40
by @halimahz
Wani abu da Fullo ke ji akan Ilham ya tsaya mata a ƙirji kamar ƙurji, har ta baro upstairs ɗin wani irin ɗaci take ji a tare da ita da bata san dalilinsa ba.
Lokacin da ta fito compound zata wuce ɓangarensu ta tarar ana rage flowers ɗin gidan, wajen duk ya yi kaca-kaca, tausayin masu aikin cirewar da gyara wurin ya kamata, neman halal da wuya, kuma a haka namiji ke fita ya sha wahala ya kawo, macen da bata arziƙi ba tayi masa ɗiban albarka, ta girgiza kai tana mai jin tausayin kowanne namiji a cikin ranta amma banda Hayyo mahaifinta.
Sai da ta je gab da shiga gate ɗin na su kawai maganar macijin jiya ta dawo sabuwa a cikin kanta, take kuma tsananin tsoro ya rufeta ganin wani reshe na flower da aka sare wada ya yi kama da jikin macijin, ba shiri ta kurma uban ihu tana duƙewa a wajen sai kururuwa take, da sauri masu aikin suka yo kanta suna tambayar lafiya, dai-dai nan Khalil ya ƙaraso wajen shima yana duƙawa gabanta da tambayar lafiya.
Cikin kukan da take ta ce,"Maciji ne".
With suprise kowa ya ƙara maimaita abinda ta ce,"Maciji kuma?".
Ta ɗaga kanta jikinta sai rawa yake yi. Nan da nan masu aikin suka shiga laluben wajen, Khalil kuma ya ce ta tashi a wurin, sai ta girgiza masa kanta ta ce,"Ba zan iya ba".
Ya ce,"Kin gurɗe ne?".
Ta ƙara girgiza masa kai ba tare da ta ce komai ba. Yana murmushi ya ce,"Daure ki tashi babu komai anan, macijin ai ya tafi ga shi can sun kashe shi".
Tun ɗazu da ta duƙe sai a yanzu ta ɗago da kanta tana rarraba idanuwa, yadda take yi ɗin ba ƙaramin bawa Khalil dariya ta yi ba. Bai kasa riƙe dariyarsa ba ya saki yana ce mata,"Tashi na raka ki".
Ya faɗa saboda yadda yaga duk ta firgice, firgicewar da ba zata iya tafiya ita ɗaya ba. Ta miƙe da ƙyar sai ƙanƙame ƙafarta da jikinta take yi, ya wuce gaba yana cewa,"Mu je".
Idonta ya sauka cikin compound ɗin nasu, maganar Turaki ta cewar ai wadda ma macijin ya maƙale mata mutuwa ta yi, sai ta ji inaa ba zata taɓa iya shiga ɓangarensu ba, tana jin ma kamar sai dai Kaka ta dawo nan itama. Ba shiri ta ja da baya ta ce da Khalil,"Hammah Khalil ba nan zani ba ɗakinmu zan wuce".
Tana tafe tana ɗage ƙafafu haka ya rakata har ƙofar ɗakinsu, zaune ta sami Ɗausiyya na gyaran zogale, ganin Fullo yasa Ɗausiyyan ƙyalƙyalewa da dariya ta ce,"matsoraciyar kawai".
Fullo na hararta ta ce,"Tsoro ai halal ne, kuma tsoron me kika kalla na yi".
Ɗausiyya ta ce,"Ai ina kallonki sanda kika zube, har na yo wajen na ji ana batun maciji babu shiri na yo reverse".
Fullo na ƙara harararta sanda take zama kan gadonsu ta ce,"Ashe kema matsoraciyar ce".
Ɗausiyya ta yi dariya tukunna ta ce,"Kwana biyu kina makarar shigowa".
Fullo na kwanciya akan gadon ta ce,"Wani lalataccen barci nake fama da shi, in kuma kina da magani sammani".
Ta yi maganar tana jin jikinta a saɓule, yanayinta duk babu daɗi kamar wani abu na shirin faruwa mara kyau.
Ɗausiyya ta ce,"Ai ko dai ki nemi magani, Allah sa ba zafi ne a jikinki ba. Kin san ɗazu da Hammah Babba zai wuce yana cewa da Adda Zaytuna wai in ya je can wurin da zai je zai sayo mata maganin daina bacci, da kina nan kema da kin faɗa masa tunda naga yana da kirki, kawai dai baida sakin fuska, jiya ma dubu biyu ya bani".
Lokaci ɗaya Fillo ta ji allon ƙirjinta ya girgiza, Turaki ya tafi? Tare da Bello suka tafi, ta ya zai iya kula da kansa? Ya tafi da maganinsa?.
Tarin tambayoyin da suka zo wa cikin kanta kenan a lokacin, ga shi babu ɗaya da take da amsarta, don haka ido kawai ta lumshe kamar mai bacci, tana jin Ɗausiyya nata magana amma bata jin zata iya buɗe baki ta amsa mata, saboda faɗuwar gaban da take ji, wani irin yanayi da bata taɓa jin kanta a ciki ba, like kamar dai something bad will happen soon.
