5
by @hilfat
***
*WOMEN OF WORDS*
_Writers Association_
*(WOW)*
*TURMIN DANYA*
*NA*
*FATIMA UMAR KAS*
_HILFAT_
(5)
Wasu mata ne suka yi sallama suka shigo gidan, idon su akan su Nura ƴar dubai da suke zaune suna shan shafta. "Ke meye kike kallona? Ko idon ya miki yawa? ƙwaƙwulo ɗaya mu raba" Ya faɗa da waƙa "Ahayye wiiii! Suka faɗa a tare suna tafawa, matan ba su bi ta kan su ba suka ƙarasa gaban matar suna gaisawa "Ga rabin kuɗin kayan gadon nan za mu ciko nan da jibi." Ta miƙa mata kuɗin, karɓa Ramatu dillaliya ta yi ta soke a jikin zani "Ba damuwa Allah ya nuna mana."
Sallama suka mata suka fice, "Auntyna wai wanne kayan gado suke magana akai ne?" Ƴar Ɗagwas ya tambaye ta yana ranƙwafowa. "Waɗanne kuwa idan ba wanda idonka yake gani ba yanzu? Ai babu wasu kayan gado seti yanzu a ƙasa bayan wannan?"
"To ai ni idan ban manta ba kayan nan kin karɓi kuɗin mutum uku kenan a kan shi. Rannan ma na ga wadda ta zo cikon kuɗi kaɗan za ta kawo ta kwashi kaya." cewar Ƴar Dubai "Hmmm naku wasa ne idan ba ku yi ba ni wuri, rigima uban wa ta kashe? Ai wannan kaya da kuke gani mutum uku ne a kan shi kuma duk na san yadda zan yi da su. Ramatu dillaliya nake fa, wannan harkar ai sai ka iya ta take ɓullewa da kai gobena nake dubawa ai ba ta wasu ba"
"To Allah ya kauda ɓacin rana" In ji Ƴar ficika "Amin." suka amsa daga nan suka ɗora da wata firar.
Tana zaune a cikin ofishin tana rubutu aka ƙwanƙwasa ƙofar "Yes" Ta ce kawai ta cigaba da aikinta. Wata matashiyar budurwa ce ta shigo da za su yi sa'anni da ita. Murmushi suka sakar wa juna sannan ta ja kujera ta zauna. "Agogo sarkin aiki? ke ko gajiya ba ki yi?" Cewarta, murmushi ta kuma saki kafin ta ce "Zaitun kenan to ya za mu yi tunda aikin namu haka ya gada? aikin al'umma muke yi dole za mu yi ta cin karo da wasu abubuwan da za mu fito wa da al'umma su."
"Haka ne kam amma dai a dinga barin ƙwaƙwalwa na samun hutu, don ni dai ba na takura kaina kamar ke ɗin nan, sama-sama dai, kin san me? Wata magana na zo miki da ita fa yau ban sani ba ko za mu iya wani abu a kai."
"Ina jin ki me ya faru?" Ta mayar da hankalinta kan ta "Akwai wata ƴar damfara da ta ɓullo tana nan tana yawo tana yashe maza da suka faɗa komarta. Shekaranjiya Uncle ɗina da ya zo na ga yanayinsa duk babu daɗi, to da na matsa masa yake faɗa mini bayan ya saka na masa alƙawarin ba zan sanarwa kowa ba musamman matansa.
Sun haɗu da yarinyar wurin dinner ɗin abokinsa har suka yi musayar number, daga nan suka fara soyayya da ita duk da kasancewarta ba ta magana, za ta ji amma baza ta mayar ba, sai dai suke tura wa juna saƙon soyayya, a wurare mabambamta suke haɗuwa, idan ya ce zai je gidan su sai ta hana, har a ƙarshe ta buƙaci ya ba ta nashi adireshin ita ta zo, take ya ba ta adireshin gidan hutawarsa. Aikuwa ta zo ya kawo mata lemo da ruwa ya koma ciki don samo mata snack, to dai ya ce a tafiyar nan tasa ta saka masa maganin bacci a lemo. Don bayan ya dawo ya tarar ta zuba tana sha sai ta miƙo masa ɗayan ba musu ya karɓa yana sha a hankali har ya shanye, daga nan ya fara hamma sai bacci ya ɗauke shi.
Bayan farkawarsa ya neme ta ya rasa, sannan ba haka ta bar shi ba, ta buɗe inda yake ajiya ta kwashe masa kuɗaɗensa, har da takaddun kadarorinsa. Da makullin mota guda ɗaya. Kuma ya ce har kawo iyanzu bai kuma haɗuwa da ita ba, layin nata ma bai kuma samu ba tun daga ranar. To abin da nake tunani ba iya shi ta yi wa hakan ba da alamu ta saba yi ne duba da yadda ta haɗa masa tarkon, na zo wurin ki mu yi shawara ne, ta ina kike ganin za mu ɓullo wa al'amarin?"
Ajiyar zuciya Nuratu ta sauke kafin ta ce 'Kin sanar wa oga?" Girgiza kai ta yi kafin ta ce "A'a dake na fara maganar, da na fi so mu fara ƙoƙarin yin wani abu akai tukunna ta yadda idan mun je masa da maganar za mu ce ga a kan matsayar da muke sai ya fi jinjina mana."
