Page 16
Hhhh sautin dariyar sa kawai kakeji amma baza kataɓa gane waye ba saboda yadda ya juya bayansa,waya ce kange A kunnen sa,ya kuma gyara zaman wayar yayi A kunnen sa,kana cikin wata murya me ƙarfi da wani irin sauti,yace"da kyau ɗan kaka aikin ka yanayin kyau,inaso kaci gaba da ɗora mun ladidi A kan hanya ita kuma tana ɗora mana yarinyar A saiti yadda zan samu biyan buƙatata batare da tasan mai nake shirya wa ba,kar kasake kayi abinda zata gane shirin mu A kanta!'
Daga ɗaya ɓangaren, na kaka yace"ranka ya daɗe Hajiya ladidi baza taba gane dawa take aiki ba, saboda duk wata hanya na tosheta A binda kawai nasan tasani shine tana aiki da ɗaya daga cikin ahlin ALHAJI BALARABE, amma baza ta taɓa gane da waye ba in dai ba gaya mata A kayi ba, kuma ina da tabbacin babu yadda za'ayi ta sani dan mun toshe hanyar, kaga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya saboda mun haɗa kifayen mu A guri ɗaya, ba ƙaramar nasara nake ganowa A tafiyar nan ba,
Ogan nasa ya sheƙe da wata muguwar dariya kana yace"naga fa kifayen nan suna da matuƙar wayo yaƙin suka fito da gaske, sai dai kuma ta yaro kyau take bata ƙarko basu san suna tun karar masifa da kansu bane, mutuwarsu suke kira, dan dazarar munci moriyar ganga zamu yada gauranta,ƙit ya yanke wayar tare da cire layin ya taune,cikin alfahari da kansa da yadda yake wasa da ƙwaƙwalwar mutane yace"shi yaƙi ɗan zanba ne idan baka iyashi ba zai kife da kai.
A hankali ta tura ƙofar falon saida ta tabbatar baya ciki kana ta shiga, kimtsa falon ta farayi kamar yadda ta saba, sai da ta tabbatar da komai yayi daidai kana ta faɗa bedroom ɗinsa saida ta gama wanke toilet ta gyara ɗakin, tana cikin sharewa taji wani zumm zumm A ƙugunta,zabura tayi dan sam ta manta da wata waya A jikinta,cikin sauri ta ciro wayar ta danna ok A lokaci ɗaya tana ɗorawa A kunnen ta, muryar Hajiya ladidi ta doki kunnenta, cikin rawar murya tace" Hajiya ina kwana!'ta can ɓangaren cikin yin ƙasa da murya Hajiya ladidi tace"ke kina ina yanzu ina san zanyi magana dake? kamar zata yi kuka Bintu tace" ina falon ya Abdallah ina gyarawa!'Hajiya ladidi ta saki wani uban tsaki, tare da cewa kaji banza ƴar shishshigi A yaushe ya zama yayan naki? in dai har zaki fara tunanin ya zama yayanki ashe bazaki saki jiki kiyi mana yadda mukeso ba,to bari jiki da kyau inaso kisa A ranki wannan aikin da zakiyi shine rayuwarki gazawar ki A aikin yana daidai da ɗaukewar numfashinki, dan haka ki gaggawar fita daga inda kike zan magana dake!' tana gama faɗar haka ta kashe wayar,A dai-dai lokacin da Bintu take ƙoƙarin maida wayar ma adanarta shi kuma ya sawo kai cikin ɗakin,A matuƙar firgice Bintu take kallonsa ƙirjinta babu abinda yake sai wani irin bugu da ƙarfi tamkar zai fito waje,
Abdallah sam bai gane me Bintu take ciki ba, Amma yanayin firgici da tsoro da ya gani akan fuskarta yasa ya gane bata da gaskiya, zuba mata ido yayi yana so ya ƙara karantar yanayin ta, A yayin da Bintu tayi ƙasa da kanta tana ɗan jajjan zara zaran yatsun hannunta,jikinta kuwa da za A ɓula baza a sami jini ba,saboda tsabar fargaba, (Allah sarki Bintu Abinka da wanda bai saba aikata rashin gaskiya ba)
Cikin maganar shi ta ɗaukar hankali yace" da ita ina breakfast ɗina?wata sassanyan Ajiyar zuciya ta sauke cikin ƴan sakanni ta dawo haiyacinta,cikin shagwababbiyar muryarta tace" yanzu zan je na kawo!'cikin janye jikinsa daga bakin ƙofar yake cewa A ransa, meye wannan yarinyar take shiryawa suwaye ne suka turota? ƙwafa yayi hmm ko meyene zan kamaki da hannuna,ranar kuwa ta tabbata bata da mai ceto.
