TALES OF THE WAZEERIS

Back to nigeria

by @surayyahms

24...🦋🦋🦋

SURAYYAHMS

Tales of the wazeeris

Ata bangaren areesha kuwa iya harkokin charity event dinta da taje halartan sa a abuja shine ya dauke mata hankali musmmn ma datasan anata zancen dawowar yarima gida

ita kawai so take yau tayi abubuwan da tun kafin nan yarima shamsan yazo ya ganta zaiji sunanta abakin mutane kaca kaca musmn talakawa marasa karfi da kuma mabukata.

so take ta zamto full package sunanta yay tashe snn tayi farin jini a ko ina kuma ace duk wani hali da ake bida awajen matar yariman tharim vale asame shi ajikinta.

anan wajen event din a abuja ta sake haduwa da platonic boy friend inta na kwalta wato Farees salman.

already tasaka shi dan dolensa ya kawo mata kudi kuma shine ya tsaya tare da ita kusan shine ma ya kara tbtar mata da cewa Shamsan wazeeri zai iso nigeria gobe.

wannan labarin daya kawo bakaramin sauya gaba daya mood inta yayi ba.

da Wani irin farin ciki aranta tay maxa maza ta karkare event din dan ta dawo gidansu tazo maza maza tafara shirin tarban yarima dan farees ya tabbatr mata da cewa abakin matarsa rihanna yaji komi ayayinda take waya da mamansu gimbiya hajarat sakina batamasan yajita ba.

ana gama program kusan jirgi tabiyo frm abuja to kano dan adawo da ita zamkora akan lokaci.

excitement kamar xai fasa mata kirji cos each time takalli lkci xakaga tana murmushi ita kadai.

gabaki daya texes da missed calls din ushna data gani tunjiya har izuwa nadazu kaff dinsu intentionally tayi ignoring dinsu tabi tay banza wofi da ita cos honestly harga Allah mugun haushi yarinyar takeji.

a wannan lokacin kuma gabaki daya hankalinta baya kan komi yana kan batun dawowar Sultan ne

especially yanzu da tasan zai dawo nigeria kuma a kano zai fara sauka.

wajajen karfe tara na dare jirgin ya iso da ita kusan karfe 10 dai dai motar gidansu dayaje daukota anan airpot yashigo da ita cikin royal palace dinsu na zamkora.

wanda tun daga bakin gate guards suke miqa mata gaisuwa cikin tsananin girmamawa.

haryau kowa yana mata kallon mutuniyr arziki, jaruma, kuma sarauniya me tsananin taushin hali, nitsuwa da tausayin talakwa da nakasashhu

fadar zamkora gaba daya na dauke da wani irin warm northern royal ambience..

dukiya, tsaro da karfin mulkinsu ya ja baya sosai amma babu laifi gidan sarautar tasu bai gama lalacewa ba

sarauniya Areeshah tana shigowa ciki kai tsaye ta wuce cikin dakinta dake personal chamberta, nan da nan tacire dogon heels dinta tanamai mikawa maid snn tay kimtsa kanta kai tsaye ta nufi parlourn mahaifiyarta

gimbiya amani noorain na zaune abakin wani irin fankacecen gadon sarauta tana duba wasu invitation cards na upcoming royal gathering da zaa yi a wani kauye nan kusa dasu

dede lokacin ne yarta sarauniya areesha ta shigo looking calm amma tarin zumudi ne acikin ranta, batare da tay sallama ba sai gata nan turus a tsakar dkin dan ita tana da wnn jiji dakai din bata fiye son yin sallama ba

dagowa ahnkli gimbiya amani noorain tayi tana kallon diyarta cikin wata nutsuwa da kasaita irinta gimbiyoyi acikin muryanta tace finally… kin dawo..how was the event?

da jan kasaita da aji areesha ta karaso ta zauna kusa da ita tanamai gyara dogon gashinta ahankli tace it was fine but exhausting though.

cikin kyabe baki gimbiya tace yawwa dama jiranki nake ki dawo yar uwarki ushna fa ta kirani dazu.

atake areesha ta dan hade fuska kadan kafin nan ta kakalo wata klr murmushi tace “is she okay?

gimbiya amani noorain ta gyada kai tace dama wai zata dawo nigeria ne sbda internship placement tace min wai an turota nigeria ne daga makarnta.

dan karamin shiru ne ya ratsa tsakaninsu jin Areesha batace uffan ba

yasaka ta cigaba da cewa “i was thinking maybe mu sanar da mai martaba kafin tazo.

dawata kalar makirtccen nitsuwa Areesha tace toh, muje kawai ynzu mummy kinga dare yay kuma kinsan baba zai yi tafiya gobe kar mu tara masa surutai akansa..

