27
*KUNDINA*
*SASAAL*
***
27
SALIM;
Ya jima a tsaye yana kuka mara sauti, ganin kamar hankalin mutane ya fara dawowa kansa ya sa ya cigaba da tafiya, yana goge fuskarsa..
Ba shi da ko sisin da zai yi kuɗin Mota a jikinsa, gashi tsakanin ɗakin taron da babban titi a kwai ƴar tafiya..
Haka ya tako, zuciyarsa na tsananta yi masa ciwo.
A zahiri yake tambayar kansa, dama dagaske akwai mutane marasa tsoron Allah irin Hajiya Babba?
Bai taɓa gani ba, shi ko a finafinai ya gani baya yarda sai ya ce shirine kawai..
Yana fitowa babban titi ya samu shagon Pos ya cire kuɗi..
Maimakon ya wuce gida, gidan lawal da rabonsu da yin magana tun ranar da suka samu saɓani akan maganar Fatima ya nufa..
Ya na zuwa aka ce baya nan, dole ya haƙura ya dawo gida..
Zuciyarsa cike da fargaba ya kwanta a Parlo yana jiran dawowar Hajiyarsa, don yasan yau sai abinda hali yayi tunda sun haɗu da Hajiya Babba..
HAJIYA TURAI;
Cikin takaicin da ya haɗe da tsanar Fatima bayan ta gama bin bayan Salim da kallo ta ce;
"Ai da wallahi nasan Salim ƴar kishiyarki yake so, da tuni na yiwa tumkar hanci"
Hajiya Babba tana jin haka, ranta yayi fari ƙal, tana ganin kamar wannan ne damarta na ƙarshe da zata rushe auren Fatima, banda ma tana tsoron Alhaji, ai da Farida zata yiwa hanya, amma tasan ko zata mutu ta dawo Alhaji ba zai yarda ba, don haka gara dukkansu su rasa..
A zahiri murmushi ta yi ta ce;
"Hm ki bari kawai Turai, ni ba ma wannan ba, wallahi da yarinyar tana da tarbiyya ba ni da matsala akan auren, ai ɗa na kowa ne, amma halin Fatima da tarbiyyarta ba abu bane mai sauƙi ga salihin Namiji irin Salim"
zaro ido Hajiya Turai ta yi ta ce;
"Allah dagaske Sara? Ohhh Salamatu! Salim yana shirin kwasomin masifa, wallahi bai isa ba, dole a dakatar da auren nan, indai ni na haifeshi"
Hajiya Babba kai ta jinjina cikin jimami ta ce;
"Turai taho mu shiga ciki, tsayawa anan da gajiya, idan aka gaigaisa sai mu fito mu nemi abin zama, hirar zata fi daɗi"
Kamar raƙumi da akala haka Hajiya Babba tabi bayan Hajiya Turai data yi adonta na kece raini, a cikin ranta, tana tsara irin kalaman da zata ƙara yin amfani da su wajen cikar muradinta...
Ba su samu damar fitowa daga ɗakin taron ba, sai da aka fara kiraye-kirayen sallar La'asar..
Harabar wajen suka firfito masu yin Sallah sukayi, wasu kuma su na ta ɗaukar hotuna ana raha..
Bayan sun idar Hajiya Babba tankwashe ƙafarta tayi..
Itama Hajiya Turai ta juyo suna fuskantar juna..
Babu wani labari na ƙarya da gaskiya da Hajiya Babba bata bayar akan Maman su Fatima da ƴaƴanta ba, har labarinsu Marigayiya Aunty Su'ada sai da ya shigo ciki, akan dukka sun mutu ne saboda abun kunyar da suka aikata..
Gwauron numfashi Hajiya Turai ta sauke, Bayan gama sauraran bayanin Hajiya Babba da ta bawa yardarta ɗari bisa ɗari, cikin takaici ta ce;
"Yanzu Saratu da bamu haɗu ba, ba zaki tambaya a group group har ki sami lambata ba, yanzu da shikenan haka ɗana zai auri ƴar da babu tarbiyya, gaskiya ban ji daɗi ba, yanzu yaya kike ganin zan ɓullowa lamarin nan?"
Hajiya Babba sai da gama yi mata bayanin irin wahalar da tasha akan neman lambarta bayan ya goge a wayarta Sannan ta bata shawarar su karɓe komai nasu har motar hawa a wajen Salim, su buɗemai wuta idan ya ji wahala ta ko ina tunda ya saɓa da daɗi zai haƙura...
Dariya Hajiya Turai tayi suka tafa, anan suka ƙare zamansu, har lokacin tafiyarsu ya yi, suka yiwa juna sallama tare da musayar lambar waya..
Har Hajiya Turai ta dawo gida Salim yana kwance a Parlo, ba tace mai komai ba, ko gefensa ma bata kalla ba ta shige ɗakinta...
