14
by @hilfat
TURMIN DANYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(14)
Bayan isar su kai tsaye ofishin Jagaba suka wuce, yana duba wasu takaddu da aka yi photo copy ya ɗago jin sallama. Amsawa ya yi cikin sakin fuska domin duk cikin maaikatan nasu ya fi ji da su biyun saboda yadda suka ƙware a ayyukan su tare da mayar da hankali.
"Ya ake ciki an dace kuwa?" Ya jefa musu tambayar, suka kalli juna kafin Nuratu ta girgiza kai, Zaitun ce ta buɗe baki ta ce "Yau ma dai jiya iyau, za dai mu cigaba da gwada sa'armu ko za a dace. Kuma a ganina ya kamata jami'an tsaro su shiga cikin lamarin ko da wani abu da za su iya akai."
Ya girgiza kai cike da gamsuwa sannan ya ce "Ai tuni sun fara nasu binciken su ma, domin tun a ranar da aka saki shirin rahoton ya fita wani Inspecter Ma'aruf ya zo ya nemi ƙarin bayani daga gare ni kuma mun tattauna. Don haka ina tunanin a bar musu sauran aikin kawai tunda da alamu jama'a za su ba da tasu gudummawar su ma."
"Eh gaskiya kam da alama kwalliya za ta biya kuɗin sabulu idan aka yi duba da saƙonnin masu sauraro da aka samu bayan kammaluwar shirin. A cikin saƙonnin mun samu na wasu guda biyu da suka nemi a sakaya sunansu, sun faɗi yadda suma abin ya ritsa da su ta musu kwaf ɗaya, kuma kamannin da suka zayyano nata duk ita ce bayan na buƙaci hakan daga gare su" Nuratu ta faɗa cike da ƙwarin gwiwa.
"Yawwa to kun gani, kar ku cigaba da wahalar da kan ku ɗin akan wannan, yanzu kin kammala shirin ki na yau?" Idon shi a kan ta. "Dalilin dawowar mu kenan ma tunda lokaci ya kusa, bari na je na ƙarasa kimtsawa sai na gabatar." Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta gyara naɗin abayar tata. Ita ma Zaitun miƙewar ta yi suka fita tare bayan sun masa sallama.
Ita Zaitun Ofishinta ta shiga ya yin da ita kuma ta shige studio. Bayan ta mayar da ƙofar ta rufe ne ta ciro wayarta. Kai tsaye ta shiga inda take jera gajerun labaran da take samowa. A kan wani labari da ta yi wa alama ta tsaya, na wata marubuciya ne da tun da ta same ta sai ta tsayar da hankalinta a kan ta ganin yawanci labaran kai tsaye na tafiya akan abubuwan da ke kan faruwa a yanzun ne.
Zama ta gyara sannan ta fara magana a saitin mic ɗin. "Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Masu saurarenmu a halin yanzu barkan ku da warhaka tare da fatan alkairi a gare ku. Ina godiya a gare ku da jimirin bibiyata a cikin wannan shiri namu mai farin jini wato DANDALIIIIN MARUBUTAAAA (Ta ja sunan) In da muke karanto muku gajerun labaran hausa na ƙwararrun marubuta, mu ƙarƙare shi cikin taƙaitattun mintina kuma saƙon ya isa yadda ake so. Haƙiƙa ina jin daɗin saƙonnin da nake samu daga gare ku akan wannan shiri ta yadda da yawanku ke gyara wasu halayen su saboda wani labari da aka karanta da ya yi shige da rayuwarku.
To a yau ma gani da labari mai taken TUDUN KUMFA, wanda nake fatan ku ƙaru da darussan da suke cikinsa kar ku ji ku wuce kawai bayan kun bar shi a nishaɗi. Za mu tsunduma kain da nain cikin labarin tare da ni makaranciyar taku wato Nuratu Tahir Mai Nasara. mu je zuwa
TUDUN KUMFA...
Duniya tamkar teku ce, mai ban sha'awa daga nesa, sai tarin haɗari ga wanda ya faɗa ba da shiri ba. A wani lokacin kuskure guda na iya zama hanyar da za ta mayar da rayuwarka tamkar mafarki mara kyau. Haƙiƙa idan rami ya wuce ƙafa, to fa ba kowa ba ne ke iya tsallakewa. Kuma idan wani ya yi rawa an ba shi kuɗi, wani idan ya yi ɗankaren duka zai sha!
Kalaman da alkali ya yi ne suka dawo da ni daga tilawar wasiƙar jakin da na afka.
