KUDURAR ALLAH

page 3

by @zahrawriter12

Bismillahirrahmanirrahim

Zuri'ar alhj balarabe zuri'ace daza a'iyakiranta da babbar zuriya.

Ahline wanda yatara mutane kala kala masu hali da ban da ban dabi 'a kala da kala.

""Bazaka' iya fahimtar fuskar kowa ba bazaka iya, gane halin kowa ba me kyau ko mara kyau.

Gidan alhj balarabe, zuriyace guda daya amma yaarika kusan hudune agidan saboda aurataiya da ta hada.

Alhj balarabe balaraben maroko ne,kuma cikaken dan malamai dan abinnasu gadone. mahaifinsa babban malamine akasar ta maroko.

"Mahaifinsa malam habu da mahaifiyarsa nana Wanda' asalin sunanta shine' aishatu.

Asalin 'kaurarsu daga maroko, shine sanadin wata annoba da itace tayi sanadin kaurarsu zuwakasar nijer, daga nan suka sami masauki cikin kauyen agades.

Balarabe mutumne, me tsananin zuciya da kokarin neman nakansa,shiyasa beyi kasa agwiwaba ya, bazama neman sana'a.

Balarabe yayi sana' o'i da dama kama daga kayan gwanjo, kayan masarufi robobi da dai sauransu.

"Yawo yakeyi gari' gari kasa' kasa yana kokarin kafa kansa.

Alokacin da ya fara samun rufin asari se Kuma mahaifinsa yace !" yakamata yanemi yarinya me hankali ya aura,

an dauki dan lokaci kafun ya gabatar da wata kanwar abokokinsa, safiya cikakkar buzuwa ce gaba da baya, me ilmi da sanin yakamata ga hakuri da kau da kai,

Ba aja wani lokaciba aka daura aure' aka rufa, safiya' aka kaita gidanta wanda yake kusa da gidan iyayen mijinta.

Shekara daya da yin auren yabawa iyayensa amanar safiya' yace!" shifa bega ta zama ba dole ze tafi neman kudi, mahaifinsa be hanashi ba sede ya gargade sa da ya dinga zagayo gida saboda matarsa.

Haka kuwa balarabe ya, shiga duniya neman kudi Wanda be zauna ahaka ba ya se da ya hada da neman ilmin boko

Be manta da gida ba Dan yana zuwa yayi, kwanaki se ya koma, ahaka ya hada masters dinsa

Duk, fadi tashin da yake hakan besa ya manta da matarsa ba Yana me addu ar samun zuria ko sakara yawa dannyanaso yaga yatara zuri me yawa ko dan shi kadai ne oho?

Kwanci tashi balarabe ya samunrufin asiri har ya gina musu gida, shida iyayensa suka koma.

"Awata tafiya da yayi me duguri anan ya hadu da ya gana asalin babarbariya, kamar wasa se ga magana tayi karfi, rana daya balarabe yazo ya tafi da babansa da amininsa kuma makocin, su. aranar da sukaje washe gari aka daura auren suka juyo da amarya yagana.

Alhj balarabe yafara tara kadarori ga kuma zuria me albarka

"Bayan auren sa da yagana da wata biyu Allah ya albarkaceta da samun juna biyu, base na gaya muku irin murnar da, wannan' ahli sukayi ba, farinci kam iya farin ciki anyi awannan gida.

"Bayan watanni, yagana ta haifi yarta mace' akasa mata sunan iya nana wato aisha

Haka rayuwa tadinga gangarawa, kwanaki na zama watanni, watanni na zama shekaru yayin da arzikin alhj balarabe yake ta habaka, haka kuma yagana taketa ta hai famasa, yaya.

""Yayan yagana hudu kenan duk mata, ita kuwa safiya har lokacin Allah be kawo mata ba,

Alokacinne kuma alhj balarabe ya kwashi, iyalansa da iyayensa suka koma nageria saboda ya riga ya kafa sana o'insa acan. Yana da manyan shaguna akano cikin kasuwar kofar wanbai wanda ake sauke dilolin, kayan gwanjo da kuma, kasuwar saban gari nan ma runfunane dashi kusan guda bakwai duk na dilolin gwanjo. se kamfanin sarrafa roba acikin garin abuja shima guda uku. se kamfanin shinkafa da na fulawa.

""Wannan kadanne daga cikin dukiyar alhj balarabe.

Jigon dawowarsa nageria cikin garin abuja aiki yasamu ababbar kotun koli amatsayin alkali.

"Ambashi katan gida da motar hawa duk da Yana da nasa.

Daga nan rayuwa taci gaba da gungurawa alokcin yagana ta kuma, samun rabon da namiji.

Alhj balarabe ya kara auren wata abokiyar aikinsa me suna zainab, wayayyar mace yar gayu, ita kuma zainab bafulata nar yolace iyayenta da danginta duk suna yola, Se dan' uwanta guda daya daya kenan abj shida iyalansa. shine yasamar mata aiki anan kotun kolin ta abj

Matan alhj balarabe uku cas, yayin da mata biyu suke ta zazzago masa haihuwa, dan itama hjy zainab tuni ta jona da ya gana

"Ayanzu haka yagana yayanta shida hudu Mata biyu maza, yayin da zainab take da hudu duka mata ita kuwa hjy safiya' buzuwar agades har yan zu shiru Babu rabo.

