TALES OF THE WAZEERIS

Sultan shamsan wazeeri

by @surayyahms

22...🦋🦋🦋

SURAYYAHMS

Tales of the wazeeris

washegari da safe bayan ta idar da sallan fajar ta sake komawa bacci sai can wajejen karfe shida da rabi ta farka ahnkli wanda a duban farko idonta ya sauka akan golden sunlight dake shigowa ta giant windows din suite nata so beautiful ta tsaya kawai tanafa kallon view din cikin nutsuwa

sai can sannan tamike tsaye cikin saibin jiki da gjiyar bacci tashiga cikin bathroom, warm shower tayi me tsayi ta wanke dogon gashinta da Olaplex shampoo da conditioner data gani awajen kafin nan tafito tashafa rare beauty moisturizer da sunscreen kafin nan tamaida hankalinta duka akaan breakfast da aka kawo mata cikin nitsuwa ta xauna ta ci iya abunda taga zata iya ci snn tabar musu sauran awajen

har lokacin zuciyarta baigama warwarewa game da abunda xata je ta tarar awajen progrm din ba amma dai haka tayi kokarin danne tsoronta tare da maida hankalinta kan abunda yakawota.

bayan tagama cin abinci nan ta mike ta bude kayanta tana mai deciding abunda zata saka daga karshe ta dauko wata elegant coffee brown abaya set me mugun kyau saudi designer brand

tasaka fitted nude inner dress me tsari ataciki snn ta daura chocolate brown silk mini hijab perfectly.

dan karamin golden van cleef bracelet ta saka ahannunta snn ta dauki classic YSL nude midi handbag dinta to match da heels dinta.

gabaki daya kamshin turaren original Maison Francis Kurkdjian ne yake wani irin sanyin tashi a dakin da kuma ajikinta yanamai kara mata wani irin clean rich aura da already take dashi wanda duk ka kalleta saikaga wnn sanyin aji nasu na jinin sarauta mai hade da yanayin soft feminity dake atattare da ita.

kafin karfe tara na safe har ta gama shiryawa tsaf, the same black luxury suv din jiya shi yazo daukarta saidai this time hanyar dubai royal Gulf Real Estate Main Headquarters suka nufa one of the biggest luxury real estate companies in Dubai...

kusan karfe tara da rabi yadan wuce dai dai black luxury suv din ya shigo da ita har cikn gaban Royal Gulf Real Estate Headquarters.

tun kafin ushna ta fito daga motar idanunta suka tsaya akan yanyn ginin dan wata arniyar glass skyscraper ne data tsananin haduwa ga girma wanda gaba daya yake reflecting morning sunlight din dubai cikin wani irin luxury aesthetic. tun daga gate din tagane security dinsu daban ne. black cars masu tsada na shigowa da fita,men in suits, arab elites,soft expensive arab perfume scents was all over a iskan wajen.

atake gabanta ya hau faduwa tafara addua

cikin ranta tana mai ambaton Allah dan ya taimaketa koda komi zai xo mata da sauƙi

suna gama parking driver din ne ya sauko kasa ya bude mata kofa respectfully, da murmushi a fusknsa yace“welcome ma’am.

ahankli ta fito daga motar tanamai gyara handbag dinta politely tace thank you..

kai tsaye tafara tafiya nan take wasu staffs guda biyu dake bakin entrance suka dan juyo suna kallonta saboda wani irin classy calm presence data shigo dashi wajen..

ko kadan yanayinta babu hayaniya,babu wani over dressing ko kauyanci saidai duk inda ta wuce akwai wani irin soft royal presence dake biyo bayanta kai zakace awajen take aiki...

YSL heels dinta masu tsananin kyau da aji are making this soft sounds akan marble floor din lobby yayinda manyan chandeliers ke haskawa ata samanta

ana bude mata kofa kai tsaye wajen wata receptionist ta nufa she was a beautiful lebanese woman ta dago kanta tanata kallon ushna for like two seconds kafin nan tayi polite smiles da dan fargaba a voice inta tace good morning ma’am. how may i help you.

ushna ta mayar mata da murmushi ahankli kuma politely tace "morning my name is ushna m. saleem, i am here for the royal gulf qualifiers..

matar ta dan kara dago kai tana kallon ushna daga sama har kasa can kafin nan tay murmushi tace wow, for a second i thought maybe you were one of the preety daughters of the gulf billionaires attending the ongoing shareholders meeting upstairs.

