GARGADA

Chaptee 1

by @kyautadagaallah10

*Gargada*



  Na 

 Ikilima Adam 



Ina mika sakon gaisuwa da fatan alkhairi da yan uwa da abokan arziiki na.

Duk wani alkairi dake cikin wanna littafin Allah ka bani ladansa akasin haka , Allah ka  yafe min.

 Littafin nan ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba.
Kuma ban yarda ayi amfani dashi ba , babu izinina ba .

Littafin kudi ne akan naira 700 kacal zaki sha karatunki bayan gama sakin free page.

Bismillahi rahmanin rahim 


Page 01


Shari'ar da ake gudanarwa a kotu, wadda gidajen talabijin ke haskawa har da tashar canal 3 , sharia ce mai tashin hankali inda aka gurfanar da wata yarinya yar shekara sha biyar.

A gidan Alhaji Abdullahi,  sosai iyalan gidan hankulansu ya karkata wajen kallon wannan sharia da ake gudanarwa tsakanin matar attajirin da aka kashe , da kuma wannan yarinyar yar shekara  sha biyar .

Alhaji Abdullahi dake zaune kan kujerarsa ta alfarma ,gefensa matarasa ce da yayansa da dukansu hankalinsu na kan wannan shari'ar.

" Alhaji yanzu yara kanana suke kisa , daga masu kashe mazan su don kishi, sai masu kashe maza dan kwadayi , yanzu duba wannan yar cokalin yarinyar wacce autarka ma ta girmeta wai ita ce ta kashe uban gidanta" sai ta numfasa tana mai kallon Alhaji Abdullahi dake jinjinawa da kai hakan yasa shi fadin.

" Amma kuma kaga yarinyar nan wallahi kamar ba zata aikata ba , yarinya karama daga ganinta bata ma gama mallakar hankalin kanta ba , kuma sai nake ganin kamar ba zata iya kashe bera ba bare har ta kashe mutum , don dai ance mugu bai da kama da sai ince akwai lauje cikin nadi" sai yayi shiru yana jin yarsa me shekara 18 na fadin .

" Dad ni dai don Allah ka taimaka mata , ko tayi kisan nan yarinya ce fa " shiru tayi ganin isowar babban yayansu a falo .

Sanye yake cikin shadda fara sol mai  sheki  .kallo na masa na tabbatar Allah ya nuna ikonsa a wurin halittarsa.  fari ne sol tamkar zubin  larabawa, tsaye yake , dogon namiji ne wanda bashi da kiba , sannan ba za'a  sashi jerin ramammu ba , jajjayen labansa ba karamin kyau suka kara masa ba , zanen hancinsa ya tafi cif-cif . Agogon hannunsa yake kallo yana mai durkushe har kasa gaishe da mahaifinsa da matar ubansa dake kusa dashi . Kannensa mata ukun dake wajen duk sai da suka gaishe shi , amsa musu yake cikin cool voice dinsa.
Idanunsa ya kai kan talabijin akan sharia da ake yi , kana ya dauke idanunsa yana mai fadin.

" Dad , yau zanyi saurin fita, daga cen zani sallah juma'a " yayi magana ne yana kokarin barin falon.

" To Assadiq Allah ya kaika lafiya " cewar Alhaji Abdullahi da kannensa .matar uban nasa Hajiya Rahma cike da jin dadi ta furta.

" Gaskiya Assadiq yaron nan akwai ladabi , Allah ka bashi mace ta gari , shi da kaninsa Ahmed".

"Ameen " cewar Alhaji cikin jin dadi . Kana yana kallon yanda yaran suke kallon wannan shari'a suna kwallah musamman inda suka ji ana cewa yarinyar bata da lauya.
" duk kun tada hankulanku akan case din yarinyar nan " cewar Hajiya Asmaou cikin mamaki.
Fuska a shagwabe khairat wacce ita ce karamar gidan tayi.

