Page 53
Innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un,t faɗa tana da ɗa murza idanun ta cike da mamakin wadda ta gani,ba ƙaramin shock ta shiga ba ganin matar dake tsaye gaban ta,cikin tsananin ruɗani da mamaki gami da tashin hankali take nunata da yatsa bakinta yana rawa ta gaza furta abinda take son furtawa,zuciyar ta babu abinda take sai ta riyo mata irin karamci da Mutuncin matar,kai ita Dije ma zata iya cewa duk gidan Alhaji Baba babu macen da tafi kirki da mutunci a idanun ta kamar wan nan dake tsaye agaban ta,ta tuna lokacin da tazo gidan amatsayin mai neman masauki,itace wadda ta fara karbar ta,tare da bata masauki kafin daga baya ta haɗa ta da ɓangaren Dady Mansur,to hakan yana nufin duk shiri ne?dama da manufa tayi mata hakan?lallai kuwa idan haka ne wannan mata ta cika cikakkiyar makira kuma shu'ma,zilwaja haini,katse Dije tayi da cewa,kinyi mamaki ko Dije?to amma kuma idan kika bi ta wani fuskar ai ba wani abun mamaki bane,yanzu dai duk ba wannan ba abinda nake so dake shine ki tashi ki tattara yaranki da komatsanki zan baki kuɗin aikin ki,ki bar garin Abuja gabaki daya kiyi nesa da ita,bana buƙatar ganin ki acikin garin nan,saboda hakan shine rufuwar asirina!'Dije bata ce komai ba, sai miƙewa da tayi ta haɗa hannuwan ƴaƴan ta suka fara tafiya,matar tace"Dije baki ce komaiba me shurun ki yake nufi?Dije ta ɗan dakata ba tare da ta juyo ba tace"babu abinda shuru na ke nufi sai Alkhairi,kuma bana buƙatar komai daga gareki tunda kin riga kin cika alƙawarin da kika yi min haka ma na gode!'daga haka ta ja yaran ta suka yi waje, zuciyarta cike da baƙin cikin rashin Bintu ko Abdallah a wajen,gashi yanzu bata san yadda za ayi ta haɗu dasu har ta fayyace musu abin da ke faruwa ba.
Wata mashahuriyar dariya ta fito tanayi wadda ke nuni da tsananin farin cikin da take ciki ji take kamar ta samu Abubakar ta gama,gashi kuma ta toshe duk wata hanya da zata iya tona asirin ta,dariyar tace ta tsaya lokacin da tashiga dakin Laila,zubawa ɗakin Ido tayi cike da razani da tunanin inda Laila ta shiga,da sauri ta buɗe ƙofar toilet ɗin dake ɗakin, dubawa ta shiga yi loko da sako,amma babu Laila babu labarinta,cikin wani azababban sauri ta fito tana ƙwalawa masu tsaron su kira,cikin rawar jiki duk suka nufota yayin da ita kuma ta waɗa dakin da fafi yake ciki,ga tsananin mamakinta shi ma baya nan, babu komai aɗakin sai tarkacen kwanikan da ake basu abinci,ihu ta saka tare da zunduma musu wata iriyar gunndume miyar ashar,cikin tsawa da yanayin hauka hauka na zaucewar tunani take cewa,me kuke yi suka gudu? kuna ina aka sace su?ɗaya daga cikin sune yace"ai Hajiya lokacin da kuka shigo gidan nan daga dakin su nake na kai musu abinci!'babban cikin su ma yace"tabbas Hajiya lokacin da kuka zo gidan nan ajiyar ki suna nan,sai dai idan bayan shigar mu dakin nan ne suka gudu!'zubewa tayi agurin cikin ɗora hannu aka take cewa shike nan asirina ya tonu,ya akayi na bari haka ta faru?ya akayi akasan da gidan nan duk takatsan tsan ɗin da nakeyi?dungu yace"Hajiya anya kuwa matar nan tana da gaskiya?anya bata haɗa miki gadar zare ba?wata irin zabura tayi cikin ihu tace"ku bi Dije ku samo min ita duk inda take,ku kawo min ita nan!'ta faɗa tana sharce gumin da yake ta wanke mata fuska,da gudu suka bazama neman Dije.
