Page 71
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page7️⃣1️⃣
Ni kuwa ko da na faɗa ɗaki kuka ya ƙwace min na shiga rerawa, ina jin zuciyata da nauyi na rasa me ke yi min daɗi a duniyar, sunan Abba na dawar min tunani ko wani daƙiƙa, na kasa gane abun da na yi daidai ne ko ba daidai ba?
WASHE GARI.
Muna zaune a gurin cin abinci gaba ɗayanmu, Khairat sai surutu ta ke yi amma a yau babu mai biyeta, saboda duk idanuwansu da hankalinsu a kaina su ka ajje shi, duk da suna cin bincin amma ba kamar ni ba, sai juya cokali kawai na ke yi cikin plate hasashena ya yi nisa ban ma san cewa suna lure da ni ba.
Alhaji ne ya ja numfashi sannan ya ambaci sunana, amma kasancewar na yi nitso cikin tunanin abun da ke shirin dawowa rayuwata yasa ban ji sa ba. Taɓani da aka yi ya fargar da ni, na yi saurin juyawa ina kallon Mu'azzam da shi ne ya yi hakan, shima da kansa ya rasa gane mini domin babu wanda ya yi masa bayani.
Kallon da na ke masa yasa shi faɗin, "daman Alhaji ne ya kiraki har sau biyu baki amsa ba" da sauri na kuma maida kaina inda Alhajin ya ke, nan na ga ashe sauran ma duk kallona su ke, cikin neman afuwa na ce, "ka yi haƙuri Alhaji, daman... ban ji ba..." kafin na ƙarasa ya katseni da cewa.
"Tun jiya na yi miki tambaya amma ki ka ce babu abun da ke damunki, ki ka ƙara da roƙona kan na bar komai don Allah. Duk da kuwa abun da na ji ya faru acan asibitin, amma na bar komai domin kin tabbatar min da kina lafiya. Nuriyyah!" Ya kai ƙarshe da ambatan sunana.
Na amsa da sunkuyar da kai, "amma yanzu na lura da ba kya cikin kwanciyar hankali.... abun da na ke so da ke shine, kamar yadda na san cewa kin ɗaukeni tamkar mahaifinki, to ki sanar da ni mecece matsalar da ke hanaki sukuni? Ni kuma a matsayin 'yata zan magance miki shi na yi alƙawari. Ba na jin daɗin ganinki a wannan yanayin, duba can..." Ya faɗi yana nuna su Ummee ya ƙara da cewa, "dubi yadda su ke, duk sun kasa natsuwa saboda ke ma ba kya cikinsa".
A hankali na ke kallonsu tabbas na ga damuwata acikin idanuwansu. Ni da kaina na rasa gane dalilin da yasa na kasa daurewa na kuma kasa dannewa, ban san takamemmen abun da ke matsalata ba, kalaman da Abba ya yi min na ke tunanowa kowani lokaci.
Ƙara kirana da Alhaji ya yi ne yasa na juya gefensa, ya ce, "ina jinki faɗa min..." ijjiyar zuciya na yi na buɗe baki zan yi magana, sai dai kafin na furta wani harafi ƙwanƙwasa ƙofan da aka yi ya katse min hanzari, "laa, waye a ofa?" Faɗin Khairat, murmushi na yi na miƙe ina dubansu, "bari na je na duba".
Ko da na isa gaban ƙofar na sanya hannuwana ina buɗewa, ɗan aikin gidan na gani a bakin ƙofar, ina shirin yi masa magana numfashina ya tsaya, sakamakon Abba da na gani ya fito daga gefen ƙofar, daskarewa na yi ina kallonsa da mamakin abun da ya kawosa, duk da dama zaton zuwansa tun jiya ya ke a raina.
"Yata Nur!" Kalmar Momy ta daki kunnuwana ba tare da na ganta ba, sai da na rufe ido domin na yi kewar me kirana da wannan suna, "Momy" na furta cikin sanyin murya bugun zuciyata na ƙara tsananta.
