10
by @hilfat
TURMIN DANYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(10)
Tana zaune ta haɗa kai da gwiwa cikin zurfin tunani na halin da ta tsinci kan ta a ciki. Tsawon kwana ukun nan ba ta cin abincin kirki, sai dai ta ɗan yafita shi ma sai da ta ji tana shirin mutuwa ne, ruwa kawai take moɗa da yake ƙulle mata ciki shi ma. Ta gaji da zaman wurin ji take yi tamkar akan ƙaya take. Gefe kuma fargaba da ta cika ta da ta wayi gari yau ɗin cikin wani irin yanayi na canjin da take ji a jikinta, gabaɗaya a tsorace take.
Ji ta yi an buɗe ɗakin an shigo, ba ta motsa daga inda take ba. "Ke fito yau kin yi free Allah ya tarfa wa garin ki nono" Da sauri ta ɗago sai dai har ya fice mai maganar. Ƙwafa ta yi tana miƙewa tsaye da ƙyar da niyyar bin bayansa. Ji ta yi ta taka abu mai tsini ba zato bare tsammani, ta ɗan yi ƙara jin yadda ya cakar mata ƙafa, ta ɗuƙa ta ɗauka tana dubawa. Ɗan kunne ne na mace guda ɗaya, take ta fahimci ba ita ce mace ta farko da aka kawo cikin akurkun wurin ba. Ta gyaɗa kai tana cije leɓe cike da wani ƙuduri a ran ta.
Ta tsaya a filin tsakar gidan tana rarraba idon ta inda za ta fita a wurin sai kawai ta ji ana ɗaure mata ido da ƙyalle, ta rintse idanunta da ƙarfi har ya gama. "Mu je" Ya ce da ita "Ta ya ya zan iya tafiya ka rife mini ido." Ta ce cikin takaici, sai kawai ta ji ya damƙar mata hannu, fizgewa ta yi da ƙarfi "Kar ka kuma taɓa ni tunda ba muharramarka ba ce ni ɗin." "Muharrama?" Sai ya sheƙe da dariya, ya kuma gimtse ta yana zaburowa kan ta "Ke ni sa'an wasanki ne kike mini kashedi na taɓa ki ɗin, na lura da ke fa ba ki da kunya, kar ki sake ki mini tsiwa yanzu sai na yi ƙasa-ƙasa da ke, kawo hannunki mu tafi" Ya kai hannu ya kuma damƙar hannunta sai kuwa ta ƙara fizgewa ta yi baya tana shirin faɗuwa sakamakon jirin da take yi, mari ya ɗaga hannun zai zuba mata "Ka buɗe mata idon idan kun fita sai ka mayar mata" Ya tsinkayi muryar babba ɗin. Wani kallo ya maka mata na za ki sani ya hau sassauta ɗaurin ya yi mata ƙasa da shi.
Ta watsa masa wani kallo ta nufi ƙofar dake gefenta wadda ta fi zaton ita ce hanyar fita. Fili ne sosai da bai yi kama da cikin gari ba, gidan kuma shi kaɗai ne a wurin, tana cikin nazartar wurin ta ji ya ce "Hau mashin ɗin nan mu tafi kina ɓata mini lokaci ba shiri ta kama za ta hau don ta matsy ta bar wurin itama. Ƙarar jirgin sama ne a hankali ke ratsa wurin, duka suka kai kallon su kan shi. A hankali ya sauka daga can nesa da su. Ƙaramin jirgi ne irin Helkwafta ɗin nan. Ga mamakin ta sai ta ga bayan ƙofar jirgin ta buɗe wasu sun nufi wurin jirgin suna gaisawa da waɗanda suka zo a ciki, kafin a hankali suka fara fito da makamai suna ajiyewa a ƙasa. Ido ta zaro ƙirjinta na bugu me kenan?
"Wai uban me kike kallon ne?" Ta ji ya daka mata tsawa, ta ƙarasa hayewa mashin ɗin tana murguɗa baki. Tana gama hawa ya fizgi ɗankwalin kan ta ya tamke mata ido tamau, sannan ya kama hannayenta ya ɗaure su ta baya da ƙyalken hannunsa, shi ma ya hau mashin ɗin ya fige shi da mugun gudu da ƙiris ya rage ta sullumo ƙasa jikinsa rataye da bindiga.
Ita dai ba ta san ina ake yi da ita ba kawai tafiya ta ji suna yi, sun yi tafiya a ƙalla ta mintina ashirin kafin ta ji an tsaya. Ji ta yi yana waya. "Eh na hango ka, ka ajiye jakar mu gani."
Shi kuwa daddyn sammakon ya doko kamar yadda suka ba shii umarni, ya dinga bin kwatancen da suka turo masa har ya iso bayan ya ci tafiya kamar mai shirin barin garin. Ya jima a wurin amma bai ga kowa ba, ya ciro waya ya kira duka lambobin da suka yi magana amma babu wadda ta shiga. Ya kusa minti talatin da zuwa har ya fara cire rai ya ji rurin wayarsa. Yana ɗagawa kuwa ya ji yace ya ajiye kuɗin suna kallonsa.
Buɗe murfin motar ya yi ya fito da jakar kuɗin a hannunsa. Ajiye ta ya yi yana waige-waige amma bai ga kowa ba. "Ka koma motar za a zo a ɗauka". Ba musu ya yi hakan, bayan minti goma wani ya zo a mashin ya ɗauke jakar ya bar wurin da shegen gudu.