Bayan kwana biyu aka kawo akwatin sa ranar auren Fullo daga gidan su Amir, Innarsa da wasu Anties nasa guda biyu na ɓangaren mahaifi su ne suka kawo, akwaiti guda ɗaya da atamfa huɗu a ciki sai less da zai kai dubu shida guda biyu, shadda ɗaya da material guda ɗaya, da fashion na yari da sarƙa guda biyu sai takalmi da jaka duk guda ɗaya, sai kuma hijabs har ƙasa guda biyar da dubu biyar a haɗe, aka sa ranar aure wata biyu masu zuwa.
Kaya dai ma sha Allah sunyi kyau sosai gwanin san barka, kowa ya gani sai ya yaba, haka akaita zuwa ana gani ana tafiya da ma sha Allah, Amir ya yi ƙoƙari ba kaɗan ba, lallai Fullo ta yi dace da mijin kece raini, su Yami kam baki har kunne jikarsu ta yi goshi.
Sai dai fa duk wannan bidiri da ake yi Fullo bata ko ga tayar akwatin ba balle kayan da suke ciki, dan ƙememe tun ranar da Turaki ya tafi ta kasa zuwa ɓangarensu tsaboda bala'in tsoron da ke ranta, kayan sawarta ma sai Maijidda ce ta kawo mata ta ce musu wai jarabawa za ayi musu, kwana suke suna karatu ita da Ɗausiyya shiyasa.
Farko dai a tsorace take da zuwan, to amma da aka kawo kayan sai tsoro ya haɗe da kunya shiyasa ta kasa ko da zuwa, idan ta je bata san ta ya zata fara haɗa ido da mutane ba, ta san kuma halin Maijidda zata sata a gaba ne da aikin zolaya, dama tun washe gari ma ta zo tana mata lissafin abubuwan da za su yi da biki, ita dai har ta ƙaraci surutunta bata ce mata ƙala ba, Maijidda ma da haushi ya cikata ta karɓi wayar Yami da ta zo amsa ta yi wucewarta da cewar bata ƙara zuwa, ita zata je ta yi nata shirin ita ɗaya.
Tun ranar da aka kawo kayan Amir ke ta doka mata kira akan zai zo, ta yi masa godiyar kaya yake tambayarta ko sun yi, ta ce masa sun yi tunda har Maijidda ta faɗaz dan ita bata je ta gani ba. Amir dai juyin duniya ya zo yaga Fullo sam taƙi, idan ta yi kamar ta ce masa ya zo sai ta ji inaa a dai yi auren tukunna, ai haka ta ji Turaki ya ce duk masu yin zance a gidan, shiyasa ga ƙannensa nan cikinsu babu wadda ke yin zance ashe dalilin kenan, Amir tun yana lallashi da roƙo da ƴar murya Fullo dai taƙi yarda da zuwansa, yay fushi ma washe garin ranar gaba ɗaya bai kirata ba, kuma sai sauƙi ya zo mata, ranar Yami ta aiko Maijidda ta karɓar mata wayarta.
Kuma da Hajiya Madina ta yi mata batun me yasa bata zuwa wurin Kaka sai ta yi mata ƙaryar ai ta yi tafiya ne, sai dai fa a wannan kwanaki biyun Fullo ta yi muguwar rama, tun daga kan fuskarta har jikinta, na farko tsoro ya hanata sukuni, na biyu kuma kewar Kaka duk ta addabeta.
Ɓangaren Amir dai da yaga ba zai iya da azabtuwar rashin ganin Fullo ba ya kwaso ƙafa ya zo gidan, ya sanarwa mai gadi cewar wurin Hajiya Madina ya zo saboda ya sami damar shiga cikin gidan kai tsaye, ta yadda zai zaƙulo Fullo a duk inda take ya fito da ita, shi ba zai iya da rashin ganinta ba, yana ƙara kwana bai sata a idonsa ba tsab zai iya samun ƙatuwar matsala.
Mai gadi ya sanar ma da Hajiya Madina, aka yi masa iso zuwa parlon baƙi, ta je ta same shi suka gaisa, zatonta ma ko masu buƙatar taimako ne amma sai ta ji yana mata bayanin wurin Halima ya zo.
Kusan minti guda Hajiya Madina ta ɗauka tana kallonsa cike da nazarinsa, tare da kuma mamaki matuƙa akan batun wurin wacca ya zo, ashe yanda take tunanin Fullo ba haka take ba?.
