TURMIN DANYA

2

by @hilfat

*WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
     *(WOW)*


*TURMIN DANYA*


         *NA*

*FATIMA UMAR KAS*
       _HILFAT_


(2)

Yana zaune kan wata kujera ya ɗaura kan shi saman kujerar, hannuwansa ma na kan saman kujerar, a lumshe idanunsa suke da za ka zaci bacci yake yi, sai ka lura da girgiza ƙafar da yake yi sannan za ka tabbatar idanunsa biyu. Ingarman namiji mai ƙirar sadaukanta, a ƙalla zai yi shekaru talatin da takwas. Yana da ɗan  haske ba sosai ba, leɓensa baƙiƙirin a buɗe, sumar kan sa duk ta cukurkuɗe kamar sheƙar angulu.

    Yaran da ke gabansa ne suka kuma gyara tsayuwa kawunansu a ƙasa, domin sun gaji da tsayawar ga shi ba su da damar tafiya sai lokacin da ya ga dama don kan shi, domin a kodayaushe umarninsa kawai suke bi.
 A hankali ya buɗe idanun nasa da suka yi fici-fici kuma sun yi  ja ya sauke akan su. Sai kuma ya buɗe kwalin sigari ya  zari ɗaya ya kunnata ya fara zuƙa yana fesar da hayaƙin. Sai da ya yi mata zuƙa biyar sannan ya yar a ƙasa ya bi da ƙafarsa da wani ƙaton takalmi ke ɗaure jikinta ya murje sigarin. Kamar wanda baya son magana ya fara faɗin "Kuna nufin har yanzu ba su kawo kuɗin fansar yaran nan ba? Me suke jira ne? Ko an faɗa musu muna da lokacin ɓatawa ne?"

    "Ai kawai sun raina mana hankali ne Gadanga, kawai a aika yaran barzahu a aika musu da gawarsu tunda hakan suka zaɓa." Cewar Goje yana wani ciccijewa irin ta riƙaƙƙun ƴan dama. "Ai ni da an bi ta tawa tun suna kwana uku za mu gama da su, tunda iyayen nada kuɗin fansar tasu amma kuɗin suka fi so akan rayukansu."  Cewar mai yagi yana huci.

   Shiru ya kuma yi kan shi a ƙasa, ya ɗau aƙalla minti goma kafin ya ɗago idanunsa a kan su ya ce "Ku ƙara basu lokaci daga nan zuwa gobe, a yau za mu matsa musu lamba har muryoyin yaran ku tura musu da su ku kuma jaddada musu za mu kashe su nan da gobe idan ba su biya kuɗin da muka yanka ba."

    "An gama ƙusar yaƙi." Goje ya faɗa "Za ku iya tafiya," Ya ce kamar baya so ya koma yadda yake da farko ido lumshe yana girgiza ƙafa. Suna juyawa da niyyar fita wani matashi ya shigo ɗakin da sallama. Da ganin shi shi ma irin ƴan iskan unguwar nan ne, duba da shigarsa da kuma askin kansa, ga leɓensa da ya yi baƙiƙirin."

    "Babba ina gaisuwa" Hannu kawai ya ɗaga masa alamun amsawa "Abokan harƙalla sannunku" Ya ce da su "Yawwa ɗan uwa, akwai wani labari ne?" Maiyagi ya ce da shi. "Zazzafan labari ma kuwa, domin wannan karon za a samu gwagwgwaɓar riba idan komai ya kammala cikin sa'a." "Yi gaggawar sanar da mu, kana iya zama" Goje ya faɗa. Sai da ya zauna sosai kafin ya fara faɗin. "Akwai wata yarinya da na samo muku, budurwa ce don baza ta haura shekara ashirin da biyar ba. Mahaifinta nada kuɗi sosai don an ce shi kan sa bai san nawa ya mallaka ba, sunansa Alhaji Tahir Mai nasara. A nan bayan layinmu suke, mahaifin yarinyar yana ƙaunarta sosai domin gata iya gata yana mata ba ta nemi komai ta rasa ba. Duk da tana da ɗanuwa su biyu ne ƴaƴan nasa amma idan aka yi amfani da ita za a fi tatsar shi yadda ya kamata. Yanzu haka yana gari komai sai ya fi tafiya daidai."