Can wayar wanda ya kawo ta ɗin ta yi ƙara ya ɗaga "Sun cika kuma ba lakwayen a tare da shi." Aka ce masa ta wayar. Fizgo ta ya yi daga mashin ɗin zuwa ƙasa sannan, ya hau ya fige shi da gudu ya bar wurin ta cikin surƙuƙin bishiyu. Sai da ya koma can sansanin nasu sannan ya turawa daddyn cewa ya duba bayan bishiyun nan zai ga yarsa. Da wani layin daban. Daddyn har ya fitar da rai da ganinta ya ga saƙon nasu. Ya fito a motar yana dudduba ta amma bai ga bishiyun ba sai fetal ɗin fili. Gaba ya yi yana ƙwala mata kira "Nuratu!!!" Ya ce da ƙarfi amma shiru. Ya cigaba da zagaye wurin yana ji kamar ya yi kuka. Ita kam a hakan take tafiya tana harɗewa cike da ƙarfin hali tana neman hanya. Kamar daga sama ta jiyo an ƙwala kiran sunanta kuma kamar daddynta. Wurin da ta ji sauti take nufa katsam ta ji ta ci tuntuɓe da wani ƙaton dutse, ta rintse ido saboda azaba kwalla na zubo mata. a hakan ta cigaba da tafiya sai kuwa ta ji gif ta kuma karo da bishiya wannan karon ƙara ta ƙwalla sai kuma ta fashe da kuka "Daddy!!!!" Ta faɗa da ƙarfi itama. Jin abu na bin fuskarta ya sa ta durƙushe a wurin.
Kamar daga sama ya jiyo muryarta, sai da ya ɗan ƙura ido sannan ya hango bishiyun da suke nesa da shi cikin duhuwa, Motar ya faɗa ya tayar da ita ya nufi wurin. A bakin ya tsaya ya fita yana cigaba da dudduba ta. Sai kuwa ya ji ya ci karo da abu, yana dubawa ya gan ta kwance jini ya wanke fuskarta kamar ba rai a jikinta.
A zabure ya duƙa ya ɗago ta "Nuratu, ke Nuratu buɗe idon ki, don Allah kar ki mutu ki bar mu" Ya dinga jijjiga ta amma ba ta motsa ba, sunkutarta ya yi ya fice a wurin a miliyan. motar ya buɗe ya shimfiɗe ta a baya sannan ya bar wurin da mugun gudu.
Sai da ya ga ya hau titi sannan ya sauke ajiyar zuciya. Yana yi yana waigowa ya kalle ta cike da faɗuwar gaban kar su rasa ta. Asibiti mafi kusa da ya tarar a hanya ya tsaya ya nufa da ita. Asibitin ƙarami ne amma dai da babu gara babu daɗi, ya samu sun karɓe ta suka rufu a kan ta. Cikin ikon Allah ta dawo daidai da ma jinin da ya zuba ne ya dinga ɗibarta har ta fyaɗi, sun yi sa'ar tsayar da shi sannan suka mata duk abin da ya dace.
Sai bayan ta farfaɗo ɗin ne daddyn hankalinsa ya kwanta har ya samu bin kiran Mamyn da ya ga yana ta shigowa amma ba shi da nutsuwar ɗagawa. "Alhaji ya aka yi na ji ku shiru kuna lafiya ko?" Ta ce a ruɗe.
"Lafiya ƙalau muna hanya ma, amma zan tsaya da ita a asibiti a duba mana lafiyarta tukunna." Take ta ce za ta taho asibitin, ya ce ta bari ba jimawa za su yi ba ai amma ta ce sai ta zo ya gan ta hankalinta zai kwanta. "Shike nan amma muna hanya ba mu ƙarasa ba, idan mun isa zan sanar da ke. Daga haka suka yi sallama. Sallama ya buƙaci a ba su su tafi take kuwa aka sallame ta. Ya riƙo hannunta yana bin ta da kallon tausayi ya saka ta a motar.
Yana tuƙin yana waigowa ya kalle ta "Sannu" shi yake ta jera mata duk idon ta ya yi zuru-zuru har suka isa asibitin.
Gado suka ba ta sannan suka saka mata ruwa don tana buƙatar shi, ya kira ya sanar mata sun isa, ta tambayi asibitin ya faɗa mata take tace gata nan. Dama suna gama waya ta shiga kicin ta sama mata abu mai ɗan ruwa-ruwa, sai ruwan zafi a flask, ta riga ta yi wanka dama a shirye take. Take ta saka Nura (Ƴar dubai ) a gaba ya ɗaukar mata kwandon abincin suka fice. Direba ne ya kwashe su zuwa asibitin. Daddyn ne ya fito ya tare su zuwa ciki. Ai tana ganin ta ta ƙarasa gaban gadon ta rushe da kuka ganin yadda ta dawo cikin kwana uku kawai. Ta rame sai wani uban haske da ta yi fayau, ga ƙuraje duk sun ɓata mata fuska jikinta duk shatin cizon sauro. "Nuratu haka kika koma? Kai Allah ya isa tsakaninmu da waɗannan mutane. Wannan ciwon mene a goshinta me suka ce likitocin? Ta mayar da tambayar kan shi cike da fargaba. Shiru ya yi yana tunanin ta yadda ma zai fara faɗa mata.
"Ka faɗa mini Alhaji, kar ka ce mini sun keta mutuncinta?" Ta ce bayan ta miƙe tsaye tama kallonsa kamar yadda shi ma kallon nata yake da rinannun idanunsa. Shi ma Nuran kasake ya yi yana fargabar abin da zai fito daga bakin daddyn......