Arziki fa se kara samun guri yake agidan alhj balarabe, dan' ayanzu shi kansa bazece ga' iya arzikin da yatara ba,

yayansa kuwa duk sun tasa babbar yarsa wadda suke Kira da nana,karama itace me she kara goma se kanne, wanda duk ba wani taza_ rane 'atsaka ninsu masu yawaba dan dukan su da yagana da zainab din, kwai' nika sukeyi, dan haka tazarar bata wuce shekara daya zuwa da rabi.

Cikin KUDURAR ALLAH hjy safiya' ta samu nata raban hakika alhj balarabe yayi farinciki tamkar ba ataba yi Masa haihuwa haka iyayensa mlm habu da nana sunyi, matukar farinciki da wan nan babbar kyauta ta, ubangiji.

Kwanci tashi Allah me KUDURA ya sauki safiya' lafiya wadda yara suke mata lakabi da hijiya babba, ta haifi santalelen danta me kama da ubansa sak, saboda farinciki alhj balarabe kyautar kujerar makka yadingayi tare da hadawa da manyan kudade masu auki, hakika farin cikin wannan bawan Allah baze misal tu, ba.

Abubakar yasamu soyayya ta wajen kakanni da kuma uba yaro mafi soyuwa acikin ahlinsa.

"Daga nan kuma haihuwa ta bude tabangaren hjy babba, wato safiya yar agades, takara haifar yan biyu mace da namiji se kuma namiji me suna, aliyu Usman nabi masa se Kuma auta Ibrahim, maza biyar mace daya KUDURAR ALLAH, kenan, seda sukayi nasu suka gama sannan ita kuma. tazo tayi nata har taso, ta wucesu.

Alhj balarabe,mutumne kamili, me tsananin riko da addini, me kokarin bin dokokin' Allah yana da, kyauta base lokacin zakka yake kyauta ba, kullum hannunsa abude suke akwai temakon addini, Yana kyautatawa iyalinsa balle kuma iyayensa,shi mutum ne me San gaskiya da fadin ta dan haka yake da farinjini cikin al umma talakawa sunyi kokarin jan ra ayinsa dan yatsaya musu amatsayin gwam nan jiharsu amma fir yace!" shi baze saka kansa aharkar da zatasa ya kauce hanya ba, dole haka suka hakura. Awannan tsukinne malam habu da matarsa nana sukace !"dole zasu koma gida, dan duba bayan ragowar yan' uwa, sede Kuma ashe ajali ne ya kirasu jirginda suka hau gaba daya ya tarwa tse' asakamakon birki da ya kwacewa matukin,

"hakika alhj balarabe yaji mutuwar iyayen nasa, sede dole ce, Kuma rigace ajikin kowa yadda, mukazo haka zamu koma.

Rayuwa taja, shekaru sun tafi, alhj balarabe ya samarwa yayansa in gan taccen ilmi na zamani da na boko.

"ya' aurar da nana karama ga dan babban amininsa, salisu se sakina da ya aurawa yaransa rufa' i

Alokacinne kuma'aka gama, gina babban estate dinsa wanda yakeso ya tasar da zuri' arsa ya hade su guri guda,duk kuma asannan ne yaje ya taho da danginsa na kasar maroko dan cika burin mahaifansa .

"Baffansa 'kani ga malam habu, se kanwarsu wadda ta kasance' auta' adakinsu, sune danginsa najiki tare da iyalansu.

"Baffa ali duk da ya tsufa amma' da dan kwarinsa , Se matarsa inna hafsatu, da da yayansa biyu,bab ban shine sa' an alhj balarabe sunansa hashir yana da matarsa daya yayansa uku se kaninsa me bi masa Mas' udu Shima matarsa daya da yaya hudu ahmad da, sadi se kuma nadiya da maryam. anan yazo ya hadesu' awaje daya kowa da bangarensa, ya bawa ko wannensu abunyi,kana kuma yayansu ya sanya su amakarantu ya basu' ingantaccen ilmi babu nuna san kai ya dauki yayan yan' uwansa tamkar nasa na cikinsa.

Yayan hajiya yagana wadda' ake mata lakabi da hajjah sune nana karama, sakina hafsa, bilki, mansur, habibu

Se yayan hajiya zainab ita kuma ana mata lakabi da inno, yaranta hudu mata sadiya,amina, zakiya, asiya

Yayan safiya yar agadex wadda ake mata lakabi da hjy babba,sune' abubakar, hasana da husaini, se aliyu, usman,

A yanzu gaba daya wadan nan iyali suna hade guri daya banda matan da sukayi aure awaje.

Tofa anzo gun, ku gyara. zama domin jin me ake shiryawa,ake kullawa? suwaye masu shiryawar ? suwaye bosa bosan cikin estate din alhj balarabe?

A, fage na gaba zamu zakuloka fatash dole ka fito muganka mujika ehe har yanzu ba'asoma wasanba.

Dattijon bauci fafin bintu anya kuwa kana da gaskiya? ammafa bani na fada fans din, KUDURAR ALLAH ne....

Comments........ Follow this link to join my WhatsApp group: ***

💕 *KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` ***

*_____________________________________*