigo hannun ta riƙe da kular abinci ganin Alhaji sani cikin yanayin da bata saba ganin sa ba ta ce"Alhaji lafiya kuwa miya faru"

ajiyar zuciya ya sauke ya faɗa mata dukkan Abinda ya faru tahir da kuma yadda aka ƙi yarda a basa belin sa kuma ya ƙara da cewa wallahi bazan taɓa barin ɗana ya wulaƙan taba" 
a ranta ta ce"ta baya kuma ta rago ai duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa ke duka"

Amman a fili ta ce"Alhaji ina ganin ka bar doka tayi aikin ta kafi kowa sanin waye Tahir,ka sani ko hakan ya zama sanadiyar shiryuwar sa"
 Alhaji sani ya ce"Ai ke daman nasan from day one baki kaunar Tahir, kuma hakan da kikayi baida nasaba da cewar bake kika haife saba,ke da kina haihuwar da waya san wasu kalar yara zaki haifa gaki nan shekaru sama da Ashirin ko batan wata baki taɓa yi ba, kinga ko ai bakisan ciwon haihuwa shiyasa zaki fadi haka.

Hajiya saudat har ranta taji zafin gorin da Alhaji yayi mata murje ido tayi ta ce"Ai Alhaji da haihuwar yaro irin Tahir Gara rashin haihuwar wallahi"

tashi tayi zata fita ya ce"kinga Malama dawo ki kwashe wannan kulolin naki abincin bazan ciba kuma kema kin bi a hankali ki ka cigaba da aiba min Tahir sai kin bar gidan nan"

"ai da auren mutun irin ka gara zama babu aure in banda nabi umarnin mahaifina babu abinda zai sa in auri mutun irin ka" haka tayi niyyar faɗa masa amman kawai tayi shiru dan batan san maganar tayi tsayi.

tana fita yaja dogon tsaki!!! ita ko ji tayi ranta yayi mata tass  dan hatta masu aiki ba sa san zama a gidan duk girman ka Tahir baya shayin yi maka Maganar banza hakan yasa da an kawo mata masu aiki rana tsaka suke guduwa hakan yasa yanzu tama hakura da yan aikin bakin ɗaya addu'a tayi akan Allah ya karshen sane ya zo.

Daren Ranar yadda Alhaji sani yaga rana haka yaga dare babban tashin hankalin sa bai san ya Tahir ya kwana ba yasan yana chan sauro da zafi duk sun dame shi gashi kwata-kwata bai saba da Rayuwar wahala ba ya tashi  cikin gata mahaifiyar sa ta rasu tun yana sa shekaru ukku kacal a duniya mahaifin ya cigaba da kula dashi cikin so da kauna baya yadda ko kuɗa ya taba shi makarantu ko yasha chanza masa saboda ana dukan sa,isilamiya kuwa ma ba'a maganar ta haka ya taso a sangarce bai san ya nemi abu a hanasa ba Alhaji sani baida niyyar ƙara aure sai da mahaifiyarsa ta taƙura masa akan ba zai yiyu  ya zauna haka ba mata ba,kwatsam wata rana ya haɗu da saudat yaje wajen abokin kasuwanci sa tun Ranar da ya ganta ya kamu da santa,nan ya fara Binciken halayen ta wajen abokin nasa ya faɗa masa zawara ce mijinta ya rasu tana zaune a gidan su,ta wajen mahaifin ta ya nemi auren bai wani sha wahala ba sakamakon kudaden da ya riga basa hakan yasa ya daura masu aure ba tare da zurfafa bincike ba.

tun Ranar farko data tare ta lura da dabi'un Tahir kwata-kwata bashi da tarbiya duk girman ka baya shayin ya zage ka ko ya faɗa maka magana tun yana yaro bai damu da Sallah ba tayi iya kokarin ta wajen ganin ta dawo da shi kan kanya amman ina hakan yaci tura hakan yasa kawai ta sa mashi ido.