Chapter 8
Zahra ta wuce ciki. Tana shiga babu kowa a main parlor, hakan yasa ta wuce sama direct zuwa ɗakin Mami. Da sallama ta shiga, ta samu Mami na zaune tana ordern kaya a waya. Da gudu taje ta rungume ta. Mami tayi saurin kashe kiran ta juyo tana kallon Zahra da mamaki, tace, “Zahra me haka kamar wata mai ciwon kanjamo?”
Zahra tayi dariyar yake tace, “Mummy kanjamo kuma? Me kika gani?”
Hararanta tayi tace, “Kina ganin kanki kuwa? Ko shi mijin naki baya faɗa miki yadda kika koma ne?”
Tace, “Mami rashin lafiyan nan ne yasa nake ramewa amma, zan samu sauki ai.”
Daga haka ta haye kan gadon ta kwanta ta bawa Mami baya. Hawaye ne suka fara zuba daga idanun nata, a haka bacci ya kwashe ta.
Can wajen Magrib Mami na tare da Abbah tace, “Ai Zahra tana nan fa, tana dai bacci ne amma raman ta ya fara damuna.”
Yace, “Ko dai wani abu ne yake damunta?”
Tace, “Ina zan sani? Amma ba ranar Mummynsu tace ciki ne gare ta ba, kuma dukkan alamu ya nuna hakan ne. Ko zata dawo gida ne tayi laulayin cikin ne har ya girma?”
Abbah ya ajiye wayan hannunsa yana kallonta with full attention yace, “Amma kin tabbatar babu abin da yake damunta? Ko da dazu muke waya babu wannan vibes ɗin Baby da na santa da shi. Ke ce uwa, ke ce zaki saka ta a gaba ki matsa mata ta faɗa miki abin dake damunta.”
Sauke ajiyar zuciya tayi tace, “Na barta tana bacci ne tun ɗazu, bari zan taso ta tunda Magrib ma yayi. Zaka ga yadda ta sake lalacewa.”
Miƙewa tayi tace, “Ka tafi sallah bari na haura sama na tashe ta.”
Da “toh” ya amsa mata, ita kuma ta wuce sama.
Mami na shiga ɗakin ta samu ta tashi, tace, “Yauwa kin tashi ko? Ki shiga kiyi alwala, Magrib yayi. Idan Abbanku ya dawo daga sallah sai ki sauka ki tafi wajensa.”
Kai ta gyada ma Mami, daga haka ta wuce toilet, Mami kuma ta sauka kasa.
Can sai ga Mami ta sake buɗe ɗakin ta shigo da tray a hannunta na fruit, ta ajiye mata a gabanta tace, “Ki sha kafin Abbanku ya dawo.”
Ta kalli Mami tace, “Nagode.”
Apple kawai ta iya sha, ta ajiye bowl ɗin a gefe sannan ta miƙe ta fita a ɗakin.
A parlorn ta haɗu da Mummy tana zaune ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana kaɗawa, kuma ga waya a manne a kunnenta.
Zahra tace, “Mummy ina wuni.”
Tace, “Yaushe kika zo?”
Tace, “Ɗazu ne.”
Tace, “Okay, ya mai gidan ki?”
Tace, “Lafiya. Bari na tafi wajen Abbah.”
Daga haka ta fita zuwa parlorn Abbah. Ta shiga da sallama, yana zaune yana kallon news. Jin sallamarta yasa ya ɗaga kai ya buɗe mata hannayensa alamar ta ƙaraso jikinsa.
Karasawa tayi ta shige jikinsa, kawai taji wani kuka ya taho mata tunawa da memories ɗin baya.
Yace, “Baby ashe kina gidan nan?”
Tace, “Eh Abbah, dazu da muka yi waya shine naji nazo gida na ganka saboda ka yarda ban manta da kai ba.”
Murmushi yayi yana shafa kanta yace, “Nasan baki manta ni ba, wasa nake wa Baby na.”
Tashi tayi a jikinsa ta zauna gefen ƙafafunsa.
Yace, “Ya maganar project ɗinki?”
Tace, “Abbah ai yaron yayi nisa da min, har result na practical ya gama cirewa.”
Yace, “Ma Shaa Allah. Idan ya gama miki gaba ɗaya ki turomin da numbern sa tare da account details ɗin sa.”
Tace, “Alright Abba.”
Daga haka suka fara hira sosai, har aka kira Isha’i suna tare. Mami ce tare da Ya Umar suka shigo.
Tace, “Wai har yanzu kuna nan?”
Dariya tayi tace, “Ina tare da Abbahna muna hirarmu.”
Ya Umar ya zauna akan kujera yana kallonta yace, “Sannu ‘yar Abbahnta.”
Dariya tayi tace, “Kuma ‘yar Mamin ta, Mummy da kuma Ya Umar ɗinta.”
Abbah ya miƙe yace, “Ahtoh.” Sai kuma ya mayar da kallonsa kan Ya Umar yace, “Tashi mu tafi masallaci.”
Daga haka suka fita. Mami kuma ta wuce cikin bedroom ɗinsa ta soma gyara wa haɗi da sa turaren wuta, Zahra ta wuce sama.