    "Ina ne unguwar, ka ba mu cikakken adireshin." Cewar goje. "To kamar yadda na ce a bayan gidanmu ne, zan muku cikakken kwatance na tura muku kamar yaddaaka saba. Yarinyar ai tana zuwa aiki saboda ƴar jarida ce."

  "Ƴar jarida?" Sai lokacin ya yi magana yana buɗe idonsa. "Eh tana aiki a wani gidan jarida kuma na san ranakun da take fita da lokacin da take dawowa. Sannan a shawarce idan kun tashi ku nemi manyan kuɗaɗe domin ina da tabbacin ko nawa kuka ce mahaifinta zai ba ku."

   "Shike nan, aikinka na kyau ɗan uwa, ka je za mu yi magana, abu na gaba ka kuma  lura sosai fa haɗi da takatsantsan matsayinka na informer ɗin mu kar ka bar wata ƙofa da za a gano ka."

   "Ai ba zan taɓa bari a gano ni ba, ko ka manta inkiyar tawa? Dila fa ake ce mini, dila kuwa da wayo aka san shi, na bar ku lafiya, ina fata kasona ya zama  na musamman ni ma." "Ba ka da matsala" "To godiya nake. Daga nan ya musu sallama ya fice.

    Alhaji Ubale Lamiɗo na zaune a tanƙamemen ofishinsa yana cike wasu takaddu, mutum ne mai jiki da tsayi zai iya ba wa shekaru hamsin baya. Wayarsa ce ta fara ruri, kai kallonsa kan wayar ya yi, sai ya tsaida idanunsa akan wayar, ganin sunan da ke yawo jikin screen ɗin ne ya saka ya ajiye aikin da yake yi ya ɗauki wayar ya kanga ta a kunnensa. "Aliyu ya ake ciki?" Bayan ya ɗaga wayar. Ba a jin me ake cewa daga can ɓangaren sai ya kuma cewa "Ok to indai kayan aiki ne ba ku da matsala da su, za a kawo muku nan da kwana biyu, ku cigaba da lura. yawwa to" Daga nan ya kashe wayar.

  Sai kuma ya lalubo wata lambar ya danna kira, ana ɗagawa ya ce "Kayan hannun yaran nan fa sun yi ƙasa, ya ake ciki da waɗanda aka shigo da su ɗin nan an samu wucewa kuwa?" Ya yi shiru yana jin me ake cewa, sai ya kuma faɗin "Yawwa ka ƙoƙarta don Allah ba na so a samu matsala, kuma kar sunana ya fito. To shike nan sai na jika." Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar ya cigaba da aikin da yake yi bayan ya gyara zaman glass ɗinsa.

   Misalin ƙarfe huɗu na yamma ya fito daga ɗakin nasa bayan ya datse shi, cikin falon ya shiga, nan ya tarar da Hajiya Iyami a zaune tana waya, sai da ya jira ta gama kafin ya karkace kai "To Mamy Allah ya mana fitowa." 
"To Nura Allah ya tsare, don Allah kar ka jima fa ka dawo da wuri."
"Ke ma dai Mamy da wani zance, ni fa na ce miki Allah ya sanya alkairi kawai zan yi na dawo, shi ma don kar ya ce ban je ba ne kuma na masa alƙawari shi kuwa kin san kaya ne."

  "To na ji sarkin zuba, ka fara magana kamar kanyar da ba ta nuna ba." Yana shirin magana Nuratu ta yi sallama ta shigo falon, a kujera ta zube  tana cire ɗankwalinta ta ajiye kan kujera "Sannu da gida  Mamy" Tace a gajiye. "Yawwa Nuratu an dawo ya aikin."
"Alhamdulillah kin gan ni nan na dawo liƙis." Ta ƙarasa da lumshe ido

   "Jiki duk gajiya" Suka tsinci muryarshi ya faɗa, sai kuma ya zuge jakar hannunsa ya cire hodar madubi, soson hodar ya ɗauka yana ƙara goge fuskarsa. "Yaya sai ina kuma?" Ta tambaya "Ina ruwanki, ni fa ba na son shishshigi da ƙwala kai a faranti."
"Allah ya ba ka haƙuri daga tambaya?"
"Riƙe haƙurin ki zai yi miki amfani watarana."
"Wai walima aka gayyace shi shi ne zai je?" Mamyn nasu ta bata amsa "Mamy da yamman nan?"
"Ina ruwan ki munafiuka?" Ya ce yana kai mata ranƙwashi mai kyau a ka da zoben hannunsa.

