7
by @hilfat
WOW
TURMIN DANYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(7)
A lokacin da suka jefa ta motar figarta suka yi da gudu suka bar wurin, fizge-fizge take yi tana dukan motar da ƙarfi tana faɗin "Ina za ku kai ni? Ku buɗe mini mota na fita, wayyo Allah ɓarayi." Mari na kusa da ita ya zuba mata. Duk da haka ta cigaba da ƙoƙarin kai hannu domin ta buɗe motar amma ta kasa, wani marin aka kuma zuba mata sannan ya buga mata tsawa kan ta yi musu shiru. A tsakiyar su suka saka ta, ɗan kwalin kan ta ɗaya ya fizge ya ɗaure mata ido da shi, bayan ɗayan ya riƙe mata hannuwa ta baya tamau, sam ta kasa motsi sai bakinta da ya ƙi shiru tana ihun kiran taimako. Sai dai babu wanda zai ji ta kasancewar motar a ɓame take kuma gilasanta masu duhu ne
Tun tana ƙoƙarin ƙwatar kanta har ta haƙura domin ta galabaita. Sun ci tafiya sosai kafin suka iso sansaninsu. Tsayar da motar suka yi sannan suka fito da ita suka tunƙuɗa ta ciki. Ɗaya ya saka makulli ya buɗe ɗakin suka tura ta ciki da ƙarfi sannan suka mayar da ƙofar suka rufe.
Da sauri ta cire ɗankwalin da aka ɗaure mata ido tana ƙare wa wurin kallo. Tashi ta yi tana jijjiga ƙofar gami da dukanta da ƙarfi amma ta ji ko motsi ta ƙi yi alamun a ɓame take. Kuka ta fashe da shi tana faɗin "Hasbunallahu waniimalwakil! Abin da nake ji a wai yana faruwa yau ga shi ya kasance da ni, ina ne nan suka kawo ni to? Allah ka kare ni daga sharrin waɗannan azzalumai." Ta cigaba da zagaye ɗakin tana yi tana jijjiga ƙofar amma shiru ko motsin wani ba ta kuma ji ba.
Sai can da rana ta ji ana buɗe ƙofar, kallonta ta yi tana jiran ganin wanda zai shigo. Abinci kawai aka ziro mata da ruwa aka mayar da ƙofar aka rufe. Ko kallon abincin ba ta yi ba, ruwan kawai ta ɗauka ta ɗaura alwala ganin biyu saura lokacin da ta kalli agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta. Tana gama wa ta ɗauki ɗankwalin ta yafa ta tayar da sallah anan wurin duk da tana tantama ko wurin zai yi sallah, amma dai da babu gara ba daɗi. Ko bayan ta idar addua ta yi sosai kan Allah ya kuɓutar da ita daga wurin nan.
Gefe ta koma ta rakuɓe tana tunanin halin da iyayenta za su shiga idan suka samu labarin ɓatan ta. Tuno wa da Zaitun da ta yi da shirin fitar da suka yi a ranar ya kuma karya mata zuciya, domin ta san tana can tana jiranta. Wani kukan ne ya kuma kufce mata ta fige ɗankwalin ta yi jifa da shi
Haka ta kasance a wurin cikin zullumi ta haɗa kai da guiwa har ta ga lokacin sallahr laasar ya yi. Da alwalarta don haka ta miƙe ta tayar da sallahr laasar ɗin ta koma inda take. Sai can ta ji an kuma buɗe ɗakin, ko motsawa ba ta yi ba balle ta ɗago.
Ya shigo idon shi a kan ta da ta haɗe kai da gwiwa sai hakan ya ba wa yalwataccen gashin kan ta damar zubowa. Kujera ya jawo gabanta ya zauna ya yin da yaran nasa su biyu ke tsaye a gefe da gefensa. "Ke ɗago" Ya ce cikin kaushin murya, tana ji ta masa banza "Ba dake nake magana ba, ki ɗago da kan ki na ce" Cikin tsawa ya mata maganar da ta saka ta ɗagowa ba shiru. Karaf suka haɗa ido ita da shi.
Ɗan kallon sakanni ta masa ta mayar da kan ta yadda yake bayan ta maka masa wani mugun kallo, kuma baza ta ce ga kamanninsa ba tunda ya rufe kansa ruf da wata ƙatuwar hular sanyi da ya janyo ta har goshi, kuma ya saka takunkumi a fuskarsa iya idon shi kawai take gani.
Sai da ya ƙare mata kallo har ya lura da shatin yatsun dake kan fuskarta kasancewarta fara sannan ya ce "Me yasa ba ki ci abincin da aka kawo miki ba?"
