Chapter 20
🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 20
“Ki fito.” Ya sake furtawa a karo na biyu, fuskarsa babu alamar rangwame, razannanun idanuwansa kafe cikin nata da ta suka juye saboda tashin hankali, yayinda a zuciyarsa yake jinjinawa karfin halin yarinyar. Dakyar ta bude bakinta da ya bushe ƙamas, muryarta na ɗan rawa ta ce “Su waye ku? Me ku ke so a gare ni? Me na yi... “Fito na ce.” ya katse ta da cewa cikin tsawa mai firgitarwa tare da dukan saman motar a fusace. Sai da ta saki ɗan guntun fitsari tsabar razani, sai dai kafiya irin tata, maimakon ta fito sai ta sake shigewa can karshen motar ta maƙure tana faɗin, “Ba zan fito ba, ai ban maku komai ba, ni ku mayar da ni gida.” Duk yadda yake daure wa ya riƙe fushinsa kasa jurewa ya yi wannan karon, a fusace ya zagaya ta bangaren da ta koma, ya bude tare da fincikota waje, ya hade hannyaneta waje guda ya yi mata riƙon maza, ya shiga janta da karfi tana turjewa, tare da faɗin “Ka kyale ni.” bai saurareta ba, sai da ya danganata da ƙofar rantsattsen grand two-storey mansion ɗin da ke farkon gidan wanda ya fi kowanne gini da ke cikin harabar gidan girma da haɗuwa. Ba tare da ya saki hannunta ba, ya mika hannunsa ɗaya ya dannan wasu madannai dake jikin kofar wajen, take ta bude bayan ta yi scan na fuska da yatsarsa. Hankaɗata ciki ya yi har sai da ta kusa kifawa, bai ɓata lokaci ba ya mayar da kofar ya rufe ta waje. A kunneta motarsu ta bar cikin gidan a guje, take wani irin shiru ya ratsa ƙwaƙwalwarta, tabbacin babu wani mahalukin dake motsi a cikin gidan sai ita rak.
Ƙafafunta ne suka ɗauki rawa, tsoro da tashin hankalin da take dannewa da karfin tsiya suka bayyana a kan fuskarta, motsi ta ji daga bayanta hakan yasa ta juya a tsorace da bala'in sauri, babu kowa sai iska dake ƙada fararen labulayen da ke kewaye da falon, rarraba idanunta ta shiga yi a wargajejen falon da ba shi da wadataccen haske. tsananin girmansa yasa ta ga kamar yana juya mata take ta zube ƙasa tare da fashe da wani irin kuka, ji ta yi sautin muryarta ya karaɗe falon tamkar wacce ta yi magana a amsa kuwwa, hakan ya karasa rikitata ta yi saurin dunkulewa waje guda ta cusa kanta cikin ƙafafunta jikinta na rawa kamar kazar da tasha dukan ruwan sama.
Kamar wasa karamar magana ta zama babba, tun su Salman na saka ran ganin Aysha a kusa har lamarin ya fara ba su tsoro, domin babu inda ba su duba a ciki da wajen gidan ba, Suraj da megadi tuni suka bazama cikin Estate da makota. yayinda Salmah da Salman su ka shiga rige-rigen kiran layinta, yana ringing amma har ya katse ba a ɗagawa, Mother kan ta hankalinta ya tashi sosai, ta kasa zaune ta kasa tsaye, musamman idan ta tuna yanda ƙasa ta lalace da sace-sacen mutane ga kidnaping da ake yi yanzu na isa da mallaka har makwancin mutum ake binsa a sace, to balle wannan da akan hanya take, amma da tana kyautata zaton in sha Allah ba wata gagarumar matsala bace domin Estate ɗin su a kwai tsaro duk wanda wanda ya shiga ya fita ana da record ɗinsa infact ba ma kowanne irin abin hawa ake bari ya shiga wajen ba sai yantattu, idan kuma moto ko keken haya ne sai mai register.
“To ko dai gida ta tafi?” Salman ya faɗa yana kallon Salmah da a karo na ba adadi ta kara wayarta dake ringing a kunne tana tsammanin jiran a ɗaga. Da sauri ta kallesa, sai kuma ta girgiza kai, ta ce “ Bana tunanin haka, Aysha ba za ta tafi gida sai dai idan da wata matsalar.” “To ko za mu kira Ammie mu tambaya.” “A'a kar ku kira ku ɗaga musu hankali, mu dai kara duba ta tukuna, Khairan in Sha Allah.” Cewar Mother, Salmah ta bude baki za ta yi magana, Suraj da megadi suka shigo tare da megadin makotansu, wanda shine ya yi musu gamsasshen bayani game da ganin da ya yi mata ta tari keke napep ta hau, nan suka dinga jero masa tambayoyi game da yanayinta har ma da shigar jikinta, yana amsa musu daidai, hakan ya kara basu tabbacin tabbas ita ɗin ce. Ajiyar zuciyar samun natsuwa Salmah ta sauke ta daura da faɗin “ To amma me ke faruwa me yasa Aysha za ta yi haka?” Salman ne ya amsa mata “Ki kwantar da hankalinki, kin fi kowa sanin wace ce ita, duk ma abinda ya sanya ta hakan to dalilinta mai karfi ne.” Gyaɗa kai ta yi ta ce, “Kuma haka ne.” Da wannan tunanin suka samu karfin gwiwar komawa cikin gidan suka ci gaba da sabgoginsu bisa umarnin Mother da ta sake kwantar masu da hankali da kalamanta masu taushi...