Tashi ta yi tana ce masa ya jira yanzu zata zo, aka kawo masa ruwa da snacks da kuma juice na pineapple, kayan dai na aje kan table ɗin dake gabansa yana kallonsu amma ya kasa ko taɓa ruwan, bini bini sai ya duba agogon hannunsa, shiru shiru Fullo bata fito ba, wucewar mintina goma da tafiyar Hajiya Madina, a ransa sai ya fara tunanin kamar ko ba zata zo ba ne, kuma kamar Hajiyar ce ba zata barta ba, sai ya ji ransa ya yi mugun ɓaci, tare da ƙara jin tsanar aikin nata a ransa.
Ɓangaren Fullo kuwa suna can suna aikin suyar wainar shinkafa Baffa zai yi baƙi, suna faɗansu ita da Ɗausiyya kan ita Ɗausiyya na cika mai a suyar, ita kuma Fullo na zuba kaɗan, faɗan dai ya tashi akan kowacce ta sakawa ƴar uwarta ido, Zaytuna da Nihal kuma na gefe suna haɗa miyar agusi da ganda, suna jinsu suna yi musu dariya.
Nihal ta waigo ɗauke da dariya a fuskarta tana kallon Ɗausiyya ta ce,"Ke fa ke ce aikinki baya kyau, mai idan ya yi yawa a abinci baya daɗi Ɗausiyya, kuma kin san dai akwai masu ulcer".
Fullo na kallon Ɗausiyya ta yi dariya ta ce,"Ah tou kin dai ji, in kuma man kike so ai sai ki bari in ta zo ƙarshe ki soya taki da duka galan ɗin, lafiyarki ba lafiyar wani ba".
Ɗausiyya ta galla mata harara ta ɗauki waina guda ɗaya a cikin wadda Fullon ta soya ta wuce wurin Nihal tana faɗin,"Adda Nihal kalla fa ki gani, abu ƙamas ai sai ta ja mana magana ace muna da maƙon mai alhalin akwai wadatarsa".
Ta buɗe cikin wainar tana ƙara faɗin,"Ji fa aba a bushe kamar ba'a saka komai ba, yanzu dan Allah cikin abokan Baffa wani ya kai bakinsa ai direta zai yi dan wannan dai ba zata ciyu ba Allah".
Nihal na taɓa wainar ta ce,"Gaskiya kuma fa haka ne, mutane da basa rasa abin faɗa sai su tafi suna cewa Baffa ba ya wadata gidansa da isassan man abinci".
Ɗausiyya ta kalla yanda Fullo ta cika ta yi fam ta ce,"ah tou, dan haka ki zuba mai isashshe ki yi suya Malama, in ya so kya yi tsumulmularsa a gidanki, babu ruwan kowa, ƙarƙari ki ja wa mijinki magana wurin abokai da dangi a tafi ana yi da ke biki iya girki ba".
Ta yi ƙarashen maganar tana dariya. Fullo ta ce,"Ko ba komai dai mijina ya ce ina da tattali, ke kuwa kullum sai kin sha masifa akan haukar almubazzaranci da kike masa".
Zaytuna ta yi dariya sosai. Nihal da bata fiya shigowa kitchen ɗin ba ta ce,"Haka kuke aikin dama kamar kaji?".
Har sannan dariya bai ɗauke akan fuskar Zaytuna ba ta ce,"Kika biye su ba abin da zai hana bakinki yagewa, dan kamin barinki kitchen ɗin nan sai kin ji wani complain ɗin na daban".
Dai-dai nan Hajiya Madina ta shigo, duk suka yi shiru, ta dubi Zaytuna da Nihal ta ce,"sannunku da aiki".
Suka amsa da yauwa, ta ce da su,"Ina Samha?".
Nihal ta ce,"Na ga ƙawarta ta zo ɗazu sun fita".
Maama ba ta ce komai ba ta maida kallonta ga Fullo tana cewa,"meet me in my room". Ta faɗi hakan tana juyawa ta fita.
Fullo ta miƙe tana wanke hannu a sink, ta yi wa Ɗausiyya gwalo ta ce,"Kuma ayi aiki mai kyau in ba haka ba ran mutum ya ɓaci".
Ta faɗa tana mata gwalo sannan ta fice daga kitchen ɗin.
Tunda ta shiga room ɗin Hajiya Madina ta ga yanayin fuskarta sai jikinta ya yi sanyi, ta ƙarasa shigowa ta zauna a ƙasa tana fuskantarta, duk lokacin da taga fuskar Maama a haka ta san to da matsala.
Farkon abin da ya zo cikin kanta shine Turaki, kwana huɗu dama ta ji Zaytuna na faɗin zai yi, ga shi yau har kwana biyar, lafiya? Meke faruwa? Ko kuma yana kan hanya?.
Rashin sanin amsa yasa ta ɗago kai da sauri ta kalli Hajiya Madina da ke ta kallonta ta kasa cewa komai.
Murya a hankali ta ce,"Maama lafiya? Hamman har yau bai dawo ba".
Hajiya Madina ta sauke numfashi ta ce,"Za su taho jiya sai Baffa ya tura su El-Salvador za su yi signing wani contract da wani kamfanin fulawa a can, jibi in sha Allahu za su sauka".
