KUDURAR ALLAH

Page 15

by @zahrawriter12

Tamkar A mafarki haka yake ganin Al'amarin,ihun da Bintun take har cikin tsakiyar kansa, juyi kawai yake tsakiyar tattausan gadon,bakinsa ɗauke da addu'o'i, lokaci ɗaya kuma komai ya tsaya cak tamkar ɗauke war nefa, A hankali ya tashi zaune hannun sa dafe da kansa, wannan Al'amari bakaramin hautsina masa tunani yayi ba, to me hakan yake nufi?me ya kawo wannan yarinyar cikin mafarkinsa?meye haɗin ta da wannan ɗakin? meye kuma A cikin ɗakin?Anya kuwa ba abinda yake zargi A kan yarinyar bane Allah ya nuna masa? tabbas hakan yana nuna masa turo ta A kayi, to amma waye ya turota? me aka turota ta aikata masa? komawa yayi da baya ya jingina da fuskar gadon tare da tattaro bedsheet ɗin ya ciku kuyeshi ya watsa shi ƙasa, miƙewa yayi ya fara zagaye ɗakin yana furzar da wani irin zazzafan huci daga bakinsa, idanunsa har sun sauya kala saboda tsananin zafin zuciya, lailai dolene ya binciki yarinyar nan,A sannu zai kamata da lefi dumu-dumu, bathroom ya faɗa ya ɗauro Alwala ya kama jera na filfilu.

Tunawa da Abinda ta gani yasa ta kuma rikicewa jikinta ya shiga wata iriyar kakkarwa, cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi ya rufeta, A matuƙar tsora ce take da gidan nan, wannan wane irin gidane suka kawoni? ta faɗa cikin kakkarwar jiki da tashin hankalin da yaƙi barinta, raɓewa tayi can ƙarshen ɗakin tanajin kamar A lokacin abun yake faruwa, runtse idanun ta tayi, cikin tashin hankali tace"wayyo Allah katemakeni ka kuɓutar dani daga hannun waɗan nan mutane, ya Allah katemakeni ka tsareni daga shiga haɗarin gidan nan, ka kawo min mafita cikin gaggawa!'kuka tasaki me matuƙar bantausai da karya zuciyar mai imani,A hankali cikin jin tsoro da ɗar-ɗar take takawa har zuwa cikin bathroom,Alwala tayi ta fito ta shinfiɗa sallaya ta tada kabbara domin miƙa Al'Amuranta gurin sarki Allah buwayi gagara misali.

Garau ta tashi washe gari tayi aikinta kamar yadda ta saba, ta haɗa karinsa ta nufi falonsa da tunanin ya fita motsa jiki kamar yadda ta saba zuwa ta tarar ya tafi, shi yasa basu fiya haɗuwa ba,tana shiga falon ta ɗan yi jim, kana kuma ta wuce ta jera kayan karin,juyowa tayi bayan ta A jiye da nufin ƙara Sachin ɗin falon dan ganin inda bai gyaruba ta kuma kimtsawa, saboda tun kan ya farka take shigowa ta gyara falon idan ya fita motsa jiki kuma sai ta gyara ɗakin da wankin toilet, dafe ƙirjinta tayi tare da saurin ja da baya ganin mutum kwance yayi luf cikin kushin, A kimtse yake cikin kayan motsa jiki damtsensa sai glowing yake idanunsa A rufe tamkar mai bacci, murguɗa ɗan ƙaramin bakinta tayi tare da motsashi A hankali tace"haka kawai sai mutum ya dinga bani tsoro kuma bani da damar yin ihu ko kuka sai A fizgeni a wulla waje,mutum sai kace kurma ba abinda ya iya sai ɗacin rai!

A hankali ya shiga buɗe lumsassun idanunsa masu dawo da mutum cikin nutsuwar sa, ya ɗora su Akan kyakkyawar fuskar Bintu,tsaf yaji duk abinda tace, saboda shi Abdullah ya kasance daga cikin mutane masu tsananin ji, dan haka bai sha wahalar jin duk abinda take faɗa ba.

