6
by @hilfat
TURMIN DANYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(6)
Cikin shirin fita ta fito jikinta sanye da baƙar abaya ta yane kanta da mayafin rigar wadda ta kuma haska ta sosai. A falo ta tarar da su a zaune Mahaifiyar tasu da yayan nata, ta ƙarasa ta zauna kusa da mamy "Na fito Mamy" Ta ce cikin murmushi. "To ƴar albarka sai kin dawo Allah ya taimaka."
"Amin summa amin, yaya ba ka yi mini adduar ba kai"
"Na fa soke yayan nan ko? Aunty shi nake so saboda ba ni da wani bambanci da ke ke ma kin sani ehe." Ya juyar da kai "Tashi ka ba ni wuri, ban hana kana gabana kana canja jinsinka ba?" Cewar Mamyn "Yo ai Momy ba a canja wa tuwo suna. Shike nan yanzu za ta haɗa ni da ke muna zaune muna ƴar firar mu ta tsakanin ƴa da uwa, daga zuwanta za ta saka ki kore ni, ke dai ba ki ji daɗin halinki ba wallahi munau." Ya dungure mata kai yana miƙewa tsaye. "Uhm inji mai ciwon haƙori ni na yi nan sai na dawo." Ta fice daga falon tana kallon agogo.
Motar ta ta faɗa Lawwali direba ya ja suka fice. Sun ɗan yi tafiya mai nisa don sun wuce cikin unguwa kawai ba zato bare tsammani wata baƙar mota ta sha gabansa, da sauri direban ya taka birki. Wasu mutane ne suka fito su uku fuskarsu a rufe sun riƙe manyan bindigu suka iso motar. Tuni jikin direban ya hau rawa, buɗe motar suka yi suka fizgo shi waje, sai itama suka janyo ta har sai da ta kai ƙasa guiwarta ta guje a ƙasan kwalta ɗin.
Motarsu suka jefa ta suka rufe, da sauri ya miƙe ya isa wurinsu "Me ta muku ina za ku kai ta? Wai babu jama'a a kusa ne a kawo mana ɗauki" Ya fara ihu. Kafin ya rufe baki suka buga masa kan bindiga aka, take ya silalo a wurin, su kuma suka fizgi motar tasu suka bar wurin da matsanancin gudu.
A can wurin aikin nasu kuwa Zaitun ke ta jiran zuwanta amma shiru, tuni ta shirya tunda ta ce mata da wuri za su fita su dawo amma ga shi har an shafe awa ɗaya tana zaman jiran ta ba ta zo ba.
Ganin an doshi awa biyu sai ta cire waya ta kira ta, sai dai wayar a kashe, tsaki ta ja ta koma ta zauna cike da takaici, wasa-wasa lokacin ya cigaba da ja, tun tana saka ran zuwan nata har ta fitar da rai. Cire mayafin jikinta ta yi ta yi ta jefar ta yi alwala ta tada sallah, tana idarwa ta koma kan kujera ta zauna ta hau aikinta cike da takaicin jirga ta ɗin da ta yi ta ɓata mata lokaci, haka ta gama aikin da za ta yi na ranar cike da ƙunci tuni ta ƙudurta sai ta biya ta gidan su ta nuna mata ɓacin ranta kafin ta tafi gida.
A hankali ya fara buɗe idanunsa jin hayaniya a kan shi, har ya yi nasarar buɗe su gabaɗaya. "Yawwa ya farfaɗo, sannu bawan Allah" Ya tsinkayi muryar wani a kan shi. Kan shi ya ji ya masa nauyi sai ya mayar da idon ya rufe. "Daure ka tashi bawan Allah nan kan titi ne dama shirin ɗauke ka muke yi" Ya kuma ji an faɗa. Ƙara buɗe idon nasa ya yi sai ya shiga ƙarewa wurin kallo take ya tuno abin da ya faru, sai kuwa ya miƙe a zabure yana faɗin "Nuratu, ina Nuratun, shike nan sun tafi da ita. Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" Ya fashe da kuka "Kwantar da hankalinka bawan Allah ka mana bayanin abin da ya faru. "Muna cikin tafiya zan kai ta wurin aiki kawai suka tare mu, bindiga suka buga mini suka saka ta a mota suka tafi da ita."
"Su wanene?" Wani ya tambaya "Ban san su ba ni ma sun rufe fuska. Ya kuma saka kuka "Ka ga kwantar da hankalinka in sha Allahu babu abin da zai sami ƙanwarka, yanzu ka samu a sanar da gida abin da ya faru" Ba musu ya ciro waya ya kira mahaifin nata, da ya ɗaga kuma sai ya kasa magana. Wani dattijo ne ya karɓa ya fara yi masa bayani.
Take hankalinsa ya tashi kuwa, cikin ɗimuwa ya hau faɗin suna daidai ina yanzun? Ana faɗa masa yace ga shi nan zuwa. Ba a fi minti talatin ba kuwa sai ga shi ya iso wurin a ruɗe yake kuma tambayar abin da ya faru, bai ɓoye masa komai ba ya kwashe ya sanar masa.
"Shike nan sun sace mini ƴar, magauta sun fara sako ni gaba, to ina suka kai mini ita, kai kana kallon me har suka tafi da ita ba ka taɓuka komai ba?" Ya mayar da tambayar kan shi "Wallahi Alhaji na yi ƙoƙarin dakatar da su suka buƙa mini bakin bindiga daga nan na faɗi ban jima da farfaɗowa ba."