"Ba na ci ba zan ci ba, kuma ba zan taɓa cin ko me za ku ba ni ba" Ta ce a tsiwace cike da jin haushi ba tare da ta ɗago ba. "Keee ya ishe ki haka ki iya bakin ki ki san da waɗanda kike tare ba sakarkaru ne mu ba." Cewar goje yana zaburowa. Hannu kawai ya ɗaga masa alamun ya rabu da ita, sai kuma ya ɗage kafaɗa irin ko a jikin nan nasa, kafin ya ce "Kar ki ci wa kika yi wa? Cikin ki ko na wani? A miƙo mini wayar nan tata", na gefen damansa ne ya miƙa masa. Amsa ya yi yana faɗin "Karɓi ki nemo mini lambar mahaifinki." Sai lokacin ta ɗago ta kalle shi da jajayen idanunta. "Kuna nufin garkuwa kuka yi da ni za ku karɓi kuɗin fansa? To ku sani babu wanda zan kira muku domin ba zan taɓa bari a ba ku wasu kuɗi ba, azzalumai macuta kaw..."
Tasss ya ɗauke fuskarta da mari, ya kuma ƙara mata a ɗaya kuncin. Ko ɗigon hawaye bai kuma zubowa a idonta ba, cike da dakiya take kallonsa. Idonta a buɗe "Ki karɓa ki kira mahaifin ki aka ce" Ya kuma daka mata tsawa. "Wallahi sai dai ku kashe ni amma ba zan taɓa kira muku babana ba, saboda kuɗin da ake biyanku ya sa kuke cigaba da yin taaddancin, da ana hana ku da kun daina tunda ba riba, kuma abin takaicin karɓar ba ta saka ku saki mutum da rai sai kun kashe shi turr da halinku, ƴan wuta kawai." Wannan karan Maiyagi ne ya nufo ta gadan-gadan amma ya kuma dakatar da shi. "Ku rabu da ita da alamu kan ta ke hayaƙi kuma mu ba a mana iskanci da ɗanyen kai a nan, zan saita mata zama ne." Daga haka ya kunna wayar ta kawo haske, sai ya cire ta a jirgin da suka saka ta. shiga wurin lambobinta ya yi yana dube-dube har ya samu wadda yake nema. Ba tare da ɓata lokaci ba ya kwafe lambar a wayar a tashi watar sannan ya kuma kashe ta ya miƙa masa.
Kira ya danna take kuwa ta shiga. A lokacin ne kuma daddyn da suke zaune jigum-jigum a falo kiran ya shigo wayarsa har ya kasa ɗagawa. "Ka ɗaga mana Alhaji" Mamyn ta faɗa "Ai baƙuwar lamba ce ban san wanene ba" Ya ba ta amsa ƙirjinsa na cigaba da bugu. "Ka sani ko kiran ya danganci Nuratu? Ɗaga da bissimillahi kawai mu ji." A lokacin kiran ya katse ma, sai ya samu kan shi da bin kiran. Kamar baza a ɗaga ba sai kuma aka ɗaga.
Abin da aka fara cewa shi ne "Yarinyarka na hannunmu, mu muka ɗauke ta muna neman kuɗin fansa naira miliyan ɗari kacal." A zabure ya miƙe tsaye "Kuna nufin Nuratu tana hannunku yanzu haka? Ku haɗa ni da ita don Allah, na roƙe ku kar ku cutar mini da ita don Allah" Ya ce cikin roƙo, itama tuni ta miƙe jin ya ambaci Nuratu. "Ba doguwar magana muka kira mu yi da kai ba, wannan dai shi ne, ƴar ka na hannunmu ka biya kuɗim fansar ta ka karɓe ta, idan ba haka ba ka yi bankwana da ita kenan har abada domin za mu kashe ta bayan mun keta mata haddi mu kuma turo maka bidiyo ɗin, kwana uku muka ba ku, za mu kuma kira domin faɗa muku inda za ku kai kuɗin. Ba zan ce kar ku sanar wa ƴan sanda ba, ku bada himma." Daga haka aka katse kiran, da sauri ya kuma bin lambar amma a kashe.
Juyowa ya yi suka haɗa ido da ita "Alhaji yi mini bayani kai da su waye?" A ruɗe "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Kidnapers ne suka ɗauke ta, yanzu ma su suka kira ni, wai tana hannunsu kuma suna buƙatar kuɗin fansa miliyan ɗari sun ba mu kwana uku.
"Miliyan ɗari? Wannan ai kuɗi ne maƙudai masu yawa? Ta ina za mu samu waɗannan kuɗin? Ta faɗa cikin tashin hankali, jagwab ya koma kan kujera ya zauna ya riƙe haɓa yana wani nazari da lissafe-lissafe, itama zaman ta yi dirshan a ƙasan capet tana cigaba da sallallami, falon ya yi shiru an rasa me magana.....