Cikin rikecewar da kaifafan idanunsa masu tsananin maiƙo da sheƙi suka sakata,cikin yanayin fargaba da matsanancin tsoro da ya saukar mata A lokaci ɗaya, cikin sanɗa ta taka dan tsira daga waɗan nan shu'uman idanuwan nasa da suke neman kassara duk wata gaɓar da ke gudanar da jini A cikin jikinta,

Wata tsadaddiyar murya taji tamkar amsa sarewa acikin kunnuwanta,wadda ta saka gaba ɗaya ragowar kuzarin dake tare da ita ya ƙarasa malalewa,cak ta tsaya A inda take batare da ta ƙara wani ƙwaƙwƙwaran motsi ba, cikin yanayin maganarsa na fitar da magana ɗai ɗaya tamkar wanda akasashi yi dole,yace"karki sake ganina ki tsorata,numfashinta bai gama dai dai tuwa ba ya kuma rigirgizo mata tambayar da ta motsa ƴan hanjin cikinta, tare da wata iriyar juyowa sosai tana fuskantar sa, yayin da idanuwan nan suka kuma fitowa cikin firgici da tsoro,sai da ya gama karantar yanayin ta tsaf kana ya kuma mai maita mata tambayar,yace" dake nake jiya misalin ƙarfe biyu me ya fita dake waje har kina neman fasawa mutane kunnuwa da shegen ƙaranki,me kikeso kishiga kiyi A wannan ɗakin? hantar cikinta ya kuma kaɗawa, to ma wai miyene na jin tsoron bayan nasan ban yi komai ba,wata ƙila ma shine yake wani mugun abun A cikin ɗakin, idan ba haka ba me yasa da yaji ihun nawa baizo ya tai makeni ba?kuma ya akai yasan na fita? kai wannan mutumin A kwai baƙin mugu!' gigitacciyar tsawar da ya buga mata ne yasa ta dawo haiyacinta,ya nunata da yatsa yana cewa duk ranar da na tabbatar da rashin gaskiyar ki to ki tabbatar da cewa sai nayi gutsi-gutsi da namanki A cikin gidan nan,wuce ki fitamin A falo!tun kan ma ya gama rufe bakinsa ta arta da wani shegen gudu,bata tsaya A ko'ina ba sai tsakiyar gadonta tana maida numfashi me cike da razanar da tayi da Abdallah, Allah kafitar dani daga cikin wannan gida na mutane marasa tsoron ka, kowa munafiki ne A wannan gidan, duk basu da gaskiya, duba Irin kallon da wannan Ammin Rahiman takeyi min dagani itama so take tasani wani mugun aikin!'

Ammi ta dubi Rahima tace" auta ina ƙawarki kuwa zahra?Rahima ta saki dariya tare da miƙewa zaune tana cewa" wai ta gidan inno? ni wallahi ma banje ba tun washegarin da Aka kai Amare, faɗa mukayi da inno! ta ƙarasa maganar tare da ɗan turo baki, Ammi tace"to ai ba da ƙawar taki kukai faɗa ba ya kamata dai ki dinga zuwa kina ɗebe mata kewa!'to Ammi amma sai na huta sosai zan koma zuwa!' Ammi tayi murmushi kawai A ranta tanajin haɗa kusanci tsakanin Rahima da Zahra shine kawai hanyar da zata 'iya bi dan fahimtar abinda take so ta sani A game da Zahra,tasan ko bata tambayi Rahima ba zata dinga bata labarin Zahra,ita kuma zata dinga hankalta da inda yarinyar ta sa gaba idan A kwai wani Abu maka mancin na rashin gaskiya zata sani.

Duk tsarin da Hajiya ladidi tayi shine ya kasan ce, sau biyu ne tasa Alhaji munir ya kira Alhaji Baba,ba tare da wani shan wahala ba tsarinta ya tafi yadda take so koma fiye da haka tunda A cikin kwana biyu Alhaji Baba yaji san sha'awar ya mallaka wa Bintu waya,ko dan sudinga gaisawa da bawan Allah Alhaji munir, tabbas yana jin daɗin yadda Alhaji munir ɗin yake nuna kulawarsa A kan ƴar marainiyar Allah Bintu,shi yasa yaji A ransa gwara ya bata waya dan shi Alhaji munir ɗin yasamu damar kiranta kai tsaye,