To ya akayi Dije ta shammace ta haka?tabbas babu wanda ya isa yazo gidan nan sai wanda ya biyo bayan su,to waye ya biyo bayan su?wata zuciyar tace mata Dije ta riga ta shirya komai kafin haɗuwar ku,tabbas wannan shirin dagaDije ne makircin daga Dije ne,dama sun shirya yin komai ita da Bintu,to ya akayi BINTU tasan cewar iyayen ta suna wajenta?a kwai fa matukar ɗaurewar kai a cikin wannan al'amari,bata ga ta zama a wajen nan ba,dole ta tafi estate ta kasa ta tsare taga daga inda al'amarin ya ɓullo.
Dije tana fita ta ɗauki hanya, sauri suke tamkar zasu tashi sama,saida sukayi dan nisa daga gidan kana suka tsaya maida numfashin gajiya,kamar daga sama suka ga mota A gaban su,kafin ta gama mamakin yadda akai mota tazo nan,taji Muryar Abdallah yana cewa yi sauri Mama Dije ku shigo!'Dije bata tsaya sanya ba da a zama ta tura yaran ta cikin motar kusa da fafi,itama ta shiga,da wani azabar gudu Abdallah yaja motar kafin ƙiftawar ido sun bace sai ƙurar motar sa,a daidai lokacin kuma yaran Hajiya suka ƙaraso gurin basu ga mota ba sai ƙurar mota,a take kuwa zargin su ya tabbata,juyawa sukayi jiki a san yaye,dan sun san zasu sha bala'i gurin Hajiya.
Wai Abdallah har gida nawa ne dashi ne?nice nayi wa kaina wannan tambayar,ganin ya kuma kawo su Dije da Laila wani gidan mai shegen kyau, A hankali ya fito da fafy daga cikin motar,Laila ta kama hannun sa suka shiga takawa su Dije na binsu Abaya,sai da ya kai fafy har cikin daki yayi masa duk wani abu da ya kamata,kama daga karin ruwa allurai da sauran su,kana ya Umarci hafiz ɗan Dije da ya zauna a dakin tare da fafy ya dinga kula dashi,su kuma ya wuce dasu sama inda ya bawa Dije da salma ɗiyar ta daki ɗaya,daga nan kuma ya kai ummi Laila lafiyayyan ɗaki,sai alokacin yayi magana da ita,duban ta yayi cikin nutsuwa da girmamawa yace"Ummi ga nan dakin ku zauna a gidan nan gaba dayan ku,saboda kuna bukatar tsaro gaba dayan ku!'juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya sakamakon jin muryar da yaji tamkar Bint ɗinsa na magana, tace"samari ya kamata kayi min bayanin ko kai waye da kuma dalilin taimakon mu da kayi? ɗan murmushi yayi wanda sai da zuciyar Ummi Laila ta buga sakamakon ganin tsananin kama da ta hanga kan fuskar sa da kuma yanayin sa da mutumin da baza ta taɓa mantawa dashi arayuwarta ba,yace"karki damu ummi yanzu kuna buƙatar hutu zakiji duk abinda kike bukatar ji,amma kiyi haƙuri yanzu da akwai babban matsalar da nake son warwarewa,yanzu zan aiko muku da abinci!'ya faɗa yana ficewa daga ɗakin,zuru tayi tana daɗa kure bayan shi da takun shi da kallo,sak Umar ɗina ta faɗa tana waɗawa toilet dan yiwa jikin ta kyakykyawan wankin da ya dade bai samu ba.
Abdallah bai bar gidan ba sai da ya tabbatar su ummi basu da wata matsala,har satar kallon ummi Laila yake saboda yadda take masa tsananin kama da Bintun sa gashi kuma tayi wanka tayi fes da ita cikin doguwar abayar da ya siyo mata,shi yasa duk damuwar sa ta karu ya ƙagu da yaga lafiyar Bint,tazo ta ga ya cika mata alƙawarin da ya ɗaukar mata akusa,yana matuƙar san ganin farin cikin ta wanda kuma hakan bazai taba samuwa ba har sai ya kuɓutar da ita daga hannun wani can azzalumin ya kuma kawo ta gaban ummin ta da fafyn ta, Daniyal ya kira ya kawo musu take away,kana ya umarce shi da ya zauna tare da su ya kula dasu A matsayin sa na namiji kuma ma aikacin tsaro,daga nan fita yayi shi kaɗai ya ɗauki Dady jafar A gida suka nufi inda suke son zuwa,tashar jirgin sama suka nufa inda suka haɗu da wani farin Bature, daga Ni ma dai ya ɗan jima yana jiran zuwan nasu,bayan dan gaisuwa ta mintuna ya miƙawa Abdallah saƙon hannun sa yana cewa gaskiya kayi sa a, sosai da samun wannan sakon a cikin kwana ɗaya da yini ɗaya! murmushi kawai Abdallah yayi ya juya suka bar tashar.
