4
by @hilfat
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
*WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
(4)
Tsaye ta yi a ɗakin nasa tana ƙare masa kallo, komai tsaf sai dai ɗakin ya fi kama da ɗakin mace duba da yadda aka cika gaban madubi da kayan shafa. A hankali ta dinga bin kayan kwalliyar tana kwashewa, sai da ta ɗebe tass iya turarukansa kawai ta bari sannan ta buɗe ƙofar ta fice saɗaf-saɗaf.
Ta ci sa'a ba kowa falon sai kawai ta mayar da spire keys ɗin inda suke ta shige ɗakinta da kayan, tana shiga ta zube su kan madubi tana bin su da kallo cike da takaici. Allah ya sani ba ta son wannan rayuwar da ɗan uwan nata ke yi, amma ta lura ya yi nisa ba zai ji kira ba Kwashe su ta yi ta zuba a leda ta wurga su can ƙarƙashin gado cike da dakiya domin dai ta san ta jangwalo tijararsa. Jakar da take ajiye takaddu masu muhimmanci ta janyo ta fito da su ta fara aikin da ke gabanta.
Alhaji Sammani cike da nishaɗi ya fito a bathroom ɗin, sai kuma ya yi turus ganin ba ta ɗakin. Waige-waige ya fara yi amma bai hango ta. Yana kallon inda ya zube abubuwansa ya ga wayam. Gabansa ne ya ɗan faɗi don haka da sauri ya nufi ƙofa sai kuwa ya ji ta a buɗe, a ruɗe ya fice yana cigaba da dudduba wurin har ya sakko wurin maaikatan hotel ɗin. "Ina yarinyar da muka shigo tare ɗazu kun ga wucewarta ne?"
"Ban kula ba gaskiya Alhaji" Ɗaya ya faɗa "Tabbas na ga wata budurwa ta fice ɗazu ban sani ba ko ita ce." Cewar ɗayan "Wanne irin kaya ne a jikinta?" Ya kuma tambaya "Baƙin less ne da jan mayafi." Ai tun kafin ya gama ji ya doshi ƙofar fita da sauri.
"Alhaji ba kaya a jikin ka fa"
Sai lokacin ya kalli jikinsa, daga shi sai gajeren wando, tsaki ya ja yana komawa ciki, kamar zai kifa, gudu-gudu sauri-sauri ya zira kayansa ya fito, ko rufe ɗakin bai yi ba ya ba su makullin ya ce su je su rufe. Motarsa ya faɗa ya fice a get ɗin yana dudduba ta amma ko mai kama da ita bai gani ba. Duk yadda ya so ƙaryata zuciyarsa da take faɗa masa ƴar damfara ce ta yashe shi ne ta gudu sai da ya fara gasgatawa, ga shi ko lambarta bai karɓa ba.
Rasa abin yi ya yi ma, tunowa da ATM card ɗinsa da ta haɗa da shi ya sanya gabansa yankewa ya faɗi. Sai kawai ya nufi banki duk da ya san lokaci ya ƙure.
Ƙarshe dai abin da yake ta fargabar sai da ya kasance domin ta yashe kuɗin bankin nasa kaf, hannu ya ɗora a ka kamar ya zunduma ihu haka yake ji. Motarsa ya koma ya ɗora kai akan sitiyarin motar yana tuno haɗuwarsu.
Wucewa zai yi cikin motarsa ya hange ta tsaye a bakin titi, tun daga nesa yake kallonta, take ya ji ta masa. Ya matsa gabanta ya taka burki. "Yammata ina zuwa haka?" Shiru ta yi tana kallonsa. Sai ya yi murmushi "Ai kin cancanci ki ja ajin girmanki ne ran ki ya daɗe, idan ba damuwa ki shigo na rage miki hanya mana". Yanzun ma kallonsa take yi sai kuma ta yi gaba. Kashe motat ya yi ya fito ya bi ta. "Bai kyautu kamar ke kina tsaye a nan kowanne kare da doki na kallonki ba, ki taimaka ki shiga mota na je na sauke ki." Wannan karon da hannu ta masa alamun ba ta magana "Oho na fahimta, to dai ko kurma ce ke ɗin kuma bebiya ni dai na gani na ƙyasa kin mini a haka." Ya cigaba da mata magiya har a ƙarshe ya yi nasara ta shiga motar suka tafi. A motar ma maganar yake cigaba da yi yayin da take ba shi amsa da hannunta.
Daga nan ne suka je restaurant inda daga nan ya wuce da ita hotel kuma daga shiga wanka ta yashe shi ta gudu. "Duk inda kike wallahi sai na nemo ki, kuma sai kin gane ba a haintata, duk inda na gan ki ai zan gane ki, kai Allah ya isa kin cuce ni kin taƙaita ni, kin kwashe mini maƙudan kuɗi, Allah ya isa." Ya ce cike da takaici idon shi ya kaɗa ya yi jajir da ka gan shi za ka fahimci tsantsar ɓacin rai da yake ciki.
Wai wanne mai hannun ɓeran ne ke shiga mini ɗaki yana mini sata a gidan nan? To wallahi tun muna shaida juna da mutum ya fito mini da kayan kwalliyata. Na siya an sace na kuma siya an sace wannan wacce irin ƙaddara ce?" Ya ƙarasa da watsa hannu.
