TURMIN DANYA

11

by @hilfat

WOMENT OF WRITERS
      Association

TURMIN DANYA


         NA

FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)

(11)

Wata wawiyar ajiyar zuciya Daddyn ya sauke yana samun wuri ya zauna sannan idon shi a kan su ya ce "Zazzaɓi ne ya mata kamun kazar kuku sakamakon cizon da sauraye suka yi mata, sai ciwon kai. Raunin goshinta kuma ina tunanin faɗuwa ta yi ko ta buge saboda idanunta a rufe suke haka hannayenta."

    Ta hau girgiza kai idanunta a kan ta kafin ta ce "Yanzu sai yaushe suka ce za ta farka?"
"Eh to a kowanne lokaci ma za ta iya farkawa. Ni bari na je na dawo tunda kin zo, ki kula da ita." Kai ta gyaɗa tana neman wuri ta zauna shi kuma ya fice. Nuran ya ƙaraso ya sauke jakar kafaɗarsa ya zauna a bakin gadon shi ma duk suna jiran farkawarta.

   Sai can yamma sannan ta farka, ji ta yi kan ta ya mata nauyi "Sannu Nuratu" Suka haɗa baki wurin faɗa. Kai ta gyaɗa tana dafe kan ta da ke sara mata. Kama ta ta yi zuwa banɗakin ta wanko mata baki. "Ina so na yi wanka Mamy" Ta ce a hankali" Mayar da ita ta yi ta zaunar sannan ta ɗauki filas ɗin shayin da suka zo da shi. Kasancewar ta samu bokiti a banɗakin ruwan zafin rabi ta zuba ta sirka mata don flask ɗin ƙato ne.
Banɗakin ta kama ta ta kai ta "Za ki iya wankan ne?" Kai ta gyaɗa alamun eh. Ta fita ta ja mata ƙofar. Kafin ta fito ta haɗa mata ruwan shayin. Sam Mamyn ta manta ba ta zo mata da kayan da za ta canja ba saboda hankalinta da ya yo gaba. Dole na jikinta ta mayar sannan ta zauna a bakin gadon tana kurɓar shayin a hankali. Farfesun kayan cikin da ta yo mata ta zuba mata a plate ta miƙa mata yana tururi. Ba musu ta karɓa don tana shaƙar ƙamshin ta ji ranta ya biya, take tsohuwar yunwarta ta taso mata.
   
    Sai lokacin wani tunani ya faɗo wa Mamyn, waya ta zaro ta danna wa Zaitun kira. Kashewa ta yi daga can sannan ta kira ta. "An samu Nuratu fa, yanzu haka muna asibiti." Ta ce bayan ta ɗaga kiran. Tana jiyo murnarta ta cikin wayar take tace ta faɗa mata asibitin da suke gata nan zuwa. Bayan ta sauke wayar ta shiga kiran ƴan uwa da duk ɓatan ya dame su tana sanar musu an gan ta. Barister Sahabi ne kaɗai ya rage a waɗanda za a kira ɗin amma ba ta da numbersa. Dole sai da daddyn ya dawo sannan ya kira ya sanar masa. Bai yi ƙasa a gwiwa ba kuwa ya yi wa asibitin tsinke. Kan ka ce me duk sun hallara a asibitin kowa baki har kunne, sai ka rasa wa ya fi murna ma da ganin nata. Ita Zaitun tana zuwa ta je ta rungume ta ta fashe da kuka, itama duk ta yi wani zuru-zuru, yayin da mahaifiyarta da suka zo tare suke gaisawa da mamyn tana mata barka da arziƙi.

   Shi kan shi Barister ɗin ji yake kamar ya je ya rungume ta tsabar farinciki amma ba dama, baya ga haka ma ɗakin a cike yake, sai dai bai ji daɗin ganin yadda ta zabge ba sai ƙashin wuya. Gefe ya ci alwashin idan ta sanar masa waɗanda suka ɗauke ta ɗin sai iya inda ƙarfinsa ya ƙare. A ranar da dare aka ba su sallama suka tafi gida. Nan da nan kuwa labarin bayyanar tata ya baza unguwa, tun a daren ake ta shigowa taya murna.

   Tunda suka dawo ta zame ɗaki ta canja kayan jikinta ta watso su waje don ba ta jin za ta iya kuma saka su a jikinta. So take ta samu keɓewa ita kaɗai ta yi tunanin da take son yi. Abin ya tsaye mata a rai, ba komai ba ne face wannan makamai da ta gani an kawo su a jirgi, kuma duk tunaninta wurin son gano wanda ke da alhakin hakan abu ya ci tura. Fefe guda kuma tunanin ta yadda daddynta ya iya bayar da waɗancen uban kuɗin ya karɓo ta shin a ina ya same su? Wai ma wacce irin sana'a yake yi ne?
 Sai da ta yi kwana uku da dawowa sannan ta warware sosai, tun a ranar ta so komawa aiki iyayen suka ce sai ta kuma warwarewa. A ƙalla ta samu wata guda kafin ta koma ɗin, kuma daddyn ya ce ta daina fita haka sakaka excort zai nemo mata masu kula da ita.