Dady jafar ya ɗan dubi Abdallah kana ya maida kansa zuwa hanyar da suke bi,yace"yanzu meye mafita ta ɓangaren samun kiran nasa,kaga mun gama shirin mu yanzu shi muke jira!'abdallah yaɗanyi slow da motar kana yace"nima tunanin da nake kenan!'bai gama rufe bakinsa ba, sai ga wayar mutumin,da sauri Abdallah ya ɗauka yana mai fatan samun nasara tunda ya gane ko waye yake kiran,ba tare da ya bari ya saurari abinda zaice ba Abdallah ya tari numfashin sa da cewa,ɗan zaki ya shirya zuwa karbar zakanyar sa!'wata irin dariyar mugunta ya sheƙe da ita kana yace"yauwa ɗan zaki ka kyauta,ke nan ka shirya zuwa inda zaka samu zakanyar ka!'yace"kai nake saurare?cewar Abdallah ke nan,da zuciyar sa ke wani irin tuƙuƙi saboda sauraran Muryar wannan baƙin ƙumurcin,nanu yace"ina mai kuma yi maka gargaɗi akan zuwa da wasu mutane ko kuma jami an tsaro,yin hakan daidai yake da rasa matar ka da mahaifinka,nayi alƙawarin kashe su koda zan rasa rawa rayuwar kuwa!'cikin ƙosawa Abdallah yace"ina jiran address wannan duk na dade da kiyaye su!'hakan yayi kyau ɗan zaki,ka kalli fuskar wayarka zata haska maka inda zaka same mu ba tare jinkiriba!' Dady jafar ya dube shi da sauri yace"maza muje mu dauko Abubakar ɗin kar lokaci ya ƙare!'cikin hikima suka karbi Dady Abubakar daga wajen Malam na zaure,daga nan kuma sai suka dauki hanya,yana tafe yana waya dasu Safwan akan shirin kama su Alhaji Hashir da Alhaji Nasir da dai duk sauran ƴan tafiyar su,
A can kuma su Abba Umar wani ɓoyayyen gidan sa ya kaisu su Hajjo,tare suka ɓoye kansu,dan gabatar da shirin da suka shirya,
Da sauri ta ɗaga wayar da tun ɗazu tana hannun ta dan ta kasa ajiye ta gani take kamar labarin wani abun zai iya wuce ta,cikin sauri tace"ya akayi ina fata dai komai ya kammala?bansan amsar da aka bata acan ɓangaren ba sai kawai ta sheƙe da dariya cike da farin cikin samun nasara akan burin rayuwarta,tace"Barka" inawa kaina Barka kafin nayi muku Barka da arzikin dake bunku yadda kuka cika min burina nima zan cika muku alƙawarin da nayi muku dan haka yanzu ina jiran shaidar kashe su da kuma asusun bankin ku!'kashe wayar tayi ta bar su da sakin baki gaba dayan su wayar suke kallo yayin da suka shiga tunanin yadda za ayi su tura mata shaidar kisan da tasaka su aikata,sai dai kuma abunka da ƴan ta adda waɗan da suka saba aikata kisa a kowane lokaci kuma su ajiye record saboda wata rana,shi yasa basu sha wuyar turawa Nafisa fake ɗin gawar Abba Umar ba,sun tura mata kuma shirin su yayi daidai da irin ƙwaƙwalwar Anty Nafisa dan bata gane komai ba tunda ita dai taga gawar mutum kuma taga ƙonannen gida bata da wata damuwa,take ita ma ta tura musu kudaden su, zuciyarta fes bata da wata sauran damuwa sai ta cin duniyar ta da tsinke.
