13
by @hilfat
TURMIN DINYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(13)
Yana zaune a bakin katifarsa ya ɗora hannuwansa akan gwiwowinsa. Idanunsa na lumshe yana sauraren shirin da ake yi a rediyon da ke gabansa. Kamar daga sama ya ji muryarta raɗau a cikin rediyon. Ba shiri ya buɗe idanunsa, tabbas itace, yarinyar da ta hargitsa masa tunani ta bar ƙwaƙwalwarsa da tunaninta ba dare ba rana. Sosai yake son yakice ta a ran shi domin shi ba shi da lokacin ɓatawa a soyayya amma abin na son fin ƙarfinsa.
Ya furzar da wani huci mai zafi sannan ya maimaita sunan da ya ji ta faɗa a ƙarshen shirin wanda sai a ranar ya san sunan nata. Ya kuma kallon mitar tashar don so yake ya riƙe saboda shirin da ya ji alamun ita ke gabatarwa kodayaushe. Yana ji shirin ya zo ƙarshe ya kashe ya koma ya kwanta rigingine yana kallon rufin ɗakin, take ya shiga tunanin abin da ke gaban su domin shi ne Next target ɗin su...
Tagumi ta zuba da dukkannin hannayenta biyu ta yi zurfi cikin tunani. Dafa ta ɗin da ta ji an yi ya saka ta ɗagowa da sauri. Ajiyar zuciya ta sauke ganin wadda ke tsaye. "Lafiya Nuratu?" Ta tambaye ta idanunta a kan ta. Kai kawai ta girgiza mata alamun bakomai, ido ta ɗan ƙura mata sai kuma ta zagaya ta zauna kusa da ita. "Labarin zuciya a tambayi fuska ai, ga damuwa nan kwance a fuskar ki kuma ki ce ba komai?"
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Kin san barister Sahabi ya turo magabatansa jiya? Sun kawo kuɗin komai saura rana kawai da za a tsayar?" Ta ƙarasa kamar za ta yi kuka.
"Kai ma sha Allahu amma dai na ji miki daɗi za ki shiga daga ciki ke ma. Mu ma Allah ya kawo namu nan kusa."
"Hmmm ba za ki gane ba Zaitun, shike nan dai kawai"
"Na san matsalar ƙawata, amma ina ganin wannan ba zai zama abin damuwa ba tunda har an kawo kuɗi yanzu kuna tare ga shi manya sun shiga ciki, ki daure a hankali za ki so shi, ai barister ba shi da makusa ya cancanci a so shi shi ma. Ga shi kammalallen mutum ne mai hankali da nutsuwa, abin da kike son samun ga mijin da za ki aura, na tabbata za ki ji daɗin zama da shi"
"Soyayyar fa? Daɗin aure ka auri wanda kake so yake son ka. Zan iya rantse miki ban taɓa jin daidai da ƙwayar zarra na soyayyar shi ba a raina. Kawai dai yana da girma da kuma ƙima ne a idona da ba zan iya wulaƙanta shi ba shiyasa nake sauraren shi. Ya jima yana ce mini zai turo ina dakatar da shi, kuma kawai sai ya shammace ni bai sanar da ni ba saboda yana taƙamar duk gidan mu sun san da zamansa? Sai yau fa da daddy yake sanar mana da safe." Ta ƙarasa cike da takaici. "Ki yi haƙuri kin san shi aure nufin Allah ne, kuma matar mutum ƙabarinsa. Ni wallahi a ra'ayina ma da na auri wanda nake mutuwar so gara na auri wanda yake mutuwar sona. Kin ga ni yanzu Haisam muna soyayya sosai da shi kuma shi nake son aura amma ya fara sire mini, saboda kule-kulen ƴan mata gare shi sannan wayewarsa da buɗewar idonsa ta yi yawa, ga shaye-shaye da yake taɓawa abin da duk muka tsani ganin namiji na yi. Yanzu dai ki bar wannan tunanin ki bar wa Allah zaɓinsa ki cigaba da addua da sannu zai shiga ran ki. Aikin ki yana da yawa yau. Ga karanto saƙonnin masu sauraro na shirin da ya gabata, ga sabon shiri da za ki yi, kuma kin ga yau ma za mu fita gwada sa'armu ko za a dace."
Ta ɗan yatsina fuska "Ni fa na fara gajiya da fitar nan, wahalar da kan mu kawai muke yi ba ganin yarinyar nan za mu yi ba."
"Duk da haka dai mu jarraba in sha Allahu wahalarmu ba za ta tafi a banza ba, kuma kin ga za mu ceto wasu alummar ne daga kaidinta."
Da ƙyar ta lallaɓata ta miƙe suka fice. Gabaɗaya fita suka yi daga ciki suka faɗa mota. Kai tsaye wurin da Zaitun ɗin ta kuma samo musu suka nufa. Bayan sun zauna aka kawo musu list don su zaɓi abin da suke so. Zaitun ce ta zaɓar musu ta miƙa masa, ya karɓa ya juya bayan ya kalla.
Bayan mintina ya dawo da duk abin da suka ce ɗin ya ajiye musu a gabansu.
Ba wannan ne a gaban su ba face abin da ya kawo su. Ta ƙasan ido Zaitun ke ƙare wa mutanen wurin kallo da suke ta sha'anin gabansu. Yawanci masoya ne ƴan mata da samari ke ciye-ciye suna taɓa fira, sam ba ta ga wata abar zargi ba a wurin. Ta dawo da kallonta kan Zaitun da itama ke ɗan bin su da kallo sama-sama. "Gaskiya fa a haka babu abin da za mu gano face wahalar da kan mu kawai da za mu ke yi, tunda mu dai ba jami'an tsaro ba ne bare a kallo ɗaya mu gane mai laifi, yakamata mu sake sabon tunani."
