“SANADIN ƘADDARATA”

Page 70

by @zahratulqalam51

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️     
⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 


❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 


Free book📓


By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_


Page7️⃣0️⃣





Rai ɓace Haidar ya nufo inda Abba ya ke Bayan ya wurgar da duk abun da ya taɓa haɗa su na mutunci tsakaninsa da Abba. Daman ya ce ka da su sake su bari ya gane ɗayansu, don haka yanzu ba zai ƙyale Abba ba!!!.....

Cakumar rigarsa ya yi yana fitar da huci, bare yadda labarin da na ba shi ke ta dawo masa zuciya yanzu. Sai dai fa shi Abba kamar bai ji abun da aka yi masa ba, sai yunƙurin tahowa inda na ke da ya yi bakinsa na shirin yin magana idanuwansa ya tara ƙwallah. Amma ɗaga masa hannun da na yi cikin wani yanayi idanuwana a dake shi yasa shi gimtse bakinsa.

"A ah! Kar ka soma, kar ka fara yin hakan, saboda ba zai taɓa yin tasiri a wurina ba, zai fi yi maka alkhairi ka haɗiye kalmar da ka ke shirin fitarwa, domin kuwa a san da zai shigar min kunne, zai zame mini kalma mafi muni a cikin raina!". Abba ya matse ƙwallahn da ya tarun masa ko da jin kalamaina masu tarwatsa masa zuciya.

Ba na cikin natsuwa ko kaɗan, kukan da ke shirin taho min ya sanya ni juyawa da gudu ina fita daga ɗakin, ganin haka yasa Abba bin bayana ya kufce daga cakumar da Haidar ya yi masa, murya na rawa ya ke faɗin, "don Allah! Nuriyah! Please kar ki tafi, ka da ki kuma guje min, ki saurareni! Ina da kalamai da yawa da na ke son sanar da ke, ba zan iya cigaba da jurewa ba, 'yar uwata, ke jinina ce Nuriyyah!!..." abun da Abba ke faɗa kenan yana bin bayanta zuciyarsa na tsananta bugu kamar ba gobe.

Haidar ne ya yi gaggawan dakatar da shi, har a lokacin kuma fiskarsa a haɗe ya ke, "ina za ka je?!" Ya daka wa Abba tsawa, shi kuwa cikin magiya ya ke sake cewa, "Haidar help me, don Allah Haidar, wallahi ita che rayuwata, ina son Nuriyyah, ka ce mata ta saurareni, wallahi na yi dana sanin abun da na yi mata, ka taimaka min, i love her! Ina..." kafin ya ƙare maganar wani irin jiri ya ɗibeshi mai ƙarfi, ya fara tangal-tangal zai faɗi, ba jimawa ya yanki jiki ya yi ƙasa yaraf sumamme. Ko da ganin abun da ya faru hankali ɗage Haidar yasa salati yana ambatan sunansa, "Abbaaa!!".

Kafin na kai ga isa sashin Ummee da na dosa na ji muryar Haidar na faɗin haka, wani irin mahaukacin bugawa zuciyata ta yi, "me ya same shi?!" Na furta a raina. A gigice da gudu na yi ribas ina komawa inda su ke, wasu sabbin hawayen na sake fitar min tun kan na ga me ya same shi.

Rasa hankalina na ƙara yi ko da ganin Abba kwance kamar wanda duniya tai m yankan ƙauna, ban san lokacin da kalamai su ka fara fita daga bakina ba ina cewa, "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'una na shiga uku! Me ya same shi yaya Haidar? Don Allah mu kai shi asibiti cikin gaggawa, ba zan iya ganin faruwar wani abu garesa ba, ba zan iya jurar wani abu ya sameshi ba, don Allah ka taimaka min yaya Haidar na roƙeka..."  

Jijjigashi na cigaba da yi ina kuma faɗin, "Yayana! Yayana!! Ka ta shi ka tashi na roƙeka, kar kai min haka, me yasa za ka min haka? Yaya Haidar asibiti, mu kai shi!!" ina ƙarewa na fasa wani kuka mai ban tsoro. 