" Humm mommy kun san hukuncin kisa shine aka kashe , wannan yarinya ce fa ku dubi yanda take a firgice yanzu sai a yi shiru ana kallon zaluncin da zaa mata " tayi magana tana kukan zuci da fili.
Dad da mamaki yake kallonta kana ya numfasa yana saka hannunsa cikin aljihun wandonsa alamun waya ze ciro.

"In banda abunki khairat , ke da kanki kin ce hukuncin kisa shine a kashe , to me kike so ayi ne "?.

" Ni kawai so nake a dauakar mata lauya , shine ze bata damar fadan gaskiya".

Cike da murmushi Alhaji Abdullahi ya tabbatar mata da ze duba lamarin nata , ya fadin hakan ne yana mai kokarin fita da falon nasu izuwa tsakar gida. Yayinda hajiya Asmaou ta take masa baya , su kam yaran duk jikinsu a sanyaye.

Mafi yawan lokuta Alhaji Abdullahi yana son zama tsakar gida nasa inda sautin mabubbugar ruwan ke nutsar da duk wata hayaniyar kasuwa da ya baro. A nan,karkashin inuwar dabinon da ya dasa shekaru biyu da suka wuce, yake jin lallausan kafet din da aka shigo masa dashi daga kasar waje, yana kara tabbatar masa da cewa, lallai jajircewa a kasuwanci takan samar da hutu na alfarma.
Bayan ya samu zama ne , ya fara kokarin kunnar kira'a karatun alkurani mai girma daga cikin wayarsa iPhone17promax .
Kamar an tsinkaye shi haka ya ji sautin maganar Khairat na ataimaka wa yarinyar na masa zarya cikin kunnuwarsa.
Hajiya Asmaou yake kallo da take kiran ma'aikata domin ajiye masa kayan fruit irinsu kankano da inibi sune abunda yafi bukata a wannan lokacin.

Kashe gari.

Assadiq ya fito daga bayi yana goge sauran digon ruwan da ke fuskarasa da wani karamin tawul mai laushi. Ya dade yana kallon kansa a cikin madubin dakin nasa wanda ya mamaye rabin bangon, yana jin dadin yadda hutu ya kara fito da kyawunsa.

Ya karasa gaban katuwar talabijin dake manne a bangon dakin , ya dauki remote ya danna ta . Nan take hasken talabijin din ya gauraye da hasken rana dake shigowa ta labulen dakin.

 Yana shiga tashar *Canal3* idanunsa suka gane masa abin da bai tsammani ba .

" Wanna ai shari'ar jiya ce da na ji ana zance , kuma naga su khairat da Dad suna kallo" yayi magana a zuci idanunsa na kan tv.

 Yarinya tsaye a gaban sharia, fuskarta na nuna rashin tsoro . Karkada kai ya shiga yi yana kallon yanda ake wannan shari'a wanda hakan ya mantawa da shirin sanya kaya da yake shirin yi. Nattaro hankalin yayi wajen shafa mayuka masu tsada da suka wa fatarsa laushi , ya nufi dakin sanya kaya , ya dauko wando mai kalar navy bleu da kuma riga kalar sky bleu mai dogon hannu wanda aka nade hannun kadan.
Agogon gwal ya sanya , feshe jikinsa yayi da turaren oud wanda kamshinsa ya cika ko'ina a dakin. Ya kalli kansa a madubi, ya gyara agogonsa na gwal ,sannan ya zura kafarsa cikin takalmin fata mai sulbi. A lokacin da ya fito falo , takunsa kadai yana nuna cewa lallai shi namiji me ji da kansa .koda ya zauna dinner table domin yin karinsa , lumshe idanunsa da yayi sai yake ganin kamar mahaifiyarsa da ta dade da rasuwa tana masa magana cikin kunne.

" Assadiq duk halin da kake ciki ka kasance mai tausayin mata " wannan shine kalaman da yake yawan yawo a kunnesa muddin ya tuna ta .
 Lumshe idanunsa yayi yana kallon kayan abinci cikin mamyan kuloli da kuma flask da kayan tea.

