KUDURAR ALLAH

Page 19

by @zahrawriter12

Dije ta dubi Bintu cikin nutsuwa kana tace" Bintu ina so ki gayamin gaskiyar dake cikin zuciyarki ki yarda dani kamar yadda Nima na yarda dake,nasan cewa yadda da mutumin da yafito daga cikin ESTATE ɗin ALHAJI BALARABE,Abune mai matuƙar wahala,amma Ni inaso ki yadda dani ki bani amana Ni kuma zanyi miki alƙawarin bazan taɓa ci miki ba, kamar ƴa nake kallon ki kuma A cikin jikina nakeji ke ɗin ba Macuciya bace dan haka inaso ki gayan kaɗan daga cikin abinda ya kawo ki cikin ahlin ALHAJI BALARABE!'

A hankali Bintu tasa hannu ta share hawayen da suka fara gangarowa daga manyan idanunta masu kyau da sheƙi, zuciyarta kuwa babu abinda take sai kai kawo da wasu wasi, anya zata iya amincewa da Dije da sauri haka kuwa,Fafinta fa yace"mata ko ƙwaro ne yazo zai fita daga ESTATE to ta tabbatar tasa masa ido har sai ta yadda da gaskiyar sa,bata sani ba ko dai Dije yau darar ta zatayi,Dije ce ta katse mata tunaninta da cewa, Bintu banga laifin ki ba lallai ke ɗin yarinya ce mai zurfin tunani da hangen nesa hakan kuma shi ya tabbatar min da cewa zamu haɗa hannu dake dan yaƙar maƙiya da azzalumai,dan haka Ni zan fara gaya miki sirri na ba lallai ne sai kin yadda dani A yanzu ba amma zan baki dama daga nan zuwa duk sanda kikaji zuciyarki ta gamsu dani ta kuma tabbatar miki da bazan taɓa iya cutar dake ba!'

Cikin Ajiye numfashi ta cigaba da cewa Bintu Ni dai da kike ganina sunana Dije kuma ina da yara guda biyu marayu mace da namiji, sanadin mutuwar mahaifinsu shi ya kawoni aiki cikin ahlin ALHAJI BALARABE,inayiwa Hajiya Rabi matar Alhaji Mansur aiki kuma yau kimanin shekaru Ashirin ke nan ina aiki A gidan,ta ɗan da kata tare da goge hawayen fuskarta taci gaba da cewa A cikin wa ɗan nan shekarun ne na haɗu da matar nan wadda har yanzu ban san wacece itaba ko magana zatayi dani ba da ainahin Muryar ta take min ba na daɗe da sanin wannan kuma farko da na nuna mata bazan iya cin amanar ahlin ALHAJI BALARABE ba sai ta kwashe min yarana duka ta ɓiyesu har yanzu bansan ina suke ba, idan tasani wani abu nayi kuskure akansu take hucewa,kullum addu'a nake Allah ya tona asirin wannan baƙar ashanar ya kawo min ƙarshenta!' ta ƙara sa maganar tana toshe bakinta saboda kukan da yake son kufce mata, cikin wani irin tausayi Bintu ta kama hannuwan ta tana ɗan jijjiga wa, kana A hankali ta buɗe baki tace"mama Dije kiyi shiru dan Allah kar ki jawo hankalin mutane masu giftawa kanmu,ki saurareni zan gaya miki iya abinda nasani da dalilin zuwa na estate din nan!' shuru Dije tayi tare da nutsuwa dan fahimtar labarin Bintu.