"Bayan kotu ta gama sauraren duk wasu hujjoji da kuma shaidun da suka gabata, ta tabbata waɗannan matasa sun aikata laifuka masu muni na sace-sace da fasa shaguna. Amma kafin faɗar hukunci za mu yi amfani da wannan dama, wurin jawo hankalin masu unguwanni da su ƙara yawan 'yan kwamiti, domin tsare dukiyar al'umma. Domin kullum abin ƙara ta'azzara yake yi, sai ka ce wutar daji. Kuma muna kira ga gwamnati a kan ta samar da wata ƙungiya ta dillalai, ta haramta sana'ar dillanci kara-zube a cikin gari ko kasuwanni.
Kamar yadda sashi na 316 na Penal Code ya yi bayani a kan ma'anar kayan sata, kuma sashi na 317 ya bayyana karɓa ko saya wanda zai kai mutum gidan gyaran hali ko biyan wasu kuɗaɗe. Don haka su waɗanda aka sayar wa kayan za a ɗaure su shekara uku da tarar kuɗi, sashi na 317 kundin laifuka (penal code law of northern Nigeria). Sata kuma horon shekara biyar ne, a gidan yarı sashe na 287 kenan. Idan kuma cikin gidan mutane suka shiga suka yi satar, kamar dai waɗannan to za a hukunta su under section 289 wato shekara bakwai a gidan kaso."
Babban abin da ya ɗugunzuma hankalina shi ne batun yanke mini hannaye da likita ya zo da shi bayan ma'aikatan gidan yarin sun miƙa ni asibiti. Ya ce wuƙar da aka sare ni da ita, akwai tsatsa a jikinta kuma ba a kai ni asibiti da wuri ba har ciwon ya fara zagwanyewa. Tamkar ruguzowar aradu da ka haka na ji maganar, wani guntun fitsari ya kufce mini. Take na shiga magiyar a bar mini hannuna zai warke, amma dayake bakin alƙalami ya bushe sai da aka yanke su.
Rayuwa ta jefa ni a jarabawar da na shirya da kaina. Kuma na girbe abin da na shuka, na ɗanɗani ɗacin ɗanyen abin da na dafa shi da hannuwana. Take ƙwaƙwalwata ta shiga tariyo mini, yadda rayuwata ta kasance tamkar a faifan majigi.
Sunana Karimatu, shekaruna ashirin da biyu. Mahaifimu ya yi faɗi-tashi a kanmu don ganin rayuwarmu ta inganta, amma abu ya faskara sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da ita. A dole muka haƙura da karatun boko, domin babu halin biya mana. Mu uku ne a wurinsu, daga yayana sai ni sai autanmu. Na kasance mafi soyuwa a zuciyar iyayena, musamman mahaifiyata sam ba ta ƙaunar ganin laifina. Ina da farin jinin mutane, da dama na cewa kyawuna yake janyo mini soyayyar jama'a, amma daga baya sai kyawun ya zama na ɗan maciji.
Tun tasowa ta nake da ƙaunar kashe kuɗi, duk abin da na gani ina so sai na tada ɓalli an siya mini. Kasancewar mama tana 'yan ƙananan sana'o'i, ya sa take kwance mini bakin aljihu har ta kai na san ma'ajiyar kuɗinta, don ta sha cewa na je na ɗauka. Mahaifina ya so nusar da ita illar hakan, amma ta ce ai ƙuruciya ce zan daina.
A wannan tsakankanin mahaifinmu ya kwanta dama, a lokacin ne muka kuma shiga matsin rayuwa. Sai na daina samun kuɗin kashewa daga wurinta, ta so dakatar da ni amma da yake na yi nisa ba na jin kira. Domin na yi wa kuɗi mugun sabo, wannan tasa na fara ɗaukar nata idan ban samu ba har na maƙota. A haka na taso har na zama budurwa, wannan ɗabi'a ba ta fita a jikina ba. Daga baya ma sai likafa ta ci gaba, domin kasuwanni nake shiga ina ɗauke hankalin maza mayun kyawawan mata da labari na yashe su. Ban taɓa soyayya ba, domin ba ita ce a gabana ba. Ko a gidan biki da na suna duk wacce ta yi wasarere da jakarta, ko wayarta za ta rasa ta. Kai hatta gidan kitso da ƙunshi, ba na ƙasa a gwiwa wurin yada zango na yagi rabona. Har sai da ta kai an gane ni, ko dangi na shiga kowa yana kaffa-kaffa da kayansa. Wannan ya janyo wa mamanmu hawan jini, saboda baƙincikin da nake cusa mata. Yayana kuwa tun yana jibga ta kamar Allah ya aiko shi, har ya zuba wa sarautar Allah ido. Domin kuwa idan ƙaho ya fara girma da wuya a iya lanƙwasa shi.