Ba yabo babu fallasa gimbiya ta amince ska tashi kusan atare suka fito..

lokaci kadan aka sanar musu da cewa sarki murad yana falonsa

nan take suka nufi babban royal parlourn nasa dake cike da simple decoration na northern royalty

dark polished woods da soft scent na oud yanadan tashi acikin wajen.

sarki murad zamkora da damuwa yariga ya sakashi yafara tsufewa yana zaune cikin farar jallabiya na sarauta mai tsananin kyau yana tattaunawa awaya da wasu elders

yana ganin matarsa da yarsa areesha ya dan saki fuska kadan ya katse wayar tareda basu ixinin karasowa

areesha ce ta karaso kusa dashi cikin nuna masa tsananin so da biyayya har sanda ta gama gaidashi cikin girmamawa kafin nan ta nemi waje ta zauna.

gimbiya amani noorain ce ta fara tambayarsa yadda preparations dinsa na tafiyarsa mali gobe suke tafiya .

yafara mata bayani kenan nan take sai areesha tashiga cikin conversation din gaba daya, cikin tsabar iya waina makirci hakanan tahana mahafiyrtan kawo maganan ushna.

dan acikin nitsuwa ta hau jero mada tambaya akan schedules dinsa na zuwa international meetings dinsa na goben, kai har wani kara masa wasu information takey akan event din san tare da nuna masa cewa tafi kowa damuwa dashi sosai.

cikin wayo ta canza changa topic din gaba daya musmn dan kar ataba kawo masa batun ushna.

shikuma ya tsani in Areesha tana masa magana ana katsesu sabd bakaramin son ta da darajata yakeyi ba

she is his golden child.

haka gimbiya amani noorai tay shiru tanata jin mamakin areesha aranta har sukaci minti arbain ana hira, sai can saboda gajiyar dake tattare dashi ya katse hirar snn mike yana cewa princess kije ki huta i need some rest tomorrow will be long

tay murmushi atare suka masa sallama cikin girmamawa kafin nan ya barsu anan ya wuce private wing dinsa.

yana fita gimbiya amani ta juyo tanata kallon areesha tace“why did you stop me from telling him about ushna bayan kinsan abunda ya kawomu kenan

areesha tayi shiru kafin nan tasaki karamin murmushi me cike da nuna tausayawa da sanyin murya tace

“Allah ya huci zucyarki mummy…wallahi bana son akara stressing din baba ne shiyasa.

Da bacin rai gimbiya ta budi baki zatay magana maza

ta sauke murya kasa ta cigaba da magana cikin hikima..

haba mummy kawai gani nayi kmr hakan bai dace ba, ki kallesa dai dakyau wallh duk ya gaji, he already has international trip to prepare for tmrw, idan ushna zata dawo gida aiba sai ance mata ta dawo gidan ubanta ba please lets not stress him pls kinji mummy

namiki alkwari inde batun schl inta ne intadawo zamu taru duka ayi maganar komi idan yadawo daga tafiyarsa lafiya.

gimbiya amani noorain ta dade tanata kallon yanayin Areesha dan abu me matukar wuya ne ka iya gane salonta

magananta da tsananin tausayi da hikima takeyinsa har ma tasaka kaji kamar kaine baka da hankali da tunani

babu yadda ta iya sai kawai ta gyada kai ahankli tace toh shikn Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.

areesha tayi karamin murmushi tace Ameen mummy..

while daga cikin kokon zuciyarta tana jin wani irin strange relief dan tasan babu wanda zai sanar da sarki cewa yarsa Ushna zata dawo nigeria.

she needs to handle that information by herself dan ita kanta batasan meyasa har yau zuciyarta baya son ayi maganar kanwarta ushna a gaban sarki ba especially yanzu da yarima zai iso nigeria.

bata son ace wani abu yaxo yadauke attention din kowa a kanta ko kadan.

washe gari karfe 6.30 am na safe ushna ta farka

a hankali tamike zaune jin karar wayarta ya cika dakin nan ta jawo wayartan daga gefen bedside table ganin sunan supervisor inta ne yasaka ta dauka da wuri...

tafara gaishesa da ladabi, kai tsaye ya tambayeta meyasa bata wuce nigeria jiyan ba duk saita rasa me ma zata gaya masa sai kawai tace masa ciwon ciki ne yahanata amma kuma

yau yau zata tafi..

jadadda mata yay akan iya lokacin da suka bata danta taje nigeria tasamo wajen attachemnt cos ders is almost no excuse for delays..

bayan sun gama wayar hanklinta taji ya tashi sosai marmaza ta kira aka kara reshudling mata flight inta..

