BARRISTER SUHAIL
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----5
haka Tahir ya cigaba da rayuwa,ba san Abinda yake dai-dai ko akasin haka ba Alhaji sani ya rasa mike masa ɗadi hakan ya sa ya tashi ya nufi office din Barrister suhail bayan nadia ta masa iso ya shiga ciki Suhail ne zaune akan kujera sanye yake da blacks and white suit sunyi bala'i yi masa kyau hannun sa riƙe da cup din coffee yana sha.
Alhaji sani ya shigo cikin office din zama yayi bayan sun gaisa da suhail ya ce"sai dai ban gane ka ba"
cike da natsuwa Alhaji sani ya ce"ni ne mahaifin Tahir yaron da kasa a ƙama, murmushi gefen baki Suhail yayi ya ce"okay ina jinka mike tafe da kai,
Barrister nazo muyi magana akan case din Tahir duk da nasan kuɗi ba matsalar ka bace amman ka faɗi abinda ka ke buƙata daga Naira million goma har zuwa million hamshin a shirye nake na baka su matuƙar zaka ƙori case din nan.
Suhail ya jinjina kai kaɗan tare da haɗe hannayen sa saman table ɗin dake gaban sa ya ce"Ai tun farko ban karɓi case ɗin nan dan kuɗi ba,sai na na kawo ƙarshen duk Wasu mutane masu irin Halin ɗanka wanda suka dauki fyade a Matsayin Ado da basu kunyar aikawata ga kowa, a ganin su ko da an kai su ƙara babu abinda zai faru tunda iyayen suna da kudin da zasu fito dasu to ina so ka sani wannan ƙarin ɗan ka zai fuskanci hukunci dai-dai da Abinda ya aikata"
Kalaman Suhail suka doki zuciyar Alhaji Sani amma ya danne ya ce"Barrister ka taimake ni Tahir shi ƙadai ɗa na a duniya"
miƙe wa Suhail yayi ya ce"kamar yadda yake ɗa tillo a wajen haka itama yarinyar da yayi fyaden take wajen iyayyen ta amman suna ji suna gani haka ɗan ka yayi sanadiyar mutuwar ta,ka gode Allah kai kana da kudi su ko talakka wa ne bayin Allah masu neman na abinci kullin"
bai jira Alhaji sani ya ƙara cewa komi ba ya fice ya barshi cikin office din Alhaji sani ya kife kan sa kan teburin hawaye masu ciwo suka fara zuɓo wa daga idanun sa kaicon sa da ya kasa ba yaran sa tarbiya data kamata tun a duniya Allah ya fara nuna masa Aya ina ga idan anje lahira,ta ko ina ya tausayawa kansa Ashe ba kullin kuɗi ke maka rana ba.
sai ya kama kukan mai cike da tarin nadama ya goge fuskar da babban rigar dake jikin ya fita ya shiga moto driver ya ja suka koma gida.
sai Suhail ya tabbatar Alhaji sani ya tafi kafin ya dawo office din a reception ya tsaya wajen nadia ya ce"ta kira mutanen da ta fada masu Ranar Litinin za'a fara sauraren karar su"
cike da girmamawa ta ce"okay sir" ko office din bai shiga ya wuce gida kasancewar ya gama aikin sa kaf na Ranar.
Yau ta kama Litinin kuma a yau ne court zata fara sauraren Shari'ah Tahir Sani da kuma iyayen yarinyar da yayi wa fyade Alhaji sani ya ƙasa halartar zaman court sai daya daga cikin yaran sa ya tura dan bazai juri ganin Tahir a wannan yanayin ba.
cikin ƙasa da kwana ukkun da Tahir yayi a police station yayi baki ya rame bakin sa duk ya bushe idan har kasan Tahir a baya ka kallesa a wannan lokacin sai ka tausaya masa,ko ido ya ƙasa dagowa ya kalli mutanen dake wajen ko da Alkali ya karanto masa abinda ake tuhumar dashi bai musa ba ya ce ya aikata dan yana ganin a yanzu babu sarki sai Allah gara kar ma ya wahalar da kansa ya faɗi gaskiya, a shirye yake ya amshi duk wani hukuncin da kotu zata yanke a ƙansa dan ya riga ya yanke duk wata alaƙa ta jin daɗin duniya.
Hatta Suhail sai da ya tausaya masa a lokacin dan duk a tunanin zai kafe ya ce bai aikata ba tunda babu wata shedar da zata tabbatar da shi yayi laifin
WALLAHI NI KAINA SAI DA NAYI WA TAHIR KWALLAH KU BIYO DAN JIN HUKUNCIN DA KOTU ZATA YANKE MASA