Fullo ta ce,"Allah ya kaimu ya dawo da su lafiya".
Ta faɗa kanta na ƙasa. Hajiya Madina na karantar yanayin nata ta ce,"Kun yi da wani zai zo wurinki ne?".
Tambayar ta ji ta a wani iri, hakan yasa ta yi saurin ɗago kai tana kallon Maaman, kan ta yi magana Hajiya Madina ta jefa mata tambayar,"Amir ya zo wajena ya ce min yana son ganinki. Waye shi? A ina ku ka haɗu? Dama can ya sanki ne? Da yaushe kika fita har ya ganki ya biyo sawunki?".
Fullo ta sadda kanta ƙasa tana wasa da fingers dinta ta ce,"Wanda zan aura ne, amma wallahi ba mu yi da shi cewar zai zo ba yau".
Da matuƙar mamaki Maama ta ce,"Wanda za ki aura Fullo, kamar ya wanda za ki aura?".
Fullo ta kwashe duk bayanin komai har kayan sa ranar da aka kawo ta faɗawa Hajiya Madina. Ita dai kallonta kawai take tana ganin kamar yarinyar ƙarya take yi, ƙarama da ita haka ace za ayi mata aure? Me ta sani game da rayuwar auren.
Tasan cewar su ƴan ƙauye ne da ba su fiya bawa rayuwar ƴa mace muhimmanci akan yanda zamanin yanzu ke tafiya ba, amma bata taɓa tsammanin za'a iya aurar da yarinyar nan kusa ba kasancewarta mai ƙaramin jiki sosai, in ba sani ma ka yi ba zaka iya rantsewa ba ta doshi shekarunta ba.
Dalilin da yasa tun a ranar da yarinyar ta kwanta mata a rai ba ta yi hanzarin shigar da tata buƙatar garesu ba kenan, kiwon Fullo da take yi tanadi ne take taiwa ɗanta Muhammad Turaki, ashe har wasu sun mata shigar sauri, wani ya riga ɗanta, wani daban zai mallaki kamilar yarinya mai natsuwa da hankalin da irinta ke da wuyar samu, ba ɗanta Muhammad Turaki ba, wani daban can.
Yanzu wa zata ƙara kama masa? A ina zata samo masa irin Fullo? Har cikin ranta bata ji daɗin wannan batun ba sam, to amma ya zata yi, shirinta da lissafinta daban ne, hakama yanda ubangiji ya shirya lamarinsa daban, kuma na ubangiji shine dai-dai, kuma dama ita kullum addu'ar zaɓin Allah take nemawa yaranta.
Don haka yanzu addu'a ta rage mata akan Allah ya yi wa Turaki da Khalil zaɓin mace mafi alkhairi a gare su. Ta sauke numfashi tana daɗa kallon Fullo ta ce,"Amma Fullo me yasa baki faɗa min an saka ranar aurenki ba na fara shiri? Ko haka kike so na kai ki babu wani shiri, kin manta na ce ke ƴata ce? Ƴata fa kamar Zaytuna, Nihal da Samha. A sahun su na saka ki, ba Nihal ce Auta ba, ke ce Autata Fullo".
Ta faɗa cike da dukkan abin da take ji a cikin ranta, Fullo kanta na ƙasa bata iya cewa komai ba saboda kunyar da ta kamata.
Hajiya Madina ta miƙe ta isa wadrobe ta buɗe ta ɗauko wasu sabbin kaya irin na ƴan turkey, kayan da Baffa ya taho wa da Nihal ne tsaraba, ta ciro set biyu a ciki ta bawa Fullo ta ce,"Ungo ki yi maza ki je ki shirya yana parlon baƙi yana jiranki tun ɗazu".
Fullo ta kalla kayan sannan ta ce,"Maama zan je da waɗan nan ma".
Ta girgiza mata kai ta ce,"Daga wurin suyar waina fa kika ta so, haka za ki je wajensa kina tsami? Salon ya raina min ƴar tawa tun yanzu. A'a je ki gyara jikinki shaf shaf ki je ki samesa dan ya jima, kusan minti ashirin, idan kin dawo ki zo ki yi min list na abin da kike so na siya miki, wanda zan kai ki ɗakin ki da su".
Fullo ta karɓi kayan tana ta zuba godiya ta fita, fuskarta kawai ta ɗauraye ta ɗauki turaren Ɗausiyya ta fesa, sosai ta yi kyau a cikin kayan kamar dama dan ita aka siyo.
Haka kawai sai take jin sam bata ƙaunar zuwa wurin Amir, alhalin tun randa aka kawo kayan sa rana take ta so ta gansa, kwana biyar ta san ta yi kewarsa sosai da soyayyarsa, tunda in sunyi waya ma faɗa suke yi, bata saka mayafin kayan ba tasa hijab saboda yanda ta jita uncormfortable a riga da wandon.
