KUDURAR ALLAH

Page 1

by @zahrawriter12

Bauchi unguwar dutsen tenshi.

Unguwace ta masu k'aramin k'arfi wanda suke da wadatar zuci,lungu ne wanda baida wasu wadatattun gidaje gida huɗu ne kawai acikin lungun. gidana karshe shine gidan daya fi kowanne lalacewa aciki.

Wani kyakykyawan dattijo ne wanda bazai gaza shekaru arba in da takwas zuwa hamsin ba yake k'ok'arin shiga gidan da yake da 'yar langa langar kofar gidan,ga dukkanin alamu bai da cikakkar lafiya, kafarsa yake takawa ! ahankali har yashige cikin dan matsakaicin tsakar gidan Wanda yake share Kal tamkar ba kasance na 'kasa ba, sai zabga kamshin kasa yake.

Sallama yayi cikin wata kimtsatstsiyar murya da sauri ya karasa cikin wani karamin ɗaki dan jiyo sheshshekar kukan da yayi kutsa Kansa yayi cikin ɗakin gami da ambatan sunanta " Fatima Bintu subhanallahi !"da sauri ya ajiye ledar dake hannunsa cikin tsananin damuwa yasa hannu ya dago kanta.

Kyakykyawar yarinyace me cike da wata irin baiwa da ilhama Wanda Rabbi ya bata, fuskarta me cike da kwarjini ta dago tare da zubawa mahaifin nata idanunta masu tsananin sheki.

Cikin sautin muryarta me sanyi da dadin amo tace" Fafi fafi Ina katafi kabarni ? Inajin tsoro fafi kadena fita Ina matukar jin tsoran rasaka kabarni in fita Mana ni naje nasamo abin da zamu ci dan Allah fafi na rokeka karkasake fita zanyi duk abunda ya dace kaji fafina!". ta karasa maganar Tana mai hade hannuwanta biyu.

Wani zazzafan numfashi ya fesar sannan cikin lallama yace.

" Haba Bintu dani da ke wayafi cancanta da ya fita?ko kin manta keɗin macece me rauni ? Bintu kisani cewa babu wani abun tsoro sai Allah karki da aranki wani zai cutar dake face abinda Allah ya lamunce ya Zama kaddararki ke yarinya ce mafisoyuwa agareni lallaba rayuwarki nake Bintu kullum addu'ata Allah ya kauda idon Makiyaa akanki yakareminke tare da mahaifiyarki aduk inda take. "

Yana kaiwa Nan yayi saurin goge kwallar da ya cika idanunsa Mik'a Mata ledar hannunsa yayi tare da cewa "maza tashi ki jika Mana garin rogone nasan kina jin yunwa" sosai yana faɗa da murmushi afuskarsa dan samar Mata da nutsuwa, aiko itama murmushi ta saki Wanda hakan yakara fito da zahirin kyanta ga hakoranta da yar siririyar wushirya da Kuma lobawar kumatunta " Ma sha Allah !".haka papinta yace bayan ganin mik'ewarta tana murmushi.

*********

Abuja

Tamfatsetsen gida ne irin gidajen nan nakasashen waje Wanda aka ɗauko tsarinsa tundaga US azo aka ginashi idan ka shiga cikin ainahin cikin gidan anan aljannar duniyar take.

Birgima take tun karfinta tana Shure- shure tare da wani irin kuka me haɗe da ihu mutane, kusan goma ne akanta ana bata baki gami da rarrashi amma tamkar turata suke sai faɗin

"Wooo jixos ka taimakeni ka dawomin da yarona ina son nagan shi cikin Addinina fatash ka dawo hankalinka, katemaki mamanka kaji kaina ko sau ɗaya ne a rayuwa ban turaka karatu dan kasauya ba na turaka ne dan kaji k'aina kadubeni da kulawa amma Kuma gashinka dawo min da abinda zai iyasawa zuciyata ta buga bazan iya laukar wannan abun ba." sai ta kuma kecewa da wani irin gigitaccen kuka. Dattijo ne ɗan kimanin shekara hamsin da ɗoriya yake saukowa daga upstairs yana karasowa yayiwa mutanen falon alama da su fice, sum sum ɗaya bayan daya suka fita.

Zama yayi cikin k'awatattun kujerun da suka yiwa falon k'awanya Wani zazzafan kallo ya Willa Mata Wanda hakan yasa bashiri ta Mi'ke zaune tare da gyara zamanta dukda cewa Bata daina sheshshe'kar kukan ba.

Zuba Mata Ido yayi na Yan wasu dak'ika kana ya numfasa tare da huro iska daga bakinsa ya ce.

"Abigel kin kyauta kenan abinda Kika aikata kin tara mun jama a kina kokarin tona min asiri ko kina tunanin abunda ki kai zai canja shi daga Kan wannan ra'ayin nasa Kin manta waye shine ? Kin manta halaiyarsa ne? sirgiza Kansas yayi cikin takaici yace abigel Baki da tunani tunda harkika manta halaiyar wannan baudaddan Dan naki,se Kuma ya saki wani ɗan muafikin murmushi kana ya cigaba da cewa dama duk Wanda yase rariya yasan zata zubda ruwa muskutawa yadanyi Yana me hada hannayensa guri guda kana ya dubeta har yanzu hawayene suke satata daga idanunta, Shin kin manta baya ne ? Ko kin manta wahalar daya sha ahannun jams ? Kin manta ruɗanin da yasa kaki ? kin manta abinda yake Miki idan weekend yazagayo? Abigel be kamata ki manta duk wannan ba ballantana Kuma me Kan Kat yadda fatash be daukeki matsayin uwa ba".

Azabure ta kalleshi idanunta cike taf da kwalla tace " Na rok'eka kadaina faɗan wannan kalmar tacewa fatash bai kallona amatsayin uwa ". kallonta yayi ya ce.

" Ni dai yanzu shawara da zan baki ki sani duk abinda zakiyi ba fasawa zaiyi ba gara ki canja salo ko awannnan Karan Kya dace".

Yana gama faɗin haka ya Mik'e tare da haye wa sama.

Itama mik'ewa tayi cikin wani irin mutuwar jiki da wani irin fargaba dake yawan sawa zuciyarta na bugawa har haɗa Hanya take saboda yadda tsananin duhu ya mamaye idanunta.

Adai dai wannan lokacin Kuma awannnan rana ta juma' a, ranar da kowane musulmin k'warai keyin haramar tafiya masallaci.

Sai dai Kuma adaidai wannan lokacin ne wasu baragurbin dake cikin musulmai suka hada Kai da Makiya addinin Allah, suna Saɓa masa. Wata iriyar murya me tsananin Kara.....

*KUDURAR ALLAH*

*NA*

*Fatima y Adam*