SARTSE COMPLETE

11

by @legendspen


    (11)

“Kai yaro gyara bakin ka.” 

Turaki ya faɗa yana kallon Sardauna. 

“Ni kake cewa yaro?”

Sardauna ya faɗa yana ƙarasowa wajen. 

“Relax boy.” 

Turaki ya sake faɗa, hannu Sardauna ya sa ya fisgo ni na faɗi ƙasa, da sauri Matar da na ji suna cewa Hajiya Maama ta shi tana faɗin. 

“Sardauna bita a hankali, ba ita a lamarinku.”

“Maama me ya sa zai zo kusa da iyalina, mene haɗin shi da ita.” 

“Shut up malam, bansan har yarintarka ta kai haka ba, na yi tunanin duk wani abu da yake tsakaninmu zai ƙare a tsakaninmu ba sai ya shafi iyalanmu ba, amma na fuskanci har yanzu da yarinta a kanka.” 

Cike da wani irin fushi Sardauna ya yo kansa, Hajiya Maama ta ce. 

“Dakata Sardauna, anan kaine baka da gaskiyya. Duk wani abu da yake between you guy’s ku tsayar da shi iya ku biyu, karku sanya familinku.”

“But she is not our family she is mine, my family, so ya yi baya da ita.” 

“Sardauna karɓi wannan, ka ce she is not our family she is yours?” 

Wata dattijuwar mata ta faɗa, ni mamakina ma yadda aka yi ta iya turanci har haka. 

“Dada wasa yake.” 

Turaki ya faɗa, sai a lokacin na fuskancin yafi Sardauna wayo ne. 

“No let him, allow him to say his mind.” 

“Dada wasa nake.” 

Sardauna ya faɗa. 

“Are you kidding your parents?” 

“Wannam tsohuwa da mita take.”

Na faɗa a raina. 

“Kar nasake jin irin wannan.” 

Ta faɗa tare da komawa ciki, ni kuma na tashi zaune, Sardauna ya fice sauran kowa ya koma ya zauna. Haka su ka yi ta fira har zuwa 12 iyayensu maza su ka shigo suka tattauna abinda zasu tattauna daga nan aka ci gaba da hirarrakin su, banda Sardauna da ya fice. Duk lokacin da na ɗaga kai sai na ga munyi ido huɗu da Turaki, wani lokacin ya yi min murmushi wani lokacin kuma ya yi kamar bai ganni ba. 

Haka aka gama zama kowa ya watse ya tafi, Sardauna ko a mota baice dani ƙala ba, bare kuma da aka koma gida. Nima dai ban ce masa ci kanka ba haka shima bai ce min ba, sai zuwa dare bayan ya sake dawowa na yi masa sannu da zuwa, sai da ya kallani sannan ya ce. 

“Aini yanzu dole na kama kaina, nasan matsayina tun da kin raina ni bakya so na.” 

Bakina har rawa yake na fara magana. 

“Wallahi ba haka ba ne, shi da kan shi ya yi min magana kuma ni bansan shi ba.” 

“Waye? Kar dai ki ce min yaron can, bana so! karki sake maganarsa a gidana, ni ba akan shi nake magana ba, akan ƙyale ni da kika yi.”

“Ba ƙyaleka na yi ba wallahi Allah..” 

“To me kika yi?” 

“Bakomai, kawai bana so ma cika takura ma a yadda kake ranka babu daɗi.” 

Jawoni ya yi kusa da shi, sannan ya ce. 

“Ni na taɓa ce miki kina takura min?” 

“A’a ba ka ce ba.” 

“To me ya sa kika yi wannan tunanin?” 

Na yi shiru na rasa amsar da zan bashi. “Uhm? Magana nake.” 

“Kawai.” 

Kawai me?” 

Ya faɗa yana miƙewa tare da ni zuwa ɗaki, ya ajiye ni kan gado ya hawo. 

“Ina tambayarki?” 

“Ba kowa.” 

“Tom.” 

Ya faɗa yana matseni a jikinsa, tun zamana a gidansa kusan wata huɗu yau ce rana ta farko da wani abu na aure ya shiga tsakanina da shi. sardauna ya zauna da nine kaiwa yana kallona kuma yana ba ni kula, sai a wannan ranar nagane aure da wata wahalal shi da ake faɗa. 

Tun daga wannan lokacin zamanmu da Sardauna ya canja taku, da ba ya nuna sha’awarsa a kaina, amm yanzu kullum ne, ɗaiɗaikon rana kune yake fashi. Tun ina jin wahala da azaba har komai ya wuce. Irin azabar da na sha a ranar ta mantar da ni zance jarabawa ta sai da aka kwana biyu sannan na tuna, shima sakamakon wayar da muka yi da Ra’is yake ce min na ba shi number exam card ɗina zai duba min, Jamb kuma na yi wa mijina magana ya yi min Regostration. 

Da dadare bayan ya dawo na faɗa masa amma dai ya yi banza da ni kamar bai ji ba, haka aka kwana ɗaya aka kwana biyu shiru bai sake min maganar ba, a kwana na uku na yanke shawarar ƙara tun kararsa da maganar, sai dai a lokacin ma banza ya yi da ni. 