"Ai zama bai kama ni ba, shiga motar ka wuce gida ni bari na je police station na sanar musu abin da ya faru, idan ka je kar ka faɗa mata ka jira na zo gidan tukunna." Daga haka ya faɗa mota ya fige ta ya bar wurin. Shi ma motar ya shiga ya tayar da ita, nan ya bar mutane na mayar da yadda aka yi. Daga nan kai tsaye can ɗin ya nufa ya shigar da rahoto, suka ce ya koma gida za su yi iya ƙoƙarinsu akai. Isar shi gidan ya tarar da Mamyn a birkice, tana ganin shigowarsa ta tashi da sauri ta nufe shi "Ina take? Ina Nuratun na gan ka kai kaɗai?" Maimakom ya ba ta amsa sai kawai cikin ɓacin rai ya ce "Wai sai da ya faɗa miki maganar nan? na ce masa fa ya bari na yi miki bayani a nutse saboda na san ki da ruɗewa" Ya faɗa cikin fushi "Tun kafin zuwan lawwali Zaitun ta zo gidan nan tana tambayar ina take na ce ai tun safe ta fita aiki sai ta ce wai ba ta je ba ga wayarta ba ta shiga. Ina kiranta ɗin nima ban same ta ba. Kuma katsam sai ga lawwali cikin yanayi mara daɗi na tambaye shi ina take shi ne ya faɗa mini abin da ya faru" Ta kuma fashewa da kuka. "Kin ga ki kwantar da hankalin ki, daga wurin ƴan sanda nake yanzu na faɗa musu komai, in sha Allahu za a same ta." Cikin damuwa yake maganar shi ma.
"Kai innalillahi wa inna ilaihirrajiun! mu kuma abin da muka waye da shi kenan yau, ba a tada sani ga Allah da na san haka za ta faru ba zan bari ta fita ba wallahi." Ta zauna kam kujera tana cigaba da goge hawaye. Zaitun ta ƙarasa ta zauna kusa da ita kafin ta kai hannu ta dafa ta "Ki yi haƙiri Mamy in sha Allahu tana cikin ƙoshin lafiya babu abin da zai same ta ai tana azkar mu yi addu'a."
"Tabbas kam Nuratu na da addu'a ba na jin wani mummunan abu zai same ta ina da wannan yaƙinin game da ubangiji. Amma kin san dole hankalina zai tashi musamman jin yadda abin ya kasance, fatana kar su cutar mini da yarinya" Ta ƙarasa cike da rauni, daidai lokaci ya shigo gidan da ƴar waƙarsa da ya saba da ma idan ba waƙa ba to sababi wani ya taɓo sa a waje.
Turus ya ja ya tsaya ganin su zaune jigum-jigum. "Me kuma ya faru a gidan na gan ku haka ko an yi mutuwa ne?" Ya tambaya, babu wanda ya kula shi "Yanzu babu mai iya amsa ni ina magana? Shike nan idan ta yi wari ma ji." Ya doshi ɗakinsa, yayin da Mamy ta maka masa wani kallo na takaici ta kasa magana "Nuratu ce aka ɗauke ta" Ji ya yi maganar ta daki kansa, juyowa ya yi yana kallon Zaitun da ta yi maganar "Ban gane aka ɗauke ta ba kamar wata ɗan tsako, mutum sukutun da guda kuma sai a ɗauke shi?" Ya kama haba "Eh a hanyarta ta zuwa aiki wasu suka tare su suka tafi da ita." Ta kuma ba shi amsa "Laaa'hailahaillallahu muhammadu ɗan Abdullahi, yau na ji abin da ya ishe ni, to wallahi ta Allah ba ta mutum ba, duk uban da ya ɗauka mini ƙanwa ma zai yi gaggawar fito da ita ne tun kafin rayuka su ɓaci, kawai an ga yarinya Allah ya fara ɗaukaka ta sai a fara saka ta gaba? To nan gani nan bari wallahi." Ya ƙarasa yana hararar gefe. Harara Zaitun ta maka masa don ta fara zargin kamar magana yake faɗa mata "To yaya ko kana zargi ne na ga kana jirwaye mai kamar wanka."
"Oho duk wanda ya tsargu ma da shi nake ehe." Kallonsa kawai take yi cike da talaici "Kai wuce ka ba wa mutane wuri a nan ka bar mu mu ji da abin da ya shafe mu, tunda kai dai har gobe baza ka nutsu ka yi hankali ka san ka girma ba." Daddyn nasu ya ce masa a fusace. Bai kuma magana ba ya tura ɗankwali gaba ya nufi ɗakinsa.
"Mamy bari na tafi gida ni na ga magriba ta kawo kai kar su ji ni shiru, don Allah da an samu wata alama ta inda take a sanar mini, don na san ni dai yau ba zan iya runtsawa ba."
"To Zaitun ki gaida ƴan gidan, mun gode Allah ya ba da lada." Ta amsa da amin tana ficewa jiki a sanyaye.
Kamar jiran fitar tata ake yi wayar daddyn ta hau ruri, da sauri ya zaro ta ya duba sai ya ga baƙuwar lamba ce,kasa ɗagawa ya yi ya dinga bin lambar da kallo gabansa na ɗan faɗuwa......"