Ta tafi tana ta ɓata fuska, ji take kamar har yanzu bata huce daga haushin Amir ba, kamar ranar nan da ta kulasa ba ita ba ce, kamar yau idan ta je zata yi masa wulaƙanci ne wanda zai sa ba zai ƙara dawowa gareta ba.
Tana shiga parlon ta tarar da shi ya miƙe a zuciye zai tafi, ganinta kuma yasa ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya cike da farin cikin ganin nata.
Tun daga kan yatsun ƙafarta yake kallonta har zuwa kan fuskarta, last da ya zo ta fita da mayafi bata yi masa kyau irin yau ba da take a cikin hijab. Ta tsaya daga bayan kujerar da yake tana cin magani bata ce masa komai ba.
Ya harɗe hannayensa a ƙirji ya ce,"Na yi zaton ai ba za'a barki ki fito ba dan na ga wani iko ake nunawa da ke a gidan nan, ko ba su san tawa ba ce? Ba ki shaida musu mijinki ne ya zo ba?".
Ta yi masa shiru tana ƙara ɗaure fuska tana jin kamar ta juya ta koma.
Sai ta ji ya yi ƙasa da murya cikin amo na shauƙin so ya ce,"Fushi ake da ni har haka da ba za'a min ma smiling ɗin nan da ke melting heart ɗina ba? Zunubin me na sake aikatawa wanda ban sa ni ba gimbiya?".
Sai kuma ya kama kunnensa ya ce,"Ayi haƙuri, ba zan ƙara ba in sha Allah, kar a kuma yi min horon da zuciyata ba zata iya ɗauka ba this time around".
Ba tare da ta kalle shi ba ta ce,"Tunda na ce maka ka bari zan saka maka ranar zuwa ai sai ka bari ko, ba wai ka ɗauko ƙafa ka taho ba notice ba".
Ya yi murmushi yana zagayo wa inda take tsaye, ji yake kamar ya rungumeta a duk sanda yake tare da ita.
Da ƙyar ya yi haƙurin hana kansa ya ace,"Ki yi haƙuri na yi kuskure, kasa haƙuri na yi wallahi, kwanaki biyar ɗin nan ji na yi kaman an shekara biyar, kamar an ɗaure ni a gidan prison".
Ta daɗa ɓata rai ta ce,"To ni aiki nake yi yanzu, Baffa ne zai yi baƙi anjima kaɗan".
Ta faɗa tana ƙoƙarin barin wajen, zai riƙo hannunta ta yi saurin janyewa tana cewa,"Ba fa kyau ka daina min irin haka, ni ban ma san yaushe ka lalace irin haka ba na taɓa ni".
Ya yi dariya sosai ya ce,"Tsabar ƙauna ce, amma ba zan ƙara ba daga yau, zan jure zuwa ranar da za a kai min ke. Yanzu dai kafin ki tafi dan Allah ki yi min murmushi ko zan sami sauƙi".
Ta ƙara cin magani ta ce,"Ba zaka samu ba kam, ka ga tafiyata".
Ta faɗa tana wucewa sai ya daɗa dakatar da ita da cewa,"Sorry na manta. Kaka ta yi min magana akan siyar da filayenki guda biyu saboda hidimar biki da zata yi da su, to na faɗa mata cewar za'a bada takardu ta ce suna wurinki ke kika adana su, yanzu ya za a yi? Saboda an sami wanda zai siya da tsoka, kowanne za a iya siyansa miliyan huɗu zuwa shida".
Ta juyo ta kallesa ta ce,"Kakan ta ce maka za'a sayar min da fili saboda hidimar biki?".
Ya ɗaga kafaɗarsa,"Yes, in kin koma zata daɗa miki bayanin hakan. Ko na kira Yami sai ki ji daga bakinta?".
Ta ce,"Tabɗijam, ashe gwarama da Allah yasa na ɓoye takarduna, to ai kuwa babu mai sayar min da fili ko guda ballantana har filaye biyu. Ayi haƙuri kamin lokacin da Allah zai bada yadda za ayi duk wata hidima. Ka gaida su Inna sai anjima".
Ta faɗi hakan tana ficewa daga parlon, ta bar Amir da sakin baki yana binta da kallo, fuskarsa na nuna damuwa da rashin jin daɗi.
Idan ya lura kamar yanzu bata son auren na su, ƙarara ya ga hakan a fuskarta, me ke shirin faruwa ne? Wani ne ya hure mata kunne? Waye shi? A ina yake?.
Sai ya ji wani bala'in kishi ya tokare masa zuciya, a fusace yabi bayanta don jin amsar tambayoyinsa, sai dai yana fitowa compound ɗin ya tarar babu ita, haka ya bar gidan zuciyarsa na masa ƙunci.