Cikin hanzari ta gama shirya masa karin ta koma ɗaki tare da sawa kofar key,sauri tayi ta zaro wayar ta dannawa Hajiya kira, ko gama ringin batayi ba ta ɗaga tare da cewa,uban me kika tsaya yi tun dazu? cikin sauri tace" Hajiya ai ya kusa kamani ina waya,kuma kinga idan na tawo ban gama masa aikin ba dole inno zatazo nemana kinga ai da ta ganni ina waya zata tambaye ni dawa nakeyi! Hajiya ladidi ta katse ta da cewa na fahimta bar dogon sharhin nan ki buɗe kun nan ki kiji Abinda zan gaya miki,Bintu tace tom Hajiya ina sauraren ki!' Hajiya ladidi tace" kinsan dije ƴar aikin matar mansur?tace ban santa ba!' Hajiya ta ɗora da cewa zaki santa kuma dole kisanta saboda so nake ki shiga jikinta ki gano mun matar da take wa aiki A cikin ESTATE ɗin ALHAJI BALARABE,shine aikinki na farko na biyu shine Abdallah lallai inaso nasan abinda suke shiryawa shida ubansa daga nan zan ɗora miki babban aiki, zahra kiyi ta ka tsantsan da aikin nan duk ranar da kika yi sakaci wani ya gano ki to shike nan kin kaɗe, dan ina tabbatar miki bazaki taɓa iya ambatar ko da harafin L ba bare ƙarshen sunana dan haka ki kula da aikinki rayuwarki ina kuma jaddada miki shine rayuwarki (dake rayuwar A hannuku take ba.)
Tunda suka gama wayar take kai kawo A cikin tsakiyar ɗakin sosai ta fara jin ƙwarin gwiwa,tana ganin Allah ne ya dubeta ya kawo mata mafita ta tsanin da zata hau dan kaita hanyar da zatabi dan binciko ƙullellen ƙulli mai cike da mugun zarge,cikin ƙarfin zuciya tace" Hajiya ladidi bani ce da kuka ba kece da kuka har da birgima kin jawo wa kanki da kanki tashin hankali shekarar tonon Asirinki dake da mabiya bayanki da sauran mutanen munafukan cikin estate ɗin nan yayi Ni ɗin nan sai na zame miki ciwon ido dake da duk wani azzalumi, ku shirya domin ƴar zakanya ta girma, gani nan gareku maƙiya Allah duk sai na binciko gaskiyar datake A binne, yanzu ne za a fara wasan.
Inno ce zaune Bintu kuma nayi mata tausa yayin da Hauwa'u da Rahima ke zaune saman kujera, Rahima hira take ta zubawa inno da Bintu Ita kuwa Hauwa'u gaba ɗaya hankalin ta da tunanin ta yana kan scring ɗin wayar ta wanda ba komai take kallo ba sai hoton Abdallah,inno tace zahra ku tashi na aike ku wajen Hajjah dama baki taɓa zuwa kun gaisa dasu ba Rahima daga nan ki rakata wajen Hajiya Babba ta gaidata!'tun kafin ta rufe bakinta Rahima ta miƙe tsaye tana cewa ku taso muje, Hauwa'u da sai yanzu hankalin ta ya dawo kansu, ta wani taɓe baki gami da cewa Ni bazani ba!Rahima itama taɓe bakin tayi tana cewa Mutum dai wallahi ya gamu da aiki A rayuwar sa,tayi saurin jan hannun Bintu suka fita inno tana kiranta basu karɓi saƙwan ba, amma ina tuni sun ƙule,inno ta riƙe baki tare da cewa oh Ni zainaba jikar mutum biyu kome zasuje su faɗa oho.