Cikin sauri ya gaida Hajjah ba tare da ya zauna ba,hakan ne ke nuni da irin saurin da yake dan fita daga gidan, zuba masa ido Hajjah tayi ganin yadda yake ta share gumi ga kuma yawan kallon agogo da yake yi,cikin tsare shi da ido tace"wai Mansur saurin me kake yi ne haka,gaba ɗaya ka kasa zama ba daban Ni nayi kiran ka ba ma ina ga bazaka zo ba!'ta faɗa tana daɗa tsare shi da mahukuntan idanunta,cikin ɗan sosa kai yace"wallahi Hajjah da inda zani kuma zuwan yana da muhimmanci!'tace"shi wajen bashi da suna?girgiza mata kai yayi yana ƙoƙarin tashi,ba tace"masa komai ba sai ido da tabi shi da shi.
Yana fita ya shiga mota wanda da alama bashi kadai ne cikin motar,kasancewar duhu ya farayi shi yasa ban kula da wanda ke zaune a bayan motar Ba,figar ta yayi da matsiyacin gudu,itama cikin sauri ta shiga motar ta tare da figarta a tsiyace,tana cewa Mansur bazan bari ka tseremin ba dole sai na ga inda kakai Abubakar kuma sai na kwato shi a yau ba sai gobe ba!'ta faɗa tana ɗan danna wayar ta,wanda da alama kira takeyi,cikin sakanni kuwa aka daga wayar,ba tare da ta saurari wani zance ba tace"ina fatan kuna nan inda nasa ku tsaya!'daga can aka amsa mata kana tace"yauwa to gamu nan yana fitowa kubishi Abaya Ni kuma zan biyo ku kar ku sake ku bari ya tsere muku haka kuma kar ku bari ya fuskanci ana bin bayan sa!'daga haka ta kashe wayar ta ci gaba da bawa motar ta wuta.
Dady jafar ya kalli Abdallah cikin gajiya da shiga wannan uban surƙuƙin dajin,yace"anya kuwa Abdallah ba yaudarar mu yayi ba? Amma ace dan Adam ne yake shiga gurin nan babu gida gaba babu baya!'abdallah ya dage kanshi tare da cewa tunanina kawai shine halin da Bint take ciki!'daga haka basu kuma magana ba har suka zo wajen da yayi daidai da zanen kwatan cen da yake kan wayar sa,ɗan slow suka farayi tare da yin ƴan dube dube saboda ko bukka basu gani awajen ba bare gida,gashi kuma inda aka zana taswirar akwai gida a wajen,tsayawa sukayi tare da zubawa dajin ido wanda yayi tsit baka jin kukan komai sai na tsuntsaye,kamar daga sama sukaji ance, sannun ku da zuwa ɗan zaki,munayi maku maraba kaida jajirtaccen uban riƙon ka,ku fito daga cikin mota ai kun zo inda kuke nema!'daga haka gurin ya kuma ɗaukar shuru kamar yadda yake a farko,da ambatan Bismillah da addu o in tsari suka fito daga cikin motar,ga tsananin mamakin su suna fitowa suka ga tafkeken gidan da babushi a farkon zuwan su,ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗauko Dady Abubakar dake san ƙame kamar gawa,suka shiga cikin gidan ba tare da sun tsagaita da ambatan Allah jalla wa'azza ba.
Wani fili suka fara tararwa kafin su dan gana da ƙofar da suka gani tana kallon su,itama kai tsaye suka shigeta ba tare da jin tsoro ko wani ɗar atare dasu ba,sosai suka shiga gidan da yake da wani irin zurfi ga wani irin duhu da ya mamaye gurin gaba ɗaya, da taimakon Allah kawai suke samun inda zasu jefa ƙafafunsu,gajiya sukayi da shiga inda basu sani ba kuma basu da tabbacin akwai mutane agurin,suna tsayawa haske ya gauraye wajen,bin ko ina suke da kallo cikin mamakin mutanen da suka gani agurin,kallon juna sukayi kana suka maida kallon su kan mutanen da suke zaune wasu kuma a tsaye,da wasu irin jajayen kaya ajikin su sai zane dake kan fuskar su,zasu kai kimanin su ashirin da ɗoriya,babu wanda ya tanka acikin su duka, sai daga can baya akayi magana da cewa Barka da zuwa ɗan zaki tabbas kacika ɗan halak wanda ke saka Alkhairi da halacci,ga kuma soyayya mai tsanani wanda bantaɓa jin ta ko ganin irinta ba,maza ka miko min mahaifin ka Ni kuma na miƙa maka matar ka!'Abdallah yace"ba haka mukayi da kaiba,dole sai naga lafiyar Bint kafin na baka mahaifina!'wata shegiyar dariya ya sheƙe da ita kafin yace"yaro kar ka manta fa fada ta ka shigo dan haka gaddama ba taka bace,kawai kayi abinda na saka ka inda ba haka ba zan nuna maka ƙarfin iko na,ko dake ma bar shi dama na sha alwashin ta hanyar ku zan samu cikar burina dan haka yanzu agabanka mahaifinka zai buɗi baki ya sanar dani inda suka ɓoye wannan dimon ɗin!'take ya shiga yin wasu siddabaru duk da yasan ba lallai ne yayi ba,yana kuma daga inda yake ba tare da ya fito su Abdallah sun ganshi ba,kafin ƙiftawar ido Dady Abubakar ya fara wani irin jijjiga kafin wani lokaci jikin shi ya saki yana fitar da wani irin numfashi,da sauri nanu ya fito daga inda ya ɓoye cike da mamakin farfaɗowar da ABUBAKAR yayi ba tare da yayi masa wani aiki ba dan siddabarun da yayi yanzu gwadawa kawai yayi tunda yanzu bashi da karfin siddabaru kamar da.