ushna tayi dan karamin dariya dayazo mata bazata tace “no, no i'm not.

receptionist din tana murmushi tace “well…you definitely look like one.

fuskar ushna na dauke da wani irin murmushi sai batace komi ba

daga nan matar ta bukaci ID dinta da registration code nan ushna ta bude jakarta ta cirosu snn ta miƙa mata kai tsaye

bayan matar ta gama dubawa nan da nan aka mata biometric verification da thumb prints kafin nan wani security personnel ya bata temporary access card. yace “23rd floor ma’am. ask for the program department.

ushna ta musu godiya sannan ta nufi private elevator ta danna yana buduwa ta shiga ciki sai dai duk sanda ta hade ido da mutane sai taga kaf kmar ana mata kallon wata yar billionaire arab man ne kmr yadda receptionist din ta fada.

hakan yasa taji ta fara rasa nitsuwarta taciki dan harga Allah tasan tana da sanyin aji da kyaun fuska kam sosai amma kuma bata taɓa daukar hakan da zafi ba.

duk lokacin da elevator din ke kara hawa sama kusan tare da bugun zuciyarta suke hawa

....she was so nervous nd scared alitle bit dan ita kanta bata gama yarda cewa yau wai itace aka kira cikin irin wannan wajejen ba.

tana isa upper floor din elavator ya tsaya cak a 23rd floor snn ta fito

nan taga wajen ma yaci uban inda ta fito kyau da tsari dan yana da wani irin soft luxury ambience ne ga tall tall glass walls medauke da city view da wani irin calm professionals kusan kowa awajen na aikin dake gabansa ne cikin nitsuwa.

daga can gefe taga wasu few selected students irinta suna zaune looking highly polished da confident dake yara ne da suka saba da elite spaces

lokaci guda taji kafarta yai nauyi yana neman yafara harhadewa sbd fargaba.

cikin sanyin taku ta taho itama ta zauna akan waiting chair da ake jera kusa da wata kyakkyawar asian girl dake scrolling apple ipad dinta..

qamshin ushna yasaka yarinyar tadago kai zata dan kalleta kawai sai suka hada ido waje guda atake yarinyar tace wow..you are genuinely one of the prettiest girls i’ve ever seen.

ta mike ma ushna hannu tace i am jisso, korean.

ushna tayi murmushi cikin mamakin irin confident din babe in kafin nan itama ta bata hannu tace..thank you…i am ushna.

jisoo tace are you from morocco?

tace “no…nigeria. but i grew up in london

jisoo tace damn girl

your features are insanely beautiful.

ushna bata san me zatace ba kawai tayi mata murmushi me sanyi..

can yarinyar ta dan matso kusa da ita cikin casual friendliness tce are you nervous too?

ushna tayi saurin gyada kai tace“very.”

yarinyar tayi dariya kadan da harshen turanci tace..same here, but apparently this program is a huge deal kusan dole kowa yadanji fargaba aransa

da harshen turanci ushna ta amsata tace well, ni bansan komi game da program din ba kawai zaɓa ta akayi kuma wnn karo shine karo nafarko na zuwa na qasar dubai

jisoo ta sauke murya kasa kasa da harshen turanci tace... inde haka ne, yakamata ki shirya sosai, cos did u even know the kind of students they select here?

ushna ta girgiza kai

yarinyar tace duk wanda kika gani anan they are mostly top rated international students from elite universities kamrsu cambridge, yale,john hopkins, MIT, havard

da wasu private elite school,wasu daliban da aka gayyata already sunada established startups business nd companies.

lokaci guda ushna taji hanjin cikinta yadan cure, yarinyar ta cigaba da cewa many of the student here are from influential families dan da mugun wuya ake samun wnn daman.

ushna takasa cewa komi dan sosai bugun zuciya da nervousness dinta yakara hawa nn tafara ji kamr bazata iya ba hala..

dan ita kanta batasan ta yaya aka accepting dinta cikin irin wannan babban program din ba wanda duk dama bata gama sanin kalar muhimmncinsa da girmansa ba, bt it seem like a place da zai iya sauya mata rayuwarta har abada.

ganin fuskar ushna ya canza jisoo tay dariya tace hey relax you’re here already. zaki iya!

ahnkli ushna ta sauke ajiyan zuciya tace i hope so, amma ina sauran student din suke the place seem quite ko iyakan mu kenan?

