KUDURAR ALLAH

Page 4

by @zahrawriter12

'Ya'yan alhj balarabe kaf dinsu, su goma sha biyar ne,maza takwas mata ta- ra, sai kuma na 'Yan uwansa hashir da mas'- udu guda uku-uku,

Alhj balarabe Yana da abokai ko nace aminai guda uku, wa'yanda yayi matukar yadda dasu abokaine na amana matuka da gaske, alhj kabir me auduga da alhj nasir sai alhj shams, amintar dake tsakanin su ne yasa har suka hada au re tsakanin 'ya'yansu, alhj kabir 'ya'yansa uku namiji daya mata biyu, sai alhj shamsu shi yaran sa biyu'amma 'kananu ne kasancewar basu fara haihuwa da wuri ba sai bayan shekara goma sha biyar, sannan allah ya ba su yara biyu duk maza, alhj nasir ma babban dan sa guda daya ragowar guda biyu duka yarane shima tunda'aka haifi' ila wato isma'il saida aka ja shekaru kana aka samu kannensa,

Ayanzu haka alhj balarabe ya dan man manyanta tunda har an fara aurar da jikoki amma baza ka taba gane haka ba, saboda tsufan alhj balarabe tsufane me kyau, wanda yake cikeda jin dadi gami da kwanci yar hankali, dan da 'kau yake,to baffansa Ali ma yake nan babu wata ta waya atare dashi sai na tsufa bare kuma shi da yake da manya 'ya'yan banki,

Nana karama babbar 'ya agurin alhj balarabe ya aurarta ga dan amininsa alhj kabir me suna salisu suna zaune suma acikin garin abj da yaransu hud u khadija, haulat da Fa'iz da kuma ahmad, sai sakina da rufa'i yaran babanta alhj balarabe su kuma suna kano shi ya ke rike da shagonsa na daban gari,'ya'yansu biyar mata biyu maza uku,

Sai hafsa ita kuma tana maidugu a 'bangaren mahaifiyarta tayi aure yaranta hudu itama duka mata rukayya fauziya kal tume da amina (amna)

Sai Kuma bilkisu da nura hashim,yaransu uku najib da najiba sai hauwa'u,

Habibu da saratu hashim yaransu hudu duk mata, farida zainab da sakinatu

Husaini da nadiya mas'u d 'ya'yansu biyu mace da namiji,

Ahmad da hasana yaran su uku duk maza nabil nazir da Kuma najib,

Amina da bashir yayansu su kuma kananu ne basu haihu da wuri ba yaransu hudu,

Zakiya kuma da dan alh nasir wato isma'il suma basu taba haihuwa suna nan cikin anguwar metama sule,

Acikin 'ya'yan alhj balarabe e wadan dan sune sukayi auren zumunci,

Abubakar shine da mafi soyuwa azuciyar mahaifinsa, kuma babba awajen mahaifiyarsa hjy babba, daya tashi sai bai tsaya, a ko'ina ba sai jihar gombe ya auro san kace ciyar bafulatanar matarsa zulaihat, kyakykyawar ba fulatanar gombe me kyak kyawan asali da tushe, ta kuma shigo cikin zuriya r alhj balarabe, taketa zaz zago masa kyawawan 'ya 'ya maza har guda biyar cur sai auta rahima, su shida ke nan, ayan zu haka biyar ne awajensu, mu'azzam muhamud abdurrahim da abdulsha- kur da Kuma auta rahima ,

Sai asiya itama tana kd da nata iyalin guda hudu

Mansur abokiyar aikinsa ce me suna rabi'a yayan su uku Yar kanoce aikine ya kawota abj take zaune gurin yayanta,

Aliyu Kuma kanwar aboki nsa ce" yayansu hudu maza biyu mata biyu

Shi kuwa umar hjy zainab (inno) itace" ta hadashi da ' yar' aminiyarta hjy ladidi me suna nafisa,

Hjy ladidi ' yar' salin garin minnace, aurene ya, kinki mota ya kawota garin abj da yarta guda daya tilo nafisa ba sai nace muku nafisa ' yar gata bace ku kanku zaku fada, kasan cewa kowa yasan yadda d'a guda daya yake agun iyayensa to irin wan nan son akewa nafisa agidansu, ""itaka kadaice'acikin suru kan alhj balarabe bata taba haihuwa ba ko batan wata kuwa,

