Chapter --- 11
Bismillahir Rahmanir Raheem
***Namiji Ƙanin Ajali***
By
(Amdy Tejj d'Unique)
Page----1️⃣1️⃣.
Da wani murmushin farin ciki wanda tun daga zuciyata take fitowa tare da wani fata nace"shikenan sai ka dawo kaima ka kula"da murmushi ya mayar min sannan ya juya ya tafi Ni kuma na tsaya ina binshi da kallo ina murmushi kamar wata gaula sai da ya ɓace min kafin na juya na hango wata yarinya wacca muka siya kamu a wun yayarta a cikin tashar,ita na tambaya sunan tashar ta gaya min kafin na ɗau hanyar da bansan ina ne ba.
Haka na hau bara baji ba gani,inyi nan inyi can,bani a cikin gari bani a wajenta,da haka har nazo wani kwalta na samu wasu mabarata da yawa a zaune a wajen wata bishiya mai yalwar inuwa suna zaune masu wucewa wasu su basu sadaka wasu su wuce, idan mota ta tsaya a wajen ko go slow ya tsaida ta,haka za'ayiwa motocin rumfa kowa na miƙa hanu,haka nima na shiga cikinsu kasancewar lokacin azahar ya wuce,a wajen na samu damar yi ina hango mai pure water na kirata na siya guda uku na sha ɗaya nayi alwala ɗayan na ba matar dake gefena, bayan nayi alwala na shimfida ɗan kwalina nayi Sallah banyi wata doguwar addu'a ba dan bani da natsuwa,a haka muna zaune har la'asar nayi sallah, nidai daga yaran har manyan banga wacce tayi sallah ba,da har zanyi magana na tuna ba hurimina bane dan akwai wacca tayi jika ma dani, balle ince yara ne basu da hankali,ina zaune ina tunani wai ni yau nake bara hmmmm na tuno asalina, na tuno gidan da na fito,na tuno waceceni, amma soyayya tasa na manta da duk wannan yanzu idan gidanmu sukaji wannan labarin wai ni naje bara ya kenan, zuciyata ta karye hawaye suka cika min ido,jin ina neman karya wa kaina ƙwarin gwiwar da nake dashi yasa nayi saurin kau da tunanin,wata mota baƙa mai baƙaƙen glass data faka a wajen ne ya dauki hankalin wasu daga cikinmu sai dai banga kowa yaje ba yasa nima ban tashi ba,motar ta ɗauki mintina kafin a sauke gilashinta daga inda nake bana iya hango na ciki kuma ban damu hangowar ba to mai ma zaisa in damu ina ruwana dashi na sanshi ne,ina wannan tunanin ne naga wani ɗan dattijo daga cikinmu ya miƙe ya nufi motar sai dai ba wanda ya bishi da alama dai ina ganin su suka kirashi ,wani tunanin can ya ɗaukemin hankali dan ƙawata kenan kullum,bansan sanda suka gama ba,magana naji akaina na ɗago na kalle me maganar dattijon ɗazun nanne na kai kallo na inda motar take,ta tafi ban masan ta tafi ba,da sauri na amsa da"na'am baba"dan a tunanina yazo kawo min nawa kason ne,ƙila mutumin baya son hayaniya shiyasa ya bashi kawai ya raba mana,amma sai naji abinda ban taɓa tunani ba tambayata yake wai ina lasisin yin bara na?,tofa nan kaina ya kulle to wai dama bara sai kana da lasisine kakeyi?na tambayi kaina a zuciyata, tambayar da bani da amsa bani da dalilin ta,dan ban sani ba,a ɗan diriri nace"ai bansan sai kana da lasisine zakayi baran ba" a yatsine ya kalleni sannan yae ce "ohh kin raina baran kenan,to itama sana'a ce kamar ko wanne dan haka sai kinyi ragista"ya faɗi register cike da rashin iya faɗa, mamaki ya kamani na ma rasa abin faɗa,yo dole ai narasa abun faɗa.
