Chapter 21
🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 21
A gigice ta farka, dalilin saukar ruwa mai ɗan karen sanyi a jikinta, cikin fitar hayyaci ta miƙe tsaye idanunta a rufe tana ambaton Allah, ba ta yi aune ba santsin tiles ya kwashe ta. Tif! Ta sake zubewa a inda ta tashi. Faduwa mai kyau ta yi kanta ya bugu da ƙasa sosai, take zafi ya ratsa har kwanyarta.“Wayyo Allahna!” ta furta a wahalce tare da fashewa da wani irin marayan kuka, har lokacin bata gama dawowa hayyacinta, sai da ta tsinci deep husky voice ɗinsa a kanta, cike da fushi ya daka mata razananniyar tsawar da ta sanya numfashinta daukewa na hucin gadi. “Tashi munafuka!” Ya sake daka mata wata tsawar da tafi ta farko. A rikice ta kuma mikewa jikinta na rawa, zuciyarta na wani irin bugu na wuce ka'ida. A karo na santsin wajen ya kuma ɗibanta, rintse ido ta yi da karfi irin ta yi giveup, ba zato ta ji an taro ta, gaba ɗaya ta faɗa jikin mutum, samun wannan damar yasa ta ƙanƙame shi da karfi tare da cusa kanta a jirjinsa tana sakin ajiyar zuciya da sauri da sauri kamar wacce ta yi gudun ceto rai.
Wutar kansa ne ya ɗauke ɗif, wani baƙon yanayi ya ziyarce zuciya, ƙwaƙwalwa, dama ilahirin jikinsa baki ɗaya, tsigar jikinsa ya hau cirawa. Kusan sakan talatin suka kwashe a haka, kafin kamar saukar wahayi wani ɓari na zuciyarsa ta jeho masa tambaya kai tsaye “Me ka yi kenan Ahmad?” “Taimako domin Allah.” Ya furta a kan laɓɓansa yana lumshe ido saboda yadda hucin numfashinta da ke dukan kirjinsa yake yi masa tasiri, da gaske buguwar da ta yi da farko ta bashi tausayi, yana da tausayi na ban mamaki balle a kan mace, “Hakan na nufin ka bada kai makiya sun ci galaba a kan ka kenan? Wannan ba komai ba ne illah makirci irinta gogaggun matan bariki. Be wise mana, wannan ba abar tausayi ba ce” Zuciyarsa ce ta sake yi masa wannan hudubar, lokaci guda ya ji komai ya tsaya cak tamkar an yi ruwa an ɗauke, nan take ya dawo hayyacinsa, ba shiri ya ware idanu tare da fisgeta daga jikinsa ya watsar gefe. Faɗuwan ta kuma yi sai dai wannan karon Allah ya agajeta ta faɗa kan capet ɗin da ke malale a tsakiyar falon mai azabar taushi.
Sai lokacin su ka yi ido biyu, sai lokacin tasan da wa take tare, sai lokacin ta fahimci jikin wa ta faɗa. Yanayin fuskarsa kaɗai abin tsoro ne take ta ji fitsari na shirin kwace mata. “Me ya same shi, ya sauya mummunar sauyi,Wannan ba shi ba ne Babangidana bw, wannan ba shine Babangidan Shatou ba, ba zai taɓa zama shi ba har abada.” Ta furta hakan a ranta kuka na sake kwace mata.
Wani shegen kallo yake watsa mata da idanunsa dake cike da tsantsar kiyayyarta a bayyane, yayinda ya shiga takawa yana nufarta. Baya ta dinga ja daga zaune da take, a haka suka dinga tafiya har ta dangana da jikin royal cshion ɗin dake falon. “Ba... Ban gi...da.. Ka da ka cutar da ni.” Ransa ne ya kara ɓaci jin sunan da take kiransa da shi kenan ba za ta daina raina masa hankali ba, ta rantse dai sai ta yi wasan kwaikwayo da shi, to kuwa zai nuna mata karen bana shike maganin zomon bana, zai gwada mata idan ita yar yau ce shima haka. Wani shegen murmushi ya saki, kafin ya miƙa hannu ya ɗago habarta ya miƙar da ita tsaye ba tare da ya sake ta ba yace “ Da kyau hadaddiyar yar kafce, aikin ki yana tafiya da kyau successfully gaskiya kin burge ni. Yanzu dai duk ba wannan ba. Su wane ne? Nawa suka biya ki?” “Ba...ban...gida..” Ta sake faɗa a hankali tana kallon fuskarsa da ke daure tamau, yayinda hawaye ke tsere a tata fuskar. Tamkar ta watsa masa wuta haka ya ji da ta sake ambatar sunan Babangida, rintse ido ya yi da karfi ya buɗe tare da fesar da hucin takaici, ji yake kamar ya shaƙe ta har sai ta daina numfashi, a duniya rainin hankali