" Zan taimaka mata " shine kalmar da ya fita a bakinsa ba tare da ya shirya hakan ba.
  " Yaya yau kai ne , ka riga mu isowa dinner table " wannan sautin murya mai dadi ya fito daga bakin kaninsa Ahmed dake sanye cikin shiga irin na Assadiq.

Zama yayi kana , ya kara da fadin " yaya ina magana kayi shiru me kake tunani ne ".
Cewar Ahmed wanda suke tsantsar kammani da Assadiq sai dai yayan nashi ya fi shi kyaun halitta.

" Ina son ka binciko min bayani akan shari'ar da ake yi da wannan yar yarinyar da bata da lauya , ka nemo min kwararen lauya " sannan ka samo min address din gidan yarin da take " yayi kai kace ba shine yake magana ba.

" Wai shari'ar jiya na yar shekara sha biyar"?. cewar Ahmed cike da mamaki dan a saninsa Assadiq ba shida lokacin kowa baya shiga abunda be dame shi ba".
 
" Toh yaya in sha Allah zan yi yanda kace , gaskiya ba sai mun jira su mummy da Dad ba , mu yi karin mu , mu fice nima ina da ayyuka yau container shinkafa ze iso, sun ma kusa karasowa" cewar Ahmed yana mai fara service dinsu da ruwan zafi a cup din tangaran.

Assadiq kallonsa yake , yana mai lumshe idanu alamun ya hada musu shayin , Ahmed ya hada musu tea , suka hada da soyayyan kwai .
Suna kammalawa Su Khairat da maimuna da Asiya suka iso falon.
Sun sha mamaki ganin wai yau da Kansu suka yi servi Kansu.
Cike da ladabi suka gaishe su.

Khairat kuwa kusa da Assadiq ta zauna ta saka hannunta cikin nasa tana kallonsa .
" Yaya don Allah ku taimaka da wannan yarinyar nan , wallahi sai mafarkinta nake , jiya na mata kuka sosai, musamman inda tace ita ko baa kashe ta ita zata kashe kanta da kanta " sai ta numfasa tana mai matse hannunta cikin nashi.
" Kuma a tsarin doka wannan yarinyar bata kai ayi sharia da ita ba 15yrs fa yaya " tayi ajiyar zuciya tana kallonsa , shima ita yake kallo dan cikin kannensa ita yafi bawa kulawa wajen sauraron ko wani shirme ko na nutsuwa da zata zo masa dashi .

" Khairat na zanyi wan abu akai in har zaki ji dadi a ranki" ya fada yana shafa fuskarta .
Murmushi tayi wanda rabonta dashi tin jiya.

Ahmed da su Maimuna da Asiya murmushi suke suna fadin .
" Sannun antin yarinyar nan da ake sharia da ita " dariya suke suna tsokanarta amma a zuciyarsu sun ji dadin yanda aka samu mai tsaya mata.
Ahmed ya riga Assadiq tashi sallama ya musu kana yayi hanyar fita .

Assadiq cikin uzuri shima ya fito bayan ya leka kicin ya gaisa da Mairo yar aikin gidan, dattijuwa , ita da yarta sun ji dadin zuwansa don in yana free sai ya leko sun gaisa , sallama ya musu bayan ya basu kudi in har suna bukatar wani abu, ya sha adua kana ya bar kitchen din.

" Idan Dad ya fito ku fada masa mun tafi " yayi magana da kannensa dake brek fast.
  Da " to" suka amsa.

____________________


Gidan Magajiya Zinaru.


Gidan magiya Zinaru daban yake da sauran gidajen unguwar. Tun kafin ka karasa, kamshin turaren wutar daka da hayakin taba zai sanar da kai cewa ka kusa isa. Sai wata katariyar farfajiya ta bayyana , cike da hayaniyar maza da mata wadda matan dukansu kamar a tsirara suke .

Daga cikin dakin Magajiya Zinaru take busar taba kana maza uku da mata uku suna zaune saman carpet su ma tabar suke zuga.