    Zaune suke a katafaren falon da ya gaji da haɗuwa, su shida ne sai shi mai gayya mai aikin cikon na bakwai da ke hakimce kan doguwar kujera masu tsaron shi a gefe da gefensa. Gadanga ya juya ya kalli Goje da ke zaune a gefensa, ya fahimci me yake nufi, take ya janyo jakunkunan kuɗin guda biyu manya ya tura masa gabansa, inda shi kuma ya tura gaban na zaunen.
  Janyo su ya yi ya zuge zif ɗin, take maƙudan kuɗaɗen suka bayyana. Rafa ɗaya ya ɗaga ya shinshina yana sakin wani shegen murmushi sannan ya mayar ya ajiye.
 "Yanzu ya za a yi kenan?" Ya tambaya idanunsa kan Gadanga. "Yadda aka saba ɗin kawai za a yi shugaba." Ya ba shi amsa, wani murmushin ya kuma yi sannan ya ce "Wannan karon kiɗan ya canja dole ne rawar ma ta canja. Yadda aka saba kashe mu raba ɗin yau zai bambanta da na koyaushe, dole ni zan ɗauki kaso uku cikin biyar, sai ku kasafta kaso biyun saboda wasu dalilai." Ya ɗago ya watsa masa wani kallo jin abin da ya ce, sai kuma ya mayar da idanunsa ya lumshe ba tare da ya yi magana "Kai nake saurare Aliyu." Ya ce masa ganin ba shi da niyyar magana "Duk yadda ka yi daidai ne Shugaba." Ba tare da ya buɗe idanunsa ba.

   Take kuwa ya kasa kuɗin inda ya ajiye nasan a gefe cikin jakar, ya tura masa nasu gabansa. Jin abu ya dunguri ƙafarsa ya sa ya buɗe idanunsa a hankali. Da ido ya yi wa maiyagi alama. Duƙawa ya yi ya ɗau jakar kuɗin ya shige ciki ya ajiye. Miƙewa baƙon ya yi ya saka yaran nasa suka ɗauki nashi kuɗin sannan ya kuma miƙa musu hannu suka ƙara gaisawa ya juya ya fice. Rufa masa baya suka yi. Shi ma miƙewa ya yi ya biyo su kamar ba ya son taka ƙasan. Har gaban motar suka rako shi, bayan ya shiga ya kuma leƙo da kan sa "Aliyu aiki na kyau ka ƙara kulawa dai" Kai kawai ya gyaɗa masa. Direban ya ja motar suka fice daga wurin.

    Ciki suka koma su ma. Kuɗin ya sa suka ɗauko masa, ya ɗan ƙura musu ido da baza ka gane kallon me yake musu ba. Buɗewa ya yi ya kasa biyu ya raba musu rabin sannan ya ajiye rabin a gefensa. Ganin yawan kuɗin ya sa  suka buga sowa gami da fito suna zabga godiya da yi masa kirari. Ya kuma ware wasu ya ce su kira matashin nan da ke musu aiki ya zo ya karɓa a ranar, shi kuma ya miƙe ya ɗau nashi kason ya juya ya fice a gidan. Motarsa ya faɗa ya tashe ta ya bar wurin.

   Tunda ya shiga gidan yake bin yaran da kallo cikin wani irin yanayi, suna ta wasan su cike da nishaɗi. Kai tsaye can ofishin ya nufa, bayan an masa iso ya shiga bakinsa ɗauke da sallama. Wata farar mata ce a zaune ta sha lulluɓi da gani ta manyanta don a ƙalla za ta iya ba wa shekaru hamsin baya. Tana ganinsa ta saki fara'a "Sannu da zuwa, ƙaraso ka zauna. Ya nemi wuri ya zauna ɗin yana gaida ita, amsawa ta yi sannan ta miƙe ta buɗe firjin da yake kusa da ita ta ɗauko masa ruwa da lemo "Bissimillah Aliyu ga ɗan abin taɓawa" Ta ce har yanzu da fara'a a fuskarta. "Alhamdulillah, na gode Maah" Ya faɗa "Haba Aliyu ko ruwan ka sha mana." Bai kuma magana ba ya ɗauki ruwan ya buɗe ya ɗan kurɓa sannan ya mayar ya ajiye. Sabunta gaisuwar suka yi kafin ya janyo jakar gefensa ya tura mata. "Sannu da ƙoƙari malam Aliyu kai kam ba ka gajiya" Tana janyo jakar ta buɗe.
  "Ai ba a gajiya da aikin lada maah"
"Haka ne, to Allah ya saka maka da alkairi ya ƙara buɗi"
Ya amsa da amin. "Kamar yadda aka saba dai yanzun ma za a yi amfani da su a inda ya dace,  Ilminsu, lafiyarsu, ci da sha da sutura ba su nemi komai sun rasa ba kam tamkar sauran ƴaƴan da suke da gata, Allah ka ɗai yasan adadin ladanka." Ta kuma faɗa "Ma sha Allahu, ni bari na koma" Ya miƙe tsaye "Har tafiya baza ka jira a kira maka wasu yaran ku gaisa ba?" Bayan ta miƙe tsayen itama. "Sai na kuma dawowa ina sauri ne yanzu." Daga haka ya fice ta biyo shi tana cigaba da masa addu'a. 

   Yaran tuni sun zagaye motar tashi, ya shafa kan wasu daga cikinsu sannan ya buɗe ya shiga, suka dinga tsallen uncle uncle har ya tafi yana ɗaga musu hannu suna ɗaga masa......