Wajen Ramatu dillaliya na haɗu da wasu mata da samari sun kawo mata kayan sata ta saya, a nan muka ɗinke da muka fahimci duk kanwar ja ce. Muka ci gaba da cin karenmu babu babbaka. Tuni na yi ƙaura daga gida na tare a gidan ɗaya daga cikinmu, saboda zaman uwa babu kwaɓa uba babu tsanani muke yi.
A wurinsu na san bin malaman neman sa'a da kuma rufa ido, na san mallakar makullai na kowanne kwaɗo da kuma almakashi. Watarana dubunmu ta cika aka kama mu, sakamakon satar gwala-gwalai da muka yi wa wata hajiya a wurin gyaran kai. Bayan mun fito sai abin ya yi gaba, domin zuciyoyinmu ƙara ƙeƙashewa suka yi, sakamakon haɗuwa da waɗanda suka dame mu suka shanye a laifi.
Sai muka ƙara fantsama sabbabin unguwa, wannan karon wacce muka shigar wa amaryar ce.
Cike da tsantsar rashin tsoro, muka ci gaba da haɗe kayan matar wuri ɗaya muna ɗure wasu a buhu. Sai da muka yashe ta tsaf, sannan muka nufi ƙofar fita. Turus! Muka yi jin ana ƙwanƙwasawa, muka shiga kallon-kallo tsakaninmu bayan mun sandare a tsaye kamar gumaka.
'Shi ke nan kwaɓarmu ta yi ruwa tsululu.' Na raya a raina haɗe da nufar ƙofa kai tsaye, bayan na ajiye kayan na zare sakatar. Take na yi arba da wani kakkauran mutumi, ya zubo mini idanuwa. Wani gigitaccen mari ya ɗauke ni da shi, wanda ya yi silar ɗaukewar jina na wasu sakanni, kafin na dawo hayyacina ya ƙara mini wani. Sama-sama kafar jina ta tsinkayo mini fusatacciyar muryarsa yana faɗin.
"Azzalumai macuta, ɓarayin banza ɓarayin wofi! Uban me kuke yi mata a gida ba ta nan? Ai na ga shigar ku ɗazu. Jama'a ku fito, yau dubun ɓerayen da suka addabe mu a unguwar nan ta cika!"
Ya faɗa cikin ƙaraji, kafin na tantance abin yi na hango wasu gungun matasa masu jiran ƙiris da makamai sun nufo gidan da gudu. Babu shiri na mayar da ƙofar na rufe, suka shiga bugawa kamar za su ɓalla ta suna faɗin sai na lahira ya fi mu jin daɗi, da ma cikinmu ne da su sai sun haife shi a take. Muka yi tsuru-tsuru a tsakar gidan, sai ka ce bayin da suka yi wa sarki ƙarya. Babu zato muka ga wani ya diro ta saman katanga, ya rufe mu da duka da gorar hannunsa muka hau karewa, sai ga wani ma ya diro a sukwane muka afka ɗakin matar. Ina shirin rufewa wani ya kawo mini sara sai a dantsen hannuna, na saki ƙarar azaba sai na kuma jin wani saran a hannun da na dafe ɗayan. Cikin ƙarfin hali, na datse ƙofar da bayana domin na san idan suka shigo kashinmu ya bushe. Tabbas wanda ya haƙa rami don wani, to shi zai faɗa a cikinsa.
Nan suka shiga jera mini sannu ina gyaɗa kai da cije leɓe, ɗankwalina Tijjani ya yaga ya ɗaure mini hannun domin tsayar da jinin. Kafin wani lokaci gidan ya cika maƙil, don sun buɗe ƙofar kowa yana ta faɗar albarkacin bakinsa.
Ƙura ba ta lafa ba sai da jami'ai suka iso bisa jagorancin mutumin nan, suka kora kowa waje suka ce mu fito.
Daga nan aka zuba mu a motar shiga ba biya, ni kaɗai ce mace a cikinsu sauran huɗun duk maza ne.
Ɗakin adana masu laifi aka jefa ni, na samu wuri na zauna cike da takaicin kamun kazar kukun da aka yi mana. Wai ya aka yi aka haihu a ragaya mu da muke da sa'a a jikinmu? An gurfanar da mu gaban alƙali, an kuma kamo sauran har dillalan da muke kai wa kayan satar idan mun yi.
Na sauke ajiyar zuciya, bayan dawowa daga tunanin da na tafi. Tabbas duk ganyen da ya riga ya bushe ba zai sake zama kore ba.
Gaskiya ne da aka ce komai nisan dare gari zai waye. Kuma kowane rai yana ɗauke da sakamakon abin da hannayensa suka aikata.(Suratul Jathiya: 22)