Can wajajen 8:30pm bayan su Abbah sun dawo daga sallar da suka fita tun ɗazu, duk dining suka nufa da niyyar yin dinner.
Mami ta leka ɗakinta tace, “Baby tashi, su Abbanku sun dawo zamu yi dinner.”
Daga haka Mami ta juya ta fita. Kamar Zahra tace mata a’a ita ta koshi dan bata kaunar a mata zancen ta koma gida, amma ganin Mami ta tafi kawai ta miƙe. Kuma ganin Mami bata mata maganar komawa gida ba yasa ta sake sakin jiki.
Fita tayi ta sauka kasa, duk sun cika a dining. A hankali take tafiya. Abbah ya ɗaga kai da mamaki yana kallonta har ta isa. Kujerar dake gefensa ta zauna akai.
Yace, “Baby me kike yi har yanzu baki koma gidan ki ba?”
Ta sauke kai ta kalli Mami.
Mummy ma tace, “Ai kuwa dare yayi ace har yanzu baki koma ba. Ni da banga ki ba ma na ɗauka ai kin koma ne.”
Ya Umar shi dai kallonta yake.
A hankali ta ce, “Abbah yayi tafiya ne, kuma baya gida. Shiyasa zan kwana anan kawai. Yanzu dare ma ya riga da yayi, gidan zai bani tsoro.”
Tun data zauna a wajen ko da wasa Batoul bata ko ɗaga kai ta kalle ta ba.
Abbah yace, “Baby ko dai akwai matsala ne?”
Kawai ya ciro wayansa a aljihu ya fara dannawa.
Mami tace, “Ba dai kiransa zaka yi ba dan confirming?”
Bai tanka mata ba, yayi dialing numbern Ibrahim. Yana fara ringing ya ɗaga. Da girmamawa ya fara gaishe da Abbah, Abbah ya amsa masa cike da fara’a. Wayan kuma a handsfree yake.
Yace, “Kana ina ne?”
Yace, “Ai Abbah nayi tafiya ne yau ɗin nan. Wani aiki ne ya taso min shine na tafi. Akwai wani abu ne?”
Yace, “A’a no, dama Fatima ce ba tazo gida ba?”
Yace, “Eh tace min zata je ai.”
Wani mamaki ne ya kusa kashe Zahra.
Yace, “Toh dama shine take son zata kwana. Tace ai kayi tafiya ma, na ɗauka kawai dan tana son kwanan ne yasa ta faɗa haka.”
Yace, “Aa no ai zata iya kwana Abba, dan nima ba yanzu zan dawo ba sai nayi 7 days. Nan Dubai na tafi, a barta ta kwana idan har sai na dawo ne ma it’s fine, zata iya zama a gida.”
Abbah yace, “Tohm shikenan, Allah dawo da kai lafiya.”
Daga haka suka yi sallama. Ita dai Mummy idonta akan Zahra yake.
Bayan sun gama dinner Zahra ta tashi ta wuce ɗaki. Har ga Allah Ibrahim ya bata mamaki fiye da yadda take tunani.
Tana shiga ɗaki ko kayan jikinta bata cire ba, tana kwanciya bacci ya ɗauke ta.
Can Mami ta shiga ɗakinta taga anan Zahra ta kwanta. Nan ta kunna mata AC, ta gyara ɗakin sannan ta kashe wuta ta fita ta ja mata ƙofar.
Washegari da safe bayan Zahra ta gama shiri ta sauka tayi wa Mami da Mummy sallama sannan ta wuce ɗakin Abbah. Ganin kamar baya nan yasa ta juya ta fita kawai.
Haka kawai take jin kaso 40 na damuwarta ya tafi saboda zaman data yi a gida. Compound ta nufa ta shiga motarta. Direct gidansu Firdausi ta nufa ta ɗauke ta, daga nan suka kama tafiya.
Zahra ta ɗan kalle ta tace, “Kinsan a gida na kwana jiya?”
Firdausi tace, “Haba dai, kuma Abba ya yarda?”
Tace, “Ya yarda mana. Toh tsaya kiji yadda abin ya kasance.”
Nan tayi mata narrating ɗin duk abin daya faru.
Tace, “Lallai Ibrahim kin san abin da yake yi kamar da gangan ne ko?”
Zahra tace, “Shi ya sani, dan ina dab da faɗa wa Ya Umar kuma duk hukuncin daya ɗauka haka zan bi, dan idan na biye ta soyayya tabbas Firdausi mutuwa zanyi.”
Firdausi ta ce, “Allah ma ya kiyaye ba abin da zai faru. Komai zai daidaita.”
“Hmm,” kawai Zahra tace.
Firdausi tace, “Yauwa yau zamu tafi gidan matan nan mai gyara.” Zahra tayi shiru
Tace, “Mu je yau. Yanzu yadda za’a yi idan muka tashi a lectures sai mu wuce gaba ɗaya.”
Zahra tace, “Ni kam har naji ya fita min a rai gyaran, kamar na haƙura wallahi.”