Kwatasam ba zato na ji ta amsa, "na'am 'yata" da hanzari na buɗe idona don ganin wacca ta amsa da murya kamar ta Momyna, saboda na yi tsammanin zuciyata ce ke min wasa kunnuwana na ruɗani, amma akasin haka ne don Momyna ce na gani a gefen Abba tsaye tana yi min ganin tsananin kewa.
"Yata ya ki ka daɗe? Su waye ne a ƙofar?" Faɗin Ummee jin na jima ban dawo daga duba ƙofar ba. Kalma ta maƙale à bakina bare na sake ambatan ko da sunan Momyn ne. Momy kuwa da ƙwallah ya taro a idonta har sai da ya samu damar zubowa, kasa haƙuri ta yi ta taho da gudu ta rungumeni, sai da na kuma lumshe ido ina jin wani sanyi ya shiga raina.
Ban yi tunani ba jikina ya amsa kansa ga Momy, na rungumeta da ƙarfi kamar wacce ta daɗe tana jira, zuciyata na neman fashewa da wani irin farin ciki mai zafi da kewa. Na matso ruwan da su ke rawa tun ɗazu a idona.
Wani irin murmushi ne ya bayyanu à fuskar Abba sosai.
_Da ƙyar ya samu damar komawa gida jiya, saboda wani irin karaya da ke zuciyarsa, ko da ya isa bai so sanar da Momy da fari ba, amma ganin yanayinsa da kuma azalzalar da Hajiya Kaka ta yi masa yasa shi faɗin komai a garesu. Kasa ɓoye farin cikinsu su ka yi dukkansu, ko da bai sanar da su yadda aka kaya ba. Tun a daren Momy ta so su zo amma Hajiya Kaka ta tausheta akan ta bari sai zuwa gobe sai su je baki ɗaya, hakan yasa ta haƙura ba don ta son ba, ko wannensu kuwa kwana ya yi da ƙaguwan son haɗuwa da Nuriyyah gobe idan Allah ya kaimu. Bayan gari ya waye kuwa su ka shirya da wuri dukkansu don ba za ayi ba su ba. Abun da su ka yi tsawon fatansa ya bayyana_....
A hankali na ɓanɓare daga rungumar Momy ina kallon sauran dangin da su ke a bayansu, kallonsu na tsaya yi, "wai lafiya 'yata ki ka jima ha..." faɗin Ummee da ta taho wurin wurin, amma ba ta kai ga ƙarshewa ba sakamakon ganinsu da ta yi suma suna dubanta......
Numfashi ne kaɗai ke tashi a cikin falon bayan Ummee ta yiwa su Momy iso zuwa ciki, maganganu da labarin da Momy ta bayar ya kashewa wasu jiki ya kuma ba wasu mamaki, Haidar suna mamakin duk abun da ya farun nan ashe wa'yan nan mutanen 'yan uwan Nuriyyah ne, ko kuwa ya ce 'yan uwansu.
Baki na rawa ya ce, "kuna nufin ku asalin 'yan uwan mahaifiyarmu ce ni da Nuriyyah?!" Dukkansu sai da su ka jijjiga da wannan sabon al'amarin, daman Nuriyyah tana da wa kenan ba su sani ba? Ashe 'ya'yan Wasila biyu ne a duniya?.
Alhaji ne ya tabbatar mu su da hakan, ta ke kiɗa ya sake sauyawa, murna ya sake cikasu matuƙa gaya, kowa ya shiga hamdala da jinjina buwayar Allah. Idon Abba kuwa tun ɗazu kaina ya ke, ya lura kamar ma ƙwaƙwalwata baya tare da su, burinsa kawai à yanzu shine ya ji kalmar yafiya daga bakina.