   "Wayyo Allah kaina" Ta faɗa da ƙarfi tana dafe kan, tuni idanunta ya tara ƙwalla don sosai ranƙwashin ya shige ta.
"Ka fa kiyaye ni Nura, sai ka fasa mata kai da waɗannan ƙwandala-ƙwandalan zobunan da suke hannunka, ka fita idona na rufe wallahi idan ba haka ba yanzun nan na hana fitar "
"Haba Mamyna ƴar baiwa mai farar aniya, kar mu yi haka da ke mana, yarinyar ce take shiga mini hanci da ƙudundune shiyasa nake fato ta. Uhmmm kin ga tafiyata na bar ku lafiya" Ya duƙa a gabanta kamar mai ruku'u cike da gwalangwaso, sai kuma ya juya zai fice.

   "Wai ba na hana ka fita da ɗankwalin nan ba? Dawo ka cire shi."
"Kai Aunty, haba Auntyna, kin hana ni ɗaura zani firrr duk yadda nake ƙulafici na haƙura, kuma shi ma kallabin sai a hana ni ɗaurawa haka zan ke yawo tsirara-tsirara. Duk ƙawayen nawa fa da cikakkiyar suturarsu suke yawo kin san ita mace duk inda take da rufe jiki aka san t....!

  "Jeka jeka don Allah, na ji tafi, yau kuma Aunty na koma, Allah ya shirya ka." Ta ce cike da takaici
"Amin Mamy godiya nake." Ya juya ya fice yana juya mazaunai, ajiyar zuciya Mamyn ta sauke ta raka bayansa da kallo tana girgiza kai.

     Yana fita ya nufi parking space, amma bai ga direban nashi ba. "Kai ina Yawale yake ne?" Ya tambayi maigadi "Ya zagaya banɗaki ranka ya daɗe." Cewar maigadin. Wani kallo ya watsa masa yana ƙanƙance idanu, "Ban hana ka mayar da ni jinsin ku ba? Kai wanne irin mai kunnen ƙashi ne? Idan baza ka girmama ni ba ka kira ni da ranki ya daɗe ka bar shi kawai, amma kar ka kuma haɗa ni da jinsin maza ka cire ni a jinsin ƴan uwana mata eheee."

     Yana gama maganar yana fari da ido gami da buga cinya, sai kuma ya nufi ƙofar fita. "Ba zan iya jiran sa ba yanzu haka kashi yake yi ga kashinsa kamar na danƙo sai ya kai magriba bai fito ba ni kam sauri nake yi, na hau Adaidaita."

   Bai jira cewar maigadin ya fice daga gidan cikin tafiyar da ta zame masa jiki ta rangwada. Dariya maigadin ya yi sannan ya koma ya zauna yana girgiza kai.
Yana fita titi ya tsaya jiran Napep, sai ga wata ta taho ya tsayar da ita. "Wata budurwa ce da wani matashi a ciki. Kasancewar matashin ne a can ciki sai ta fito domin su su haɗe "Ai da kin yi zaman ki ma ƴar uwa."
"A'a kai ne za ka shiga dai ku haɗu sai ni na zauna."
Baki ya kama zai yi magana sai kuma ya kama ƙarfen ya shiga ya zauna, itama ta shiga Mai napep ya ja suka fara tafiya, duk da haka sai da ya yi abin da ya yi niyya "Amma ƴar uwata ban ji daɗi ba, wannan abu bai mini ba sam, lokaci ɗaya kika tsame ni daga cikin ku kika mayar da ni cikin su, to ki canja hali gidan wani za ki je."

   Mamaki ya kamata sai kawai ta saki baki tana bin sa da kallo. Shi ma na kusa da shi ɗin juyowa ya yi ya zuba masa ido "Ka ga don Allah ka kalli gabanka kar ka haɗiɗiye ni don an siyar, kuma ka ɗan gyara zamanka na ga kana matse ni ka sake ka taɓa ni alƙur'an sai ka biya........!



NEXT