SARTSE COMPLETE

16

by @legendspen

 (16) Sama sama nake jin hayaniyar mutane, a hankali na fara buɗe idona, dishi dishi nake gani kafin idon ya buɗe tarwar. A take komai da ya faru ya shiga dawomin kamar an haskan majigi. 

"Alhaji!" 

Na faɗa ina koƙarin ta shi, hannuna na ji an riƙe tare da faɗin. 

"Nana! Nustu ki nutsu." 

Muryar Sardauna ce, na ɗaga ido na kalleshi tare da faɗin. 

"Alhaji!" 

Ya riƙe ni tare da girgizamin kai, sannan ya ce. 

"Alhaji is no more Nana, Alhaji ya tafi ki yi haƙuri."

Wani irin kuka na saki me raɗaɗi da taɓa zuciya tare da faɗin. 

"Innullahi wainna illahir raji'un, na rasa Alhaji na rasa gata na rasa komai, dan Allah ka mayar dani gida ka mayar da ni." 

"A'a Nana ba zaki koma yanzu ba, sai kin warke." 

Miƙewa na fara ƙoƙarin yi tare da faɗin. 

"Na warke Sardauna ka barni na tafi, na je na ga mahaifina, dan Allah." 

Kallon agogon hannunsa ya yi sannan ya ce. 

"Ƙarfe uku da rabi za ayi jana izarsa, kuma a yanzu uku da arba'in Nana, an kaishi gidansa na gaskiyya, ki yi haƙuri ki ɗauki rashi, ki karɓi ƙaddara Nana, ni zan zame miki gatan da kika rasa Nana, dan Allah." 

Kuka na ci gaba da yi, ni kaɗai nasan irin  yanayin da nake ji, ina jin kamar na fitar da zuciyata daga cikin jikina, ina jin zafi kamar an watsamin gishiri a jikin ciwo, raɗaɗi kawai nake ji da wani irin zafi yana ratsani, na gaji na rasa me zanyi, ba kuka ba, ba ihu ba, na gaji da rayuwar ma, na gaji. 

"Nana ki yi haƙuri dan Allah, ki yi haƙuri kinji." Ya faɗa yana jawoni jikinsa, na kwanta ina kuka mai tsuma zuciya, shi kuma yana shafa bayana. A hankali na fara sauke ajiyar zuciya. 

"Nana! Kina jina, Allah Yana jarabtar bayinsa ta kowanne fanni, Allah Ya jarabce ki da rasa mahaifi a yanzu, amma kuma ya yi miki sakayya da ni Nana, Nana ina son ki ɗauke ni a matsayin duk wani abu da kika rasa Nana, zan zame ki bango, zan zame miki inuwa Nana." 

Haka Sardauna ya yi ta lallaɓani da zafafan kalamai masu saukar da nutsuwa, amma gaba ɗaya a hankalina baya tare da ni, burina na ga 'yan uwana, ko zan tabbatar cewa Alhaji bai mutu ba, dan tabbas na hana zuciyata yarda da ko kalma ɗaya kan faɗin rasuwar Alhaji. Ba mu muka bar aaibiti ba sai bayan biyar, hannu maƙale da kanula sabida ba a gamin allura ba, har da ƙarin ruwa. Jama'ar da na gani a kwanar layinmu suka dawo min da kuka na sabo, so ake a tabbatar min na rasa mahaifina, na rasa Alhaji ina zan sa rayuwata. 

Yanayin fakin ɗin motar shi na fito, ban ko tsaya ba duk kiran sunana da yake yi. Da gudu na shiga cikin gida idon kowa ya yo kaina. 

"Wayyo! Wayyo!." 

Na ji muryar Hajja, wani takaici ya cikani na fara tafiya zuwa ɗakin Hajiya sai dai kawai na ji wani jirin na ɗibana, kan ka ce me na sake zuɓewa a ƙasa sumammiya. Sanyi da na ji a fuskata ne ya sa na buɗe idona, Maman walid wata maƙwafciyar mu na gani a kaina tana shafan ruwan, can na jiyo muryar Sardauna yana faɗin. 

"Ba yadda likitan baiyi ba, amma ta dage sai na kawo ta." 

"Da ba kawo ta ba, yanzu gashi ta sake zubewa." 

Banma tantance me muryar ba na ce da Maman Walid. 

"ina Hajiya?

"Tana ciki Nana." 

"Kamani dan Allah." 

Na faɗa ina ƙoƙarin tashi, ta kamani ta shiga dani ciki, anan na tarar da har da mutane da yawa a  cikin ɗakin, har da Mamansu Amina Aminu da Fauziya. 

"Nan da zafi, a fita da ita wancan ɗakin ta sha iska mana." 

Wata maƙwafciyarmu ta faɗa, Maman Walid ta sake riƙeni zuwa ɗakin da yake seat room, ɗakin yana da faɗi kuma ba komai a ciki carpet shi ya sa yake da iska.  A cikin ɗakin na ga mutane da yawa har da ƙwayena da su Yaya Radiya kowa ya yi zungwi zungwi, haka nima na zauna a raina ina ta nanata kalmar. 