" Yanzu ya ma zamu yi ne mu daukar wa Halimat lauya , ni tausayi take bani gashi dai ba wani amfani ta min a gidan nan ba , ban taba morar kudinta aka kwashe lafiya ba "cewar magiya Zinaru.

Gefensa Barde cikin amintattun ta , yana busan sigari, cikin takaici ya ce .

" Sai da na gaya miki yarinyar nan tayi karama ki bari ta kara koda shekara daya , ki kayi hakurin rainonta sai na dan lokaci zaki kasa haba Zinaru" cewar barde.

" Kai ai wannan zancen banza kake nima a shekarunta aka fara buga harka ba gashi yanzu na ci gaba ba , shegen taurin kai ne da yarinyar nan , gashi ta je fa ni a masifa , ni dai ba zan zuba ido in ga ana kisan Halima ba gaskiya" cewar Zinaru.
Nan dakin ya dau shiru dukansu suka hau lissafin mafita.

" Kawai a nemi bashin kudi koda million biyar ne domin daukan babban lauya " cewar  wata karuwar dake zaune .

" Sai dai in kune zaku shirya shiga aiki ba dare ba rana duk alhazan nan ku tabbatar kun samu kun fita dasu ku gayama sauran duk abunda zaa samu dala ba zaku ci domin hada wannan kudin " cewar Zinaru cikin bada umarni.

" Ai ko yanzu zan je in sanar musu " cewar kande , kana ta kara da fadin ai na manta jikin mu ma zai hada wannan kudin nake batun a ciyo bashi".

Numfashi Zinaru ta fesar mai zafi tana busar taba .

" Dan dakata Kande , na canza shawara  , lauya ba abunda ze mana , shi lauya Littafi ya sani , mu kuma mutane muka sani. Kada ku sake wani ya san sirrin da zan da zan yi amfani dashi ya kure, idan ta fadi dukan gida ya fadi , wannan yarinyar ba jininmu ba ce , amma tana dauke da sirrinmu , zamu fito da ita da dabarar da ta fi doka karfi".
 Kalaman Zinaru ya sa kowa fara zugar taba suna bushewa da muguwar dariya .


____________________

Hasken fitilun motar Assadiq ya haska babban get din gidan. Assadiq yana sanye da farar riga ta alfarma, gajiya bayyananniya a fuskarsa. Hamissu ya wangala get din da sauri , fuskarsa dauke da wata irin damuwa wadda ta wuce ta gaisuwa yau da kullum.
Ganin hakan ya sanya Assadiq ya rage gudun motar, ya gangara kusa da inda Hamissou yake tsaye,    
Sauke gilashin motar yayi , muryarsa a gajiye ya ce " Sannu da aiki Hamissou. Ya gidan?".

" Sannu da zuwa yallabai. Gida lafiya lau, fatan ka dawo gida lafiya".

Assadiq ya so ya tada motar ya wuce , amma ya ga Hamissou ya kasa komawa mazauninsa, sai ma kara takowa da yayi kusa da motar, yana wasa da maballan dake  hannunsa .

" Dama yallabai, alfarma nake nema gurin ka , idan ba zaka damu ba."

Assadiq gyara zamansa yayi, ya kashe wakar dake tashi a hankali cikin motar.

" Ina jin ka Hamissou. Lafiya dai ko?"

" Lafiya lau yallabai. Maganar yarinyar nan ne wadda aka kama da zargin kisan wani attajiri, kamar yarinyar yar sha biyar.  Na san kai mutum ne mai fada a ji , kuma kana da alaka da manyan lauyoyi da jami'an tsaro. Don Allah yallabai, a sa baki a maganar nan. Yarinyar nan ba ta da kowa , kuma ana kokarin murkushe ta ne ."

Zazzaro idanu Assadiq cike da tsananin mamaki, ya dade yana kallon Hamissou.

" Hamissou , har kai ka ..........

Duka duka anan zan dakata 

Mu hadu a shafi na biyu in ka ji dadin littafin nan kayi comment da abunda ya burgeka .

Domin karin bayani ko neman sani ga number ta .

*** ko +22953726162 taku har kullum kyauta daga Allah.