SARTSE COMPLETE

14

by @legendspen

(14) 

Na yi shiru har ya kammala, tabbas komai Sardauna yake faɗan gaskiyya ne, bai taɓa yi min ƙarya ba, kuma nasan bazai yaudareni ba, tun da da zai yaudareni ai da bai aure ni ba. Na buɗe baki yi zan yi magana wayarsa ta fara ringing, ya ɗaga yana faɗin. 

“Sister Memah, ya sauka?” 

Dake wayar tana handsfree na ji ta ce da shi. 

“Yeah! Kuma yana zama maganarku kai da Turaki ya fara, an sanar da shi faɗan da kuka yi last time a company, ya ce duka yana nemanku.”

“My god! Big Daddy akwai faɗa yanzu shikenan zan kira anjima thanks you.” 

Ya faɗa tare da kashe wayar, sannan ya juyo ya kalleni. 

“Ina saurarenki.”

A hankali na fara magana, nika cikin kulawa da soyayya. 

“Na yarda da kai Sardauna, na yarda baza ka taɓar cutar da ni ba, na baka ragamar rayuwata gaba ɗaya, zan yi amfani da ƙarfina da lokacina wajen sama maka farin ciki, zanje na sami Alhajin.” 

Ban ƙarasa ba na ji ya rungumo ni jikinsa, tare da faɗin. 

“Good girl, tare zamuje umara this year in sha Allah, i love you Nana.” 

“Love you More Hon.” 

Daga nan muka shiga lamarin soyayya, yinin ranar Sardauna kamar zai mayar da ni ciki, haka yake kula da ni, ko girki ba mu yi ba fita muka yi muka ci daga nan muka biya shopping duka a sabuwar motata, har ya fara nuna yadda take. 

Gaba ɗaya na manta da wani abu ya faru jiya tsakanin Sardauna da ‘yan gidanmu, hankalina yana kan mijina ban nemesu ba, suma basu nemeni ba. Haka kusa sati guda sannam Sardauna ya ce da ni gobe zan je gidan. 

******

Shi ya sauke ni, amma bai shiga gidan ba ya tafi ya ce da ni idan ya dawo zai shigo,  shiga ta gidan na tarar da Yaya Ridwan zai fito. 

“Ina yini?”

“Lafiya.”

Ya amsa bai ko kalleni ba, haka na shiga gidan jikina ba ƙwari, Hajiya ce a tsakar gidan tana ganina ta washe baki da faɗin. 

“Zuwa ba sanarwa.” 

Na durƙusa kasa na ce. 

“Na ce Hajiya ina yini?” 

“Lafiya ƙalau Nana, ya gida da me gidan”

“Lafiya ƙalau Hajiya.” 

Na amsa tare da shigewa cikin falonta, sai bayan na zauna ne na ce. 

“Hajiya ina Yaya Radiya, da Ra’is?”

“Radiya ta je makaranta wai za ta yi screening, Ra’is kuma yanzu na aiki shi siyo salat, baki ga Ridwan ba ne?” 

“Mun gaisa Hajiya, kinsan halinsa.” 

Murmushi ta yi tare da faɗin. 

“Bari na sauke miyar nan.” 

Ina nan zaune Ra’is ya shigo daga siyo salat, bai nuna mamakin ganina ba kuma bai nuna ɓacin rai ba, bayan mun gaisa Hajiya ta zuba mana abinci muka ci abinci, bayan Hajiya ta tashi ne Ra’is ya ce. 

“Ya zancen makarantar?” 

“Bawani labari Ra’is a yanzu har an fara jarrabawar zango ma farko ma, na zo ne kawai na faɗawa Alhaji na ji abinda zai ce.” 

“Allah Ya kyauta.” 

“Me ya faru?” 

Hajiya da ta shigo ta faɗa. 

“Mijinta je ya hanata komawa makaranta, gashi har an fara jarrabawa.” 

“Imnullahi wa’inna illahir raji’un, garin ya? Me ya faru?” 

“Wallahi Hajiya haka kawai, har Yaya Ridwan ya masa magana da Yaya Radiya ƙarshe ya yi mana rashin arziƙi.”

“Hajiya Yaya Ridwan fa fasa masa baki ya yi.” 

Na faɗa kamar zanyi kuka, da mamaki ta kalleni. 

“A yaushe a ka yi haka?” 

“An kwana biyu.” 

“Amma babu labari.” 