Da daddare tana kwance a ɗakinsu wajen tara na dare, time ɗin sun gama karatu ita da Ɗausiyya, suna hirar duniya Fullo kuma cikin ranta tana ƙudurcewar gobe zata cire tsoro ta je ɓangarensu, ta kuma bawa Kaka shawaran kar a sayar da fili ko ɗaya gwarama a sayar da dabbobinsu, kiwon da suke yi ya isa a yi mata komai in sha Allahu. Ita bata ɗauki duniya da zafi ba da za ace lallai sai an kashe mata uban kuɗaɗe a auren da ita ba ƴar kowan kowa ba. Filayenta tana da buri akan su, babban buri nan gaba, nan gaba ɗin da idan Hajiya Madina ta ƙara tsaya mata a karatu, ita kuma zata ƙara tsayawa kanta wajen zama babbar ƴar kasuwa.
Wayar ɗakin ta yi ƙara Ɗausiyya ta miƙe tana mita ta yi picking call ɗin.
Daga ɓangaren Zaytuna ta ce,"Ɗausiyya Fullo tayi bacci ne?".
Ta ce,"A'a".
"To ce mata ta zo da sauri please".
Ta ce,"Tom Adda".
Ta ajiye wayar tana kallon Fullo da har ta rufa bacci ya fara ɗaukarta, ta ce,"ki je Adda Zaytuna na kiranki".
Ta sakko daga kan gadon tana yamutse fuska saboda baccin da ke cinta, veil ɗin da ke ɗaure akanta ta warware ta yafa ta fita.
Cike da tsoro ta fito compound, tana tafe tana dube-dube har ta ƙarasa sashen su Zaytuna, ta buɗe ƙofar ɗakin Zaytuna ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ganin Zaytuna bata ɗakin ta tsaya gefe tana jan yatsun hannunta, bacci sai daɗa fusgarta yake yi. Zaytuna kuma na toilet tana wanka, jin sallamar fullo yasa ta ƙwanƙwasa ƙofar toilet ɗin, wannan yasa Fullo neman kujera ta zauna tana ta jera hamma.
Wayar Zaytuna da ke kan gadonta ta yi ringing har sau biyu, ana ukun ta leƙo a toilet ɗin ta ce,"Ɗaga please ko waye ki ce bana kusa".
Fullo ta miƙe tana layin bacci ta je ta ɗau wayan, dai-dai lokacin kiran ya katse, sai kuma ya ƙara shigowa, sai da zata yi picking ta yi noticing vedio call ne, ta ɗaga murya wajen faɗawa Zaytuna cewar Vedio call ne.
Zaytuna ta ce mata,"Wanne suna ne jiki?".
Ta ce,"DH".
Ta ce,"Just pick".
Fullo ta gyara zaman gyalenta ta yi picking tana kauda fuskarta daga kan screen ɗin wayar, call ɗin na yin connecting ta ce,"Bata kusa, idan ta dawo zata kira".
Daga hotel ɗin da Turaki yake zauna kan gado ya lumshe idonsa sannan ya buɗe ya ce da ita,"Ke kuma kina ina?".
Ta ce,"Ina ɗakinta, ita kuma ta fita".
Turaki dai so yake ta haska fuskan nata gaba ɗaya amma taƙi, sai side face ɗinta da yake kallo, ita ba ta ɗauki muryarsa ba ma, ya san halinta zata iya ta yi droping wayar, ko kuma ta bar wayar a haka ta ƙi haska fuskan ba tare da ta ƙara cewa komai ba har sai Zaytuna ɗin ta zo.
Ya miƙe daga kishingiɗen da yake a jikin pillow ya zauna sosai sannan ya ce,"Bata ɗakinta ta fita, ke kuma kika shigo har kike ɗaga mata waya. Me hakan ya ke nufi? Sata za ki yi, ko kuma jiran kiran mijin aurenta kike, ki yi mata snatching?".
Ai furucinsa na ƙarshe yasa Fullo bata san ma lokacin da ta haska screen ɗin wayar gaba ɗaya ba a fuskanta, shi kuma dama ya faɗi hakan ne domin ya san halinta, hakan kaɗai zai sa ta kalli screen ɗin ba tare da ta shirya ba, imma ta fashe da kukanta tana masa bayanin ba sata ta zo yi ba, ko kuma ta yi masa tsiwa ta ce ita ba snatcher ba ce.
Ta cune tana ɗaga gira duka biyun sama ta ce,"Ni ba ɓarauniya ba ce, ban haɗa hanya da ɓarayi ba, kuma wallahi tallahi ni ba snatcher ba ce. Ina da mijin aurena a hannu idan ma baka sani ba, kuma ai ita me wayan da kanta ta ce in an kira na ɗaga, idan ba don haka ba, ba zan taɓa picking ba ko za a tashi duniya ana kira. Ku mutane ba ku san irin maganar da zaku na faɗawa mutum ba, ita mai wayar ai Yayata ce, ka tambayeta ka ji, idan ma ta zo duk zan faɗa mata gaskiyata".