Washe gari Ra’is ya zo mun da sakamakona na WAEC da NECO na yi ta murna ganin result ɗin, ya ce da ni wai Abba ya fara tambaya akan wai na yi rijistar JAMB ko banyi ba, kar su rufe. 

Lokaci na farko da na fara yi wa wani na gidanmu ƙarya akan al’amuran gidan aure. 

“Ra’is ban masa maganar ba, kwana biyu suna aiki a kamfaninsu ne, bai ma cika dawowa da wuri ba, amma in sha Allah zan faɗa masa.” 

“Tom yakamata dai gaskiyya, kinsan su Jamb ba wani dogon lokaci suke badawa ba fa.” 

“Nasani sosai, ina Yaya Ridwan?” 

“Yana nan.” 

“Baice ka gaisheni ba? Shi fa bai taɓa zuwa ba. Kuma ya je duk  gidansu Yaya Radiya.” 

“To ai su yayunsa ne, ke kuma ƙanwarsa ce. Yaya Radiya ma tana gida.” 

“Zuwa ta yi?”

“Eyh, ta kwana biyu ma.” 

“Tafiya mijin na ta ya yi?” 

“A’a saɓani suka samu da shi, wai yana da wata matar a waje.” 

“Mata a waje? Yau she ya yi auren ba mu sani ba?” 

“Bawai matar aure ba, abokiyar iskanci.” 

Kama baki na yi sannan na ce. “Lallai chaɓ.”

“Jiya kuma Hajja ta zo ta sauke kwandon rashin mutuncinta tsaf a gidan.” 

“Da aka yi mata me? Ita kuma.”

“Wai ai Yaya ce ba tasan mene darajar miji ba shi ya sa ya fita ya nemi wata.” 

Na yi matuƙar mamakin jin wannan abun, ko da yake a son zuciya irin na Hajja inda za a bata kuɗi ta bataƙi ko kisa aka yi ba ta ce, wanda ya mutum shi ya taso ya kashe wanda ya yi kisan.

“Ita ta sani, yanzu mai Alhaji ya ce?” 

“Ita Yaya ta ce ba zata koma ba, haka kawai ya kwaso wata cutar ya goga mata.” 

“Wallahi Allah da gaskiyyarta, kuma ko ya ce zai daina ba lallai ya daina ba tun da daman ba mutunci ne da shi ba.” 

Na faɗa daman ni tun da ba gaisawa ma muke da shi ba. 

“Haka Yaya Ridwan ya faɗa, ya ce ko kotu ne sai anje an raba auren.” 

“Uhm, ni kaɗai ce Yaya Ridwan ba ya so.” 

Kallona Ra’is ya yi sannan ya ce. 

“Waya faɗa miki haka?” 

“Ra’is alamunsa na gani, kana ganin ko Allah Ya sanya alheri bai yi min ba, kai ko gidana bai taɓa zuwa ba, farkon aure na da na kirashi da ya ɗaga ya ji ni ce sai ya katse.” 

“Kinsan halinsa dai.” 

Ra’is ya faɗa yana miƙewa. “Ni zan tafi.” 

“Tsaya na baka abu ka kaiwa Hajiya.”

Na faɗa ina shigewa ɗaki, na ɗauko wata leda da daman na ajiyeya na ba shi ya tafi sannan shima na bashi dubu bakwai, wanda shine kuɗina gaba ɗaya. 

Ko da Sardauna ya dawo sai da ya tambayeni waye ya zo? Na yi mamaki sosai na yadda akayi ya sani, shi ba camera ce da shi ba amma ya sani, ko da na ce masa Ra’is ne bai wani saki fuska ba. Bayan ya ci abinci na ɗauko masa takardar da Ra’is ɗin ya ciro ya kawo min, buɗar bakinsa sai cewa ya yi. 

“Kun dage dai sai kin yi karatun ko?” 

“Alhaji yana so kasani kaima.” 

“Uhm.” 

Ya faɗa ya ci gaba da danna wayarsa, ni kuma na zauna ina wasa da ƙafarsa. Sai da aka kwana biyar da maganar sannan Sardauna ya kai ni wajen Rijsitar jamb, shima sai da na sake masa magana sannan ya kai ni. 

Masu kuɗi basu da al’adar zuwa gidan mutane, amma kuma suna da kirki idan anje musu, duk ranar da mukaje gidan Hajiyarsu kamar zata cinye ni sabida kulawa ita da ƙannensa, haka idan na kiranta a waya shima kamar zata goyani, duk mutan gidansu suna sona sosai idan na je musu, sau ɗaya ƙanwarsa Lubna ta zo shima daga lectures ta dawo shine ta biyo. 

Haka lokacin zana jarabarwar Jamb ya zo Sardauna ya kai ni na yi, idan na sami maki 189 na ji daɗi sosai domin zan sami Addmission a FUD, haka a gida kowa ya ji daɗi ya yi murna. 