A hankali cikin nutsuwa suke ta kawa har suka kai ɓangaren Hajjah, da sallama suka shiga falon tsarinsa iri ɗaya da falon inno komai iri ɗaya ne sai dai kala ta ban banta,
Hakimar macece kanuriyar asali mai matuƙar riƙo da Al'adunsu, tun daga yanayin ƙamshi na musamman da ya cika falon, tana zaune cikin kujerar ta ta alfarma, jikinta nan naɗe da lafaya mai asalin kyau da tsada,sai kuma Dady ane (Alhaji mansur)dake zaune kan kujerar data ke fuskantar ta, ga dukkan nin Alamu dai tattaunawa suke mai muhimmanci.
Amsa sallamar sukayi A tare suna mai zubawa Bintu ido dan ganin baƙuwar fuskace A garesu,kamar yadda ya kasance ɗabi ar Bintu durƙusawa tayi har ƙasa ta gaidasu,haka Rahima itama tayi, Dady ane ne ciki yanayinsa na zafi da rashin sakin fuska, yace"ke Rahima ina kuma kika samo wannan kalar zabiyar? cikin yanayin tsoron sa da ya sabar musu Rahima tace" inno aka kawowa ita dan ta dinga taimaka mata kuma tana dafawa ya Abdallah Abinci da gyara masa sashe!'tana direwa Dady ane yasaki wata banzar dariya me ƙurar da zuciya, yana cewa ayyo haka zaki ce ƴar aikin inno ce kawai amma ba sai kinyi wani dogon bayani ba!' Hajjo ta ɗan gyara kashin giɗarta kana cikin girma da nuna isa tace" wai Mansur meyasa baka girma? wannan wane irin zance ne shi ɗan Adam ai ba abin tozartawa bane kadinga kiyaye harshen ka idan ba haka ba wataran zakayi da nasani!' dawo da hankalinta tayi kansu Bintu cikin sakin fuska tace" yarinya meye sunanki? Bintu ta amsa da cewa sunana Fatima zahra amma anfi kirana da Bintu!'Hajjah tace masha Allah Bintu suna mai daraja!'gani kawai Dady ane ya tashi fice A fusace,inno ta girgiza kai tana binsa da addu'ar shiriya,Rahima tace Hajjah bari mu kewaya sashen Hajiya Babba!'Hajjah tace"to madalla amma ku kujirani kaɗan ina zuwa,tana barin falon sai ga Yaya sagir ɗan gidan Alhaji mansur kasance war dashi da Nabil ɗan gidan Anty Asiya da take kaduna A wajen Hajjah suke, turus yayi ganin su Rahima zaune, A hankali ya ƙara so cikin falon yana da ɗa ƙure Bintu da kallo, zama yayi kana suka gaida sa,Bintu duk tabi ta takura da kallon ƙuril ɗin da yake Binta dashi, cikin ikon Allah sai ga Hajjah ta fito tana cewa na barku ku kadai ko? ko da ike ma ga Aku nan Sarkin zance zata ɗebe miki kewa!' tana mai nuni da Rahima datake ta zunɓura baki dan tasan da ita take,Ya Nabil yayi zaraf ya amshi zancen da cewa,aiko Hajjah kamar kin sani tana nan ta dami friter da shegen surutu!'gaba ɗaya suka dubeshi Rahimace tayi saurin tambayar sa wace kuma haka!'ɗage gida ɗaya yayi kana yace gatanan Bintu ko ke baki taɓa ganin kamar su ba?Rahima ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa Wallahi kuwa Ya Sagir so saima sai dai Bintu har tafi friter kyau!' yauwa ƙanwas ashe kin gane!' Hajjah tace karɓi nan kinji faɗima idan kika biye waɗan nan bazaki taɓuka ko mai ba zani ce ta tadda mujemu!'gaba ɗaya dariya sukayi har Bintun, karbar ledar tayi tana yi mata godiya, Hajjah tace" karki damu duk wanda ya shigo Ahlinmu yazama namu Allah yayi muku Albarka!'gaba ɗaya suka amsa kana sukayi mata sallama, har Sagir ya yunƙura zai bisu Hajjah ta dakatar dashi da cewa ina kuma zaka bayan kasan neman ka nake!' dole ba dan ransa yaso ba ya koma ya zauna.