★washe gari matakin da ta fara ɗauka akan Salim shine, kiran mai yi musu gyaran wuta ya lalata wutar ɗakin Salim, bayan ta tabbatar Salim ɗin ya fita wajen aiki babu abun hawa, tunda bashi da motar kanshi..
SALIM;
Yana kan hanya Ya kira Fatima gashi nan zuwa..
Har ƙofar gidansu Adaidaisahu ya faka ya kira Fatima ta fito...
Fatima bata nuna mamakin ganinsa adaidaita sahu ba, ta gaisheshi Sannan ta shige ta zauna.
Su na ƴar hirarsu har suka je Makaranta.. Salim yana ta tunanin Fatima zata tambayeshi ina motarsa amma yaji shiru, a ransa sai ya ji ta ƙara birgeshi..
Da Fatima zata dawo gida ma, haka ya ƙara tarar Adaidaita sahu suka shiga tare, ya rakata har gida, sannan ya ƙara dawowa makaranta saboda lokacin tashinsa bai yi ba...
Ko da ya dawo gida, ya fahimci an tsigemai wutan ɗaki, bai ce komai ba, ko Daddynsu da baya gari bai kira ba, haka yayi kwananan ƙunci, yana jinjinawa halin Mahaifiyarsa..
★washe gari ma, haka ya ƙara ɗaukar Adaidaita sahu, har ƙofar gidansu Fatima, ta fito suka tafi tare.
Abinda ya ba shi mamaki sai hira masu daɗi Fatima take mai, bai ji tayi ƙorafin ina motarsa ba, kamar ma bata saba shiga mota ba....
A ranar sai bayan ƙarfe huɗu ta gama ɗaukar lecture, ya ce ta jirashi ya kammala komai..
Haka suka jero suna hira har bakin titi, ya tare musu adaidaita suka shiga..
Bayan an sauke Fatima, kasuwa Salim yasa mai adaidaita ya wuce da shi ya siyi sabon generator, da abinda zai yi amfani da shi, har da galan suka bashi kyauta, ya tsaya a gidan mai ya siyi petir ya wuce gida.
Da kansa ya haɗa komai ta bayan ɗakinsa, a gajiye ya gama ya shige ɗaki, bayan yayi wanka, ya fita ya nemi abinci..
Sai da ya ci ya ƙoshi ya kira Fatima tun a hanya su na ta hira har ya shigo gida..
Hajiyarsa da ƴan uwansa duk suna jin ƙarar genetor amma kowa ya yi fuska..
A cewar Hajiya Turai idan kuɗinsa ya ƙare zai dawo hayyacinsa yayi mata biyayya..
A haka Salim ya jera Sati biyu suna tafiya Adaidaita sahu shi da Fatima...
HAJIYA BABBA;
Farida ce ta kai mata gulmar ai yanzu su Fatima a Adaidaita sahu suke zuwa makaranta ita da Salim..
Murmushi tayi ta saɓa mayafi ta nufi sashen Baba..
A kishingiɗe ta sameshi, bayan ta gaisheshi.
Cikin nutsuwar da yake nuna nadamar a sarari kamar ba ita ba tace;
"Alhaji a ajjiye batun kishi a gefe, kana ganin kamar ba a ɗorawa yaron da zai auri Fatima nauyi ba, kullum ace sai ya zo da Adaidaita sahu ya ɗauketa, tunda da direbobi a gidan nan, a ganina a saka ɗaya daga ciki ya dinga kaita Makaranta yana ɗaukota, maimakon cacar kuɗin Mota sai a saka Mai, shi ma zai fi ganin darajarta, wallahi yanzu Farida take gayamin sam ban ji daɗi ba"
Ƙuri Baba yayi mata da ido, bai taɓa sanin Saratu tana da hankalin ba sai yau, shi gaba ɗaya ma bai san Salim da Fatima tare suke tafiya ba..
Da fara'a yace mata ya gode kuma yaji daɗin shawararta..
Murmushi tayi, domin haƙarta ya cimma ruwa, tasan Salim dole zai ji haushi..
Ta jima a sashen suna hira kafin ta koma Sashenta..
A daren Baba ya tattauna batun da Aunty Amarya itama tace hakan ya yi.
A waya Baba ya kira Fatima ya sanar da ita, gobe Driver zai kai ta makaranta ya ɗaukota, bai nuna ma yasan tare da Salim suke tafiya ba..
FATIMA ;
Shiru nayi bayan gama amsar wayar Baba, haka kawai naji ban ji daɗi ba a raina, nasan ina faɗawa Salim zai ce saboda yanzu ba shi da mota ne..
"To meyasamu Motarsa?" na tambayi kaina..