'Alhaji is no more.' Da Sardauna ya faɗa min, haka na zauna har dare ban nemi Sardauna ba, sai wajen tara sannan ya sa aka kirani, ko da na je ban wani saki baki na yi mai magana ba, shima kuma bai daɗe ba ya ce da ni zai tafi sai gobe zai zo. 

Haka na koma ciki, jigun jigun ba magana ba ci ba sha, sai washe gari ne ma nasami damar shan shayi da safe, Sardauna da sassafe ya zo har da wasu daga 'yan uwansa wayanda daman jiya sun zo su Big Daddy ma duk ance da su aka yi sallar Alhaji shine dai babu shi, sabida zuwansa kenan ya gani a kwance ya ɗaukeni zuwa asibiti, da yamma su Hajiyarsa da su lubna suka zo har da su Sister Seemah. 

Ranar kwana uku ya ƙara tabbatar mana da cewa Alhaji ya tafi babu dawowa, haka muka yi haƙuri muka amshi rashin Alhaji. Washe gari ranar kwana na huɗu kowa ya watse gida daga mu sai mu sai 'yan uwan Hajiya da suka zo, sai Anty Adiza matar Isa Nadabo da bata koma ba tun da ta zo, a ranar muka ƙara tabbatar da rashi musamman da muka kasance muka ɗai, ranar kwana na shida Turaki ya zo ya yi min gaisuwa, baya ƙasar sai jiya da daddare ya dawo, ya yi min gaisuwa sosai da sosai, da zai tafi ya ce na haɗashi  da 'yan uwana maza, sanin halin Yaya Ridwan yasa ban ma haɗasu ba sai Ra'is na nema, bayan sun gaisa ya yi masa gaisuwa ya karɓi lambar Ra'is sannan ya bawa Ra'is ta shi, ya kuma sanar da shi akan cewa bayan anyi kwana bakwa ya tuntuɓeshi. 

Ranar bakwai aka sake zaman addu'a, da dare kowa ya watse aka sake barin mu daga mu sai mu sai Anty Adiza da take kamar 'yar gida, 'yan uwan Hajiya ma sun tafi, su Hajja kam tun ranar da aka yi rasuwa suka tafi gida akan cewa suma zasuyi nasu zaman makokin acan, bayan sun jidi kayan abinci a shago tun da ga nan Isa Nadabo ya karɓe mukkullin shagon. 

Ranar bakwai Sardauna ya tambayeni yaushe zan dawo na ce da shi sai na tambayi Hajiya, bai tankan ba ya tafi na koma cikin gidan, a zuwa yanzu mun karɓi rashin Alhaji, mun ci gaba da wasu abubuwan har magana da cin abinci, mu kan ɗan zauna mu tattauna wasu abubuwan. 

"Yaya, ɗazu mutumin nan ya kirani da kansa."

Ra'is ya faɗa, na kalleshi na ce. 

"Wane mutumi?" 

"Wanda kika haɗani da shi ranar nan." 

"Aouho, me ya ce da kai?"

"Waye ne?" 

Hajiya ta tambaya. 

"Wani ɗan uwan Sardauna ne." 

"Me ya ce ma?" 

Yaya Radiya ta tambayeshi, sai sa ya gyara zama sannan ya ce. 

“Da farko ya ce dani a wane aji nake, na ce da shi yanzu na shiga level 1 a FUD Sai ya tambayeni sauran fa, na ce masa Yaya Radiya tana shekara ra biyu a Health, sai Yaya Rumaisa da za ta gama, har ya tambayeni wace babba na ce Yaya Radiya, na ce ai ita ba ta fara karatun ba sai bayan aurenta ya mutu, sannan na ce da shi Yaya Ridwan ya shiga 400 level a FUD sai ya tambayeni Reg ɗina nawa nw na faɗa masa da na Yaya Radiya da na Yaya Ridwan to yanzu duk ya yi budget kuɗin har kowa ya kammala wai zai kama miliyan ɗaya da duby ɗari biyu, sai ya ce ba tura mai acc zamana anan na tura mai na Yaya Radiya, yanzu ya tura min recipt ya sa miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar, sannan ya ce duk wani abu na karatu ko nawa ko na Yaya Radiya ko Yaya Ridwan a sanar da shi in sha Allah.” 

Ba ƙaramin mamakin jin abinda Turaki ya yi na yi ba, cike da mamaki na ce. 

“Shi Turakin?” 

“Shi dai wanda kika haɗani da shi.” 

“Mene alaƙarsu da mijinki?” 

Hajiya ta tambaya. 

“Kamar ɗan wa da ƙani suke, amma dai gaskiyya Hajiya a iya sani na basa mutunci da Sardauna, hasali ma abokan faɗan ne basa ga maciji kuma nasan Sardauna bai san maganar ba.” 

“Kuma kika faɗa masa wallahi Nana sai ranki ya ɓaci.” 

Yaya Radiya ta faɗa, sannan ta ce. 