babu kalar kirar da batay ma arisha da mamanta ba amma dukansu haka basu daga ba...

karshe ma taji wayar mamanta kwata kwata baya shiga..

bata sani ba ashe tun safe areesha tay kane kane ta hana mamnsu motsi, har suka zauna a falo akayi breakfst atare suka raka mai martaba mota akai dashi airpot bata bari ankawo masa zancen xuwan ushna ba..

babban burinta shine karma maimartaba yaji bare in yarima yazo akazo neman aure a tuno da wata ushna tafiso daga anzo a nuna itace kadai yarsu

sai kai tsaye bada wani ciwon kai ba maza maza akulla baikon yarima da ita.

lura da cewa ushna tana ta kirarsu a waya yasaka taje ta sace wayar mamanta ta saka shi a DND snn tay restricting duka calls din ushna daga shigowa tabi ta goge misscals dinta duka ta kuma mayar da wayan

taje ta ajiyeshi..

haka ushna tay ta gaji ta bari dan haka kawai ta aje wayar ta mike tsaye cikin nutsuwa ta nufi bathroom

warm shower tayi me tsayi sannan ta gyara gashinta dakyau acikin tsari kafn ta fito daga bathroom din sanye cikin white robe na hotel din tanufa inda aka riga aka ajemata breakfast inta a table taga fresh orange juice, croissant n some fruits da kuma coffee.

ahankli tazauna tanamai cin abincin acikin nutsuwa bayan tagama cin abincin ne tamike tanufi inda duk kayanta suke domin ta shirya saboda yau ta yanke hukunci kawai tafiya zatayi nigeria in yaso koma maizai faru ya faru bata damu ba.

nan ta dauko elegant soft all black high neck dior jumpsuit da yayi matukar haduwa wnda material dinsa yay hugging jikinta in a classy decent way.

akansa ta jefa light grey oversized blazer mai tsananin kyau da expensive fitting tadaura wata perfectly wrapped grey silk veil.

small pearl studs kawai ta saka a kunnenta da wata elegant silver Fossil wristwatch mai simple design. sai yar hand bag dinta black leather Charles & Keith bag me tsari da kyau ba wani overly flashy ba

fuskar nan tata tay wani kalar fresh as usual ga kuma uban natural beauty dinta dayake haskawa

kafin karfe goma har ta gama packing komai nata tsaf hotel staffs suka shigo suka dauki remaining luggage dinta zuwa kasa.

sosai tayi kokarin maida hankalinta kan tafiyarta nigeria dan yanzu kusan babban challenge dinta shine ta yaya nema zata samu suitable real estate company daya dace da Royal Gulf standards din su a kano.

tasauke ajiyan zuciya ahnkli kafin nan ta dauki handbag dinta ta fita daga cikin suite din gaba daya.

driver din daya kawo ta jiya already yana kasa yana jiranta da black luxury suv din yana ganinta ya bude mata kofa respectfully yace “good morning ma’am. ta mayar masa da polite smiles tace morning...

cikin few minutes suka bar hotel din suka kama hanyar dubai international airport...

5:10am dot shamsan ya farka daga bacci da kyar sabd tarin ayyuka masu muhimmaci da yayi su jiya kafin nan ya kwanta,tashi yayi da addua abakinsa snn ya shiga bathroom dinsa direct...yadan dade aciki yana wanka kafin yafito jikinshi nannade cikin wani pure white bathrobe wanda ta amshe kalar fatar jikinshi dats so fresh nd soft kamar na jariri.

zama yayi cikin nitsuwa akan chair snn ya shiga shafa tsaddn moisturixing cream dinsa mai kamshin dadi ajikin fatar jikinsa yana bin ko inansa a tsanake.

Can sannan yatashi ya nufi gaban wooody ward robe dinshi inda yaja yabude ahankli yaciro wani soft off white jallabiya da wata karamar wando wanda ya yasakata taciki tazauna ajikinshin tamai kyau sosai.

