13
by @legendspen
(13)
(Not edit)
“Bangane ba Sardauna! Bangane ba?”
Na faɗa ina miƙewa.
“Na ce ki zaɓa ‘yan uwanki ko ni?”
Wani abu na ji ya daki zuciyata, bansan haka nake ba sai yanzu, nasan dai ina son ‘yan uwana amma bansan zan iya zaɓarsu akan Sardauna ba sai yanzu.
“ ‘Yan uwana mana.”
Ya kalle ni sosai sannan ya ce.
“Nana ‘yan uwanki?”
“Ina son su, suna sona Sardauna.”
“Ni bana sonki Nana? Bana sonki? Wannan shine sakayar soyayyar da zaki yi min?”
“Sardauna ina sonka! Ina sonka, matsayin miji kake da shi a wajena mutum mai daraja a rayuwata sama da kowa, amma tabbas ‘yan uwana abun so ne, kaima kana da su kana son su, kuma na zaka juri na yi wani abu mara kyau akam su ba.”
Zama ya yi akan kujera, sannan ya ce.
“Nana ni mijinki ne, dole na yi kishinki sun san dalilin da ya sa bana son ki yi karatun? Sabida ina da kishi mussaman na ki, ban taɓa kishin wata mace a duniya ba sama da ke, Nana wallahi har cikin zuciyata nake kishinki bazan iya jurar gani kina fita kullum ba, bazan iya ba. Amma idan sun dage shikenan Nana zan sauwaƙe miki kije ki yi karatun acan, dan dama na fuskanci so suke su raba mu, zan bar musu.”
Ban taɓa tunanin jin wannam kalmar daga bakin Sardauna ba ko a mafarki, sai da na ji gabana ya yi wani irim faɗuwa. Na ɗaga kai na kalleshi amma na kasa magana, kawai na tsinci kaina da shigewa ɗaki na barshi s wajen.
“Rabuwa da ni Sardauna akan karatu? Tabbaa Sardauna baya son karatun nan, kuma hujjarsa ɗaya ita ce kishi, amma ai abinda kake so shi kake kishi, tabbas yana sona, nasake tunani.”
Haka na yi ta ƙulle ƙulle da kwance kwance a cikin raina har wayewar gari, bayan na kammala masa abun karyawa ya ci na koma ɗaki, kasanxewar yau weekend ne bai fita sai rana kuma na ji yana cewa wai yau Big Daddy zai dawo, ko waye hakan oho masa.
Ina zaune cikin ɗaki bayan na sanar da Yaya Radiya yadda muka yi da shi, tana ta mamakin yadda aka yi baya son karatu har haka, kuma gasu gidan ‘yan boko? Ni kaina abun ya ɗaure min kai sosai da sosai. ‘yanzu Sardauna ya sake ni ina na kama ni Nana, zan iya rayuwa ba na jin numfashim Sardauna a kusa da ni kuwa?.’
Irin tambayoyin da nai ta jefawa kaina kenan har zuwa yamma, ko ayyukan gidan bansami damar yi ba sai da yamman, ina cikin aikin su Yaya Radiya da Yaya Ridwan da Ra’is suka zo, nasan akan maganar ne sabida ba sa so Alhaji ya san da maganar, ni kam Allah Ya gani karatun ya sauka daga kaina, amma an sauke min shi haka na ji, kalmar saki ta girgizani.
“Wai dagaske kike sakinki ya ce zai yi?”
Yaya Radiya ta faɗa cike da ruɗewa, bayan na gama gaya mata abinda ya ce da ni.
“Wallahi Yaya, sai na ji gaba ɗayan na tsorata.”
“Kuma kina ganin dagaske yake?”
Ra’is ya tambaya.
“To nima bana ce ba, amma fa yau ko magana ba mu yi da shi ba, kawai ya ce duk abinda na yanke ya yi daidai.”
“Amma mijin nan naki ɗan iska ne, bai da mutunci.”
Ra’is ya faɗa, na watsa mai harara, sannan na ce.
“Bana ciki da iskanci.”
“Ridwan mene abun yi yanzu?”