"To wai wannan tijarar da kake ta yi da wa kake? Ni ce ɓarauniyar kenan da ka tsaya a kaina kana mini ihu ko?" Mamy ta faɗa cike da takaici "A'a kowa ya yi zagi a kasuwa ai ya san da wanda yake? Haka ake rayuwa a ce ba ni da damar ajiya a ɗakina sai an shiga an ɗauke, sai a ke yi mini bincike a ɗaki kamar an ba ni ajiya. Ke bari na fito miki a mutum ai ba tsoronki nake ji ba Nuratu ke nake zargi don haka tun wuri ki tashi ki ɗauko mini jambaki da hoda ta har da man shafawa."
Ya juya ido yana watsa su zuwa kan Nuratun "Ni ban ɗauka ba ka kuma dubawa ɗakin ko wani wurin suka faɗa." Tace tana tura baki "Ai ko makaho ya yi ajiya ya san inda ya ajiye. Kece kike sace mini kaya wallahi ba ki fito mini da su ba jikin taƙaura sai ya yi la'asar ehe."
"Nura! Nura!! Nura!!! Sau nawa na kira sunanka?" Mamy ta faɗa tana tsare gida. "Haba mamy don Allah, haba mana ki dinga ce mini wani Nura ba gishiri bare magi, suna ba daɗi ba dadaɗawa. Ni wallahi bana son sunan nan kawai ba yadda zan yi ne. Ƴar Dubai ya fi daɗi wallahi idan aka ce Ƴar dubai ɗin nan daɗi ratsawa yake yi har maƙwallatan zuciyata." Ya ƙarasa da ɗora hannuwansa kan ƙirji yana lumshe ido.
"Oh ni kuma ƙaddarata kenan, zakkar da aka fitar mini kenan kai, Allah ya shirye ka gane gaskiya ka bi ta, ka kuma gane ƙarya ƙarya ce ka kauce ka bar ta don matsayin Abban Binta."
"Amin Mamy" Cewar Nuratu.
Juyawa ya yi zuwa ɗakinsa bayan ya taɓe baki yana kwarkwasa ya banko ƙofa, duk suka bi shi da kallo "Me yasa kike kwashe masa abubuwansa, wannan tijarar da yake zuwa yana mana daɗi ce?" Ta tambaye ta "Wallahi mamy ba na son ganin yaya a wannan rayuwar da yake yi, ya yi ta zubar mana da mutunci a waje, duk masu ganin girman daddy sun daina yanzu. Shiyasa nake kwashe masa kayan matan da yake siya, ki duba fa wai har da mayukan bilitin yake amfani ko ni ba na shafe-shafe Mamy sai shi yana namiji?"
"To ya za mu yi Nuratu tamu ƙaddarar kenan, jarrabawa ce sai fatan Allah ya ba mu ikon ɗauke ta. Kuma kin san don kin kwashe ma a banza ba fasawa zai yi ba ƙara siyo wasu zai yi, mu cigaba da bin shi da addu'a kawai."
Kafin ta yi magana ya fito daga ɗakinsa ya doshi ƙofa "Ina za ka je kuma?" Mamyn ta tambaya "Ɗinkin ankon nan zan miƙa fa, kar lokaci ya ƙure tunda bikin ya taho."
"Dawo baza ka fita yanzu ba, ka bari a miƙa maka idan za ta fita aiki "
"Haba-Haba don Allah ni dai gaskiya, ana nuna mini wariyar launin fata a gidan nan, yanzu duk wasu ƙawayen namu fa an ɗinka musu nasu, sai ni da suke wa kallon babbar yarinya ace ban saka ankon nan ba ai na faɗo babu girma sai a raina n...."
"Na ji don Allah na ji" Ta katse shi. Ya juya ya fice cikin tafiyar da ta zame masa jiki yana waƙe-waƙe. "Allah ya shirya" Maigadi ya faɗa ƙasa-ƙasa don kar ya ji " Faɗi kar ta kashe ka, ai na ji abin da ka ce, to amin idan da gaske kake." Ya yi gaba, mota ya faɗa direba ya ja suka fice a gidan. Wani shagon ɗinkin suka je da ake ɗinkin mata ya miƙa atamfar ya kuma cake kuɗin ɗinkin sannan ya fito.
Kai tsaye daga nan gidan uwarɗakinsu Ramatu dillaliya suka nufa. A waje direban ya tsaya shi kuma ya shige ciki. "Gafaranku dai masu gida" Ya faɗa "Heeeeheeheeeee wiiii" Suka faɗa a tare kafin suka wara hannuwa suka tafa a tare. Wasu ƴan daudun ne su huɗu sai shi cikon na biyar "Auntyna kina baza kafasiti fa irin wannan ɗashewa haka." Ɗaya ya faɗa yana kama haɓa "Fari Nuran ya yi da ido "To ya ranki ƴar ɗagwas "Rai fesss ba hawan jini ba olcer, kuma ba baƙincikin ɗa namiji " Ƴar ficika ta faɗa, sai kuwa suka sa shewa "Hehehehehe A hayyaye nanaye casss" suna kwashe wa da dariya haɗi da tafawa.....!
***