Yakamata musan meye halaiyar alhj balarabe,

Alhj balarabe mutum ne me tsananin addini da ku ma amfani dashi yana da tausayi da hakuri haka kuma ya' iya mu' amala da mutane yana da san kyautatawa' al 'umma, ya gina makarantu da masallatai babu adadi, ga asibitocin da ya gina dan kawai tallafawa marasa karfi da Kuma marayu, wannan dalilin ne talaka wa su kaso ya tsaya musu amatsayin gomnan jiha amma sai yaki fur, acewa rsa" bazai taba iya shiga abinda zaisa yasa 'bawa mahaliccinsa ba, da wannan' hujjar tasa suka hakura badan sun so ba,

Alhj balarabe baisan wace irin waina ake toyawa a,cikin estate dinsa ba,zuciyarsa daya yake kallan kowa baya kuma tunanin ana aikata wani mummnan ta adi,

Yana can hadadden ban garensa shi da matansa dattijan da jin dadi da da ula suka boye tsufansu,

Inaso makaranta kuyiwa labarin KUDURAR ALLAH kyaykywar fahimta, shine dalilin da yasa na fayya- ce muku sunayen ' ya'yan alhj balarabe da kuma wadànda suka rabeshi,

Hali,dabi'a da Kuma manufa duk suna cikin labarin,

CIGABAN LABARI

...…..Estate.....

Wani kimtsetstsen falo ne me matukatukar gir ma da kyau wanda yaji kayan more rayuwa da dima- diman kujeru masu tsananin kyau da burge- wa,babu wasu yawan tar- kace acikinsa bayan sai- tun kujeru kala biyu sai kuma run dumemiyar placzima tv,

Wani sanyayyen kamshin turaren wutane tare dana air freshener, wanda suka hadu suka bawa falon wani ni'imtaccen kamshi me san yaya zuci ya,

Saidai duk wannan ni'ima hakan bai hana damuwar hjy zulaihat kassara ruhin ta ba, ""cikin tsananin damuwar dake cin zuciyarta tasa hannunta ta dafe saman kanta dake barazanar barin gan-gar jikinta sabi da tsananin sarawar da yakemata,

Rahima dake tsaye akarshen matakalar da zata sadaka da falon ta bangaren hagu,yayinda hjy zulaihat ke ta bangaren gabas akan 'kawatattaun kujerun dining table din da ya ma maye gurin,ayanzu kanta a,kife yake dan haka batasan rahima ta zoba, sai kawai ji tayi andafa kafadarta, cikin tsananin tsoro da firgita!' ta dago kanta, ganin rahima ce yasa ta saki wata 'kak'kar far ajiyar zuciya, kana' ta yi saurin goge hawayen da suka 'bata kyakykya- war fuskarta tare da 'kirkiro murmushi akan fuskarta.

Hannun rahima ta kamo tare da kokarin boye damuwarta, tace" rahima 'yanmatan Abbie ba ki koma bacci ba? rahima da tacika da tausayin ' ammin tata, tace" ammina yaza'ai na iya bacci bayan kina nan cikin wani'mugun yanayi da tsananin damuwar da take neman hargitsa farin cikina, "taci gaba dacewa" ammi tun ban mallaki hankalin kainaba nake ganinki cikin wannan damuwar, kuma duk sanda natam bayeki saikice mun bahurumina bane, ammi meyasa? ta fada cikin zubar da wasu zafafan hawaye,

""Cikin nutsuwa irin ta mata masu tsananin hakuri ammi tace"rahima kinutsu kidena wannan ihun haka!dan wani zai' iya shigowa ya Kuma fuskanci halin da muke ciki,hakan Kuma bakara min hatsarine agaremu ba dagani harke! wannan damuwar da kike gani' atare dani sirrin rayuwata ce"kuma jinsa ga wani fansane garayuwata da kuma rayuwar wasu,dan haka inaso kikama kanki da dakyau ki adana wadàn nan shir mammun tambayiyin'naki!takarasa maganar da wani irin hada rai dan karma rahima tasamu damar ragargazo mata wasu tambayiyin,

Sai dai duk da hakan bata tsira ba,dan tana dasa aya,rahima ta dora da abinda yake cikin' zuciyarta tace" to ammi meyasa bazaki fadawa Koda 'ya'yan cikin ki bane? idan, ni kina ganin nayi kan-kanta da jin damuwa ko kuma sirrinki!kai tsaye ammi tace mata" saboda ban yarda da kowaba, ban' amince da kowaba, ban yarda, da amanar kowaba, haka kuma ban yarda da gaskiyar kowaba, da sauri rahima taca" ammi harda mu 'ya 'yanki ? wani' irin murmushi' ammi tayi me dauke da tarin ma'anoni kana tamike ta bar rahima zaune a agurin baki bude da madaukaki Yar mamaki!!!!

Fatash........

Maman hamra rufe bakin taji nace fatash to se a