KUDURAR ALLAH

Page 11

by @zahrawriter12

Tunda ya kwanta bashi ya farka ba sai da yaji kiran sallar asuba acikin kunnensa, ahankali ya bude manyan idanunsa dasuka koma wata kala mai matukar kyau da burgewa saboda baccin da bai isheshi ba, cikin yar kasala ya mike daga kan lallausan gadon nasa ya nufi hanyar toilet dan dauro alwala, yana fitowa yaji ana taba nock din dakin, ahankali ya karasa jikin kofar yana mamakin kowaye acikin wannan lokaci, ga tsananin mamakinsa Alhaji baba ya gani tsaye yana doka masa nutsatstsan murmushi wanda yake gauraye da wata irin mashahuriyar kauna,cikin tsananin kulawa yace" abdallah jikana fito mutafi masallaci ba nisa bane acikin estate dinnan yake dannasan haryanzu akwai gajiya atare dakai!'jinjina kai kawai abdallah yayi tare da kama hannun Alhaji baba yana cewa na fito, ai da kasani baka zo har nan ka wahalal da kanka ba sai mu hadu amasallacin!'Alhaji baba ya gyada kansa ayayin da suke jerawa yace" abdallah daka yanzu duk sanda kaga banzo na ta da kai mun tafi sallar asuba ba to ka kaddara aranka ba lafiya ba, dan tun daga yau na wajibtawa kaina, sai dai kuma idan baka nan ko na mutu ko kuma kayi aure kayi nesa dani!'adai-dai lokacin sukazo kofar masallacin dan haka zancen nasu ya yanke.

Ko da aka idar da sallah sun jima aciki suna karatun alkur'ani Alhaji baba ba karamin dadi yajiba da yasamu abdallah yadda yake tsammata, wato mai tsananin ilmin addini da kuma aiki dashi,saida gari ya danyi haske kana suka fito Alhaji baba har kofar dakinshi ya kuma rakashi kana ya dubeshi cike da kauna, yace"abdallah kaje ka kwanta za'akawo maka kayan karinka idan katashi nasan yanzu kana bukatar hutu!' ahankali abdallah yace"na gode!' alhaji baba bai saurareshi ba ya wuce dan komawa bangarensa.

Lumshe manyan idanunsa yayi wanda suke cike da zara-zaran eyelashes,yana mai jin kansa awata duniya ta daban, gashi dai acikin yan uwansa kuma mahaifarsa amma bayajin farinciki da walwala atare dashi, abu daya yaji tun shigowarshi gidan shine kauna da tausayin Alhaji baba sai kewa ta mahaifansa da ta lulllubeshi,yana jin kewar mahaifiyarshi saidai bazai iya haduwa da ita ba ahalin yanzu domin bazai iya jurar ganinta batare da ya nuna tsananin kewarta da dokinta agareshi ba,ko ita ma ta mantashi?ko tana tunanin sa ahalin yanzu?kwanciya yayi asaman gadonsa yana mai shafo tattausar sumar kansa da tai matukar kayatuwa wadda tai dai-dai da dan siririn sajen da ya kawata fuskarsa ma'abociyar kwarjini da haiba, rufe idanunsa yay yana mai kokarin gayyato bacci ko yasamu kansa ya daina masa ciwo.

Kaiwa take tana komowa kamar mai safa da marwa, can dai kuma ta zauna,tana mai cije bakinta ta rasa ma wani irin tunani zatayi karfa garin sanyin jiki tabari abubuwa su cakude mata, kai Ina ai haka ma baza ta taba faruwa ba,duk yakin da nakeyi shekara da shekaru amma ace lokaci daya wasu banzaye suzo sucini da yaki ina bazan taba barin haka ta faruba, sai na ga abinda ya turewa buzu nadi!' takarasa fada tana fitar da wani irin zazzafan huci.

Majalisar da take kasancewa afalon inno ce yau take ta tafka mahawara kowa da a bokin yinsa kasancewar bikin da yake ta da da matsowa dan yau sauran kwana goma afara shagalin bikin,shiyasa idan suka zauna basu da wani zance idan ba na yadda bikin zai kasance ba, amare hudu angwaye hudu sai dai dake da akwai zumunci tsakanin iyayen amaren da angwayen yasa komai za ayishi ahade dan haka suke cewa' bikin mutum takwas za'ayi 'acikin estate din na Alhaji balarabe, Khadija da haulat yayan nana karama wadda suke kira da hajiya mama sai kuma yarinyar aunty hafsa, ita kuma suna mata lakani da maman maiduguri, ita kuma zata aurar da rukayya babbar yarta, yayan maman maiduguri gaba daya su hudun suna nan cikin estate kamar yadda duk dan da aka haifa ba daga cikin estate ba to sai yay kaura ya dawo cikin yan uwansa, shiyasa yaran gidan gaba daya suka taso awaje guda, sai Abdurrahim d'aga hajiya zulaiha yayan rahima, suna matukar ji da bikin nan kasancewar sun kwana biyu ba'ayi biki a estate din ba.