Ko Salim bai faɗamin ba nasan yana cikin wani hali, "Allah Ya fidda shi"
Na faɗa a sarari..
Ko da muka yi waya kasa gayamai abinda Baba ya ce nayi..
★ sai washe gari da Asuba ba tura mai text message..
Bai yi min reply ba, don haka na kirashi..
Bai ɗaga ba, ya katse ya kirani;
Muryarshi ƙasa-ƙasa kamar wanda yayi kuka ya amsa sallamata, na gaishe ya amsa, cikin taushin da ya sani jin wani iri ya ce;
"Wifey na ga saƙonki kin gaji da hawa adaidaita sahu ko?"
Maimakon na ce "a'a" sai nayi shiru.. sautin murmushinsa na ji, sannan ya ɗora da;
"Karki damu sai mun haɗu a makaranta"
Har ya katse kiran ban cire wayar daga kunnena ba, saboda sanyin da jikina yayi, a take na fara tunanin yaushe Baba yasan Salim yana zuwa a Adaidaita ya ɗauke ni, wanene ya kai masa gulma
"Farida saboda ita kaɗai ce ta ganmu, wannan shirin Hajiya Babba"
Na faɗa ina rintse idona..
Damuwa yasa na kasa komawa barci, ina roƙon Allah Ya sauƙaƙamin...
A kan hanyarmu na tafiya Drivern da ya ɗaukeni, yake ba ni labarin, ai Hajiya tace ita ta bawa Baba shawara ya dinga kaini makaranta...
Ban ce mai komai ba, saboda nasan duk abinda na faɗa sai ya maimaita mata..
SALIM;
tunda ya ga saƙon Fatima yaji jikinsa ya yi sanyi tunaninsa ya fara sauyawa, ko dai Fatima ta gaji da shi ne, ƙarin rashin bayar da amsarta da ya tambayeta a waya ta gaji da hawa adaidaita sahu ne, yasa tunanin ya ƙara sauyawa, sai dai bai yanke hukunci ba...
Bayan ya isa office kasa aikin komai ya yi, da ya gaji dole ya tashi ya nufi Ofishin lawal..
A can ya samu Mariya Abokiyar aikinsa da takardu a hannunta tana ƙoƙarin fita..
Da fara'a suka gaisa, tana ƙaremai kallo saboda yadda idonsa ya faɗa ciki..
"Sir Salim lafiya?" Ta tambaya da damuwa a saman fuskarta.
Murmushin yaƙe ya ƙaƙalo yana yunƙurin buɗe bakinsa Lawal ya ce;
"Ina fa lafiya, ya ɗorawa rayuwarsa bala'i, yaƙi da maganar iyaye ai bala'i ne"
Mariya fasa fita tayi ta dawo ta zauna, lawal ya kwashe duk halin da ake ciki ya gayamata..
Mamakine ya kamata don ita har ga Allah, bata kawo Salim yana haɗa lefe a wajenta bane don ya samu matsala da mahaifiyarsa, cikin taushi da nasiha ta ce;
"Sir Salim mu ajiye komai a gefe, kasan dukka wannan abun da kake yi, a ƙarshe Fatima zaka cuta? saboda mahaifiyarka bata Sonta, a ganina ka haƙura da ita, wallahi nayi alƙawarin baka ƙanwata a makarantar nan take yarinya ce nutsatsiya, ba zan yi maka dole ba, amma ina so ka gwada idan tayi maka"
Salim kallon marasa hankali yake musu, amma gudun kar damuwar tayi masa yawa sai ya ce musu ya ji zai saka rana ya zo gidanta yaga yarinya..
A nan suka duƙufa bashi shawara, shi kuma hankalinsa ya na can kan Fatima ko taci abinci ko bata ci ba?...
Ya na barin Ofishin lawal shi da Mariya, budurwarsa lawal ƴar ajinsu Fatima ta shigo..
Cikin rawar baki da rashin nutsuwa irin na wasu Mazan, lawal ya bata labarin ai Salim ya fasa auren Fatima ƙanwar Madam Mariya zai aura, caraf kuwa ta ce ai tasan ƙanwar Madam Mariya, nan suka faɗa hirar abinda basu da tabbaci a kai...
FATIMA;
ƙarfe biyu zan gama lecture, amma har ƙarfe 12 ban ga Salim ba, na kirashi har sau biyu bai ɗaga kuma bai kirani ba, a take naji raina ya sosu...
Fuskata a haɗe na kira Driver ya zo ya mayar da ni gida..
Ban tsaya jiran lecture ba, driver yana kirana ya iso na fito daga aji, a daidai lokacin na hango Salim shi da Abokiyar aikinsa suna magana..
Ban jira ƙarasowar su ba, na shige mota, zuciyata na zafi..✍🏻