BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----6




Tahir kuwa kansa na ƙasa kamar bashi ba.

Alƙali ya gyara zama tare da kallon Tahir ya ce,
“Shin ka tabbatar da duk abinda ka faɗa a baya? Cewa ka aikata laifin da ake tuhumar ka dashi?”

Cikin murya mai sanyi Tahir ya ce,
“Na sani ranka shi daɗe"

shiru ya ratsa cikin kotun 

Suhail ya miƙe ya ce"my lord,ina son kotu tayi la'akari da yadda Tahir ya amsa laifin sa,ba tare da ba Shari'a wahala ba ina roƙa masa sassauci"

 Alƙali ya gyara zama tare da ɗaukar ƴan mintuna yana duba wasu takardu kafin daga ƙarshe ya ɗago kai.

“Kotu tayi la’akari da dukkan bayanan da aka gabatar gabanta"


“A bisa laifin fyade da sanadiyar mutuwar da aka same ka da shi…”

Tahir ya runtse idanun sa gam.

“An yanke maka hukuncin shekaru goma a gidan gyaran hali tare da bayar da tarar naira millon biyu ga iyayen yarinyar"

Kuka mahaifiyar yarinyar ta fashe dashi.

Alhaji Sani kuwa ya dafe ƙirji yana jin kamar zuciyarsa zata tsaya chakk wanda shigowar sa kenan kotun yaji hukuncin da aka yanke wa ɗan sa

Tahir a hankali ya ɗago jajayen idanun sa yana kallon Suhail.

Lebe ya motsa kamar mai son magana amma ya kasa 

haka Alƙali ya salllami kowa ƴan sanda suka kamo Tahir suka fito dashi zuwa cikin motar prison da sauri Alhaji sani ya ƙara gaban su hannun Tahir ya kama yana kallon sa.

a hankali ya fara magana "Tahir nine sillar duk wani abu da ya same ka,da na baka tarbiyar data dace da duk hakan bata faru Tahir ka yafe min kuka sosai yaci karfin Alhaji sani shi kansa tahir a lokacin ya kasa riƙe hawayen sa karo na farko daya zubar da hawaye tun bayan Rasuwar mahaifiyar sa ya ce"Baba nasan duk abinda kayi min kayi ne saboda da kana so na ,baba yau nayi damar da ban taɓa irin taɓa nasan Alhakin mutane ke tambaya ta , Nagode Allah daya nuna min ƙarshen tun duniya na biye wa ƙawar zuciyata babu abinda na sani a duniya sai shan giya da bin mata Ban damu da tsaya na bautawa Ubangiji na kasa bin dokokin sa Sallah bana yi sai naga dama bare sauran abinda Allah ya hallicce mu a kai Baba kamin Addu'a Allah yasa hakan ya zama sanadiyar shiriya ta.

bai kara cewa komi ba ƴan sanda suka saka shi a mota dui abinda ya faru akan idanun suhail ya tausaya wa Tahir matuƙa Sameer dake fitowa ya hango suhail tsaye hannu ya miƙa masa ya ce"congratulation Guy"

murmushi yaƙe kawai yayi kallo ɗaya zaka mishi kaga tsantsar tausayi cikin idan nun sa sameeer ya ce"wai miyasa ka nemawa Tahir sassauci "

kallo Sameeer yayi ya ce"yaron ya bani tausayi matuƙa gashi maraya,kuma ya amsa laifin sa shi ya riga ma ya yanke wa kansa duk wani daɗin duniya"

sameer ya ce"ai shi yaja wa kansa kuma duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka kaga Mallan muje"

sameer yafi kowa sanin halin suhail mutun ne mai bala'in tausai haka ya tashi tun yana yaro ga shi yana da sa  abu a ransa ya tabbatar wannan case din ya saka shi a ransa kenan gani zaiyi kamar shine sanadiyar jefa tahir a wanann yanayin.