Alhaji Baba da kansa ya kira Alhajin Nafisa, yasanar dashi ya bawa Bintu waya kuma layin da yaƙi rasa dashi shine layin Bintun, dan haka zai'iya kiranta kai tsaye, godiya Alhajin Nafisa yayi masa kana sukayi sallama, A lokacin suna tare da Hajiya ladidi ya kuma sanar da ita yadda sukayi da Alhaji Baba,yadda Hajiya ladidi ta nuna farin cikinta,har saida ya tsaya yana dubanta cike da mamaki,ganin haka yasa ta waske tare da cewa, kai masha Allah gaskiya Alhaji Baba ya kyauta,tare da ɗaukar wayarta ta bar falon.

Ita dai Bintu kawai ganin inno tayi da ƙaramar waya ta bata,duban inno tayi tace"inno wannan wayar fa ta waye?inno tace nakine Alhaji ne ya baki saboda kurinƙa gaisawa da Alhajin Nafisa!'to inno kiyi masa godiya, yanzu zan ƙarasa aiki sai naje nayi masa godiya nima!'inno tace"aiko yace" karki sake kije da niyar yi masa godiya,yace kiyi masa addu'a kawai ita yake buƙata!'cikin sanyin jiki Bintu tace"inno ai addu'a tsakanina daku ba mai yanke wa bace, Allah Ubangiji yaja kwana me amfani!'inno ta amsa da Amin Batula,kana ta juya ta fita daga kiching ɗin.

Tunda inno ta fita ta kasa ci gaba da aiyukan ta, gaba ɗaya ji takeyi mutanen nan suna ɗaureta, wai yaya ita da take neman hanyar tserewa suke ƙara yi mata da baibayi da zaman gidan,anya kuwa zata iya ci gaba da zama A gidan tana cin karo da shaiɗanun mutane da kuma Aljanu?

Lokacin da Anty Nafisa ta shigo falon inno bata tarar da kowa ba,dan haka kai tsaye kiching tanufa, dan anan takesa ran ganin Bintu, cikin Sa'a kuwa tana shiga ta sameta tana kan tunanin mafita wa matsalar datake ta tun karo rayuwar ta,

Tana ganin Anty Nafisa jikinta ya fara rawa, cikin sauri ta durƙusa ƙasa dan gaidata, batare da ta amsa ba ta ɗora mata da tambayar, ina inno? Bintu tace"ta tafi wajen Hajiya Babba,zata dubata da jiki!'saurin kamo Hannun Bintu tayi sukayi can cikin kiching ɗin,hannu ta mikawa Bintu tare da cewa ina wayar da inno ta baki?cikin sauri tace gata can, tanayi mata nuni da kan prezer,da sauri Anty Nafisa ta ɗauki wayar tare da buɗe ta tasaka mata wani layin A ciki, kana tasata A babiratin, sai da ta gama sannan ta dubi Bintu tace"ki kula da kyau, baki wayar nan yana daga cikin shirin mu dan haka ki kula da'ita tamkar yadda zaki kula da rayuwar ki,kuma duk wani shiri da kike na guduwa muna sane da hakan,zaro manyan idanunta tayi wanda idan tayi hakan baƙaramin kyau yake ƙara mata ba, Anty Nafisa tayi murmushin mugunta,kana tace" kina mamaki ko? to inaso kisani duk yadda kika zacemu mun wuce haka, mun zarta tunanin babban kaima barantana wannan ƙaramin kan naki, inaso kuma ki dinga sarrafa wannan shegen tsoron naki dan watarana zai iya hhhh gaiyato mana matsala cikin aikin mu, inaso kuma ki iya bakin ki A cikin gidan nan dan duk wanda kika gani ba Abin yadda bane ESTATE ƊIN ALHAJI BALARABE YA WUCE TUNANIN MAI TUNANI munanan munajira muga yadda ƘUDURAR ALLAH zata tarwatsa mugayen zukata da ɓara gurbin IYALEN ALHAJI BALARABE dan nasan namu ba komai bane shiyasa bana tunanin yin na dama akan abinda nake aikatawa ko kuma nace na aikata,A da har na fara karaya, na fara tunanin makomata sai Hajiyata ta nusar dani tare da ɗorani bisa hanya mai ɓullewa.