Cike da tsananin mamaki Abdallah ke kallon shi cikin rawar baki ya nuna shi tare da cewa"Dady Mansur kai ne dama?Dady jafar yace"haba Abdallah me na gaya maka ai Ni ban yi mamaki ba saboda duk wasu alamu sun gama nuna Mansur a fili!' cikin wani taku irin na taƙama ya ƙaraso gaban Dady Abubakar wanda ya buɗe idanun sa tsaf yana bin Mansur da wani mugun kallo,hannu yasa ya ɗago habarsa yace"dan uwa yau fa ka dawo mutum ina tayaka murna,ya faɗa yana jifan su da wani shu'umin murmushi, Abdallah kuwa kallon da yakewa Dady Mansur hatta Dady jafar saida ya nutsu dan son gano ma'nar kallon.
Tun da suka zo suna bakin gurin sun rasa inda Mansur yashiga basu san ta hanyar da yabi ba,domin su dai basu ga gida ko wani waje dake nuna alamun da mutane a wajen ba,tashin da tashiga ba mai misaltuwa bane, wannan aishene ta tasamu yanzu kuma tana shirin ganin rashi,to ina wannan shu'umin ya shiga da har ya ɓace musu,gashi dai tabbas basuyi kuskuren hanya ba,daga ita har yaran nata cirko cirko sukayi suna jiran tsammani.
Ɓangaren Abba Umar kuwa,sai da suka ɗan samu nutsuwa,kana yake bawa Hajjo labarin abinda ya faru tsakanin sa da mutanen nan masu kashe su,yace"Hajjo na fahimci cewa kudi shine matsalar su dan haka sai na siye su dashi kamar yadda aka basu aikin kisa akan su to barin aikata kisan ma bazai gagara su barshi ba,dan haka sai nace dasu ya fadi farashin da akabasu Ni kuma zan ninka musu sau biyar,yadda dai ya sanar dani za abasu dubu ɗari biyar dan haka ni kuma nace zan basu miliyan biyar, su rabu dani kuma suje su cewa wanda ya saka su sun yi abinda aka umarce su,to kinji dalilin da yasa basu kashe mu ba!'Hajjo tace"ikon Allah idan kana da kuɗi babu abinda zai gagareka haka kuma idan kana dasu kana cikin tashin hankali, Allah dai yasa mu dace!' da Amin suka amsa shida Asma'u.