jisoo tace ohhh ai mune last badge, cos many students da suka zo last week har an riga an assigning musu supervisors sun tafi.

ushna ta dago kai da mamaki tace already?

jisoo tace yeah.

sunfi minti arbain suna zaune anan wajen suna cikin magana kenan kawai sukaji yanayin wajen ya wani irin sauyawa gaba daya.

atake hayaniya ya dauke cakk babu wani obvious reason ushna tafara jin wani kalar sanyi na shigarta yana mai bugar zuciyarta da kwakwalta alkci guda

atmosphere din wajen atake yabi ya canza ta rasa menene yasaka har tafara jin faduwar gaba me tsanani.

can sai taga guards din dake gefensu sun mike cikin nutsuwa da wasu staff suma suka fara gyara tsayuwarsu

wasu executives din dake kai kawo ma kaf suka dan tsaya agefe

lokaci guda zuciyar ushna tafara wani irin bugawa tana fat fat fat tanajinsa kamar zai fasa kirjinta ya fito waje atake ta dafe gefen kujerarta ahankli tace hasbinallahu wa neemal wakeell..

jisoo ma ta dago kai da sauri tanata kallon corridor glass na main entrance din

it was 11:30am na safiya adede lokacin ne sultan Shamsan wazeeri yake kkrin fitowa daga cikin private real estate executive meeting dayazo yi tare da top arab business partners dinsa wanda suma royals ne kamrsa.

He owns 40% shares of this gulf real estate company, technically wajen kamar nashi ne duk dama bashine ya kafa ba amma majority shares nawajen kusan nasa ne.

gabaki daya wajen sai da ya dauka da wani irin silent tension sbd yadda ake shakkarsa

daga jisoo har ushna basusan sanda kwayar idanunsu yabi ya tsaya cakkk daga ta wajen fitowarsan ba.

securitis ne yuuu agefe da gefe da gabansa

ushna ta dinga miƙa wuya sai can kuwa sai ta hango shi,..dogon namiji ne me wani irin intimidating elegance, yasaka wata kalar pure matured black tailored suit ajikinsa perfectly fitted akan broad shoulders dinsa..

agogon hannunsa kadai ka kalla kasan ajinsa da kudinsa ba irin na kananan kwarin masu kudi bane...

steps dinsa was calm, slow, nd controlled duk dama akwai wani irin heavy ruthless aura daya cike wajen dashi kai kagansa kasan bazaiyi saukin kai ba

sanyin da takeji atake taji ya karu sosai, cikin tsumayi taji takasa iya dauke idonta akansa

gabobin jikinta yabi ya mutu both her mind nd soul was blown away in fleet of secnds taji kamr bata ma fitar da numfashi..

kyaun fuskarshi wani abu ne da bata taba ganin irinsa ba

his sharp jawline,dark eye brows, cloudy grey eyes, da uwa uba wnn silky smooth clear skin colour dinsa me wani irin tsananin daukar ido da hankali, gashin kansan nan is silky black and neatly laid back baida yawa sosai he kept it low kamar na larabawa.

kwayar idanunsa is calm nd composed

irin maxan nan ne dat luk cold bt dangerously attractive..

numfashinta taji ya kara tsayawa cak na seconds biyu dan wani irin matured masculine beauty ne dashi me nauyi da kasaita aciki

duk da taga bai kalle kowa ba bt she notice duk wajen daya wuce ppl are secretly turning heads suna kallonsa daga maza har mata.

tuni ushna ta lula wani duniyar gajimaren da bata taɓa shigewa cikinsa ba kai tsaye taji gayen ya shige cikin zuciyarta da kuma kwakwarlta.

sai can jisoo ta sauke ajiyan zuciya ahankli tace“ God…that man’ aura is actually insane.

ushna ta hadiye yawu idanunta har yanzu na kansa bata ko kiftawa batare da saninta ba tace "hell yeahh..Nd who is he..

jisoo tace everyone here calls him Sultan.

ta kara matsowa kusa da ushna kadan tace

he is ridiculously rich and private girl..like…crazy, powerful rich.

dede nan ushna ta dawo hayyacinta ta juyo tana kallon jiso da alaman tana sauraro

jisoo tace his real estate company is literally one of the hottest firms right now across the gulf and africa many people are obsessed with him but nobody really knows anything personal about him.

ushna da har yanxu take jin zuciyarta na bugawa very strangely batare da tasan dalili ba ahnkli tace "Nice.