“Ai ni na yi tunanimn ma sun faɗa muku, ni kuma gudun ɓacin ran Alhaji yasa mana na ja baya da zuwa.” 

“Amma bai kyauta ba, to yana da wani dalili ne?” 

“Eyh Hajiya, yana da dalilinsa mai ƙarfi ma, kuma ya ce da ni ƙarshen shekara zamu tafi turai, zai sama mini wata makarantar acan.” 

“Tom Allah yasa, yawwa Nana kna fatan dai ba haɗa baki kukayi da mijinki ba, kika sha wani ani da zai hanaki ɗaukan ciki ba ko? Abun shiru ya yi yawa.” 

“Eyh Hajiya ba abinda nake sha, nama je asibiti an bani magani ina sha.” 

“To Allah Ya duba lamarin.” 

Na amsa da Amin, sai yamma Yaya Radiya ta dawo, ko da na faɗa mata sai ta ce ita babu ruwanta da al’amurana. Yaya Ridwan kam bai ma sake kulani ba, sai yamma Alhaji ya dawo wanda daman ya saba dawowa a wannan lokacin sai ya koma gab da magriba. 

Ya yi murma ganina sosai da sosai, mun gaisa dashi bayan ya shiga ɗaki na bi bayanshi, na iske shi yana duba wasu takardu. Na zauna a ƙasa, jikina duk babu daɗi haka nake ji na, bayan na zauna na fara wasa da yatsun hannunta yayin da zuciyata ke bugawa da sauri.

Alhaji ya kalleni cike da kulawa, sannan ya ce. 

“Nana, lafiya na gan kin biyo ni? Ko Akwai wata damuwa ne?"

Cikin rawar murya na fara magana. 

 "Alhaji... dama... maganar karatuna ce. Na zo ne na roke ka alfarma."

Alhaji ya gyara zama, fuskarsa cike da mamaki. 

"Ina jinki Nana. Mene ne ya faru?"

“Hon, idan kika je har kuka zaki yi masa, sannan karki kuskura ki nuna masa ni na tursasaki.” 

A hankali na fara fitar da ƙwalla daga idona, muryata ta fara rawa. 

 "Alhaji, don Allah ka yafe min, amma gaskiya na gaji. Karatun nan na nan... naga kamar wahala kawai nake sha, kuma gaskiya ba na gane komai. Kullum ina cikin fargaba, gashi kuma kishin Sardauna ya sanya ba na samun natsuwa. Yana yawan nuna min yadda yake damuwa idan na fita cikin maza a makaranta."

 "Nana, me kike fada haka? Karatun da kika dage a kai shi ne yanzu kike cewa kin gaji? Ko Sardaunan ne ya hana ki?"

Na tuna da  kashedin Sardauna, aikuwa na yi saurin kare shi. 

“A'a Alhaji, ba shi ya sanya ni ba. Tausayina ne yake ji, kuma kishi ne na soyayya. Shi kansa yana so na yi karatu, amma ya ce ba zai bari na sake yin wannan wahalar ta nan gida ba. Alhaji, Sardauna ya riga ya kammala shirinsa na tafiya Turai domin ƙarin karatu, kuma ya ce da ni zai tafi. Ya ce a can ne zan yi karatu mai kyau, a cikin nutsuwa da daraja, inda babu wanda zai rika kallo na ko ya shiga rayuwata."

Na ƙara narkar da murya. 

"Don Allah Alhaji, ka bar ni na ajiye wannan na nan. Na yi maka alkawari zan yi a can idan mun tafi. Shi Sardauna ya fi son na huta yanzu, na shirya wa tafiyar mu ta can gaba. Gani nake idan na nace akan wannan, zan ɓata masa rai, kuma ba na so na saɓa masa tunda kishinsa ne ya sanya shi yake son ya kiyaye ni."

Shiru Alhaji ya yi na kusan minti biyar, har sai da na ɗago na kalleshi sannan ya ce. 

“Kina ganin baki takura ba?” 

“Ta takura Alhaji.” 

Ra’is ya faɗa yana shigowa, sannan ya sake maimaita abinda ya faɗa. 

“Alhaji wallahi duk abinda ta faɗa karanta ma ta ya yi, baya son ta yi karatun kwata kwata, tun kafin yanzu ta faɗa mana kuma har can muka je muka same shi dukan mu, dan ya fahimce mu amma ya yi mana barazanar sakinta idan muka takura.” 

Alhaji ya ɗago y kalleni, yadda nake kuka ya bashi tausayi. 

