14
by @hilfat
WOMEN OF WORDS
Writers Association
(WOW)
TURMIN DANYA
NA
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn Mihal)
(15)
Suna isa gidan suka fito da shi sannan suka angiza shi ciki idanunsa rufe da baƙin ƙyalle. A gaban babba ɗin suka durƙusar da shi sai buhun kayan a gefe. "Buɗe masa idon" Ya ce kamar baya son magana. Ana buɗewa kam ya fara waige-waige da bin wurin da kallo idanu a zare. "Don girman Allah kar ku kashe ni wallahi tunda nake wannan harƙallar ban taɓa kashe kowa ko raunata kowa ba."
Wuri ya samu ya zauna idanunsa a kan shi ya ce "Babu ruwanmu da koma mene kake yi, wannan tamu ce ta haɗa mu da kai domin mu yagi namu kason mu ma, babu abin da za mu yi maka idan ka ba mu haɗin kai.
Mun yi garkuwa da kai muna buƙatar ka biya kuɗi ka fanshi kan ka."
Sai lokacin jikinsa ya fara rage rawar da yake yi. "Ina da kuɗi nawa kuke buƙata ku rabu da ni na tafi?" Ya tambaya.
"Duka kuɗin hannunka da na accaunt ɗinka za ka tattaro ka ba mu, sannan ka haɗa mu da wani mai kuɗi a danginka idan iyayenka ba su da shi ya fanshe ka." In ji Maiyagi
"Wabillahillazi kaf danginmu talakawa ne, babu wanda za a kira a nemi ya bada kuɗi ya fanshe ni, kuma ni yanzu ba ni da numbersu ba su da tawa, na yi shekaru rabona da garinmu, ko nawa kuke buƙata ni zan biya."
"Mu ga wayar shi" Gadanga ya faɗa cikin miskilanci, ciro ta suka yi suka miƙa masa, sai dai ga mamakin shi babu layi a wayar. "Ina layukan wayar" ya kuma tambaya
"Sun faɗi" Ya ce kan shi a ƙasa. "Ni za ka faɗa wa sun faɗi ina suke nace" Ya buga masa tsawar da ta ƙara razana shi. "Wallahi sun faɗi ba ni da layi ko ɗaya yanzu."
"Hmmm sun faɗi ko ka zubar" Ya saki wani malalacin murmushi yana tuno wani abu. "Ni ina da layin naka ai, akwai abin da na gano game da kai da ya haɗa da ƙyarya zamba cikin aminci da kuma cutarwa, ban damu da rayuwar mutum ba ko wani laifi da yake aikatawa da sai na ji komai daga bakin ka a yau kuma na haɗa ka da hukuma. Ku kai shi ɗaki na musamman ku ajiye kayan da safe zan duba." Daga haka ya fice a ɗakin.
Cukuikuye shi suka yi zuwa wani ɗaki suka watsa shi ciki sannan suka garƙame da kwaɗo. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya kwanta domin ya huta gajiyar da ya sha don ya yi aiki sosai a daren ranar, sai da ya rage kayan jikinsa, ya cire abubuwan fuskarsa sannan ya kwanta, sai dai baccin ya ƙi samuwa tunaninta ya cika masa zuciya.
Ko ya ya runtse idanun shi ita yake gani lokacin da ta ƙura masa ido da jajayen idanunta ga shatin yatsu a farar fuskarta da ya fito raɗau. Kallon da take yi masa ya fi kama da na tsana, abin da ke faɗar masa da gaba kenan. Inda ya gode ba ta ga fuskarsa ba, don ko yaransa ba wanda zai ce ga kamanninsa ko yaushe rabin fuskarsa a rufe take da wani jan ƙyalle idanunsa a zagaye da wannan abin na gwaska baƙi.
Wani tunani da ya faɗo ransa ne ya saka shi miƙewa zaune zumbur, tsai ya tsayar da tunaninsa wuri guda. Wannan shirin da ya saurara anya ba shi da alaƙa da wannan matashi da suka kamo? Ji ya yi yana so karo na farko ya aikata wani abin kirki a rayuwarsa.
A ranar ma yadda ya ga rana haka ya ga dare, aikam idanunsa duk a kumbure ya tashi. Tun a safiyar ranar ya saka suka fito masa da buhun ya zazzage su, ya dinga ɗaga kayan yana dubawa, sai kuma ya ware takaddun gidajen da filayen a gefe da kuma kuɗaɗen sannan ya mayar masa da kayan cikin buhun.
Da kan shi ya shiga ɗakin, yana ji an taɓa ƙofar ya zabura yana rarraba ido. "Mun samu takaddun kadarori da kuma wasu tsirarun kuɗaɗe. Yanzu muna buƙatar ka ba mu duka kuɗin cikin asusunka, sai mu sallame ka."
"Sai dai na ba ku ATM ɗin ku cire layin da na buɗe da shi na jima da yar da shi." Ya faɗa cikin nutsuwar da ya samu don ya gama tabbatar da kuɗi kawai suke so su ƙyale shi, kuma ya tabbata zai samu ninkin su nan ba da jimawa ba, don ya gama yanke Abuja zai tsallaka tunda manyan alhazawa sun fi yawa a can ɗin. Cikin sa'a kuwa a cikin kayan da suka tarkato an samu ATM ɗin har uku, nan suka ritsa shi ya faɗi pin ɗin.