tana gama rufe baki sai gashi nan yazo ya wucesu da gurds dinsa baiko kallesu ba.

da har zata tambayi jisoo sunan real estate kamfaninsa caraf sai wata elegant secretary ta fito daga wani office tanadan murmushi nn ta kallesu tace “the remaining qualifiers please come with me. your supervisors are ready.

nan take duka suka mike tsaye suka bita a baya aka wuce cikin wani office dasu.

ushna tafaraji kamar wani abu daga cikin zucyarta da jikinta ya sauya musmmn tun da ta kalle mutumin nan amma dai takasa gane shin meye ne.

ata dayan bangaren kuwa Shamsan yana shigewa cikin private black maybach dinsa yadan kwance classy tie dinsa ahankli tare da furzar da kramr iska ta ramin bakinsa..

jin zuciyarsa tana wani irin bugawa strangely yasaka ya dan hade girarsa sama...

from nowhere ya jawo wata expensive bottled water ya bude yasha ahankli in sips sai ya juya yana mai kallon window din motarsa akaro na farko kenan dayaji kamar ya bar rabin zuciyarsa acikin building din da ya fito.

it feels like sumting strange had happen to him in dat building ya rasa to wayene ya masa kallon dayayi draining energy dinsa batare da saninsa ba.

tun safe baici karo da abunda ya dan dauke hankalinsa daga kan business schedules dinsa ba sai yanxu

gashi bazaima iya tuna waye ko wacece take kallon sa ba amma kuma sosai jikinsa ya ke bashi cewa sumone really special has set eyes on him.

dagata dayn bangaren su ushna kuwa cikin nutsuwa matar ta raba musu supervisor nan takai jisoo wajen wani dan korea dan uwanta

ushna kuma tabi bayan wani mutumi dan egypt data samu wai shine a matsayin supervisor dinta zuwa wani elegant office na glass da soft white interiors.

office din nasa na cike da wani irin tsari da aji wanda hakan yasaka tun daga bakin kofa ta ji nervousness inta ya dan karu

a mutunce kuwa taga mutumin ya mata nuni da kujera ahnkli yace

please have a seat miss ushna.

nan ta zauna ahankli tana gyara zaman mini hijab din abayanta, shi kuma ya bude wani slim ipad yana duban personal details nata sannan ya dago kai cikin calm accent dinsa na larabwa yace so…u are from nigeria right?

ta gyada kai politely.

snn tace“yes sir.

yadan murmusa yace “interesting, nd u lived nd study economics in london with real estate analytics..

tace “yes sir.

yace “very impressive. kina da kokari i can see that, especially from your academic recommendations.

ushna tayi dan murmushi batare data ce komi ba saboda har yanzu ita kanta tanata mamakin yadda harma aka zabi sunanta cikin wann program din

da turanci mutumin yaci gaba da cewa Royal Gulf program ba ordinary internship program bane. most students here are selected based on leadership potential, good behaviour and academic excellence kin fahimta ko!

sai ya dan matso gaba kadan yana kallonta ido cikin ido ahnkli snn yace "honestly miss ushna…we are very much interested in expanding stronger luxury real estate partnerships into africa especially a kasarku ta nigeria nd that is actually one of the reasons why u were selected, u are currently the only african student representative in this program dan haka karkiyi wasa da wnn babban dama da kuma daukakar.

kafin tace wani abu sai ya dauki wani file ya mikamata yace “our goal is simple. after this training period, each students will be attached to top real estate firms in their own countries for internship asessment.

ya kara da cewa“zamu turaki nigeria dan kece kawai xakije ki mana representing africa nd once kikaje you will secure a real estate company in nigeria dat is willing to work with you temporarily, idan kika samu suka amshe ki saiki turo min da dukkan bayani daga nan kuma we will officially contact them ourselves for approval.

ushna na sauraronshi cikin nutsuwa amma sosai zuciyarta yake bugawa taciki .

mutumin ya cigaba cikin serious tone

yace in har aka amshe ki kuma internship performance dinki awajensu yay kyau there is a possibility of automatic employment under Royal Gulf in Dubai. daga nan wajen zamu baki aiki batare da wani interview ba.

da wani irin mamaki da murna aranta tace masha Allah sai ta dan yi murmushi me sanyi abayyane tace i wll do my best sir.