Ni kam na riga da na bushe da mamaki ko motsi ƙwaƙwƙwara ba na yi, duk wannan daɗewar da gwagwarmayar, ashe cikin ahalina na rayu ba tare da sani na ba? Cikin dangin mahaifiyata wanda na daɗe ina fatan haɗuwa da su? Allah kenan mai iko, wanda ya ke sarrafa komai yadda ya so a kuma sanda ya so, wanda ya ke ɓoye komai sannan ya bayyanashi a lokacin da ya dace.
Hannuna da aka kamo ya katsar da ni na juyo da nannauyun idanunwana, wa'yan da su ka saba fitar da ruwa a duk lokacin da zuciyata ya yi irin wannan motsawar. Haidar ne ya dafa ni sannan ya yi min nuni da kai zuwa ga su Momy da su ke ta faman yi min magana da neman yafiyata a jere.
Murya na fara ji a hankali cikin kunnuwata, wato muryar mahaifiyata,, sakamakon tunowa da na yi da kalaman da ta taɓa sanar da ni a baya,
_"yafiya ga ɗan uwanka yana daga cikin abun da zai kai bawa zuwa aljanna, tabbas duk wanda ya aikata maka laifi sannan ya nemi yafiyarka abu mafi kyau shine, ka yafe masa ka kuma mance da abun da ya yi maka, ko da kuwa shi mutumin bai zo ya nemi yafiyarka ba, idan ka yafe mishi kana da lada mai girma sannan ƙimarka na ƙara ɗaguwa. Nur, ina jin daɗin yadda ki ke nuna irin wannan halin mai kyau" sai da Umma ta numfasa haɗi da dafa kaina, yayin da ni kuma na ƙara natsuwa ina tura duk kalamanta cikin ma'ajiyata. Tana mai murmusawa ta kuma cewa, "bayan haka, ina son ki cigaba da riƙe duk kyawawan halayenki da na san kina da su, musamman haƙuri da juriya, ina mai tabbatar miki idan ki ka cigaba da haka wata rana za ki kasance abun sha'awa ga kowa, sannan abun yabo da kwatance. Allah ya yi miki albarka 'yata Nur"_
A sannu na baro tunanin bayan jinsu sun ƙara ratsani, a sannan na ji muryar Momy na cewa, ''yata Nur, don Allah ina mai baki haƙuri, ki yafe mana abun da mu ka aikata miki", duk da cewa ba ita ta aikata min lefin ba, amma ta san dalilinta ne komai ya faru, Asma'u ce ta taso cikin kunyar abun da ta aikata ta durƙusa kusa da ni tana cewa, "yar uwata na roƙeki ki yi haƙuri akan abubuwan da na yi miki a baya bisa rashin sani, na ci zarafinki, na kuma bari kalaman wasu ya yi tasiri gurin rusa yardar da na ke da shi akanki, alhali ceton rayuwata ki ke ta ƙoƙarin yi, wallahi ke 'yar uwa ce ta haƙiƙa". Ta faɗi tana share ƙwallah.
"Saboda yadda na so mahaifiyarki shine yasa ni sanya sunanta Wasila kan 'yata da na haifa, saboda na rinƙa jin tana kusa da mu a duk lokacinda aka ambaci sunanta, amma sai ga shi na tsaneki ba tare da na san ke jininta ba ce" Mama ce me wannan maganar tana jin takaicin halin da ta sha nuna min à baya. Haka Dady ma cikin sanyin muryar ya ce, "nima ina neman gafararki 'yata, duk da cewa kin ɗaukeni a matsayin uba, amma ni nakasa amincewa da ke a lokacin da ya dace".
"Tabbas mun ci zarafinki sannan mun aikata miki laifi mai girman gaske... amma jikata don Allah ki yafe min, na kasance marar tuna..." faɗin Hajiya Kaka cikin rarraunar murya mai cike da dana sani, musamman da ta ke tunano abubuwan da ya faru, sai da idonta ya cika da hawaye suna fita, kamar yadda kusan duka 'yan falon a bun da su ke yi kenan.