Ta yi maganar tana murguɗa ƙaramin bakinta, ko waye ya bata haushi ya ɓata mata rai, duk da ba'a son ranta ta faɗi hakan ba, stealing fa! Ya san mene ma'anar danganta ta da sata?
Turaki ya yi murmushi sai kuma ya ɗaure fuska ya ce,"Ni kike yiwa rashin kunya? Sa'anki ne ni? Ita Yayar taki ni ba Yayanta ba ne".
Sai a lokacin ta ɗauki muryarsa, a tsorace ta murza idanuwanta tana ƙifƙifta su, ta shiga uku ita ce kalmar da ta ambata cikin ranta. Sai ta ji ƙirjinta na duka a lokaci ɗaya, ta marairace fuska tana yin kamar zata yi kuka ta ce,"Ka yi haƙuri ban san kai bane ai".
Ya ƙara tamke murya ya ce,"Ɗago kanki ki kalle ni da kyau, sai ki yi min tsiwar yanda za ki ji daɗi".
Ya faɗa muryarsa a ɗage. Ta ɗago kanta tana dab da fashewa da kukan da ke ƙasan ranta, ta tsana, ta tsani wannan ɗaga muryar da yake yi mata. Kuma a yau babu abin da zai hanata faɗa masa kar ya ƙara raising mata wannan deep voice ɗin nasa.
So ta yi itama ta ɗaga murya wajen faɗa masa ta yadda zai shaida gargaɗinta garesa, amma sai ta ji muryarta ta yi sanyi tana ce masa,"Bana so kake ɗaga murya haka don Allah".
Turaki ya shafo wuyansa ya ce,"Are you commanding me?".
Ta girgiza kai ba tare da ta ce komai ba, tana sa hannu ta goge hawayen da ya sakko mata. Sannan ta ce,"Adda Zaytuna ɗin wanka take yi, zan faɗa mata idan ta fito".
Ta faɗa tana ƙoƙarin kashe wayar ya yi saurin dakatar da ita, shin bata san tun randa ya taho ba ya rasa natsuwarsa saboda tunaninta, tunanin halin da take ciki, bata san tun ranar da ya taho ba yake jin fargaba akanta ba, kuma tun da ya sauka a kowanne bugawar sakan na agogo so yake ya ganta, ya ga motsinta, ya ga yadda lafiyarta ke ciki, ya yi kewar ganin kukanta, ya yi kewar tsiwarta, komai nata kewarsa yake yi. Bata san a daren yau ya rufe ido yafi sau biyar ba amma ya kasa baccin duk saboda yana so ya ganta, ko ya samu hankalinsa ya kwanta, ko wannan faɗuwar gaban ta bar shi.
Ya tausasa muryarsa ya ce mata,"Haka na ce ki ɗago ido ki kalle ni bawai ki kashe wayar ba".
Da ƙyar ta iya samun courage ta ɗaga ido ta kallesa tana jin ƙirjinta na ta duka, sai dai kallo ɗaya da ta yi masa sai ta kasa ɗauke idon nata gaba ɗaya, wannan tsoron ganinsa ɗin da take ji, sai ta ji ya yaye, ta ji tana so ta kalle shi, ta yi ta kallonsa.
Kallonsa take yi ta kasa ɗauke idonta a kansa, zata iya cewa kamar ya rame, kamar yana cikin damuwa, kamar yana buƙatar wani abu.
Ya katse tunaninta da faɗin,"Kina da matsala ne?".
Har yanzu idonta na kansa ta ce,"Me ka gani?".
Ya ce,"Me ya sami idonki?".
Ta lumshe su tukunna ta ce,"Bacci na ke ji".
Muryarsa na ƙara yin ƙasa ya ce,"Bayan bacci fa?".
Ta ce,"Ba komai".
Ya ce,"Are you sure?".
Ta ce,"Eh mana".
Ya ƙara kallonta sosai sannan ya ce,"Daga tuesday zuwa yau, faɗa min kalar fitinar da kika yi".
Ta waro ido waje ta ce,"Fitina kuma? Ai ni bana fitina, da hankalina na girma fa, baka gani ba".
Ya murmusa kunci sosai ya ce,"Na gani kuwa, ga ki na kin girma kin zama ƙatuwa. To Kuka fa?".
Samun kanta ta yi da ba shi amsa kai tsaye da cewar,"Ai dama kai ne kake sani kukan, kuma baka nan".
Ya ce,"Really?".
Baki kawai ta cuto gaba. Leɓensa ya tale da murmushin da bai shiryawa ba ya ce,"Magani fa?".
Ta bone fuska ta ce,"Wannan ma ai kai ne kake min dole, kuma da baka nan duk bana sha".
Ya ce,"Abinci fa?".
Ta juya idonta tana jin baccin na ƙara zuwa ta ce,"Ina ci mana". Ta faɗa tana ɗan shagwaɓe fuska.