Haidar da ya saki baki yana kallona kukan da nasa ya kuma ɗaga mai hankali... yadda na ke wa Abba magana ɗazu, daga ji kalmar fitowa ta ke daga yanayin tsana da rashin so, amma bayan abun da ya faru yanzu, ba sai ya jira ansanar da shi cewa Nuriyyah har wa yau tana ƙaunar Abba ba, saboda tsantsar soyayyar da ya ke gani a cikin kalamanta.

  Kamar yadda na ce da gaggawa shima ya fara ɗaga Abba don kai shi asibitin.

HOSPITAL.

Hawayena ya ƙi tsayawa ko na daƙiƙa guda, na kasa natsuwa saboda wani irin harbi da jinin jikina ke ta faman yi, sai safa da marwa na ke da sauri ina neman rasa tunani na. Haidar da ke zaune na kallona da tausayi haɗi da mamaki lokaci guda, duk da kuwa shima ya damu akan halin da Abban ke ciki.

Tsayawa na yi da zirga-zirgan da na ke ina kallon ɗakin da aka shiga da shi, ko minti biyar ba ayi ba amma ni gani na ke kamar awanni mu ka shafe ba mu ji daga likitocin ba. Na yi saurin zuwa inda Haidar ke zaune ina hawaye na ce, "yaya Haidar, me ka ke tunani likitoci za su ce akansa?, ina fatan ba abun da zai samesa, tsoro na ke ji ace wani abu ya samesa, ya zanyi idan hakan ya faru? Wayyo Allahna!" na faɗi tare da haɗe hannuwana ina roƙon buwayi gagara misali.

"Ya Allah ina roƙonka ka nisanta bawan nan na ka daga duk wata matsala ta jinya, kasa ciwonsa mai sauƙi ne, ka kuma sa ya tashi ba tare da wani hatsari ba, Ameen" na furta ina matse hawaye masu zafi. Haidar da tausayina ya gama cikasa, a karo na uku ya kuma cewa, "ƙanwata, kamar yadda na ce miki ki kwantar da hankalinki, in sha Allah ba abun da zai same shi", da hanzari na ce, "da gaske yaya Haidar? Zai tashi ya min magana? Allah ya amshi maganarka" sannan na miƙe ina kuma safa da marwan da na ke.

Ummee ce ta taho wurin cike da damuwa, don har mu ka fita kafin ta san abun da ke faruwa, saboda Haidar ya sanar da ita. 

Ina kallonta na sa sautin kuka haɗi da zuwa na rungumeta da ƙarfi, rarrashina ta hau yi har mu ka samu damar zama akan kujerar. Tana rarrshinnawa ta ambata, "yata ki daina kukan nan, idan ba so ki ke nima na yi ba, me yasa za ki ta da hankalinki muma ki ƙara ta da mana da namu haka? Dubeki kamar ke ma ba ki da lafiyar fa, ki natsu 'yata". 

"Ummee ba shi da lafiya ne fa, lokaci ɗaya ya faɗi, kuma har yanzu doctor ba su fito ba, bare su sanar da mu halin da ya ke a ciki, kuma Ummee kin san irin wannan faɗin lokaci guda yana da illa matuƙa. In har wani abu ya samu yaya Abba ni ce SANADIN sa" na kai ƙarshe a sanyaye, "me yasa za ki ce haka 'yata?" Cewar Ummee, a sanyayen na ba ta amsa da, "saboda na ƙi tsayawa in saurare shi a lokacinda ya ke buƙatata, sannan na nuna masa kalamansa tamkar guba ne a gareni, da ace na saurare shi da ba abun da zai sameshi yanzu".

Cikin haushi Haidar ya katseni da cewa, "ya isa!!" Ɗif na yi na kasa wani motsi kalamaina su ka maƙale. Ya cigaba da cewa, "ya isa na ce! Wai kina ma a cikin hayyacinki kuwa ƙanwata? Kin manta abun da ya aikata miki ne shi da ahalinsa? Wai kin ma yin tunanin cewa, da ban haɗu da ke ba wancan ranar da me zai faru da ke?". Ya faɗi yana kawar da kansa gefe cikin takaici, sai kuma ya dawo da kan na sa yana yi min nuna da hannu ya ɗaura cewa.