na daya daga abinda ke saurin ɓata masa rai, wato dai yarinyar nan ba za ta yi giveup ba kenan. Jijjigata ya yi sai kuma ya hankaɗata da karfi ta faɗa kan cushion, ya dafe goshinsa yana tunanin abinda zai mata don ya huce takaici. Juyawa ya yi ya ɗan duka kanta cikin tsatsar ɓacin rai ya ce, “ Wannan shine karo na Uku da zan sake maimaita miki cewa, Ni ba Babangida ba ne, AHMAD KANGIWA nake ko kin gane.” lokaci guda ta ji Zuciyarsa ta dake duk wani tsoro da shakkarsa da take ji ya kau, cikin karaji ta ce “Karya ka ke yi kai ne, wallahi kai ne Babangida, kuma ba zan daina kiranka da Babangida ba domin da shi na sanka, mugu kawai azzalumi, kana tunanin raba Ni da budurcina da jefe rayuwata da ta iyayena a cikin garari da ka yi, za ka ci bulus ne, never wallahi ko mutuwa na yi fatawalta sai ta hana rayuwarka kwanciyar hankali.” Kauuu! Ya ɗauke ta da mari yana huci ya nunata yace, “ Wane ne ya ɗauki budurcin naki, Ni za ki yi wa ƙazafin zina, Oho sai yanzu na fahimci inda ki ka dosa, in dai haka ne to ashe ke karamar yar wasa ce” Ya ja baya yana kallonta daga sama har kasa , sai kuma ya yi murmushi ya ce, “ Ciki na yi miki ko, ɗan wata nawa ne?” ya faɗa cike da isgili, Dafe kuncinta ta yi tana jin tamkar zuciyarta na rarrabewa “Anya kuwa shi ɗin ne?” ta yi imani Babbangida ba zai taɓa marin Shatou ba. Sai dai tuna hotunan da ta gani dazu gewaye da bangon ɗakin ya rushe wannan hasashen nata da ta fara. Kamar zararriya ta mike da gudu ta nufi wajen hoton da ta gani na shi dazu tana faɗin “ Idan ba kai bane Babangida to wanene wannan?” turus ta taka burki, lokacin da idanuta ya sauka akan hoton, sabanin abin da ta gani dazu, yanzu hoton mutumin da ke gabanta ne, bana Babangida ba, hoton kusa da shi ta kalla inda wanda suke su biyu, nan ma hoton shi ne shi da familynsa. Wani hoton ta kalla nan ma haka. Bin hotunan falon ta dinga yi amma kamar almara babu ko ɗaya daga cikin hotunan da ta gani dazu ko ire irinsu a falon. Kafafunta ne ya ɗauki rawa yayi da wani irin tsoro ya kamata, sai kawai ta zube a wajen ya yanka ihu mai karar gaske tana dage da kanta da ke juya mata.
Kallonta AA ya tsaya yana yi cike da shakku, anya wannan kanta ɗaya, “ Kai ina! Ya faɗa tare da girgiza kai, da ya ɗauka yar wasa ce, amma yanzu ya gama yin ammana da cewar mahaukaciya ce. Lokaci ɗaya zuciyarsa ta yi laushi, har ya ji kamar ya fara jin tausayinta, lamarinta yana da matukar daure kai, a zahiri gaskiya ba ta yi kama da mai larurar Hausa ba amma maganganunta da aikinta sun nuna hakan, to me ke faruwa gareta, wanene Babangida mai ya aikata mata haka. Wadannan tambayoyi ne da bashi da amsar su a yanzu don haka sai ya nemi guri ya zauna, tare da zaro wayarsa ya dannawa Ussy kira. Mintuna biyu tsakani ya shigo falon, har lokacin Aysha na duke a inda take dafa da kanta tana kuka.
“Ku fita da ita mahaukaciya ce?” Ya faɗa ba tare da ya kalli Ussy. Kallonta ussy ya yi cike da mamaki yana maimaita kalmar hauka a zuciyarsa, kasa daurawa ya yi ya ce “Megida anya ba pretending take yi ba, don gudun tonuwar asirinta.” “ Bana tunanin haka, lamarinta akwai sarkakiya a ciki, ina ganin wani ne ya cutar da ita, har hakan ya yi affecting din ta sosai, ku kaita gida kawai.”
Jiki ba kwari ussy ya matsa kusa da ita, yace “Ki taso mu kai ki gida.” kamar abinda take jira kenan ta mike zaraf. Gaba ya yi ta bisa a baya tana harde hanya, AA ya zubawa bayanta ido cike da nazari, yana cin zuciyarsa na narkewa wani abu mai nauyi ya yi matsa tsaye ba tare da ya san ko mene ne ba.
Wacce ta shirya payment yanzu kafin mu gama Book 1, 800₦ ne a saka a wannan account ɗin 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, a turo shedar biya ta ***.