"Kuma kin yi magana ke ma. Ina tunanin ta hanyar wannan uncle ɗin naki za mu samu makamin da za mu kama har mu yi nasara, abu na farko da ya kamata mu mayar da hankali akai shi ne ziyartar wuraren shaƙatawa da kuma na cin abinci. Sai ya kasance muna lura da shige da ficen kowa da kuma ƙare wa mutanen wirin kallo a fakaice musamman idan mace da namiji ne, wannan zai taimaka mana."
"Dakyau ƙawata, daɗina da ke ƙwaƙwalwarki na ja, ni ai kaina kullewa ya yi gabaɗaya na rasa ta ina zan fara ma, amma yanzu kin ba ni aidiya."
Ta ƙarasa da yi mata alamar jinjina ta hanyar ɗaga mata babban ɗanyatsanta. Murmushi kawai ta ma ta sannan tace "Kai wane mutum ya kama kura ai ban ko kama ƙafarki ba, yanzu kamar yaushe kike ganin yakama mu fara?" Tace tana kallonta "Ai ina ganin nan da gobe haka kin ga da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, gara mu yi da jiki tun kafin wasu ma su faffaɗa tarkon nata, yau ma ba don lokaci ya ƙure ba da mun je ko na kusa ne."
"A'a yau ina da baƙo gaskiya, sai dai gobrn sai mu fita da wuri."
"Uhmm! Ko dai na ƙasan ran ne a tafe?"
Harara ta ɗago ta galla mata cike da gatse take faɗin "Eh mana ai kin san son shi har toshe mini numfashi yake yi." Dafa ta ta yi tana gyara fuskarta sosai "Wai ƙawata har yanzu bawan Allahn nan bai shiga zuciyar ki ba?"
"Faɗa ma ai ɓatawa Zaitun. Wallahi har yanzu ba na jin son barister sahabi a raina, ga shi dai ba shi da wata makusa amma na kasa jin zan iya aurensa, kin san fa ni daga yanayin aikin mu da ya hahhaɗa ni da shi shike nan ya maƙale mini. Ina dai kula shi ne a dole kuma ina ganin mutuncinsa ba zan iya wulaƙanta shi bs."
"To shike nan Allah ya zaɓa miki abin da ya fi zama alkairi, amma dai gaskiya ban ga aibunsa ba ni dai, ya yi ta koina."
"To ko kina som shi na haɗa ku?"
"Wa ni? rufa ni ki saya, ai ya san da ni ɗin ya ce ke, ni ma Allah ya kawo mini babba mai hankali kamar shi, don ni fa ba zan auri yaro ba. Uhmm bari ki ga na dinga yi ina rage aikina ni ma, na zo nan na rashe ke kuwa kina ta mini wayo." Ba ta jira cewarta ba ta matsa can ta ja kujera ta zauna gaban nata teburin tana kiciniyar sakko da jakatya. "Da dai ya fi miki" Tace tana murmushi kafin ta dawo da hankalinta kan aikin ta cigaba da yi.
Tafiya yake cikin yanga ya riƙe gefen jallabiyarsa da yatsu biyu yana kwarkwasa. Ido suka haɗa da wasu matasa guda biyu suna kallonsa. Tsayawa ya yi yana musu wani shegen kallon sama da ƙasa na tara saura kwata, sai kuma ya taɓe baki ya cigaba da tafiya "Nuraddeen" Ya ji an faɗa a bayansa yana shirin tura gidan ya shiga, kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya ja ya tsaya ba tare da ya juyo ba.
Ƙarasaowa ya yi ya sha gabansa. Irin ustazan nan ne da suka ɗan ajiye gemu suna magana da ƙaƙalee "Ya Nuraddeen assalamu alaikum" Ya miƙa masa hannu, maimakon ya miƙo shima sai ya noƙe, "akan me za ka gaisa da ni bayan ba muharramarka ba ce ni ɗin?"
"Subhanallah! Ya salammm! Ya kai wannan yaro da ke kan hanyar ɓata, wato ainahin ƴar nasiha ce zan yi maka a matsayina na musulmi ɗan uwanka. Wato ita wannan turba da kake kai ba daidai ba ne, yakamata ka yi wa kan ka faɗa ka gyara rayuwarka."
Tun da ya fara maganar ya juya masa ƙeya haɗi da ƙara tura ɗankwali gaban goshi "Faɗa wa ƙeya ɗankwali ya ba ka amsa." Hakan da ya ce masa bai sa ya yi shiru ba ya cigaba da nasihar tasa "Ka ga ustaz ni fa na gaji da tsayuwa ga shi babu abin da na fahimta a maganganun naka, idan za ka saki baki ka yi magana sak zai fi maka, kawai ka zo da wata fuskarka ƴar kuyas kamar an silala karas, ka wani ajiye gemu sai ka ce jelar tsafi kana wani wato ainafin, idan waazi za ka yi hau turmi, ni ka ga tafiyata." Daga haka ya tura ƙofar jikin get ɗin gidan ya shige.
Turus ya yi ganin baƙuwar mota a fake, bin ta ya yi da kallo sannan ya doshi ciki "Wahalallu ku dai kun ji jiki kullum ba ku da aiki sai zance, shi ko gajiya ba ya yi koyaushe yana hanya sai kace wanda ya ci ƙafar kare. Ni wallahi ba zan iya wannan rayuwar takurar ba, ko ya yake yi da aikinn nasa oho masa" Ya ƙaraci mitarsa ya shige ciki yana cigaba da sababi shi kaɗai wanda yawanci shi ne sallamarsa......!
NEXT