ya dan murmusa ganin murnan dake kan fuskarta sannan yace

however…if eventually the internship doesnt progress into an employment, koda ace baki yi kkri ba, alkwari ne all of you selected students will receive some royal prizes nd certification plus a one hundred thousand dollar startup grant.

numfashinta ya dan tsaya na seconds tace

$100,000?...

yace "yes..my dear.

lokaci guda tafara jin wani irin mix emotions na tsoro, farin ciki,

hopes, da kuma uwa uba pressure dan kusan atare duk suka cakudu mata lokaci guda har tarasa wanne tafi ji guda daya

100$k is like 140+ million naira in nigerian currency. hakan yana nufi koda bata wani ci nasara ba ashe bazata tashi abanza ba.

mutumin yace miss ushna…this is a very serious opportunity nd we hope u will take it seriously.

ta gyada kai da sauri

tace “in sha Allah i will sir. thank u so much.

daga haka ne ya fara mata sauran bayanin assignments dinta daya bayan daya

kamarsu company research, luxury housing structures,

market behaviors da

investment reports da uwa uba African urban development har ma da monthly evaluation meetings da zasu nayi ta internet intaje gida

sannan ya karbi duka account details dinta domin anasaka mata monthly allowance da kudin accommodation a duk inda zataje da full travel sponsorship dinta zuwa nigeria dan nan da sati biyu aka bata taje nigeria ta dan huta kadan snn ta tabbata tasamu wajen da zatayi aiki sai tay musu report dan a rubuta mata letter of aproaval.

bayan sun gama tattaunawa, kafin ta fita a office din sai da ya sake mata nasiha cikin mutunci yadda dai larabawa suke da son balain darajawa da respecting in mata

yace “u are very intelligent dan haka dont underestimate yourself because of where u come from, dan ina so ma ace kinzo na daya dan ki nuna ma duniya cewa Africa has what it take to take the world stage kinji ko??

cikin girmamawa ta masa godiya kafin nan ya sallameta ta fito daga cikin office din tana rike da sabon file dinta tightly.

da bataga jisoo ba kawai sai ta basar ta fito waje.

driver din Suv dinta ta samu awaje wanda yana ganinta ya taso ya bude mata kofa ta shiga ta zauna

yana fara janta tadan sauke ajiyan zuciya tare da bude file din dan ta kara duba rules da abubuwan dake ciki

tana dora ido akai taji zuciyarta yana wani irin bugawa da karfi

da abin mamaki sai taga mind inta bama

akan program din yake ba gaba daya hanklinta da tunaninta ya dawo tunowa da kyakkwar fuskar sultan din nan ne

sanyin qamshinsa da fuskarsa kawai ke yawo acikin kanta ynxu

rike da file din ta rabka tagumi cikin lumshe ido tafara tunowa da yadda ya shigo wajen

da yadda wajen ya wani canza gaba daya da yadda taga kwayar idonsa soo dangerous yet suka kasance cold and calm.

kamar a mafarki ta kara lumshe ido tana mai kwanciya akan seat tana sakin wani irin murmushi me dan karan sanyi batare da tasan meyasa ba

sai can ta dafe kirjinta ahankli tay dariya me sanyi me cike da kunya ahankli tace GOD what is wrong with me…ko nafara haukacewa ne?

driver yana sauketa a hotel wanka tayi sn tay oder na abunda zataci dake azahr ya riga ya karato

tana kwance akan gadonta cikin yanayin tunani wayarta ya fara vibrating da gwuiya ta jawo dan har yanxu tunanin sultan bai wani saketa ba

nan taga kawarta ziyada ce nan take ta daga tace hello zeya...

daga dayan bangaren ziyada ta fara surutu

heyyy madam dubai har kin fara mantawa damu kenan ko u dint even call me

karamin murmushi ya kwacewa ushna tace

kedai nagaji ne ziyada

dan yanxu na dawo so nake naci abinci sai na kiraki ke akwai wata gist wallh

ziyada tace hmmm bani musha, toh ya program din ne..

mikewa zauna ushna tay tafara bata labarin komai da komai daya faru har da yadda aka gama tsara yadda za’a maidata kasar nigeria taje tanemo wani real estate company domin internship dinta

ziyada dake murmushi kamar mumu tace first of all ush wannan huge opportunity ce dan irin rayuwar da mutane dayawa suke kan mafarkin samu kenan

ushna tayi dariya dan kadan tace im actually sooo nervous girl.

