15
by @legendspen
(15)
Ci gaba.
Babu abinda na iya yi har Sardauna ya dawo, ina zaune jigum kamar wacca aka yi wa mutuwa.
“Honey! Me ya faru na ganki so sad?”
Tashi na yi na faɗa jikinsa na fara hawaye, gaba ɗaya ya rikice yana faman tambayata.
“Honey ki faɗa min mana.”
Cikin muryar kuka na ce.
“Alhaji ne ba shi da lafiya sosai.”
“Ya salam Honey, me yake damunshi haka?”
“Nima bansaniba wallahi.”
“Wa ya faɗa miki?”
“Ra’is, kuma Yaya Radiya ta kirani ban ɗauka ba, ashe faɗamin zata yi, sai yanzu da Ra’is yazo.”
“Ki kwantar da hankali kin ji, gobe zan kai ki.”
Ya faɗa yana zaunar da ni akan kujera.
“Ki yi haƙuri kin ji, nima yanzu akwai wani abu da ya taso min.”
“Mene?”
“Big Daddy, bai kyauta min ba, ta dole sai ya haɗani da wancan yaron, ya sami duka labarin abubuwan da suke faruwa, a yanzu ya bamu gida ni da wancan yaron Turaki, ya ce dole mu koma can da iyalan mu mu zauna, gidan part biyu ne wai sabida faɗan da muke yi.”
“To ai nasani, wani abun ya sake faruwa?”
“Eyh ya ce a cikin satinan zamu koma.”
“Yanzu barin gidan nan zamu yi?”
“Eyh. Haka ya ke so kuma nan da next week.”
“To shi Turakin yana da aure ne?”
“Ina yake da aure, yana can sai lalata da ‘ya’yan mutane.”
“Lalata kuma?”
Na faɗa a tsorace.
“Eyh mn! Hon ace mutum ya yi wannan girman babu iyali ai kuwa sai dai idan lalata yake da yaran mutane, shekara talatin da ɗaya fa.”
“Talatin da ɗaya!”
Na faɗa cike da mamaki, ya gyaɗa sannan ya ce.
“To kinga kuwa.”
Ni ba zancen turakin yaban mamaki da tsoro ba, illah Sardauna, rufe idona na yi a take na tuna lokacin da na tambaye Sardauna shekarunsa, lokacin da ya zo makarantarmu. Ya ce da ni ashirin da biyar, har na ce irin mijin da nake so kenan, kuma ance shida Turaki ko kwana biyu ne a tsakaninsu ‘shin Sardauna ƙarya ya yi min a wancan lokacin? Sardauna zai iya yi min ƙarya kenan? Ko dai wasa yake min? Gaba ɗaya na ji jikina ya yi sanyi, ina so na tambayeshi amma bana buƙatar ɓacin ransa, ko ya ga kamar ban yarda da shi ba.
“Yau bazaki kwanta ba ne?”
“Uhm uhm zan kwanta mana.”
“Na yi tunanin dan Alhaji bai da lafiya ba zaki yi bacci ba, zaki zauna ki yi ta yi masa addu’a.”
Wani iri na ji a raina, gaba ɗaya a al’amurana ban iya tashi cikin dare na yi addu’a ba, idan ka ga na yi addu’a to bayan kowacce sallar farilla ce, tabbas mahaifina yana buƙatar hakan daga gareni.
“Eyh zan jira ƙarfe ɗaya na yi sallah.”
Dawowa ya yi ya zauna daga miƙewar da ya yi sannan ya ce.
“Dagaske?”
“Eyh dagaske.”
“To ai yanzi akwai tazara sosai zuwa ƙarfe ɗaya, ki tashi mu shiga ciki idan kin yi bacci ni sai na tashi ki ƙarfe ɗayan.”
Ta shi na yi nabi bayanshi zuwa ɗakin, ko a ɗakin ma na daɗe a zaune har sai da ya ƙara cewa na kwanta zai tashe ni sannan na kwanta.
Ƙarar alam ce ta tashi ni, wanda na saita ƙarfe biyar daidai na asuba. ‘Sardauna ya manta.’ Na faɗa a raina ina saukowa, a gurguje na shiga banɗaki na ɗaura alwala na fara yin nafila kafin na gabatar da asuba, cikin hanzari na haɗa masa abin kari sabida ina son na fita da wuri, duk hankalina yana wajen Alhaji gaba ɗaya, ji nake a jikina kamar ni ce sillar kwanciyarshi wannan rashin lafiyar.
Haka Sardauna ya yi ta jan lokaci, ba shi ya fito ba sai sha biyu da kwata, kuma a hakan ma bai yi breakfast, har ƙwalla sai da na yi.
“Am sorry Hon, na ɗan duba wani abu ne shi ya sa na makara, yanzu ma ban ƙarasa ba amma ki zubamin breakfast ɗin na yi ke sai kije ki ƙarasa mayar da takardun kafin na kammala.”