"Ni idan na ga yarinyar fa zan iya gane ta saboda Uncle ya mini kwatancen yadda zubin halittar ta yake." Ta ƙarasa tana cigaba da rarraba ido.
"Ke ba fa abin da za ki gane, tunda ba taɓa ganin ta kika yi ba shi kaɗai ne idan ya gan ta zai gane ta ɗin, kuma gidajen abinci da wurin shaƙatawa nawa muke da su a garin nan? Ko nufinki duk sai mun zagaye su muna nemanta?" Ta ƙarasa idon ta a kan ta.
"Shike nan dai kawai yanzu mu tafi tunda mun baro ayyuka a office sai wani jiƙon kuma" Miƙewa suka yi ba tare da sun taɓa komai a wurin ba. Kuɗi ta zaro da ba ta san adadinsu ba ta miƙa wa maaikacin wurin suka fice. Mota suka faɗa direban ya ja suna cigaba da tattauna maganar da kuma hanyar da za su bi domin ɓullowa lamarin...
Suna tsaye a gabansa yana ba su umarni, ya ƙarasa da faɗin "Ku kula ku kuma faki idon mutane kar a samu matsala." Suka rissina cike da girmamawa suka fice. Suna fita shi ma ya shirya ya fice ya tafi na shi aikin.
Suna isa unguwar suka kakkasu, cikin shigar mutunci suke da babu mai ganinsu ya zarge su. Cikin mutane suka shige har sai da dare ya tsala, don a gaban idon su mai shayi ma ya tashi, dayawan mutane sun sun jima da barin duniyarmu sun tafi ta bacci. Gaskiyar masu iya magana da suka ce dare mahutar bawa ta wani ɓangaren kuma suturar mugaye. Ɗaya daga cikin su ya ƙarasa ƙofar gidan ya ƙwanƙwasa a hankali, shiru ba a buɗe ba. Ya kuma ƙwanƙwasawa shiru, ɗan waige-waige ya yi kafin ya kuma doka gidan da ƙarfi.
Muryar namiji ya ji daga cikin gidan an ce waye? Shiru ya yi bai kuma magana ba, da hannu ya yafito sauran suka matso suka raɓe jikin ginin gidan da bindigu a hannunsu. Kuma bugawa ya yi ya jijjiga ƙofar "Wai wanene zai ɓalla mini ƙofa da daren nan?" Ya kuma faɗa a kausashe daga cikin soron "Ko ka buɗe ko kuma ka bari mu ɓalle ƙofar mu shigo wallahi ko ɓurɓushin ka ba za a gani ba, gara ma ka buɗe salin'alin don ba kai muke nema ba." Cewar Maiyagi a kausashe
Jin abin da aka ce ya saka jikin shi fara rawa abin ka da mara gaskiya, hannu na rawa ya zare sakatar ya leƙo da kan shi a hankali don ya ga su wane. Da sauri suka banke shi suka shige cikin gidan. Ɗaya ya ritsa shi da bindiga biyun suka shige ciki amma basu ga kowa ba.
"Ina sauran mutanen gidan suke?" Suka daka masa tsawa "Ba kowa ni kaɗai ne nan ɗin gidana ne" Ya ce cikin rawar jiki "Ƙarya kake yi, ina budurwar gidan nan take, don tabbas nan ne gidansu."
"Ni ne." Yace jiki na ƙarma. "Wallahi ko ka faɗa mana ko mu fasa kan ka da bindiga yanzun nan."
"Wallahi tallahi ni ne, babu wanda ke rayuwa a gidan nan sama da ni, don girman Allah kar ku kashe ni gara ko gidan yari ne a kai ni, da ma na san dole watarana asirina zai tonu."
Ganin yadda yake musu rantse-rantse duk ya haɗa gumi ya saka Goje fito da waya ya danna wa ogan nasu kira, yana ɗagawa ya ce "Oga mun zo gidan nan fa amma ba mu samu yarinyar ba sai wani muka samu a gidan, kuma ya tabbatar mana gidan sa ne shi kaɗai yake rayuwa a ciki. Oga duka alamunsa ya nuna ba shi da gaskiya dole shi ma akwai wani abu da yake aikatawa a ɓoye duba da wannan lungu da ya shigo kuma iya gidansa ne kaɗai a lungun."
Shiru ya yi daga can ɓangaren yana wani tunani, sai can tukunna ya ce "Ku bincike duka gidan duk wani abu da kuka gani ku haɗa da shi ku taho nan" Daga haka ya kashe wayar.
Ɗayan da ke tsaye a kan shi ne ya kuma gyara zaman bindigarsa a saitin goshinsa da shi kuma ya ɗaga hannu sama alamar saranda zufa na ta tsiyaya a jikinsa. Su kuma biyun suka shige ciki.
Abin mamaki kuɗaɗe ne zube a ƙarƙashin katifarsa, sai takaddun gidaje da filaye a cikin wani kwali. Ba komai ne ya fi ɗaure musu kai ba sai da suka buɗe sif ɗinsa suka ga kaf kayan sakawarsa na mata ne kuma masu tsada, gefe wurin ajiye takalma da jakunkuna. Kan madubin kuwa cike yake da kayan shafa da na kwalliya har da su sarƙoƙi da ɗankunnaye da zobuna su ma masu tsada.
Haɗiye mamakin su suka yi suka tarkata duka kayan a buhu, sannan suka tisa ƙeyarsa suka fice a gidan.
Kai tsaye motarsu suka shige suka tafi da shi zuwa can ɗin da ogan nasu ke jiran dawowarsu.......