A ɓangaren su Safwan kuwa sunyi abinda ogansu ya umarce su,dan kuwa cikin kankanin lokaci suka kama su Alhaji Hashir da tawagar su,lokacin da Alhaji Sama'ila ya ga Samira acikin jami'an tsaro na farin kaya,sai da ya suma,Samira ce da kanta ta zuba masa ruwa ya farfaɗo amma yana kuma haɗa ido da ita sai ya kuma shekawa,da ta kuma zuba masa ya farfaɗo zai koma kenan ta daddage ta sheƙa masa marika har guda biyu hagu da dama,wani irin ƙayataccen murmushi ta saki na samun nasara da cin gari,tace"Sama'ila sakarai ko da yake sakarcin ka ya matuƙar taimakamin,dan da baka kasance wawa ba da nasan ba lallai ne nasamu nasara kamar yadda nasamu yanzu ba!'zuba mata ido yayi idanun sa na ruwan hawaye ga wani irin yaji kamar zasu waɗo ƙasa,ta cigaba da cewa,Ni ɗin ƙaryace gabaki ɗaya na gaibuce labarina gaibune amma awajen ka,rayuwata tare da kai ka ƙaddara amafarki kayita yayin da gaskiya ta bayyana a farke,kuma ƙaryarka ta ƙare a farke,dariya tayi irin ta tura haushin nan,kana ta miƙe daga durkusan da tayi a gaban sa,tana cewa Sama'ila na gode fa da aikin da kayi min nasaka wahalafa da yawa to amma dai babu damuwa tunda gashi yanzu soyayya tayi rana,tunda ta ƙure ƙaryar masu ƙarya!'daga haka suka fita daga ɗakin da aka lodasu,wani irin ihu Alhaji Sama'ila ya saka tare da rushewa da wani irin kuka mai cike da nadama da takaici,sauran kuwa basu da bakin magana duk da suna so su magantu saboda tonuwar asirin da Sama'ila ya jawo musu,da kuma zubewar mutuncin su,gemai gemai dasu an watsa su a kurkuku kamar wasu karnuka,hmm kaɗan ma kuka gani dan indai akan ha inci da hassada da yaudara ne to baku ga komai ba kwarankwatsa dubu....
Daga ɓangaren su Laila kuwa tunda Abdallah ya fita suka taru gaba dayansu a falon,Laila ce ta fara neman da su gabatar da junan su,dan tana son sanin su Dije da kuma abinda ya kaisu gurin nan,Aikuwa ba tare da ɓata lokaci ba Dije ta bawa Ummi Laila duk kanin labarin abinda ke faruwa a cikin zuri'ar Alhaji Balarabe,abinda kawai da bata faɗa ba shine Bint saboda Dije har yanzu bata fahimci inda maganar matar ta nufa ba bare zuciyar ta ya kawo mata cewa mahaifiyar Bintu ce wannan,sai kuma labarin Nafisa wanda bata san duka al'amuran ba,kuma ganin ta bai shafi Lailan ba,ita dai ummi ba tacewa Dije komai akanta ba tunda ta fuskanci bata sani ba.
Cikin son nuna ƙarfin ikon sa,da kuma aiwatar da ƙudurin sa yasa afito da Bintu,lokacin da aka fito da ita hannayen ta ɗaure bakinta kuwa duk yayi alamun jini jini kana dubanta kasan tasha marika,da wani irin sauri Abdallah ya nufeta,sai dai kan ya kai ga ƙara sawa yaji an riƙeshi ta baya ita kuma Bintu wani ya saita wuƙà amaƙoshinta,Dady Mansur yace"yaro ka tsaya iya matsayin ka na gaya maka nan fadata ce"idan ka kuskure abinda nake so yanzu zan sa afarke min wuyar wannan ƙwailar matar taka!'Dady jafar ne yayiwa Abdallah alama da yayi hakuri su gabatar da shirin su ba tare da sun samu tangarɗa ba,hakanne yasa Abdallah danne zuciyarsa, Bintu kuwa duban Dady Mansur take ita ma cike da mamaki dan tunda aka kawo ta gidan bata taɓa ganin shiba,dawo da hankalin ta tayi kan Dady Abubakar da yake magana ƙasa ƙasa irin ta majinyata yace"bazan taɓa sanar da kai abinda kake son sani ba sai dai ka kasheni!'dariya Dady Mansur yayi tare da cewa yo ai bakai zan kashe ba kaga waɗanda zan kashe,wata ƙilma na haɗa da ɗan raino!'ya faɗa yana kallon Dady jafar,cikin abinda bai wuce sakanni ba, Bintu ta dinga tariyo Muryar a ƙwaƙwalwar ta tana kuma auna a wajajen da take jin muryar da kuma fuskar mai Muryar,kamar an fuzgo maganar daga bakinta,haka kuma tamkar dirar mikiya su Abdallah sukaji maganar,nunashi tayi da yatsa bakinta na rawa tace"YAH,,,ABDALLAH WALLAHI,,,,WANNAN BA DADY MANSUR BANE DADY HABIB NEE,,,......
Wash
Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` ***
*_____________________________________*