"Da hakan bai faru ba da rayuwarki ta tagayyara! To ki saurareni, tun da su ba su yi tunanin abun da ka iya faruwa da ke ba su ka fitar da ke daga ahalinsu, to bai kamata ki yi irin wannan zaucewan akan ɗaya daga cikinsu ba. Amma shine yau ki ke nuna wannan damuwar akan Abba don kawai kun taɓa yin soyayya da shi!?..."

Shiru na yi kaina a ƙasa na kasa ce masa komai, shi kuwa sauke numfashinsa ya yi, sannan ya share gumin ɓacin ransa, Ummee ce ta dafa shi don ta tsaidashi akan abun da ya ke cewa, sai da ya kalleta sannan ya kuma dawo da dubansa gareni, ya sake faɗin, "eh, na san da damuwa ka ga mutum a halin da Abba ya ke ciki yanzu, kuma nima na damu da shi, haka Ummee ma, sai dai me yasa ke na ki damuwar ta wuce kima?... Tun da ki ka zo sai kuka ki ke yi, kin kasa natsar da kanki, kuma duk akan wanda ya jefa rayuwarki cikin garari shi da 'yan uwansa? Ni ban san saboda me ki ke yin hakan ba kuma....".

"Saboda har yau ina son sa!" Ba tare da na sani ba kalmar ta fito daga bakina cikin sanyin murya ƙwallah cike a idona. Numfashi ya tsaya a wurin Ummee da Haidar sai aikamin da kallon mamaki su ke yi.

Dama na yi ƙasa da kai na, don haka na ɗago ina dubansa ba tare da tuna kalmar kunya ba na ɗaura faɗin, "duk tsawon lokacin nan son Abba bai taɓa gushewa daga zuciyata ba Yaya Haidar... tabbas maganarka haka ya ke, sai dai duk da cewa abubuwan da su ka faru da kuma kalaman da ya taɓa faɗa min na yi min yawo a ƙwaƙwalwa ko wace rana, hakan bai taɓa sani jin ba na son sake yin rayuwa da shi ba. Ban san ya zan yi ba, ban kuma san ta yadda zan yi in yakice Abba a zuciyata ba, saboda ƘADDARATA haɗe ya ke da ƘADDARARSA, haka na ke ji a duk lokacin da na nemi na mance da shi a cikin rayuwata. Ummee, yaya Haidar, ina da yaƙinin za ku fahimceni".

Na faɗi hawayen da ya cika min ido ya gangara bisa kuncina. Kalamaina sun shiga jikinsu, Ummee ta janyoni jikinta da tausayawa, saboda har isonta ya yi nauyi ganin jna kuka.

Abba. Bayan ya samu damar farkawa, bai tsaya yin wani tunani ba da sauri ya yunƙura zai sauka daga kan gadon, likita su ka yi kansa suna hana shi tashi, amma ya ƙi sauraronsu, sai da ya sauka daga gadon da ya ke ɗin, ya fisge abun ƙarin ruwan da aka sa masa. 

Ko da fitowansa waje a lokacin ya tadda abun da Nuriyyah ta faɗa gaba ɗaya, ji ya yi kamar ya gama warkewa daga duk ciwon da ya taɓa yi, ya ji kalaman da bai tsammace su da wuri haka ba, "shin kunnuwana da gaske ne abun da su ke jiye min? Nuriyyahta ce ke faɗan wannan kalaman akaina? Alhamdulillah!!" Cewar Abbah a zuciya yana lumshe ido fiskarsa na bayyanar da Annuri, hawayen farin ciki su ka gangaro masa yasa hannu ya goge.

Surutun da likitoci ke yi ya maido da hankalinmu kansu, nan mu ka ga ashe da Abba su ke yi, tsayawa na yi na fara aika masa kallo zuciyata na motsawa, farin ciki ya mamaye zuciyata. Shima idanuwansa ne cikin nawa, ko sauraron kalaman likita ma baya yi, cikin rashin ƙarfin jiki ya iso gabana ba tare na matsa daga inda na ke ba, na riga da na yi nitso cikin kallon ƙwayar idonsa.