Bintu tace"mama Dije Ni marainiya ce ta ko wane ɓangaren bani da kowa, daga wani gari mukayi ƙaura Ni da mahaifina muka sauka A garin Bauchi,mutuwar da yayi ita ta takowoni garin ABUJA,nan ta ɗora mata da yadda akayi take gidan Hajiya ladidi da komai da ya gudana A tsakaninsu da aikin da suka sakata tayi da yadda sukayi mata bara zana da rayuwar ta,ta ƙara sa da faɗin mama Dije yadda na samu karɓuwa ta karamci da mutumci daga wannan bawan Allah Alhaji Baba da yadda matansa suka karɓeni suka nuna min ƙauna yadda Inno ta maida Ni mutum yasa na ji bazan taɓa iya cutar da ahlinsa ba,ranar da kika sameni da Anty Nafisa a kiching ina kuka,ba ko komai ne yasani kuka ba sai tsananin tausayin waɗanda ake shirin cutarwa batare da sunyi musu ko maiba, sai dan tsananin zalunci da ƙeta da haɗama, A fahimta ta kenan,mama Dije kinji abinda ya shigo dani cikin wannan gida sai dai yanzu,A shirye nake dan ganin kawo karshen ƙarya da tabbatar da gaskiya,indai zaki bani haɗin kai akan hakan!'Dije wani irin kamo Bintu tayi ta rungume ta tare da cewa Allah na gode maka tabbas na gari basa ƙarewa masu gaskiya basa to zarta Allah zai kuma kawo mana wani mai gaskiyar A kusa wanda zai tai maka mana da ƙarfin sa da rayuwar sa da kuma aljihunsa tare da mai kankat wato itace gaskiya!'Bintu tace" tabbas mama Dije zamuyi nasara sai dai amma akwai haɗari tare da fuskantar ƙalubale da kuma ƙoƙarin rasa rayukanmu saboda A yadda muka sani yanzu abokan yaƙin mu ɓangare biyune da ɓangaren Hajiya ladidi da kuma shu'umar matar da kikewa aiki, kuma ina da tabbacin da A kwai wata ko wani ko wasu Allah ne masani, amma da sannu zamu bin cikosu ɗaya bayan ɗaya,Dije ta ɗora da faɗin insha Allah karshen su yazo kuma mune zamu kawo ƙarshen nasu tare da taimakon Allah da ƘUDURARSA!'Bintu ta buɗe tafin hannun ta, Dije ta ɗora nata kana suka haɗa baki wajen faɗin munyi alƙawari babu gudu duk runtsi duk wahala sai dai maƙiya su gudu!

Dije tace" maza Bintu fara fita daga baya sai na biyo bayanki! tace" to mama, ki bani nomban wayanki da sauri Dije ta karɓa ta saka mata ita kuma tayi mata Plashin, da sauri ta fita daga kan gon...

Kamar walƙiya haka ya fita daga kangon,batare da ya bari Bintu ta gan shi ba,

Tana fita kuwa ta samu dan sahu ya kaita har ƙofar ESTATE, tana sauka taga wata luntsumemiyar mota zata shiga cikin estate ɗin har zuciyar ta taji motar ta burgeta, bayan motar ta shiga itama tabi bayanta tana mai hango yawan tafiyar da zata miƙa.

A hankali yace" Yahya tsaya yarinyar nan!' daga haka ya maida idanunsa ya kulle yana mai tambayar kanshi dalilin sawa a shigo da ita cikin motarsa,wani ɓangare na zuciyar sa yace" kawai dan ita ta kasan ce mace ne shine dalili,Yahya yayi ƙasa da glace ɗin motar tare da zura kansa waje ya ɗan ɗaga muryar sa yace"ki shigo mu ƙara sa dake!' kamar daga sama Bintu taji muryar Yahya da sauri ta juyo har zatayi gaddama sai kuma ta tuna zurfin tafiyar dan haka tayi shahada tare da addu'a A bakinta, kasancewar glace ɗin tintak ne shi yasa bata lura da oga Abdallah dake kwance A bayan motar ba,A hankali tasa hannu zata buɗe bayan motar Yahya yace" a'a shigo nan yana mai buɗe mata ƙofar,batare da tace" komai ba ta maida hannunta kan ƙofar gaba ta shiga da sallama tare da addu'ar da take ta nanatawa abakinta,tana rufe kofar wanan sanyayyan ƙamshin da ya zama hadda A hancinta yayi mata maraba, A hankali ta juyar da kanta zuwa bayanta,wani irin daram ƙirjinta ya buga dama shine A cikin motar nan to amma dai tasan bashi yace ta shigo ba dan A tunanin ta hakan baza ta taɓa faruwa ba, nutsuwa tayi sosai yayin da wannan yanayin da take kasancewa A cikin sa duk lokacin da sukayi kusanci da juna ya shiga mamayarta, ƙirjinta bugawa yake duk sakan da minti,fatanta kawai Allah ya kaisu lafiya.

Suna ƙarasowa ta fita da gudu kamar walƙiya haka ta ɓacewa idanunsu, Yahya kasa daurewa yayi sai da ya ƙyaƙyale da dariya yace" kai wannan yarinya kwai zabuwa ga yadda ta kwasa a guje kamar ance za a saceta!'shiru yayi saboda kallon takaicin da yaga ogan nasa na binsa dashi da sauri ya dauko jakarsa yabi bayansa da ita.