xiyada ta fashe da dariya sosai tace ai dole, tunda gashi daga zuwa dubai ranar farko kawai har kin hango mana prince charming inmu, ya kuma sace miki zuciya a bugun farko..dama kuma ai nasha gaya miki da kike cewa ke bazakiyi soyayya ba kawai dan bakiga namijin daya miki bane

da wani irin murmushi ushna tace kai ziyada its just a crush, ke wai kinga gayen kuwa??Allah na tuba yadda yake din nan hala har abada bazan sake cin darajar ganinsa bama he is so damn hottttt.

xiyada ta kara fashewa da wata kalar dariya mai cike da tsokana tanamai jin tsananin mamakin ushna data sani bata son hirar maza kuma soyayya ma haushi yake bata

wai yau ushna din ce ta zauna da murmushi tana mata descrbng in wani namiji right from head to toe batare da ta tsallake komi nashi ba hmmm toh lallai tasan gayen nan ya masifar haduwa ya kuma sace zuciyar ushna bana kadan ba

cikin dariyar tace "I am so happy for u, karki damu zakiga kinsake haduwa dashi in sha Allah kuwa shine mijin ki....

cikin kyabe baki ushna tace "tabb di jam toh sannu ziyada daga ganin sarkin fawa sai kuma miya tay zaki har kin gai maganan aure dan Allah ki bari.

ziyada na murnushi tace“Allah na ya iyayin komi kawata, kawai ki daina underestimating kanki in shine mijinki wallhi zakiga kunsake haduwa cikin sauki

sai ta kara da cewa

“wait…so daga dubai din zaki wuce nigeria kenan neman real estate company..

tace “yes. they gave me few weeks to go home nd rest sai na basu report na inda na samu.

ziyada tace toh shiknan badamuwa am sure with your background bazaki sha wahala ba in sha Allah zakisamu.

ushna batace mata komai ba ta sauke ajiyan zuciya saboda ita kanta batasan ta inda zatama fara ba dan rabonta da nigeria tun fa tana primary 3.

sunjima suna girls talk dinsu me tsayi kafin nan daga karshe sukayi sallama

bayan sun gama call din ne aka kawo mata abincin rana ta zauna taci sai kuma bacci me nauyi ya dauketa

da yamma liss ta farka ta sake shiga warm shower snn ta fito ta saka pad ta sauya kaya zuwa soft silk pajamas masu kyau ta karacin abinci kadan sannan ta zura kimono me kauri tadan fito can waje tana zaga wajeje da daddare tana kallon dubai lights da luxury stores dake cikin hotel in cikin nutsuwa

saidai duk inda taga wani hadadden namiji ya wulga sai taga bai kai mata sultan din nan haduwa ba

babu karya her heart is becoming so crazy abt him duk dama bata saka aranta cewa zata sake cin sa'an ganinsa ba

ta jima waje kafin nan wajajen goma na dare tadawo tana zama akan gadonta ta fara kirar wayar addarta Areesha saidai bata daga ba, dan haka kawai ta tura mata short text messge na cewa zata dawo nigeria soon saboda internship placement.

bata mata wani dogon bayani ba tabar text in ahaka

saita kashe bedside lamp ta kwanta cikin soft duvet dinta tana lumshe kuwa ido taga fuskar Sultan yasake bayyana mata acikin tunaninta, kawai tuna cold eyes dinsa takeyi da wann calm aura nd

dangerous elegance din tanajin kanta cikin wata kalar farin ciki da tsumayi...

tambayar kanta take anya ta taba ganin wani namiji daya tsaya mata a aranta kamar wann gayen kuwa??

da wani irin shauki ta juya ahankli tanamai kara tantame idanunta

wondering if he even noticed her....

SURAYYAHMS

KODA GA INA KIKE KARANTAWA KI DAURE KIYI MANA COMENTS DAN MUJI RA'AYINKU..

SHIN ME KUKE GANIN ZAI FARU AGABA?

GA ƳA GA KANWA AKAN MUTUM DAYA...

DAYA TASANSHI A MATSAYIN YARIMAN THARIM VALE

DAYA TA GANSA A MATSAYIN SULTAN OF THE GULF ARAB REAL ESTATE PARTNER

HMMMMM

JAMA'A AYI SHARE

ENJOY READINGS..

SON SO....MY FANS

TALES OF THE WAZEERIS

BY SURAYYAHMS

2026

***