Hayaniya suke sosai sun cika falon da shegen musu, mazansu da mata kowa so yake asaurari zancensa dan haka hayaniyar tayi yawa har hawa kai takeyi, hatta inno da bata cika damuwa da harkokin hayaniyar suba yau sai da taji sun dameta,

Ahankali yake bude shanyayyun idanunsa da har yanzu suke cike taf da bacci dan ko karyawa har yanzu baiyi ba tun da suka dawo daga masallaci da Alhaji baba wani bacci mai cike da mafarkai kala-kala yay awan gaba dashi, shine bai farka ba sai yanzu da wata iriyar gigitacciyar hayaniya mai fasa kwanyar kai ta farkar dashi, hannu yasa ya dafe saman goshinsa yana jin hayaniyar har tsakiyar kokon kansa,mikewa yayi ya nufi tailed, wanka yayi kusan minti arba'i kana ya fito yana sanye da rigar wanka sai karamin towel ahannu yana tsane kanshi,.cikin mintuna talatin yagama shirinsa tsaf cikin shigar kananun kaya wanda sukabi zubin jikinshi da kyakykyawar kirarshi ta sadaukan maza, yayi matukar kyau na ban mamaki tamkar ka daukeshi ka gudu, ya feshe jikinsa da manyan hadaddun turarukansa masu kamshi, falonsa ya fita, inda ya kara jin sautin hayaniyar tamkar afalon akeyi, runtse idanunsa yayi yana mai jin wani irin zafi aranshi tare da takaici,gashi ba gwanin magaba ballentana yace zai musu magana,Amma tunda hakane abun lallai yaran nan zasuci kaniyarsu tunda ba yadda zaiyi, zaman gurin dole ya kamashi dolene ya dauki mataki idan ba haka ba babu shakka yaran nan zasu kasheshi da wannan kadadinnasu mara tushe da ma'ana,dan bai dauki hakan ako mai ba sai tsabar rashin tarbiya.

Kadan ya tattaba kayan karin da aka kawo masa, shima tea kawai ya sha, sakamakon rashin sanin daka Ina abincin suke, tashi yayi ya nufi hanyar fita babban falon cikin takunshi mai cike da nutsuwa da wata irin ta kama, kai kace sarkine amma shi bai san duk yana wannan ba, dan haka halittarshi take,

Wani irin sassanyan kamshine ya farayiwa kofofin hancinsu sallama kana ginshirarren takunsa mai cike da nutsuwa sai kuma kwarjininshi da ilhama wanda rabbi ya bashi sai kuma kyakykyawar fuskarshi mai cike da haiba, kai bazakace ya taba sanin yadda ake murmushi ba,

Tsit kakeji falon yayi ai tuni kallo ya koma sama ,mai sakin baki nayi mai zaro Ido nayi kan uban nan Allah mai kudura da irada tsarki ya tabbatar ga ubangijn da ya halicci wannan kyakykyawar surar cewar hauwa'u kenan da takasa kawadda da idanunta akan abdallah da yasamu wata kujera can nesa dasu ya zauna, zaman nasa ma kansa abin kallone, dukkanin su suka hadiye wani kakkauran miyau da ya daskare akan harshinansu,najib ne yay karfin halin cewa kai dalla dubesu duk kun wani rikice da ganinsa sai kace baku gansa jiya ba!'amna ce tai zakal tace" kai ya najib kaima ka rikice da ganinsa bare kuma mu mata, kuma jiyan ince kinbari yay aga fuskarsa tunda ya sunkuyar da ita har akatashi ataron bai dagoba!'rahima da zuciyarta take mata wani irin mugun bugu tace" kai amna baki sani ba dai irin wadannan ko kallo zasuyi basa bari afahimta, dan haka baki da hujja akan cewa bai dago ya kalli kowa ba!' abdurrahim ne ya kallesu cikin jin haushin maganganunsu yace"yanzun dan Allah wannan tarbiyace? kudinga yi da mutum agabansa kuma babu wanda yay tunanin gaidasa, karfa ku manta da jawaban Alhaji baba koma kai tsaye nace" umarninsa akan mubi Yaya abdallah domin shine babba ayanzu da zai tsawatar mana!' fa'iz ya harareshi gami da cewa to uban tsari kai yanzu gaidashin kayi? komu cewa akayi maka bazamu gaidashin ba me tarbiya!'yakarasa zancen da mikewa kai tsaye ya nufi kujerar da abdallah yake hakimce akai, ya kwantar da kansa idanunsa alumshe tamkar bayajin muhawarar da ake tafkawa akanshi,sallamar da fa'iz yayine yasashi dan bude idanunsa, nutsuwa fa'iz ya kumayi ganin tsabar kwarjinin abdallah, amsa sallamar yayi kamar wanda yake koyan magana,dan durkusawa fa'iz yayi tare da cewa barka da asuba ya abdallah!'barka dai ya fada asaman labbah danma fa'iz din yana kallon bakinsane da tabbas cewa zaiyi bai amsa ba, ahankali kuma suka dinga tasowa daya bayan daya suna gaidashin cikin kula da taka tsantsan tamkar ansanar musu halinsa sai dai kuma atabangarensu ba komaine yasasu wannan nutsuwar ba illa tsabar kwarjini da kamala irin nasa da kuma rashin ganin fuskar wasa,