Aysha ta dade a dunkule a tsakiyar falon, cikin wannan yanayin ba tare da iya ko ɗaga kai ba balle ta sake kallon inda take, jiran tsammani kawai take yi, ta Allah ta kasance, don tana da tabbacin tata ta kare ta san dai wadannan ba masu garkuwa da mutane ba, yan mafiya ne, ko masu safaran sassan jikin ɗan adam, kuma a irin wannan gida da ake yi wa laƙabi da ihunka banza, ta tabbatar babu wanda zai ji ta balle ya kawo mata dauki sai Allah, gashi harshenta ya yi nauyi kamar an daure mata Allahn ma ta kasa kira, ko numfashi bata iya saukewa da kyau balle ta bude baki, hawaye kuwa zuba suke kamar lalatacce famfo. Kamar daga sama sautinkiran sallar azahar ya ratsa kunnuwanta, wani irin numfashi mai karfi ta ja ta fesar sai kuma ta shiga ajiyar zuciya ta dinga saukewa a jejjere tana jin wata irin nutsuwa na ratsata, tsoron na ɗan raguwa, zuciyarta na karfafa, hakan ya bata damar kama sunan Allah tana ambata. Sannu a hankali komai ya fara lafawa, kamar wacce ake yi wa umarni ta fara ɗago kanta a hankali, abinda ya bata mamaki haske ya cika ɗakin duk fitilu a kunkkune ba kamar ɗazu da babu haske sai wanda ke ratsowa ta window ba, wannan yasa tsoron da ta kasance ciki a ɗazu a yayinda take bin falon da kallo ya ragu kaso hamsin cikin ɗari. Tsananin tsaruwar falon yaso shagaltar da ita har ta so manta halin tsaka mai wuyar da take ciki, domin za ta iya yin rantsuwa tunda take a duniya bata taɓa shiga kayataccen falon da ya yi kyaun wannan ba. Kamar wawiya ta shiga bin ko ina da kallo tun tana ɗari ɗari har ta saki jiki tana kallon aljannar duniya, ko ina fes fes babu alamar kura ko ɗaya, da alamar ana rayuwa a cikin falon sa'i da lokaci. “Ina ne nan? Wane ne ya sanya a ɗauko ta, me ta yi masa me yake nema a gareta?.” waɗan nan sune tambayoyin da suka dinga yawo a kwakwalwarta, sai dai kafin ta samu zarafin hade su a bigire ɗaya ta canki amsarta, idanuwanta suka sauka akan abinda ya sanya ta miƙewa tsaye tana zaro ido cikin tashin hankali, wani katon frame ne manne daga bangon gabas na falon, ji ta yi kawai tana tafiya zuwa gareshi ba tare da ta iya sarrafa ƙafafunta ba, a gabashi ta tsaya, tana bin fuskar wanda ke jikin hoton da kallo, “Ba...ban...gi...da.” Ta furta a rarrabe yayinda ta kai hannu tana shafa hoton, duk da ba asalin hoto bane zane ne, babu abinda ya raba mutumin dake jikin hoto da Babangidanta a zahiri, sanye yake cikin rigar saƙi ta Fulani, kanshi sanye da malfa ya dogara sandarsa da ya rike da hannunsa mai lafiya a ƙasa cikin ciyayi, yayinda ɗaya hannun nasa na dama ake dauke da daurin karaya irinta gargajiya, na saƙale masa shi a wuya kamar dai yadda ake daurin hannu, fuskarsa dauke da sassanyar murmushi. Kanta ne ya shiga juyawa jiri na neman watsar da ita, “Innalillahi wa Inna ilahi raji'un, na shiga uku me ke shirin faruwa.” ta furta tana mai fashewa da kuka, hoton da ke gaba kaɗan da wannan ta kalla, nan ne ta ga abinda ya tsayar mata da numfashi na hucin gadi, shima zane ne, na mutum biyu mace da namiji zaune cikin ciyayi gabansu shanaye ne na kiwo alamar shi su ke yi, duk da sun juya baya, za ta iya shaida su, ita ce, tabbas ita ce tare da shi, a wani lokaci mai tsayi, kamar zararriya ta shiga bin duk frame din dake manne a falon tana kallo, yayinda kuka ya ƙi barin idanunta, memories din komai na dawo mata a kai, zuciyarta ta yi nauyi ta kasa gane abinda take ji game da ganin waɗan nan hotunan, wani abu ne matacce