Cikin kulawa Rahima ta dubi Bintu tace"gaskiya Fatima na fahimci kina son sunan ki!' ɗan kallonta Bintu tayi, kana tace"saboda me kika ce haka? Rahima tace kawai dai nayi la'akarine da yadda idan an tambayeki sunanki kikan faɗi duk wanda yazo bakinki, Amma mu meyasa baki gaya mana ana kiranki da Bintu ba? Bintu ta saki ƙawataccen murmushin ta wanda har sai da gefan kuncinta duka suka loɓa,kana cikin sautin muryar ta me daɗi tace" kai Anty Rahima to bagashi yanzu kin saniba,kuma kin riga kin bawa kanki amsa,dan haƙiƙa inason sunayena duka ko Batula kika kirani dashi zan amsa!' ta ƙarasa maganar fuskar ta ɗauke da ƙayataccen murmushi,Rahima ma dariya tayi tare da cewa to Ai hikenan nima duk wanda yazo bakina dashi zan kira ki!'da wannan hirar suka ƙarasa sashen Hajiya Babba.
Lokacin da suka shiga kimtsetstsen falon Hajiya Babba wanda yake cike da wani mayan ƙamshi mai sanyaya zuciya, samun ta sukai zaune akan sallaya da hijabinta fari ƙal sai casbaha dake hannunta tana ja, har gabanta suka je suka durƙusa suka gaida ta, Rahima cike da soyayyar kakar tata ta raɓa jikinta ta kwanta,cikin nutsuwa Hajiya Babba tasa hannu ta jawo Bintu jikinta tana cewa' ke kam Rahima anyi babbar kobo yanzu ai bakece autar jika ba,faɗima ce!
Bintu tayi luf jikin Hajiya Babba, yayin da wata irin ƙauna me haɗe da kewa ta lulluɓe zuciyar ta tanajin kamar ta dauwama tare da wannan mata mai tsananin kyau kamala kirki da nagarta, muryar Rahima ce ta katse mata tunani da cewa kai Hajiya Babba dama nasan haka zaki min shi yasa tunda kike cewa na kawo miki Bintu naƙi kawota nasan fada zata ƙwacen A gurinki!'Hajiya Babba tayi ɗan murmushi irin nasu na manya tana ta ɗan shafa kan Bintu, yarinyar ta shiga ranta sosai tanajin shauƙin ƙaunarta tamkar su Raihana.
Sun daɗe A sashen Hajiya Babba, Bintu ta sake sosai da ita saboda yadda Hajiya ta sakar mata fuska ta nuna mata ƙauna ta zahiri da ba ɗini, haka da zasu tafi Hajiya ta Haɗa mata kayan amfani sosai kana sukayi sallama, Hajiya taji kewar yaran sosai.
Kewayawa sukeyi cikin Babban ESTATE ɗin, Raihana tana nuna mata kowane ɓangare da kuma me shi, sunzo dai dai ta wajen hanyar da zaka miƙa ka koma ta cikin wannan ɗakin, Bintu ta da kata, yayin da ta zubawa hanyar ido tana tuno abinda ya faru ranar tamkar A lokacin yake faruwa,sai da Raihana ta taɓata kana ta dawo haiyacinta tare da cewa Raihana gurin nan ya burgeni muje ta wajen mu zaga, naga kamar lambuneee...... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` ***
*_____________________________________*