Jikina duk babu daɗi, haka na je kan dinning na zuba masa farfesun naman rago da na yi sai kuma doya da miyar kaza da na dafa, sabida ina son tafarwa da Alhaji kuma nasan zaifi son dafaffiyar doya maimakon soyayyiya. Ina zuba masa ma nufi ɗakin, takardune duk ya zubar dasu a ƙasa, haka na shiga haɗasu ina zuba su a jakar da suke, ina yi ina ɗan duba wasu. Kwatsam idona ya faɗa kan wata takardar CV ɗinsa, date of birth na fara cikin karo da shi 11/08/1994.
‘Ya tabbata dai Sardauna ba shekarunsa 25 ba?.’ Abinda na fara tambayar kaina kenan. ‘Amma me ya sa ya ɓoyemin, tabbas ƙarancin shekarunsa suna daga cikin abubuwan da suka sa na far son Sardauna.’ Na sake faɗa a raina, ƙwalla na ji ta fara zurara daga idona. ‘Ashe Sardauna zai iya yi min ƙarya? Kai ba zai yi min ba sai dai idan a lokacin ni ce na ji ba daidai ba, kunnuwana sun yaudareni.’
Haka na kwashe takardun ina ta saƙe saƙe a raina, ba mune mu ka bar gidan ba sai ƙarfe ɗaya da kwata, ni da na shirya tun tara. Kallon plast ɗin hannuna Sardauna ya yi sannan ya ce.
“Na mene wannan?”
“Ragowar doyar da na dafa ce, ban iya ci ba duk bakina ba daɗi, shi nake son tafiya ko Alhaji zai iya ci.”
“Shine kika bani kaɗan ni ko?”
“A’a ba haka ba ne?.”
“Ke kika sani.”
Ya faɗa yana shigewa motar, nima na shiga har mukaje gida baice dani ko ƙala ba, haka bai ce dani na gaida me jiki ba, amma na yi masa uziri ko ya yi mantuwa ko idan yazo ɗaukana zai shigo. Da sallama na shiga cikin gidan, mutanen gidanmu suna falon Hajiya duk sun yi zugum zugum, hankali a tashe na shiga ɗakin. Yanayin da naga Alhaji ya yi matuƙar tsorata ni, yana kwance kamar marar numfashi, baya ko motsi.
Jikin Hajiya na faɗa ina faɗin.
“Yana ganshi a haka Hajiya?”
Hajiya kuka take dannewa, ba ta iya ba ni amsa ba sai Yaya Radiya ce ta ce da ni.
“Haka kawai muka ga jikin nasa ya yi?”
Kusa da shi na matsa ina faɗin.
“Alhaji.. alhaji.”
Yana kallona da ido amma bazai iya magana ba, Ra’is ya ce da ni.
“Ba zai iya magana ba fa.”
“Ina Yaya Ridwan baku tafi asibiti ba?.”
“Nana ki nutsu dan Allah.”
Yaya Rumaisa ta faɗa, kowa fuska cike da hawaye.
Tashi na yi na janyo plast ɗin da na zo da shi.
“Alhaji dan Allah ka ci doyar nan.”
“Zo ki ba shi.”
Ra’is ya faɗa, na matso kusa da shi na buɗe plast ɗin na ɗauki doyar na mammatse ta nasa masa a baki, a hankali ya cinye ta na ƙara samasa wata, sannan na ɗauki farfesun zan ba shi Yaya Rumaisa ta ce.
“Kar ki ba shi akwai maggi, ki ba shi iya doyar.”
Daidai lokacin Yaya Ridwan ya shigo ɗakin.
“Ga motar an samo.”
A raina na ce. ‘Yanzu mota ce ta hana akai mahaifina asibiti a lokacin da yakamata? Mene amfanin motocin da suke gidana? Ina ranar motar da Sarduna ya bani wacca ba na ko amfani da ita.”
“Rid..wan.”
Alhaji ya faɗa a hankali, da sauri duka muka kalleshi, ya yi masa alamu yazo da hannu, sannan ya yi yawa Yaya Radiya da Yaya Rumaisa, ni da Ra’is daman muna kusa da shi, ɗai ɗai yake kallonmu sai da ya gama kallonmu duka sannan ya ce.
“Kaine Babba, kaine babansu Ridwan… ba ni na baka wannan nauyin ba Allah ne ya baka, ina mai rashim jindaɗin cewar zan tafi na barka da nauyi a kanka, Ridwan ka yafe min.”
Gaba ɗaya jikin mu ya yi sanyi kowa ƙwalla yake matsewa.
“Ku yi haƙuri kar ku yi kuka, ku haɗe kan ku ka zama tsintsiya ɗaya, ga mahaifiyarku nan, a tsahon rayuwata da ita babu komai sai alheri da kyautatawa, ku ci gaba da yi mata biyayya har ƙarshen numfashinku.”
Sannan ya nuna ni, ni da Ra’is.
“Sune ƙanana, ku yi musu afuwa, ku dinga haƙuri da su, mussaman Nana.”
Ya nuna ni, sannan ya ce.
“Tana sonku, ku yi mata afuwa kar ku taɓa fushi da ita, karku watsar da al’amuranta ƙaramar ku ce, ba ta da wani gata sai na Allah sai na ku.”