Yaya Radiya ta tambayeshi.
“Ya bata zaɓi biyu, ko ta yarda da karatun ta rabu da shi, ko ta zaɓeshi ta rabu da karatun farin cikin iyayenta, tun a farkon mu’amalal su Nana ita ce ta bada kanta, na faɗa karta ta sawa ranta wai alfarma zai yi mata kowani abu. A gani na farko da na yi musu tare na gane soyayyarshi ta yi wa Nana mugun kamu, sannan ta bada kanta, ta zubar da darajarta, ina mugun jin kishin wannan abun? Ƙin kulashi ko shiga al’amuran da naƙi yi ba wai son shi ne bana yi ba, a’a zallan kishi ne bazan iya jurar gani tana ƙasƙantar da kanta ba, a matsayina na ɗan uwanta, jininta Nana kina tunanin wai idan muna yi wa samarinku wani abun haushi ne ko tsana? Tun a lokacin abinda na guda mata kenan, amma bata gane ba, a yanzu idan ta takura wallahi tsaf zai iya sakinta, ya mayar da ita ƙaramar bazawara ya cuceta.”
Wani irim tsoro ne ya ratsani, ace Sardauna zai iya sakina, bana fatan wannan ranar wallahi na haƙura da karatun, ba zan ba chaɓ.
“To yanzu mene abun yi? Shikenan duk wani burin Alhaji ya tashi a banza, shikenan?”
Yaya Radiya ta faɗa, ni kam a raina ma ce.
“Alhaji zai fahimta, zuciyar Alhaji tana da ƙwari zata iya ɗaukan hakan, ni kam bazan iya ɗaukan ƙaddarar rashin Sardauna ba.”
“Nana me kika yanke?”
Yaya Radiya ta tambayeni.
“Na haƙura wallahi, na fasa karatun bazan iya ba.”
Na faɗa ina zubar da zafafan hawaye, ni kaina nasan ba abinda ke cikin zuciyata ba ne, amma bani da wani abun yi da ya wuce wannan.
“Kin haƙura da karatun fa Nana?”
Ra’is ya faɗa, na gyaɗa kai sannan na ce.
“Ra’is ya zanyi, tunda ba ya so kuma ya riga da ya aureni ba yadda zan iya.”
“To sai me dan ya rabu da ke? Sai me?”
“Ra’is ba zan iya ɗaukan ƙaddarar rabuwa da Sardauna ba, zuciyata tana da rauni.”
“Amma ai zaki iya ɗaukan ƙaddarar rashin mahaifinki ko?”
Yaya Radiya ta faɗa tana miƙewa, Yaya Ridwan ya ce.
“Abinda na faɗa muku kenan, tana yi masa mugun son da mu kammu ba ta ganin a matsayinta mutane, idan aka haɗa mu da shi.”
“Nana namiji kina tare da iyayenki ma ya kuka ƙare, bare kuma kin ce kin zaɓeshi akan kowa da komai, ban ce ki kashe aurenki ba, kuma bazan baki shawara akam hakan ba, amma ko ya ne ki nuna masa iyayenki na da daraja a wajensa.”
Yaya Radiya ta faɗa tana miƙewa, duka suka miƙe Yaya Ridwan ya kalle ni sannan ya ce.
“Nana, Allah Ya shiga al’amirinki ya kawo miki mafita, da haske amma tabbas kina cikin duhun soyayya, ina guje miki lokacin da Sardauna zai fama miki SARTSEN da ya yi miki, dan tabbas Sardauna ya yi miki SARTSE a zuciya, ba zan miki baki ba, amma tabbas bazaku kwashe ƙalau da shi ba.”
“Shikuma Allah Ya isa tsakaninmu da shi, dan tabbas ya cutar dake, wallahi Allah sai ya saka mana.”
Ra’is ya faɗa, daidai lokacin Sardauna ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi, sai da ya ƙaraso inda suke sannan ya ce.
“Kunji kunya, dam girmanku kunzo kuna son kashe mata aure, mussamman ke.”
Ya faɗa yana nuna Yaya Radiya, sannan ya ce.