Da ido Gadanga ya yi wa Mai yagi magana, sai ya ɗauki ATM ɗin ya fice, ya kuma yin magana da Maiyagi da idon shima, kai ya gyaɗa alamun gamsuwa, daga nan ya juya ya fice a ɗakin bayan ya damƙa masa waya a tafin hannunsa.
Can bayan kamar minti talatin ya dawo da kuɗaɗen da ya ciro a wata baƙar leda. Sai da Maiyagi ya leƙa ya gani sannan ya ce masa ya tashi su tafi. Har ya yi gaba yace ya dawo ya ɗauki buhun kayansa. Ya duƙa ya ɗauka daga nan ya ɗaure masa fuska katamau ya fice da shi a gidan.
Bayan ya hau mashin ɗin ya ɗora masa buhun a cinya sannan ya ɗaure masa hannuwa shi ma ya hau ya fige shi da gudu. Sun ci tafiya mai nisa sannan ya tsaya ya sauka. Buhun ya buɗe ya saka masa wayar a ciki bayan ya kunna ta, sai ya kunce masa hannuwan sannan ya koma ya haye mashin ɗin ya bar wurin da gudu.
Yana ji an kunce hannunsa ya yi saurin since ƙullin idonsa. Waige-waige ya shiga yi amma bai ga kowa a wurin ba face bishiyu, sai kawai ya ɗau buhun ya saɓi sauri har ya fito titi.
Sam babu ababen hawa a titin, kamar daga sama ya hango Napep na tahowa, ya dinga ɗaga masa hannu da sauri har ya tsaya. Hayewa ya yi da sauri, shi ma mai Napep ɗin bai tsaya tambayar inda za shi ba ganin yanayinsa ya ja suka tafi. Sai da ya ji shi a ciki sosai sannan ya fara samun nutsuwa. A lokacin ya samu damar faɗa masa inda zai kai shi.
A ɗaya ɓangaren kuwa wata alama ce ta fara bayyana a jikin na'urarsu tare da wata ƴar ƙara, cikin sauri ɗaya ya miƙe ya isa jikin naurar, tabbas kuwa lambar ce da suka ɗau lokaci wurin kasawa da tsarewa ta fara aiki. Cikin sauri na tsayen ya ɗaga waya ya kira wata number. Sai da ta kusa tsinkewa aka ɗaga. Ko gaisawa bai bari sun yi ba ya fara faɗin. "Alhaji Tajuddeen lambar nan fa da ka bada ta fara aiki yau, yanzu haka ga shi nan wayar a kunne take."
"Maza-maza ku yi wani abu akai kar ku bari damar nan ta wuce" Ya faɗa cikin sauri bayan ya miƙe tsaye a zabure.
Katse kiran ya yi ya fara kiran wani abokinsa, yana ɗagawa ya sanar masa abin da ake ciki. Da kuma inda za su haɗu, daga nan can ɗin ya nufa shi ma.
Kusan lokaci guda suka isa a lokacin tuni sun yi nisa a aikin har sun gano inda wayar take. Jamiai biyu aka ɗauka sai shi Alhajin da maaikacin ɗaya suka tafi.
Bibiyar inda wayar take suka cigaba da yi.
A wannan lokaci ne shi kuma suka iso, a bakin lungun ya sauke shi, sauka ya yi da buhun nasa ya nufi cikin lungun cikin sassarfa. Makullin da suka ba shi ya saka ya buɗe gidan ya shige.
Mai Napep ɗin na tsaye yana jira ya fito ya kawo masa kuɗin shi ya ga mota ta tsaya a bakin lungun, mutanen da suka fito daga motar ya bi da kallo, aikuwa suna shiga ciki ya ja adaidaitan shi ya bar wurin da gudu bayan ya saki wani malalacin murmushi. A daidai ƙofar gidan nasa suka tsaya, ana tunanin wanda zai fara shiga. Ƴan sandan su biyu ne suka shige da sauri. dama ƙofar a buɗe take bai rufe ba.
Shi kuwa tun shigarsa cikin sauri ya hau haɗa kaya yana tura wa a buhun, duk wasu abubuwansa masu muhimmanci ya fito da su, tunaninsa kayan gadon da suke ɗakin ta yadda zai sayar da su cikin ƙanƙanin lokaci ya haɗe kuɗinsa, har ya fara tunanin ya bar su kawai, to amma babu kuɗi isassu a hannunsa da za su kai shi abuja, .
Yana cikin wannan tunanin kawai ya ji an shigo gidan. Bai yi aune ba aka shigo ɗakin, cikin sauri ya saki kayan hannunsa ya ɗaga hannuwa sama "You are under arresting" ɗaya daga cikin jamian ya faɗa yana saita shi da bakin bindiga. "Ku bincike mini gidan ku fito da kowa da komai" Ya kuma faɗa, baki ya buɗe zai yi magana ya dakatar da shi "Kana magana zan fasa kan ka, da ganinka ba ka da gaskiya. Kai ku zazzage mini buhun nan na gabansa." Daga shi suka yi suka juye a ƙasa komai ya yi filla-filla. Wani irin yankewa gaban Alhaji Tajuddeen ya yi ya faɗi, yayin da duk suka zazzaro ido kamar sun ga abin tsoro.....