ke kokarin rayuwa a zuciyarta, ta sani har abadan da'iman ba za ta ɓata daina son Babangida ba, amma kuma ba za ta iya yafe masa ma domin ya cutar da ita. “Me take yi a nan, me yasa suka dauko ta, kenan shi yasa a dauko, kenan yasan inda take ya san tana nemansa tsayin shekara takwas ya san ta bar gida ta rabu da iyayenta duk saboda shi, me yasa ya boye bai bayyana mata kansa ba.” abinda ta dinga fada kenan a zuciyarta, bayan ta koma ta zube a tsakiyar falon, “Saboda mugun ne, ɗan mafiya ne mai safaran sassan jikin yan Adam ne.” Wani ɓari na zuciyarta ya bata amsa, da sauri ta girgiza tare da faɗin “A'a ba mugu ba ne.“ sai kuma mike a guje ta nufi kofar fita daga falon tana bubbugawa da karfi tana faɗin, “Ku buɗe ni, ku sanar da ni a inda nake, kaina yana juyawa.” numfashinta ne ya tsaya cak, ta yi baya kaɗan sai kuma ta sulale a bakin kofar ta kwanta idanuta suka rufe ruf...
Lumshe idanunsa da suke rine ya yi bayan ya gama sauraren jawabin da Giɗaɗo da ya gama yi masa, ba tare da ya furta komai ba. Cikin salon karfafa gwiwa da son kwantar masa da hankali Giɗado ya matsa kusa da yi, ya ce “ Megida ka yi hakuri ka yi imani ka kwantar da hankalinka, In Sha Allahu za su bayyana nan kusa, ko a jawabin da na baka ya kamata ka saka yakini ka fahimci an fara samun haske a cikin wannan lamarin, Allah yana tare da kai, kuma zai wanke ka gaskiya za ta bayyana, addu'a bata faduwa kasa a banza in dai mutum ya yi ta da cikakkiyar yaƙini.” “Hakuri na ya kusa karewa ne Giɗaɗo, a kwai cutarwa a lamarin, ba zan iya jurar ci gaba da ganin hawaye ta ba, kuma ina tsananin jin kunyarta, ba zan iya fuskantar a haka ba.” “ Ka daure komai ya kusa zuwa karshe.” sun dade suna tattaunawa da Giɗaɗo yana kara yi masa bayani akan ci gaban da suka samu, kuma ya gamsu sosai ya yi masa alheri, sannan ya dumbuza masa kudi masu kauri akan a je a ci gaba da roƙon Allah. A tare su ka yi sallar la'asar, kafin suka fito daga Palace, nan kuma ya tarar da mutanensu yan siyasa, manya ne da yake matukar jin nauyin su, domin yawancinsu abokan Abba ne, duk da ba shi da appointment da su haka ya tsaya ya sauraresu ba shi ya samu kansa ba sai wuraren karfe 6 na yamma.
Fitowa ya yi domin tafiya gida, sai lokacin ya duba wayarsa, a nan ya tare da missed Calls da yawa na Mother, dana Jarumi sai na Abba, a kan na Jarumi ya tsayar da idanunsa, zuciyarsa na tunano masa da ajiyar da ya sanya suka yi masa na wancen yarinyar, rintse idanu ya yi da karfi ya buɗe, sai kuma ya karya kan motarsa ya kama hanyar sabon gidansa dake By pass bayan ya kira su Ussy a kan su haɗu a can.
Assalamu alaikum mutanen arziki, sannunku da jumurin bibiyata a cikin wannan labari nawa mai taken haɗin kaddara, a yadda na tsara hadin kaddara book 1 zai kare ne a iya page 20, wanda iya shine free, yayinda book 2 nasa zai zo mana a matsayin paid in Sha Allah, to duba da sha'afa da na yi wajen sanar muku da hakan, zan ƙara five pages a kan wannan, amma kafin nan, duk wanda yake so a yi tafiyar Book 2 da shi, zai iya yin payment tun yanzu domin a saka shi a paid group wanda a shi kaɗai ne zan ci gaba da posting sai kuma Arewapen, kuɗin karatun littafin 1k ne, amma ga wanɗan da suka shirya biya kafin mu kammala book 1, za su iya biyan 800₦ ta wannan account ɗin, 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, sai ka tura min shaidar biya ta pravate, idan na fara book 2, za ku biya normal price 1k Nagode sosai.