Kafin ta kai ƙarshen kalaman na ta na tsaidata ta hanyar furta, "kar ki ce haka don Allah Hajiya Kaka" na faɗi tare da miƙewa, sannan na nufi inda ta ke, miƙewa ta yi haka sauran mutanen falon. Hannunta na kamo à hankali muryata na sarƙewa na ke faɗin, "abun da ya faru ya riga da ya wuce yanzu, sannan... na yafe muku!" Kowa ya saki murmushin farin ciki da jin daɗi.
"To idan ban yafe muku ba me ribata? Ba zan taɓa yi muku ramuwar abun da ku ka yi min ba, ku ne ku ka inganta rayuwata, ku ka barni na kasance ɗaya daga cikinku ba tare da kun san daga ina na ke ba, kune ku ka sani makaranta,kun ciyar da ni kun suturtani, kun ba ni duk abun da ɗan adam ya ke nema don rayuwa, to kuwa me zai sa ba zan mance da abun da ya faru ba? Kuma sannan abun nan da ya faru shine ya yi SANADIYYAR da na haɗu da ɗan uwana, wanda ƙila da hakan bai faru ba, ba na tunanin zan same shi cikin sauƙi, so everything has already passed. Abu mafi mahimmanci yanzu a gareni shine jin cewa ku cikakkun jinina ne, na yi matuƙar farin ciki, babu abun da ya fi min wannan daɗi".
Hatta su Ummee sun ji daɗin wannan furucin na wa, bare wa'yan da abun da su ke burin ji kenan, take falon ya kuma zagayewa da annuri fal har kowa ya rasa me ma ya kamata ya yi?......
Wasu mintuna.... Ina tsaye tare da Asma'u da wasila à tsakar gida ta gefen tsirrai wato garden muna shan iska, sai hira mu ke kowa na bayyana kewan da ya yi, muna cikin maganar na ga su Asma'u sun tsaya da hirar. Kallon Wasila na yi na ɗaga mata gira na ce, "ya na ga kun ɗauke wuta nan take?" Ba su bani amsa ba, sai sakar min murmushi da su ka yi su ka barni tsaye, bin bayansu na yi da kallo ina son nemo me aka ce acikin maganar da ya sa su yin haka? Abba da na gani a wurin ya tabbatar min da cewa shine wanda ya sa su barin wurin.
Kauda kaina na yi daga gareshi kamar ban ganshi ba. "Ba ayi farin ciki da gani na ba ne?" Ya yi furucin yana mai isowa inda na ke fiskarsa bayyane da fara'a, ni kuwa maida fuskata na yi ba yabo babu fallasa. Sai da ya sauke numfashi marar sauti ka na ya ce, "me yasa ni kaɗai za a ƙi yiwa murmushi? Ina ce anyafe mana ko?" "Anyafe muku, ka ga shikenan babu wani sauran magana ko?" Nima na bashi amsa kamar yadda ya furta.
Abba ya lanƙwasa baki tare da sanya hannunsa bisa sumar kansa, sai da ya murza laushinsu sannan ya sauke hannun zuwa aljun wandonsa ya ce, "eh haka ne, amma akwai maganar da na ke son yi da ke, game da alaƙarmu ni da..." "please stop!" Na katseshi daga maganar da ya ke son yi, sannan na juyo kai tsaye ina ƙare masa kallo.
Murya à tsaye na ke faɗin, "babu buƙatar jin komai, domin kuwa na san tatsuniyar gizo baya wuce na ƙoƙi, to ina son ka mance da ni a cikin ranka!" Sai da cikin ran Abba ya tsinke, ya yi saurin zare hannun da yasa a aljuhu ya matso kusa da ni ya ce, "amma... me yasa za ki min irin wannan hukuncin me tsanani à gareni Nuriyyah? Sannan... sannan ranar a asibiti na ji daga bakinki cewa kina so na".