“Kin kashe naki auren shine zaki kashe mata nata, ki zauna ke ba aure ita ba aure kuna yawo a unguwa daga nan ku ɓige da bin maz…”
Bai ƙarasa ba Yaya Ridwan ya sa hannu ya bige masa baki, har sai da jini ya fito, sannnan ya kama kwalarsa ya fara magana ya na wuci.
“Malam ka kama kanka, ka iya bakinka kafin na zubar ma da haƙwara wallahi Allah, ita dai da ka juyarwa da tunani ka je can, amma wallahi baka isa ka ce zaka gayawa wani magana ba a wajen nan.”
Sardauna ya yi murmushi sannan ya ce.
“Na ji na juyar mata da ƙwaƙwalwar, ku yi abinda zaku yi idan zaku iya karatu ne wallahi ba za ta yi ba, dan na fusknci kai dayyus ne bakasan kishin kanka ba, bare kasan na wani, kuma ku fice mim daga gida, kar nasake ganin ƙafar wani cikinku, dabbobi.”
Hawayene suka fara zubowa daga cikin idanuna masu ɗumi, gaba ɗaya na rasa abinda ke mim daɗi, me ma ya sa suka zo, me ya sa Yaya Ridwan zai dake shi?.
“Ba zamu sake zuwar ma gida ba, duk da cewa ‘yar uwarmu na cikin gidan.”
Yaya Radiya ta faɗa tana ficewa, Ra’is da Yaya Ridwan suka bi bayanta, nima na bisu da gudu ina faɗin.
“Yaya ku tsaya dan girman Allah.”
Amma babu wanda ya jiyo cikinsu, haka suka kaɗa kai suka tafi su ka barni ina faman zubar da hawaye. Ko da na dawo falon Sardauna baya nan
, ban kuma nemeshi ba na shige ɗaki na hau kiran layinsu amma babu wanda ya ɗauka, har wajen ƙarfe goma babu Sardauna babu alamunshi, haka na kwanta bacci.
Washe gari da safe ban iya ta shi da wuri ba, sabida ban samu bacci da wuri ba, karar bugun ƙofar da ake yi min ce ta tashe ni.
“Hon! Buɗe ƙofa.”
Ƙafafuna na sauke daga kan gadon sannan na nufi ƙofar na buɗe, ban ko kalleshi ba na yi hanyar ban ɗaki.
“Ina zaki?”
“Wanke fuska zan yi.”
“Okay ki yi sauri.”
Bayan na wanke fuskar na ɗaura alwala na fito, kasancewar lokacin bana sallah ya ƙara ba ni damar mimiƙewa ina baccin.
“Zo.. ina da wani abu na baza ta.”
Ya faɗa yana kama hannuna muka fito falo.
“Muje mu fara breakfast to.”
Ya faɗa yana nuna min wajen dinning, da mamaki na kalli wajen sannan na ce.
“Waye ya yi girkin?”
“Hon ai na iya girki sosai, muje ki ji.”
Na nufi dinning ɗin, ya ja min kujera na zauna ya shiga zuba min, gasashen biride da ƙwai sai kuma shayin Na’a na’a. Komai ya yi daɗi sosai haka na ci ina mamakin yadda aka yi duk zaman nan Sardauna bai taɓa ce min ya iya girki ba.
Ina cikin ci ya tashi. “Hon ina zuwa.” Ya faɗa tare da barin wajen, kusan minti uku sannan ya dawo hannun sa riƙe da wani ƙaramin kwali mai kyau.
“Hon, canki mene anan?”
Na yi murmushi sannan na ce.
“Mene?”
“Kin bani gari?”
“Uhm na baka.”
Aikuwa ya buɗe kwalin, kyakyawar sarƙa ta bayyana wacca aka yi ta da zinare sai sheƙi take.
“Hon naki ne.”
“Wow, na gode.”
Na faɗa bakina ya kasa rufuwa, ɗauka ya yi ya gwada min a wuyan, aikuwa ta yi kyau ta hau ɗas da ita kamat a wuyan nawa aka ƙera ta.
“Na gode.”
Na sake faɗa.