“Alhaji ka taso a kai ka asibitin dan Allah.”
Hajiya ta faɗa tana kuka, ya girgiza kai yana sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.
“Na gode, na gode miki. Allah Na gode maka da rayuwa da ka bani, Allah ga Amanar ‘ya’yana da matata, Allah ga Amanarsu nan, Allah ka kula su, ka zame musu gata a duk inda suke ka kare su Ya Allah.”
Gaba ɗaya ɗakin ya yi shiru baka jin komai sai shasheƙar kuka, ya sa hannu ya nuna Yaya Radiya ta matso kusa da shi.
“Ki yi haƙuri, ki miƙa al’amuranki ga Allah Yana gani, kuma zai kawo miki mafita, ke ce babba Allah ne gatanku, ki haɗe kanku dan Allah, karki bari wani abu ya tarwatsa ku.”
“Alhaji ka yi ƙoƙari akanmu tun haihuwar mu har zuwa yau, ka cika mahaifini na gari, ka tsaya akanmu ka kula da mu, mun gode maka alhaji mun gode maka, ko a yanzu rayuwa ta tsaya Alhaji ka cika gwarzon uba, Alhaji mun gode maka.”
Yaya Radiya ta faɗa tana fitar da wani irin kuka mai taɓa zuciya, ya yi murmushi sannan ya nuna Yaya Rumaisa, itama ta matso kusa.
“Ki dinga dannar zuciyarki, ki dinga haƙuri da ‘yan uwanki dan Allah, ki yi wa mijinki biyayya, Allah Ya yi miki albarka ya haɗa kawunanku, ku ya fe min dan Allah.”
Cikin kuka itama ta fara magana.
“Alhaji muna sonka, mun kuma gode maka da dukkan abinda ka yi mana, Alherin Allah Ya tabbata a gareka Alhaji, Mun gode mun gode.”
Ya matse hannun Yaya Ridwan dake cikin nasa, sannan ya ce.
“Haƙuri! Haƙuri! Haƙuri dan Allah, Ridwan ban so na barka maka nauyin akanka ba, amma nasani Allah Ya na gani, kuma zai shiga al’amuranka zai buɗa maka yabaka ikon kula da ‘yan uwanka, a ko da yaushe albarka ta tana tare da ku.”
Yaya Ridwan kuka kawai yake bai iya cewa komai ba, Alhaji ya kalleni ya ce.
“Nana! Ki kasance mai karɓar ƙaddara kowace iri, Nana rayuwarki tana cike da ƙalubale da yawa, Nana karki yi wa Allah butulci, karki koka, ki yi haƙuri ki sa a ranki komai zai wuce Nana, komai da komai zai zama labari.”
Rungume shi na yi na ci gaba da rera kukan da nake yi.
“Ka kasance mai biyayya, mai kyautatawa ‘yan uwa, kasa a ranka Allah ne gatanKa sune gatanka, Ra’is ka yi haƙuri a duk irin rayuwar da ka tsinci kanka, Allah yana gani ka ji.”
Shima Ra’is ɗin kuka ya fashe da shi, kowa kuka.
“Na gode miki, Na gode miki Allah Ya yi miki albarka, ya baki haƙurin rashi.”
Hajiya dai ba ta iya cewa komai ba sai faman ƙwalla da take.
“Allah ko a yanzu Alhamdulillah, Allah na gode maka, na ƙara gode maka, zan kasance mai gode maka Ya Allah, Tammat bi hamdillah Allah.”
Daidai lokacin Isah Nadabi ya shigo ɗakin, ganin dukkanmu muna kuka ya sa shi cewa.
“Me ya faru dan Allah, Ridwan ya baku tafi asibitin ba?”
Cikin Kuka Yaya Ridwan ya ce.
“Ya ce kar aje asibitin.”
Matsowa ya yi ya kama hannun Alhaji sannan ya ce.
“Alhaji akai ka asibiti dan Allah.”
“A’ah Isah, tsaya ka ji.”
Alhaji ya faɗa murya a wahalce, ya riƙe hannunsa sannan ya ce.
“Allah Yasa ka maka da mafificin alheri, ubangiji ya raya maka zuri’arka, Allah Ya dauwamarma da suttura, ɗawainiyar da ka yi akaina ubangiji ya mayar maKa, na gode.”
“Alhaji ka bari dan Allah, Ridwan kama shi dan Allah.”
“A’ah! A’ah! Dan Allah ku barni.”
“Me ya sa, Alhaji?”
“Ka barni, na ƙarasa rayuwata a cikin iyalina.”
Bai kai ga yi masa magana ba tari ta sarƙeshi, yanayi yana haɗawa da kalmar shahada. Gaba ɗaya muka zagaye shi muna kuka, a hankali har muka ji ya daina kakarin.
Gaba ɗaya duniyar ta tsaya mana cak, Isah Nadabo ne ya fara ɗaga hannuna yana faɗin.
“Alhaji Alhaji, innullahi wa’inna illahir raji’un.”
Ina daga zaune na ji wani irin jiri ya ɗebeni, aikuwa na kifi ƙasa kif.
Legendspen
***.