Firdausi tace, “Ai baki ma isa ba Zahra, gyara ya zama dole ki yi In Shaa Allah.”
A haka har suka isa school. Basu suka tashi a lectures ba sai can yamma. A gajiye suka fito a lecturer hall ɗin.
Asiya ta ce, “Kai wannan Prof ɗin yadda kasan zai cinye mu yau ɗin nan haka yaki sake mu kamar maye.”
Suhaima tace, “Maybe ku kun fahimta ma, nikam tun ina fahimtar sa har na daina.”
Duk suka kwashe da dariya.
Asiya tace, “Zahra yi dropping ɗinmu mana, dan yau bana jin zan iya takawa saboda wahalar zama.”
Zahra tace, “Kuzo mu tafi yanzu toh, dan akwai inda zani kar dare yayi mana.”
Daga haka duk suka yi wajen motarta. Bayan ta ajiye su Asiya, suka hau kan titi. Ta ɗan juya ta kalli Firdausi tace, “Amma Firdausi zamu wajen can kuwa? Ni fa nagaji.”
Tace, “Ai zuwa ya zama dole Zahra. Yaushe zaki koma gidan ki?”
Ta ce, “Gobe nake ji, amma yau ma ba iya komawa zanyi ba.”
Daga haka Firdausi take nuna mata inda zasu bi, a haka suka kama hanyar shagon matar. Tafiya sosai suka yi dan matar ba cikin gari take ba.
Sun zo bin wani roundabout, wani mota ta wuce sai da Zahra ta kusa dukan roundabout ɗin.
Firdausi tace, “SubhanAllah Zahra lafiya?”
Zahra kam ta gagara bata amsa, kawai ta figi motar da gudu gudun kar motar data gani ya tsere mata.
Firdausi ta ce, “Zahra talk to me, me yake faruwa ne?”
Amma ina, Zahra sai zufa take yi ga uban shaking da hannunta ke yi. Motar ne taga yasha wani kwana, itama kwanan ta sha ta fara tafiya a hankali ganin kamar motar ta parka a ƙofar wani gida.
Da sauri Zahra tayi parking nata motar ta sauka. Duk yadda Firdausi take mata magana amma hankalinta baya jikinta. Da sauri itama ta sauka ta fara ma Zahra magana meanwhile tana bin bayanta.
Zahra ta ɓuya bayan wani wall tana kallonsa ya fito a cikin motarsa, ya zaga ya buɗe mata nata side ɗin sannan ya riƙe hannunta ta sauka yana mata murmushi, ita kuma sai shigewa jikinsa take yi.
Zahra ta fara ganin dishi-dishi. Gagara tsayuwa tayi, hakan yasa ta fito gaba ɗaya ta nufi inda suke. Firdausi kanta sai data yi mutuwar tsaye ganin Ibrahim da wata a tsaye, looking happy together.
Zahra ta fara nufarsa duk da kalan duhun da take gani ga uban juyawar da garin yake yi mata. Bata kai ga karasawa ba tayi wani kalan ƙara ta zube ƙasa sumammiya.
Da gudu Firdausi tayi kanta. Ihunta yasa Ibrahim da matar ɗaga kai dan ganin menene. Ai yana ganin fuskar Firdausi bai kai ga ganin fuskar Zahra ba ya fara bari, dan sai yanzu yayi recalling cewa muryarta ne.
Da gudu yayi kanta, zai ɗaga ta Firdausi tace, “Bana bukatar taimakon ka.”
Ɗaga Zahra da zata yi sai ga jini yana bin ƙafarta. Daga Firdausi har Ibrahim Khalil suka sake ruɗewa.
Motar Zahra ya nufa da ita da sauri, itama tana binsa a baya. Riƙe ta Firdausi tayi bayan ya ajiye Zahra, ya zaga driver seat ya shiga, a mugun gudu ya tada motar ya jata.
Firdausi sai kuka take tana ta jijjiga Zahra dan ba kaɗan ba ta rude. Sai da suka yi ɗan tafiya kafin suka isa asibiti.
Suna zuwa aka karɓi Zahra sai emergency room. Likitoci sun fi biyar akanta. Khalil ya jingina kansa sa wall yana kallon sama, ga shi gari an fara kiran Magrib.
Firdausi ta miƙe ta fara tafiya, yayi saurin shan gabanta yace, “Ina zaki Firdausi?”
Tace, “Ina ruwanka da ni?”
Yace, “Please kar ki bari wani ya san abin daya faru. Ki taimaka min ki rufa min asiri. Zamu iya sorting wannan matsalar, yanzu fatanmu ta samu sauki ne.”
Firdausi tace, “Ka matsa min a gaba Malam. Kaji nace zan faɗi wani abu ne?”
Yace, “Please Firdausi.”
Buɗe ɗakin da take ciki aka yi, hakan yasa duk suka nufi wajen ɗakin nata.
Ibrahim na kallon likitan daya fito yace, “Dan Allah ya take? Meya same ta?”
Likitan yace, “Kai waye ɗinta ne?”
Yace, “Mijinta ne.”
Kawai likitan ya juya ya bar sa a tsaye...