Alhaji sani na zaune a wajen yana ta rusa kuka tamkar wani karamin yaro da kyar driver din sa ya kamashi ya sashi a mota.

yau ta kama Assabar kuma a yaune babbar Makarantar Usman bin affan dake unguwar dosa ke walimar yaye daliban ta guda 35 wanda suka yi nasarar Sauke Alqur'ani yayin da mace ɗaya ta samu damar haddace Alqur'ani gaba ɗaya Wannan ba kowa bace face Khadija Abdallah Iman diƴar babban limanin masallacin juma'a dake Tudun Wada, sannan Babban  malami ne da yayi fice wajen koyar da bayin Allah littaffan addini saukar ta samu halartar dubbanin Al'ummar mutane tare da  manyan Manyan Mutane kama daga malamai da masu faɗa a aji na cikin garin kaduna ciki kuwa hadda Alhaji munnir mahmud.

cikin ƙankanin lokaci aka fara gudanar da walimar tare da kiran yan sauka su fito suyi karatu kamar yadda aka tsara matan suka fara fitowa cikin Ankon Atamfa purple mai rashin fari sanye da jogayen hijab su farare har ƙasa inda mazan suka yi ankon farar Shadda karatu suke mai cike da birgewa inda suke fitar da duk wani harafi daki-daki cikin Qira'a mai dad'i.

Bayan sun gama aka kira Khadija Abdallah daga ɓangaren hadda itama sanye take cikin Atamfa baka mai rashin ja ta saka hijabin ta har kasa wanda ta dace da chocolate colour din ta ,ta hau kan mimbari ta fara karatun cikin suratul baƙara take ta janyo hankulan duk mutanen dake wajen jin sautin karatun ya banbanta dan sauran ɗaliban karatu take  tamkar a ƙasar laraba, Khadija ta burge kowa wajen Alhaji munnir da tun da ta fara karatun yake kallan ta sai murmushi yake a ransa ya ce ina ma diƴar sa ce ke rera Alqur'anin nan haka kuka taji yazo mata daidai ayar dake magana akan Mutuwa wato (Kulli nafsin za'ikatul ma'ut) wata malama ce ta janye ta ganin tana ƙoƙarin faduwa a wajen.

take wajen ya har gitse mutane ke ta yaba mata a wajen yayin da mahaifiyar ta dake zaune wajen da aka tanadar wa iyayen ke taya diyar tata kuka.
ɗaya daga cikin  malaman ya taso ya fara jawabi inda ya ce"kun saurari karatu Alqur'ani daga bakin Khadija Abdallah wada ta cikin nufi na Ubangiji ta samu damar haddace Alqur'ani a yau kuma tana daƴa daga cikin ɗalibai mafi hazaka a wannan Makarantar inda zamu karramata a wannan filin tare da bata kyaututtuka a wannan wajen muna fatan yara da yawa su kasance kamar Khadija a fannin neman ilimi don tun tana shekaru goma tayi saukar Alqur'ani ta farko a Wannan makarantar muna fatan Allah ya sa miki albarka a cikin karatun ki.

duk Makarantar nan  Khadija tafi kowa ladabi da biyyaya hakan yasa shugaban makarantar ya karramata tare da bata littafai wanda zata cigaba da neman ilimi dasu idan Khadija na kusa tazo ta amshi kyautar ta.

cike da nutsuwa take tafiya har ta iso wajen nan fa aka fara daukar ta hotuna yayin da take amsa

Nan da nan manyan mutanen dake wajen suka fara ba yadda da kyatuttukan su gare ta Alhaji Munnir ma ya bata kyautar kudi Naira dubu dari biyu ,wasu dubu dari a haka sai da ta haɗa kudi sama da millon guda da rabi ƙarin farko da wata daliba a makarantar ta samu kwatankwacin kyautar da Khadija ta samu
Da kyar Khadija ta gama karɓar kyaututtukan, hannunta na rawa saboda nauyin abin da aka cusa mata a lokaci guda ,ba na kuɗi kaɗai ba, har na kalaman yabo da ta samu a wajen malaman ta da idanu da suka cika wajen suna kallonta.

Malam ya ɗaga hannu alamar a yi shiru.

“Ku saurara… wannan nasara ba ta tsaya a nan ba Neman ilimi yana buƙatar tsayawa da gaskiya, da ladabi, da tsoron Allah,” ya faɗa cikin murya mai cike da natsuwa.

Wajen ya yi shiru na ɗan lokaci, sai dai ƙarar kyamarori da mutane ke amfani dasu 

Khadija ta sauka daga mimbari a hankali, tana riƙe da takardunta da kyaututtuka. A zuciyarta kuwa wani abu yake mata yawo ba farin ciki kaɗai ba har da tunanin barin makarantar da zata yi a yau.