Dije kuwa kasuwa ta wuce tayi sayayyarta kana ta wuce gida,yayin da zuciyarta ta samu nutsuwa, damuwarta cikin kaso ɗari taji sauƙin kaso ashirin A ciki,dan haka lafiya ƙalau ta koma gida batare da tunanin wani abu ba.

Tana shiga falon da sauran gudunta inno dake zaune ita da Najib wanda yake dakon dawowar Bintu,tace" Bintu lafiyar ki kuwa? ɗan tura bakinta tayi kafin tace" wani A bu ya shigo falon cikin sallama,inno tace au ko dai tare kuke ne? Bintu cikin gunguni tace" da inno a'a daga get suka ɗaukoni!'inno tace" ashe taimakonki akayi amma kike wannan shegan taka!'bi yayi ta gefanta ya shige batare da ya tanka ba, tana ganin ya wuce ta dubi inno cikin ɗan shagwaɓe fuska tace"Allah kuwa inno tsoro yake bani shi bashi da aiki sai bawa mutane tsoro!'inno tace" ikon Allah dama mutum yana bawa mutum tsoro? A to inno shi dai kam yana bayarwa!'ta faɗa tana shigewa ɗakinta,daga inno har Najib dariyar wautar Bintu sukayi..

Yana shiga bedroom ɗinsa kai tsaye ya wuce toilet bayan ya Ajiye jakar shi,ya ɗan jima kana ya fito ya shirya cikin gaggawa saboda kiran sallar la'asar da akayi,fes ya fito cikin shigar sa ta yau da kullum wato kananan kaya sai ƙamshinsa da ya game ɗakin gaba ɗaya, yana fitowa ya wuce Pert ɗin Alhaji Baba Dan yasan yana can yana jiransa dan zuwa Masallaci dan tunda ya fara zaman gidan kwana biyu suka koma tafiya tare kamar yadda sukeyi da Asuba, amma yanzu ba Alhaji Baban ne yake zuwa ba shi yake zuwa su tafi tare wanda da ƙyar da lallashi Alhaji Baban ya yadda da haka.

Tofa yau dai kasuwar ESTATE ce take ci dan kuwa kowa da baya gida ya dawo yaran masu gida ƴan makaranta duk sun dawo ɗan gidan Alhaji Mansur saiyid da yaran Baba Ali guda biyu Sadik da lamin duk A yau suka dawo ƙasar su cikin gidansu kuma ahlin ALHAJI BALARABE,

Sai mata da suka dawo daga b.u.k kano taufiƙa da siddiƙa ƴaƴan sadiya, kasancewar ita ba A Nigeria tayi aure ba tana can ƙasar camaroo jikokin inno kenan kuma duk A sashen inno zasu zauna, dama sunce idan suka gama karatu bazasu koma camaroo ba dan haka sai da Bintu tayi gyaran ɗakinsu,

A yayi da su kuma samarin suke ɓangaren su daban A yanzu dai samarin gidan sun kai su shida, sai ƴan mata guda bakwai wanda suke rayuwa A cikin estate, Alhaji Baba ya aurar da jikoki kusan goma sha biyar maza da mata ba iya kacin na gabansa ba kawai har na sauran garuruwa.

Rahima da amna suma sun dawo ita kuwa Hauwa'u dama tunda Abdallah ya dawo estate ta daina zuwa ko ina.

A wannan rana Bintu ta aikatu iya aikatuwa, shi kuwa girkin oga Abdallah dama babu ɗaga ƙafa,ba ita tasamu zama ba sai ƙarfe tara na dare,yayin da jikinta yake A sanyaye saboda yadda ƴan matan suka dinga kyararta da nuna mata asalin matsayinta,ta fuskanci taufiƙa da siddiƙa suna da matuƙar jin kai da ɗagawa yayin da Farida take da mugun wulaƙanci kuma A kwanta da baƙar magana, itace auta A gurin babanta Alhaji Habib kuma A cikin ƴaƴan da ya haifa duka mata ita kaɗai ce bai aurar ba,Rahima da amna su kaɗai ne sukewa Bintu kallon mutum.