"Ki tashi kibar nan tun wuri dan kowa da kika ganshi anan yana da katin shaida na bara anan”
Kafin ya ƙarasa nayi saurin tareshi da faɗin "dan Allah baba ka taimaka mahaifiyata ce ba lafiya na fito barannan kada koreni,ka faɗamin inda zanje inyi registern sai inje inyi"hmmm bari in taƙaice muku wannan mutumi da zan kirashi da mara imani a tashin farko bai barni ba duk irin magiyar da nayi mai sai da ya koreni,a cikinsu aka rasa mai tayani bashi haƙuri...
Haka na dau hanya ba tare da nasan inda dosa ba, tafiya kawai nake ba tare da nasan inane nan ɗin ba, nasha tafiya sosai kan hanyar,kaina cike da tunanin da ni kaina bansan tunanin me nake ba,bararma na kasa mamaki nake yadda talakawa ma ajunansu basa tausayin junansu nake,nama rasa ma'aunin auna wannan abu,amma ai ɗazu ya ganni ya bai koreni ba ɗazun bai gane ki bane zuciyata ta bani amsa,nayi shiru na kasa tunanin komai, ganin tunanin bazai kaini ba gashi dama yamma ya riga yayi yasa na tari nape na hau na faɗa masa sunan tashar da zai kaini ya ɗauki hanya,bamu jima muna tafiya muka isa ashema nayi kusa da tashar rashin sani ne kawai,na fito na bashi kuɗinshi na shige ciki,na hango Habibu a wajen wata bishiya zaune shida wasu mutane suna hira,har Habibu ya dawo kenan? na tambayi kaina, tambayar da bani da amsa,ban kawo komai a raina ba na ƙarasa shiga ciki kasancewar suna da yawa kuma dukansu maza ne yasa ban ƙarasa inda suke ba,ganina yasa ya taso ya ƙaraso inda nake"kin dawo?"
Ya tambaye ni na bashi amsa da"eh naga ai kai ka rigani na dawowa ma"
"Eh Wallahi ban dade da dawowa ba nima,nayi tunanin kin dawo ne shiyasa na dawo dan karki zauna ke kadai,dan nasan ba shiga cikin mutane zakiyi ba"na danyi murmushin jin dadi,dan komai kashin kulawa habibu ya nuna min inajin daɗi,bance komai ba muka ƙarasa jikin wata bishiya muka zauna,ya kalleni sannan yace"Nagode Haula, Nagode da Allah ya bani ke"
Na kalleshi nace"to godiyar ta miye kuma?"
"Wallahi Haula ba kowa Allah ke bashi irin kyautar da ya bani sai mai dace"ya faɗa wanda nake da yaƙinin da zallar gaskiyarsa yake magana
Nasan Habibu yana sona kuma so mai tsanani wannan hargitsin da muke ciki ne kawai yasa yake wasu abubuwan, kuma ina rokon Allah ya daidaita mana lamura mu dawo kamar dahhh,duk da inhar da ƴan uwansa bazan taɓa samun yadda nake soba, amma ba komai dan ba soyayyarsu nake buƙata ba ta mijina nake so,kuma dama ba komai da kake so kake samu ɗari bisa ɗari ba,na saki murmushi akaro na ba adadi sannan nace"to indai godiyace daga gare ka bana buƙata dan da Haula da komai nata mallakar Habibu ce"
Zaiyi magana nayi sauri nace"indai kalmar da zaka faɗa ta alaƙantu da godiya Please"
Yayi dariya sannan yace "Haula-Habib kenan wato har kin harbo abinda ke cikin zuciyar gwarzon naki ko?"na sake sakin murmushi dan ni ban fiye dariya sosai ba,ba wai dan bani sakin fuska ko walwala ba kawai yanayi na kenan,daga haka muka ɓarke da hirar soyayya cikin nishadi da jin dadi kamar bamu da wata matsala a duniya,duniyar taimin faɗi kamar muka ɗaine a cikinta,ba dan wulgawar mutane da nake suke tuna min ba a gida muke ba,da an tafka dan ba abinda zai hanani rungumarsa......
Kuyi haƙuri ku dakaceni anan sai mun haɗu daku a page na gaba.nagode da bani lokutanku da kukayi dan karatu...
Ina alfahari daku...
Ku cigaba da kasance dani Amdeey naku Bye Bye.