A lamarin Yaya Radiya kam, ta dage ba zata koma ba, haka Yaya Ridwan ma domin sun binciko asali ba iya wannan abun ba ne ya baro ta gidan, bayan neman mata harda shaye shaye yake yi, shima dalilin da ya sa su ka gano wata rana ne yazo gidan namu a buge ya yi wa musu tijara da hau na ƙarshe, ya ci musu mutunci sai da Ra’is da Yaya Ridwan suka fita dashi. Amma da Hajja ta zo yin ta ta tijirar sai cewa ta yi an dake shi an ji masa rauni. A yanzu Alhaji ya daina damuwa da abubuwan Hajja tsakanin shi da ita sai dai tom, amma ya faɗa mata a wannan maganar ba yadda ya iya tun da yarinya da ‘yan uwanta sun dage akan ba zata koma ba. Sardauna ya ɗan san maganar tsilli tsilli ban saki jiki na faɗa mai komai ba, tun da naga kamar bai son maganar. Da kan sa ya kaini gidan Anty Adiza har sau biyu a cewarsa duk ranar da na je ina samu sabon ilimin sarrafa fulawa. 

Kwance ta shi ba wuya a wajen Allah har aka zo lokacin da jami’a ta fara raba Addmission, kuma ina cikin mutanen da suka samu a lokacin farko. Alhaji bai taɓa zuwa gidana ba sai a lokacin ya zo ya yi wa Sardauna godiya akai, daga nan na fara shirye shiryen makaranta sai dai har zuwa wannan lokacin babu ciki a jikina, tun ina ɓoyewa har abim ya fara damuna, har na fara sanar da Sardauna amma sai ya ce shi haka yake so, da ya ga dai na fara damuwa da al’amarin bisa ga auren Malaika da akayi bayan namu, ta tafi jihar kano kuma a yanzu ta sanar da ni cikinta ya shiga watan haihuwa. Hakan ya sa na sake damuwa, sai shima ya fara nuna damuwarsa, yake kuma kwantar min da hankali. Da dai ya ga abun namu ba ƙarami ba ne sai ya ce na shirya zai kai ni naga likita. Rasheed shekoni special hospital ya kaini, asibiti da na yi ma sa gani na biyu a rayuwata, lokacin da mai mashin ya tsaya gyara. Kai tsahe wajem likitan muka je wanda daga yanayinsu kasan abokinsa sa ne, bayan ya yi masa bayani likitan ya sa na kwanta akan wani gado anan ya yi dube duben da zai yi sannan ya ce na koma na zauna. 

Kusan mintina goma sha biyar, sannan ya fara bayani. “Madam mahaifar ta yi ƙanƙanta ne da ɗaukan ciki, amma kuma yau da gobe ya sa ta fara girma, idan kika yi haƙuri kuma kin zuwa ganin likita in sha Allah za ta buɗe.” 

“To wane magani za’a ba ni.” 

“A’a babu magani fa.” 

“A’a a bata wannan pils din mana.” 

Sardauna ya faɗa, wani kallo na ga Dr ya yi masa sannan ya ce. 

“Ai zai yi mata ƙarfi, sai dai a dinga ba ta sha sau daya ko biyu a wata.” 

“Eyh hakan ma ya yi.” 

Sardauna ya faɗa, sannan ya dafa ni yana faɗin. 

“Nana ki daina damuwa kin ji ko, rashim haihuwar ba matsala ba ne.” 

Na gyaɗa masa kai, sannan ya ce. 

“Ki jirani a mota.” 

Na miƙe na fice na barsu a cikin ofis ɗin, ina fitowa waya ta ta hau ruri, ina dubawa na ga sunan Ra’is na ɗaga da faɗin. 

“Ra’is ya aka yi?” 

“An raba auren Yaya Radiya fa.” 

Gaba ɗaya sai na ji wani iri, Allah ya gani ina matuƙar tsoron mutuwar aure a rayuwata. 

“Yaushe?” 

“Shekaran jiya Hajiyarsa ta zo ta yi wa Hajiya rashin arziƙi. Yaya Ridwan ya sa ‘yan sanda suka kamata, amma a ranar aka sake ta shine ɗazu ya aiko da takardar.” 

“Ka ce tashin hankali aka yi kenan? Allah Ya tsare gaba zan shigo in sha Allah.” 

“Amin amin, ya shirin makaranta?” 

“Ranar monday zamu fara lectures.” 

“Allah Ya sa albarka.” 

“Amin amin.” 

Daga haka na katse wayar na shiga mota na jira Sardauna, sai da ya ɗau wajen mintina ashirin sannan ya fito, a hanya nake sanar da shi mutuwar auren Yaya Radiya, ya tausaya har muka koma gida. 


Ranar Monday ranar da zan fara lectures Sardauna ya tashi baya jindaɗi kwata kwata, ta dole na haƙura da makarantar ban je, sabida bai samu kansa ba sai wajen sha biyu na rana. Haka washe gari ma ya tashi da irin ciwon, gaba ɗaya na ruɗe kamar shafar aljanu, duk asuba idan ya fara juye juye bai nutsuwa sai rana ta fito, kusan sati biyu a haka, ta dole na haƙura da makarantar sabida lafiyar mijina tafi min komai a duniya, har da ni kaina. 

Legendspen
***.