Washe gari dawowar su, Bintu tana kiching tana ta sauri ta haɗawa oga Abdallah kayan karin kumallo saboda yau taso ta ɗan makara kasancewar gajiyar da ta tara A jiya, siddiƙa ce ta shigo cikin kiching ɗin tana mussika ido alamu dai ya nuna yanzu ta tashi daga bacci,A lokacin kuma Bintu ta gama haɗa komai tana shirin fara ɗauka dan kaiwa ta jera masa A falonsa,dubanta siddiƙa tayi tana wani ya tsina fuska kamar taga kashi tace"ke bani break ɗin nan da yunwa na tashi safiyar yau!' cikin nutsuwa Bintu tace"wannan ai na Oga Abdallah ne kuma ba a haɗa masa abinci da kowa shi kaɗai nakewa ki bari na kai masa sai nazo yanzu na haɗa muku wani!' tunda Bintu ta fara maganar take Binta da wani matsiyacin kallo irin na ke ɗin wacece,dan haka bata bari Bintu ta haɗiyi miyau ba ta fara sauke mata kondon rashin mutunci cikin ƙasƙanci tace" ke ɗin wacece?kuma ƴar gidan uban waye da har zaki hanani Abinda ya kasance ikona? ta daka mata wata gigitacciyar tsawa mutuniyar tuni ta gigice jikinta ya shiga rawa Bintu in da Akwai abinda ta tsana A rayuwarta to bai wuce tsawa ba, babu A binda ke saurin ruɗa ta kamar tsawa shiyasa take da matuƙar jin tsoron ruwan sama,kafin wani sakon hawaye sun fara mata ambaliya,ganin hakane yasa Siddiqa tayi saurin ƙwace tiren hannunta tana ci gaba da watsa mata ba zan kallo,cikin tsoro biyu da ya haɗar mata tace"dan Allah karki tafi dashi duka ki ɗiba iya wanda zai miki wallahi shima..bata ƙarasa ba taji tas an wanke kyakykyawar fuskarta da mari,runtse idanun ta tayi kana ta buɗe su a hankali saboda nauyin da sukayi mata,taufiƙa ce tayi mata wannan marin tana tsaye a gabanta tana mata kallon gargaɗi,tace" ke har kin isa ƴaƴan masu gida su buƙaci Abu ki hanasu ke ɗin wacece idan kikayi wasa sai na lalata wan nan banzar fuskar taki,idan baki sani ba to yau kisani mu ba A takamu ko A makaranta abinda muka gadama mukeyi bare kuma A cikin gidan mu!'kallon siddiƙa tayi tace maza kwaso mana break ɗin duka bari na yiwa Farida waya da Hauwa'u su zo mu karya anan!' siddiƙa ta bata hannu suka tafa kana suka kwashe komai sukayi waje dasu.

Dur ƙushewa Bintu tayi A wajen ta saki kuka mai ban tausayi,ta yaya A cikin ɗan lokacin da Oga Abdallah yake bata ta kammala masa break zata yi ƙoƙarin sake haɗa wani, lafiya yan kunun gyaɗa tayi masa da farfesun kan saniya sai ƙosai da tayi masa wanda yaji attaruhu da albasa da kwai sai ruwan liptom data haɗa masa da kayan ƙamshi,ko ita ɗin injice ai dole ta ɓata lokaci,sauri tayi ta miƙe dan fara sarra fa kayan, wake ta kuma ɗebowa ta gyara ta zuba A blender kana ta ta ce gyaɗa ta ɗora akan gas,

Shi ko Abdallah tunda yaga ya gama shirinsa ba a kawo break ba ya samu guri ya zauna yana ci gaba da aikinsa A laptop,wani irin yunwa yaji na nuƙurƙusar hanjinsa dan haka ya miƙe ya fito falon inno ko da zai ci karo da dalilin da ya hanata kawo masa break bayan yaga alamun ta gyara ko ina na falon da ɗakin bayan dawowarsa daga motsa jiki,zama yayi yana fuskantar ƙofar kiching ɗin..

Saura ƙiris ta kammala komai, su taufiƙa suka dawo kiching ɗin hannayensu ɗauke da kwanikan abincin saurin karɓar kwanikan tayi dan har da su a fargabarta tun da a cikin saitin kayan Abdallah suke, taufiƙa ce tace yauwa kinga Farida ba sai mun jira ba ma tunda ta kusa kammala wannan sai kawai muje mu ɗora dasu!' wani irin zaro ido Bintu tayi yayin da zuciyar ta ke wani irin bugu da sauri da sauri tasa hannu ta dafe ƙirjinta..

Comments....

Vote......

Share.... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` ***

*_____________________________________*