Tunda ya zauna ya hanasu sakewa karshe ma ahankali suka dinga zare jiki suna guduwa daga falon ba fada ba duka balle harara su da kansu sukaji sunyi tsarara abdallah yana zaune aguri suma suna zaune babu mai iya wannan karfin halin duk cikinsu,sai dai yan matanfa yau hirarsu ta canja zani dan gaba daya ayinin ranar hirar abdallah ce abakunansu karma amna da hauwa'u da kuma farida yar Alhaji habib suji labari...

Da dai matar nan taji bintu takiyi mata shiru sai ta kuma juyowa afusace ta kwaza mata wata azababbiyar tsawa wanda nan take bintu ta kuma rikicewa, tsoro ya kuma da baibaye zuciyarta, saboda ta kaici matar figarta tayi sukayi ciki bintu kuwa binta kawai take batare da tashiryawa hakan ba saboda matukar tsoro,suna shiga tafkeken falon mai matukar haduwa da tsaruwa,wani dattijo wanda akiyasce zai iya kaiwa shekara hamsin da bakwai,yace'haba ladidi kiyi mata ahankali mana bakya ganin yarinyace karama,kinsan da nafisa ta haihu da yanzu kina da jikan da ya girme mata sosai!'sakin hannun bintu tayi tana cewa haba Alhaji ya daga ganin yarinya akwararo zakace lallai sai munshigo da'ita kai kana ganin kafurin kyau irin na yarinyarnan kasan ba abin arziki ta fito shukawa ba dan bana raba dayan biyu karuwancine ya fito da ita sannan gaka ganinta kaga balarabiyar karuwa!' Alhaji munir yace" ashsha haba ladidi bazaki daina aibata yayan al'umma ba kenan kullum Ina gayamiki Amma bakyaji, ki bar ganin daya kawai kika haifa...kafin ya karasa ta tari numfashinsa da cewa kaga ni banason wannan mugun bakin naka kaima dai yarkace na gani idan kayi mata baki ta lalace bani kadaice da asaraba harda kai ehe,!' jinjina kansa kawai yayi batare da yakuma cewa da 'ita komaiba, dawo da hankalinsa yayi kan bintu da kukanta ya mutu tun sa'ilin da kamilalliyar fuskar Alhaji munir tayi mata maraba,cikin nutsuwa yace yarinya ya sunanki? cikin Jan ajiyar zuciya ta wanda yaci kuka ya koshi tace"zahra ta sami kanta da canja suna wanda itama baza tace ga dalilin yin hakan ba, ya kuma cewa to zahra daga Ina kike kuma me ya zaunar dake kofar gidana kusan awanni hudu?bintu kasa tayi da kanta ganin irin buhu-buhun harar da hajiya ladidi take aikamata,tagane daga dazu zuwa yanzu matar da aka kira da hajiya ladidi bata kaunarta, itama kuma hakanan taji matar bata kwanta mata ba, Alhaji munir ne ya katse mata tunani da cewa muna jinki zahra!'hajiya ladidi tai zaraf tace"yo ba dole tayi shiruba tana kirkiro karyar da zata shimfida mana!' Alhaji munir yayi mata kallon ki kiyayeni ladidi......... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` ***

*_____________________________________*

Aunty hasana (maman nuur)wannan page din nakine kiyi yadda kikeso dashi Ina kara mika dunbin godiyata agareki Allah ya kara mana zumunci Amin ya Allah