“Akwai wani ta so.”
Ya faɗa yana kama hannuna.
“Hau na goyaki.”
Ya faɗa yana sunkuyawa, aikuwa na hau ya ɗaukeni zuwa waje, bai sauke ni na sai a harabar gidan.
“Kinga.”
Ya faɗa yana nuna min wata ash ɗin mota.
“Wow ta yi kyau wata ka sake siya.”
“Eyh, amma wa ke, ta kice Hon.”
“Ni.. tawa?”
Na faɗa cike da ruɗewa, ban taɓa hango kaina da mota ba a rayuwata, amma sai ga shi yau Sardauna ya bani, kai ina son Sardauna.
“Ko ba kya so?”
Na yi murmushi, sannan na ce.
“Na gode mijina, na gode Allah Ya biya ka da aljanna, Allah Ya ƙara maka arziƙi duniya da lahira.”
“Amin Honey, na gode da soyayyarki a gareni, na gode sosai da sosai, muje ciki mu yi magana.”
“Tom.”
Na faɗa tare da binshi ciki, ya zauna akan kujera ya jawo ni kusa da shi, ya kura min idanu cike da wani irin tausayi na mussaman, ya fara magana cikin sanyin muryar tamkar mai shirin yin kuka.
“Nana, kin san me ya sa nake yin dukkan waɗannan abubuwan? Kin san dalilin da ya sa nake ƙoƙarin killace ki? Saboda Kishi ne, Nana. Kishinki nake yi fiye da yadda kike tunani. Duk lokacin da kika fita kika tafi wannan karatun na wahala, zuciyata ba ta samun natsuwa. Ina ganin kamar kowane namiji da kika bi ta gabansa, kallon sha’awa yake miki. Ba zan iya jure ganin wani namiji ya kalli kyakkyawar fuskarki ba, ko ya ji muryarki.”
Ya sauke numfashi, ya ɗago ya kalleni tare da matse hannuna dake cikin nasa.
“Wannan karatun na nan... Nana, wahala kike sha a banza. Kalle ki, yadda kika rame, yadda kika fita a hayyacinki saboda shiriritar malaman nan da ba sa ma san abin da suke koyarwa. Nana nasan ba kya gane komai, lokacinki kawainkike ɓatarwa, ni kuma bana son naga kina shan wahala. Shin darajar matar Sardauna Ta Ambo ita ce ta riƙa bin layin motar haya ko ta riƙa shiga aji ana cakuɗawa da ita? A’a, Nana. Matsayinki ya fi haka.”
Ya kamo hannuna ya ɗaura a kan saitin zuciyarsa, sannan ya cigaba
"Nana, kalle ni cikin idanuwa na. Kin ga wannan motar? kin ga wannan zinaren? Duk ba komai ba ne a wurina idan aka kwatanta da darajarki. Ina son ki zama sarauniyar da ba ta taka ƙasa, sarauniyar da duniya za ta kalla ta san tana ƙarƙashin inuwar Sardauna Ta ambo. Nana a yanzu ina so na baki umarni, umarnin da nake son ki bi, ki je ki sami Alhaji. Ki gaya masa cikin lallashi cewa kin fasa wannan karatun na wahala. Ba wai kin daina ba ne, a'a ki gaya masa cewa ni Sardauna zan tafi ƙarin karatu a Turai, kuma na yanke shawarar tafiya da ke can. A can za ki yi karatu a manyan makarantun duniya, inda ba za ki sha rana ba, ba za ki fuskanci cin mutuncin malamai ba. Ba zaki yi karatu a wahala ba, can ne ya dace da matsayin matar Sardauna. Amma yanzu, kin daina ɓata lokaci a nan. Ki gaya masa kin gaji da wannan, kin fi son ki huta kafin mu tsallaka can ƙasar waje."
"Nana, kina tunanin zan yaudare ki ne? Ni ne fa masoyinki. Idan ba ki bi maganata ba, za mu rasa wannan damar ta tafiya can tare, Nana ki amince da ni, sama da kowa, dan babu mai ƙaunarki kamar ni.”
Legendspen
***