“Wannan mijin naki bai da hali, shi kaɗaine bai sallaci Alhaji ba.”

“To ba suna asibiti ba ke kuma.” 

Hajiya ta faɗa. 

“Haba Hajiya, ƙarfe biyar fa aka yi sallar Alhaji kuma ya sani, ina ganin ko da yana kaita zai iya dawowa.” 

“Ƙarfe biyar kuma?” 

Na faɗa a fili, a raina kuma ina tuna lokacin da Sardauna ya ce da ni ƙarfe huɗu da rabi za ayi, kuma yanzu huɗu da arba’in. 

“Eyh mn biyar aka yi wa Alhaji Sallah, kowa ya sani wani abun ne?” 

Yaya Radiya ta tambayeni, na girgiza kai sannan na ce.

“A’a ba komai, kawai gani nake babu rabom ganawarmu, amma da na fito lokacin da na farka ai da zan same shi.” 

“Zaki samu mana, ina Dutse clinic ina gidan nan ko minti biyar ba zaku yi ba.” 

A raina na ce me ya sa Sardauna yake son fara yi min ƙarya? Mutuwar mahaifina ce ta goge damuwar ƙaryar shekarun da ya yi mini, ga shi kuma yanzu ya sake min wata, ya san mene ganawa da mahaifi kuwa, anya ya sani? 

“Yanzu ya za ayi da wannan kuɗin?”

Muryar Yaya Radiya ta katseni, sai na ji Hajiya na cewa. 

“Idan makarantar zasu yarda kowa aje a biya nasa gaba ɗaya kar ya kammala, idan kuma basu amince ba za a iya kaisu banki a ajiye idan lokacin biyan ya yi sai a dinga ɗauka ana yi.”

Daga haka aka yanke shawara, ni dai an barni da tunani kala biyu a raina, yaushe Sardauna ya fara yi min ƙarya ko me ya sa ya fara? 

Washe gari na shirya komawa gida ni da Yaya Rumaisa, bayan Hajiya da Yaya Radiya sun yi mana faɗa sosai, kuma an gargaɗe ni akan kar na sake na sanar da Sardauna abinda Turaki ya yi tin da na ce ba sa shiri, da suna shiri ne ma za a sa shi ya yi masa godiya. 

Ko da na kira Sardauna na ce da shi yazo ya ɗaukeni sai ya ce da ni yana aiki na tawo kawai, haka na sami mashin na hau har gida. Gidan gaba ɗaya ya yi ƙura ya yi datti, ba wani zauna na ba na hau gyaran gida, ina cikin yi Sardauna ya dawo. Bai nuna wani farin ciki da dawowa ta ba ko kuma irin alamun ya yi kewata ba, sai ma sanar da ni da ya yi a cikin satin nan zamu koma sabon gidanmu dake Takur Site C wanda yanzu muke a A, ganin haka ya sa na dakatar da wasu ayyukan sabida wasu abubuwan duk kwashe su zamuyi, Sardauna bai duba halin rashi da nake ciki ba, haka ya yi ta fama, sannan kuma ya ƙara matsamin akan shan magunguna wai akwai abu da yake shirin faruwa. 

Ranar juma’a da yamma muka ta shi daga gidanmu na Takur Site A muka koma Takur site C, babban gidane mai ɓangare biyu, kowanne ɓangare ɗaya yafi gidanmu na site A, namu ne a hannun hagu na Turaki a hannun dama, muna shiga na ce da Sardauna. 

“Wai to shi Turaki shi da wa zai zauna? 

“Yaran mutane zai ci gaba kawowa yana abinda ya saba da su.” 

Ada ina yarda haka Turaki yake, amma yanzu kam bana yarda kwata kwata. Gidan ya yi kyau ya tsaru sosai da sosai, komai sabo ne a cikin gidan, kowanne ɓangare sai ya ɗauki mata uku a wadace.  Abubuwan da muka tawo dasu basu da yawa, daga abin gawayi sai kayana da wasu kayan kicin ɗin. 

Ranar da muka koma da wani irin ciwon ciki na kwana, gaba ɗaya cikina ya wani irin murɗawa ta wajen marata, na sha matuƙar azaba har sai da jini ya fita daga jikina, Sardauna ya kaini asibiti wajen Dr Ɗan Adala, tambayar farko da ya yi min sau nawa nake amafani da magunguna, na ce da shi har sau biyar a wata na yi. A take ya ce na dakatar da shan maganin ba lallai ya yi wa mahaifata aiki ba, za a duban wani maganin nan gaba ko daga Turai ne sai akawo min, daga nan muka dawo gida. 

“Nana, ki daina damuwa da rashin haihuwar nan, gaba ɗaya ba mu shekara biyu da aure ba, wasu su kan shekara goma da aure ba haihuwa, dan haka ki daina damun kanki kin ji dan Allah, ke na ki so Nana, ba wai Baby daga jikinki ba, dudu nawa kike, Nana ko kinsan bana so tsufa. Nana girma bazai taɓa yi miki kyau ba.” 

Legendspen
***