“Barazanar saki ya yi miki?” 

Da sauri na girgiza kai na ce. 

“A’a ƙarya yake Alhaji.” 

“Ke dai kike ƙarya, amma dai ba ni ba.” 

“Ra’is, ka tabbatar da abinda ka faɗa?”

“Na tabbatar Alhaji.” 

“Nana yanzu kin zaɓi miji akan kowa naki?” 

“A’a Alhaji, bana so ya sake ni wallahi, Alhaji bana son ya rabu dani, ina son sa bazan iya jure rashin sa ba.” 

Shiru ɗakin ya yi kusan minti goma, sannam Alhaji ya ce. 

“Shikenan Nana je ki, Allah Ya yi miki albarka.” 

Na miƙe tare da amsawa da Amin, haka na dawo falo na ci gaba da kukana, Hajiya dai ba ta ce dani komai ba haka Yaya Radiya, sai gab da magriba Sardauna ya kirani a waya ya ce da ni ya dawo. 

“Ba zaka shigo ba?”

Na faɗa masa muryata ba ƙwari, ya kashe wayar ya shigo, da Hajiya kawai suka gaisa tun da Alhaji ya koma, Ra’is yabi shi shago, Yaya Ridwan kam ko kallo bai ishe shi ba bare Yaya Radiya ta bata ma fito ba. 

Ko da muka koma Sardauna bai tambayeni yadda muka yi da Alhaji ba, nima bansanr da shi ba. Sai washe gari yake sanar da ni, Wai Big Daddy ya basu gida shi da Turaki kuma gidan guda ɗaya ne amma part biyu ne kuma ya ce dole mu koma can, shima Turakin dole ya zuana acan idan ya yi aure. Ni bai dameni ba ko a jikina hankalina ma bai kan komawa gidan, tunanin Alhaji kawai nake yi, bayan kwana biyu da na kira Hajiya take sanar da ni baya jindaɗi, gaba ɗaya na shiga damuwa ta dole na sa Sardauna ya kaini gida, na yi ta yiwa Alhaji kuka. 

Sai da na yi zuwa uku a jinyar ta shi, har Allah Yasa ya warke, tun zuwan da ‘yan uwama suka yi gidana babu wanda ya sake zuwa har yau sai da Ra’is ya zo sanar da ni rashin lafiyar Alhaji. 

Mun ci gaba da zuwa wajen Dr Ɗan Adala, yana ɗorani akan magani amma har yanzu haihuwa shiru, Sardauna yana ta shirye shiryen komawarmu sabon gida, ya hana duk wasu ƙawayena zuwa, ‘yan uwana kam dama ba wanda zai zo ko baice ba, gashi bama fita ko ina daga gida sai gida. 

Bani da wani abu da nake yi sai kula da mijina, a kullum burina na yi abinda zaj faranta masa, son shi nake kamar raina, bana son duk wani abu da zai ɓata masa rai. Uwa uba ma tausayinsa da kullum ke cikia min zuciya, wata rana bayan anyi refeiling ɗin gas yake sanar da ni kusan dubu saba’in aka yi ya gaji ga kuma yana son ƙara abubuwa na sabon gida, kamar wasa na ce da shi ko zai siyo min gawayi da abun girki na gawayi, ba arufa sati ba sai gashi da buhun gawayi biyu da kurfoti. 

Rana ɗaya Hajja ta zo gidana tun daga ranar ba ta sake zuwa ba, sabida ya yi mata nisa gidan. Ranar da ta zo na ga tashin hankali wajen Hajja, harvsai da ta fasa min plast ɗin ruwan zafi guda ɗaya sabida fitina ta dinga yi kin kamar ƙaramar yarinya, kifin gwangwani ta ci ta ci har sai da ta yi amai, ƙarshe ta ci wai mai ƙarni na ba ta kamar ba ita ta zaɓa ba, kwana uku ta yi amma ji na yi kamar shekara uku ta yi. Sai da Sardauna ya zo da police dog gidan ta tafi, wai ita zaman jego za ta yi min tun da naƙi haihuwa. Amma tun da t ga karen ta kwashe tsunmokaranta tafi Tunda ta tafi ba ta sake zuwa ba har yau.


Ina zaune a gida na alfarma da ya ji kayan more  rayuwa amma dani da wadda ke zaune a gidan ƙasa na ƙauye marabar mu kaɗan ce. 

Wannan shine asalin labarin. 

Legendspen
***