Ummee da Haidar kam sa mana ido kawai su ka yi ba tare da sun ce mana komai ba. Ba tare da na ankara ba ya ɗaga hannunsa ya ɗaura akan fiskata ya share min hawayen da bai tsaya ba, sai a sannan na farga da abun da na ke yi, daman ban tsammaci ya ji kalamain da na yi akansa ba, "ya jikinka? Ba abun da ya sameka?".

Sai da ya girgiza kansa sannan ya ce, "na warke, ba abun da ya ke damuna yanzu, na ji daɗin..." juyawan da na yi da sauri ina goge hawaye, shi ya katsar da maganansa. Ba zan iya irga farin cikin da na ji saboda ganishi tsaye bisa ƙafafunsa ba, bare ma da kalamansa su ka ratsa majiyata. Sai dai duk da haka ba zan iya cigaba da kasancewa tare da shi ba. 

Taku na fara yi zan bar wurin, hakan yasa hankalin Abba ya kuma tashi saboda ganin da ya yi zan wuce na bar shi, da hanzari ya furta, "don Allah!" Hakan ya dakatar da ni daga tafiyan da na yi niyya, na tsaya ina sauke numfashi, a hankali ya tako ba tare da ya dawo gabana ba ya ce, "don Allah ki tsaya ki saurareni... tsawon lokaci ni da su Momy ba mu da buri da ya wuce mu ganki, mun yi nema, mun yi cigiya amma ba mu yi nasara ba, hakan yasa mu shiga damuwa ba mu da natsuwa ko wani lokaci... na san mun tafka miki babban kuskure da yafe shi zai zame miki abu mai nauyi. Mu samman ni, na san na fi kowa yi miki laifi da karya miki zuciya... amma ki yarda da ni, wallahi ina sonki... ako da yaushe ina jin cewa da ke kaɗai zan iya rayuwa, I love you Nuriyyah!".

Lumshe ido na yi ina sauke numfashi a hankali, na tuno da lokacin da ya fara furta min wannan kalmar, wanda farin cikin hakan yasa na kusa raba dare cikin sauƙi. Shi kuma ya cigaba da cewa cikin magiya, "na rasa ta ina zan fara... ban san da wani kalma zan iya neman yafiyarki ba... Nuriyyah ki tausaya min please, ki tuna yadda mu ka kasance da ke a baya, su Momy, Dady, Asma'u, da ma kowa jiranki ya ke yi, ki amincemin mu koma gida", a sannu na juyo ina kallonsa bayan na tsayar da hawayena, shiru ya ratsa tsakaninmu ni da Abba numfashinmu na sarƙewa.

Kamar ba zan ce komai ba, na ja numfashi na furta, "idan ka koma... ka gaishesu, sai wani lokaci!". Ina furta hakan na juya na kalli su Ummee, "ya samu sauƙi yanzu, mu tafi Ummee, yaya Haidar mu je". Ban kuma cewa komai ba na fice su Haidar su ka rufa min baya. 

Samu damar zama ya yi akan kujerar asibiti yana matsar ƙwallah, gaba ɗaya jikinsa ya gama yin la'asar. Bayan duk kalaman da ta faɗa akansa kenan ba ta yafe masa ba? Ko da ya ke da ma ya san ba abu mai sauƙi ba ne ta yafe masa lokaci ɗaya.

Bayan mun koma gida kai tsaye ɗaki na nufa, Ummee za ta bi bayana Haidar ya tsaidata, da cewa ta ɗan barni ni kaɗai tukunna, ƙila hankalina zai fi kwanciya idan na kaɗaice.

Ni kuwa ko da na faɗa ɗaki kuka ya ƙwace min na shiga rerawa, ina jin zuciyata da nauyi na rasa me ke yi min daɗi a duniyar, sunan Abba na dawarmin tunani ko wani daƙiƙa, na kasa gane abun da na yi daidai ne ko ba daidai ba? ....


Last page
___________________________________________________

Mutanen Arziƙi me tunaninku akan wannan lamarin. Mutuniyar fa kamar ta sauko, sai kuma ta sake rikicewa.

Shin Abba zai je ya sanar a gida ya ga Nuriyyah? Ko kuwa sai ya shawo hankalinta kafin nan?.

Shin wai shi Haidar ya ma haƙura da ramuwar? Ko da saura?.

Ku kasance da ni a kashi na gaba.


_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_