Babu abinda zuciyar Bintu take sai wani irin bugu mai tsanani, Anty Nafisa idon ta ya rufe ko lura da yadda yanayin Bintu ya koma batayi ba,dan tana gama zantukanta ta juya ta fita da sauri tabar kiching ɗin,yayin da ta bar Bintu tamkar butun butumi A daskare, tuni ƙwaƙwalwar ta tafi hutun wuccin gadi,ji tayi an jijjigata da ƙarfi,wata Irin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tayi tare da fashewa da wani kiɗimam man kuka mai razanar da zuciyar mai imani, dije ta zuba mata ido cike da mamakin meye yasa ta kuka kuma? ko dai irin matsalar su ɗaya? tabbas ta daɗe A laɓe tanajin Anty Nafisa sai dai bataji komai ba, tunda bata daɗe da shigowa ba Nafisan tafita,tsoron irin kukan da Bintun takeyi shiya kama dije,tsoron biyune ya haɗe mata na farko kukan Bintu wanda har yi take kamar zata shiɗe, na biyu tsoron kar A zo akamata ace ita tayiwa Bintun wani abu, wannan tunani da tayine yasa tayi saurin juyawa zatabar kiching ɗin, Amma kuma sai taji ta kasa wani irin tausayin yarinyar ne ya dinga kewayawa har cikin ɓargonta wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata, cikin sauri ta durƙusa inda Bintu take ta kama hannun ta tare da miƙar da ita tsaye,A hankali ta jawota jikinta ta shiga bub buga bayanta tana shafa kanta tana bata baki cikin taushin murya,tace" haba ɗiyata ko mai yayi zafi fa maganin shi Allah kiyi haƙuri ki daina kukan nan kowa kika ganshi yana da matsalarsa, wannan kukan da kikeyi ai sai ya cutar dake ki dena ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah shine zai yaye miki kinji!'Bintu da yanzu ta riga tayi shiru sai ajiyar zuciyar da take fitarwa ajejjere,sai da dije ta tabbatar Bintu ta samu nutsuwa kana ta janye ta daga jikinta tace maza jeki ɗaki ki wanke fuskar ki kar inno tazo ta ganki A haka baza taji daɗi ba!'A hankali Bintu ta fara takawa sai da ta kusan barin kiching ɗin kana ta juyo cikin muryar ta da ta dashe tace" mama na gode Allah ya biya ki dukkanin buƙatunki na Alkhairi ya kareki daga sharrin maƙiya!' da sauri ta ƙarasa fita daga kiching ɗin saboda wani kukan dayake ƙoƙarin kufce mata,

Da ido dije ta bita tana ta nanata faɗin Amin akan harshen ta,haƙiƙa idan tace bata ji daɗin addu'ar da Bintu tayi mata ba tabbas tayi ƙarya, itama fita tayi jikinta A sanyaye, zuciyar ta kuma cike da tunanika iri-iri.

Tana shiga ɗakin ta waɗa kan gadon tare da kecewa da wani sabon kukan, zuciyar ta cike take da ƙunci wanda bata san ranar gushe war sa ba,yau tayi da tasanin zuwa garin Abuja,

Ashe dama wannan baƙin ahlin shine ahlina da fafi yake gayamin?tabbas iya abubuwan da na gani kawai sun isa tabbatar min da abinda fafina yake gayamin, yanzu wannan bawan Allah Alhaji Baba shine kakana? to wacece kakata kuma? wane ne mahaina?ya Allah hhhh kafitar dani duhu ka kawo min ɗauki, to ita Anty Nafisa wacece"?kuma matar waye?me yaya Abdallah yayi musu suke san cutar dashi?shi ɗan waye ne? wacece mamansa?ɗakin nan mallaki waye menene A cikinsa?shin me dame ake shiryawa da waye da waye masu shiryawar ?su waye suke neman halakani?suwaye suka ɗauke min mamana da fafina?ya Allah ka kawo min agaji, yanzu ta ina zan fara fuskantar wannan gagarumin yaƙin, fafi abin ya wuce zaton ka bazan iya ba bansan ta ina zan fara ba. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` ***

*_____________________________________*