Turaki ya yi shiru bai ƙara cewa komai ba, tsawon sakanni masu yawa yana kallon siraran yatsunta, wanda ta tallafe haɓarta da shi.
Ya buɗe baki zai ƙara yin magana sai ta riga shi da cewar,"Yaushe zaku dawo, Maama duk ta damu".
Ya ce,"Ba yanzu ba ai, sai next year".
Jin hakan bata san ta ɗago ido ta kalle shi ba, kamar ta zabura a yanayin yadda ta nuna, ta maimaita abin da ya ce,"next year kuma?".
Ya ɗaga mata gira,"Yes, Maama zata zo idan tana son ganina, also Zaytun. Ko bayan su akwai wanda ya damu da rashina a kusa da shi?".
Ta yi shiru bata ce komai ba, duk da tana so ta ce wani abu ɗin. Amma bata san ma ta ya zata ce ba idan zata faɗa.
Turaki ya ce,"Oya kashe wayan, dare ya yi, Kaka na can na jiranki".
Ta ɗan saci kallonsa ta ce,"To na ga duk ka rame, baka da lafiya ne? Ko wani abu yana damunka?".
Ya ce,"Lafiyata lau, ina dai kewar Mum ne".
Ta ce,"Wacece haka?". Ta tambaya as if bata san komai ba.
Ya ce,"Yayar Maama ce, ta daɗe da ɓata bamu ganta ba har yanzu, tun Zaytun na jaririya, ki taya mu da addu'a Allah yasa mu ganta very soon. Ko idan na dawo za ki taimaka min mu nemota?".
Yanayin yadda voice ɗinsa ya fito sai ta ji tausayinsa sosai, ta ce,"Ka san inda za'a ganta ne?".
Ya ce,"A'a, kawai dai jikina na bani kamar ke za ki ga inda take".
Ta ce,"Sai dai na tayaku da addu'a, amma ni ban san a ina zan ganta ba".
Ya ce,"addu'ar ma mun gode. Bye".
Da sauri ta katse shi da cewa,"Da gaske sai next year ɗin zaka dawo? Da yawa fa lokacin".
Ta tambaya tana tsare shi da ido. Sai taga kamar ya yi murmushi sannan ya ɗaga girarsa alamar ehh.
Ta sake cewa,"To kana kula da kanka?".
Ya girgiza mata kai alamun a'a ba tare da ya yi magana ba.
Ta yi ajiyar zuciya kamar zata ce wani abu sai ta fasa, haka ɗaya take jin bata so ya yanke kiran, haka ɗaya take ji kamar idan ya kashe wayar shikenan ba zata ƙara ganinsa ba, hakama kamar ba zata ƙara jin voice ɗinsa ba.
Ya katse shirun nata da faɗin,"Kin daina jin baccin?".
Ta ɗaga kanta,"Ehh ya tafi. Ba zaka jira Adda Zaytuna ɗin ta fito ba?".
Ya girgiza mata kai bai ce komai ba. Ta ce,"Tom shi abokinka ɗin da ku ka tafi tare fa?".
Ya ce,"Ba shi wayar zan yi?".
Ta tura baki gaba ta ce,"Ince masa me to? Tambaya na yi ko yana kula da kai".
Leɓen Turaki ya tale da murmushi ya ce,"Ai ba wanda ya biyasa kuɗin kula da ni. Shima ta kansa yake".
Ta ce,"Kayiii, Maama fa ta faɗa masa. Shi ba ya riƙe amana?"
"A'a fa Maama bata ɗora masa nauyin kula da ni ba. Wani ƙato da ni ma kawai sai a tsaya kula da ni, ba ki ganni jibgege ba idan na tsaya a gabanki, da ƙarfina fa, zan iya tarewa kaina komai".
Murmushin da bata san da zuwanta ba ne ya ƙwace mata. Yatsanta akan leɓenta ta ce,"To magani fa? Kana sha?".
Ya ce,"Haka kawai ake shan magani dama?".
Ta ce,"Ai kai baka da lafiya".
Yay ɗan jim kafin ya ƙara cewa,"Duk kin sa bakina ciwo da tarin tambayoyin ki. Idan a kusa da ke na ke sai kina jin tsorona, ba ki iya sakewa ki yi magana da ni, jikinki ya yi ta rawa, me yasa?"
A hankali ta ce,"Ai kaima a waya ne yanzu ka yi min a hankali. Idan kana nan gida sai ka yi ta min tsawa kana bani tsoro, kuma ina ta ce maka bana son hakan."
Daga ita har shi ba wanda ya ƙara cewa komai, tana ta gyangyaɗi riƙe da waya yana kallonta, ƙarshe sai kashe wayar ya yi ganin kaman ta yi nisa a baccin da ya ɗauketa. Zaytuna na fitowa ta sameta akan gadon ta ɓingile tana bacci riƙe da waya a hannu, ta tasheta ta gyara kwanciyarta akan gadon.