Ƙasa kaina ya yi ina tuna wato lokacin da na yi wa'yan nan surutan ya ji ni kenan? To amma duk da haka, dole na sanar da shi gaskiya a yau ba sai anyi nisa ba, gaskiyar da zai iya jijjigashi ya kuma sauya masa tunani.
Ƙwayar idona na mayar kansa na kuma faɗin, "ina mai ba ka haƙuri yaya Abba, saboda dole yau alaƙar da ke tsanina da kai ya sauya, ka fice daga rayuwata, ka ɗaukeni à matsayin 'yar uwa kawai wanda a da babu hakan, ka mance da mun taɓa rayuwar soyayya ni da kai!".
Abba ya rintse ido yana jin wani raɗaɗi na ziyartar zuciyarsa, farin ciki da ke ciki na shirin disashewa, ya buɗe idon bayan ya ja numfashi, sannan ya fara matsowa kusa da ni, da mamaki na ke binsa da kallo ina ja baya a hankali.
"Ina son ki saurari bugun numfashin ki, sannan ki hasaso tunaninki, kafin ki ƙara sanar da ni cewa ba kya sona" ya faɗi ba tare da ya daina kusantoni ba, haka nima ban daina ja da baya ba, har na manne da jikin bango wato babu damar cigaba da ja baya, shi kuma ya dakata yana daf da ni har numfashinsa na ke ji wanda ya ke fita da ƙarfin gaske saboda yadda zuciyarsa ta ke bugawa, kamar yadda nima tawa ta ke motsawa da ƙarfi.
Shiru ya mamayemu sai iskan ganyayyaki da ke kaɗawa ta wurin, gelen da ke kaina ya hau lilo har ya rufe fuskata. Hannunsa ya ɗaga a hankali ya sa a fuskata don ɗauke gyalen da ya rufeni, a sannu ya ke buɗewa idanuwansa cikin nawa, sai iskar da ke wurin ta ƙara ƙarfi à garemu.
"Wannan!" Na furta hakan ya tsaida duniyar da Abba ya shiga zuwa na zahiri da mu ke a ciki, ya ɗan matsa daga daf da ni tare da juyar da kansa gefe don ganin abun da na ɗaga kuma na ambata da 'wannan', wayata ce ya ga na ɗaga, ya dawo da dubansa gareni don neman ƙarin bayani.
Wayar nima na kalla ina faɗin, "wannan wayar tawa, aciki hotonsa ya ke, wato wanda na maye gurbinka da shi!" Damn! Zuciyar Abba ya ƙara bugawa, "ki... kina nufin akwai wanda ki ke so bayan ni Abba? Akwai wanda ki ka ba zuciyarki baya ni?" "Exactly! Ina son wani ba kai ba, wanda na ji zan iya sauya rayuwata don shi kaɗai! Shine wanda ya ƙara jaddada min me ce ce kalmar so, me kuma ta ke nufi? Ya bani yarda, wanda hakan ba zai taɓa sanya shi amincewa da duk abun da aka faɗa masa akaina ba!".
Taku na yi zuwa bayan Abba na kuma cewa ba tare da dana sani ba, "labarin ba wani mai tsawo ba ne, kuma zan sanar da kai ko shi ɗin wanene? Na san za ka girgiza bayan na sanar da kai, domin kuwa shi ɗin ba kowa ba ne sai mutumin da ka sani, wato shi ɗin na kusa da kai ne... babu wanda ya san da labarin, amma dole yau za ka sani, because he is the one I’m going to marry!!!".
Last page
___________________________________________________
Toh kamar komai ya wuce kamar kuma bai wuce ba, ko waye wanda Nuriyyah ta maye gurbin Abba da shi? Don dai ba mu ji labarinsa ba. To ya Abba zai yi?
Mu kasance a next insha Allah.
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_