Designers fragnance dinsa na tom ford ya fetsfesa sannan ya wuce masjid din dake anguwar da kafarsa yana tafiya ahnkli yana jan carbi a hannunsa yana ambaton Allah..

kaiwarsa masjid din saida yay raka'atanl fajr yana gamawa aka tada sallah nan shima ya mike ya bi jam'i akay raka'a biyu na sallahn asubahi

yana sallamewa bai jima baijma ba ya dawo gida a falon kasa ya zauna yana karatun qur'an very calmly.

can sai yaji sallama ta kofa

Wani yatsine fuskarsa yayi sanin bazai wuce mayun guards dinsan Nan bane da suke yawan isarsa da naci

ya dau kusan minti 20 yanamai karasa karatunsa koda yagama kamr bazai amsa ba kafin da kyar cikin muryansa na kasaita yace"come in"..

bude kofar private qurd dinsa yay ya shigo snn chef dinsa ma ya shigo ciki a hankali dukansu sanye da neat uniform dinsu na ma'aikata....

hannun chef din rikeda da wata yar karaman luxury tray mai dauke Da small mug of hot coffee da scramble eggs akai wanda tuni dadin qamshinsa mai dadi yacika iskan dakin da qamshi....

karasowa yayi a nitse ya ijiye tray din akan dinning snn ya tsaya acan gefe yayi shiru dan dokan aikinsu ce

bayan gaisuwa shamsan baiya bukatar jin surutu in ba wai shine ya bukaci hakan ba acan gefe chef yaja ya tsaya yay shiru kamar gunki...

private gurd din ne ya matso daf tareda dan rusuna kai muryan sa kasa kasa cikin taushi da ladabi yace"your highness sir, we are leaving in the next 45 min ur flight will be taken off by 8.00am, sir.

Shiru yay Baice komi ba yadan miketsaye yanayinsa mai cikeda ruwan tsantsar mulki da kwarjini yazauna very comfortably akan dinning chair ya

Marmaza chef din ya matso kusa yay serving masa coffe da eggs din cikin sauri cikin ladabi ya mikamai yasa hannu ya karba.

a hankli yakai coffe din bakinshi yay sipping dan kadan snn yazare a bakin shi batare da ya kalle ko dayan su ba,muryan sa can kasa kasa zaka rantse bashi ne yay magana ba

yace "clear my room.

Ya fadi hakan a fili fuskarsa emotionless..

Da sauri private gurd din ya amsa snn ya yahaura private side insa dan ya tattara masa kayan da zasuyi tafiyan dashi

shamsan yacigaba dashan coffee dinsa ayangance har ya gama yatashi a hankali yafita waje ya basu wuri

Nan da nan kowa ya runtuma aikinsa wann na tattare nan wannan na kwashe can dan sauran abubuwan dazasu dauka na tafiyar da kominashi da zai bukata duk suka tattarashi suka kimtsasu tsaf acikin tsadaddun trolleys dinshi suka bar masa zallan abubuwan da yanxu zaiy amfani dasu kominsa neatly arranged.

ana kammalawa lokacin karfe bakwai na safiya yayi agurguje private gurd din yafice daga sashen domin gama kimtsawa gudun kada ya batamai lokaci.

Bayan ficewarsa da kamar mintina biyar sai gashinan yashigo kwata kwata within 40 minutes yagama iya abunda zaiyi ya kammala shirinsa ya saka tailored pieces of Soft casuals da wata doguwar hand woven blazer na royalty complete black colour..

Azababben qamshin turaren jikinshi daya rikirkita atmospheren dakin mai tsantsar shiga jiki da ruda kwakwalwa ya fetsa inda duka ilahirin dakin saida ya dauka dashi yana fitowa tun daga kan fatar jikinshi tana busowa da kamshinsa ta koina.

evrything about his looks speaks royalty nd class,

domin kayan daya sakan is xpensive nd striking gasu su ba english wears ba kuma ba kalar traditional wear na nigeria ba amma kuma royalty casuals ne da ake sakawa a kamfani amma da hannu, da ya bala'in karama masa Kwarjini bana kadan ba.

7.20am ya fito yana takunshi na jan rai da daukar hankli nan yayi gaba duka gurds dinsa suka biyoshi abaya

zuwan sa ya samu har wani ma'aikacin a waje ya bude mai mota ya shiga dan sosai ake daraja shi ake kuma shakkarsa yana zama suka dau hanyar zuwa parking space inda private plane dinsa yake ajiye kusan tun jiya captain qaddafi yake jiran isowarsu a Airport din...

Bayan isan su filin jirgi babu bata lokaci akayi musu iso zuwa wajen parking,acikin private plane din daga shi sai qurds dinsa wanda su ka kasance acan nesa da private area inda yake zaune shikadai yana dan hutawa

he look stunning,nd was quite enjoying his flight time to time haka yanadan duban jaridar dake gefensa yanamai karanta abubuwan da ke faruwa a foreing businesses.

daga bangaren ushna kusan few minutes bayan tashuwar jirgin shamsan suma nasu jirgin ya tashi..

amma dake nashi private plane ne within some hours jirginsa ya iso nigeria inda suka sauka cikn aminu kano international airport.

40 minutes late jirgin su ushna ya sauƙa taga jama'a sun taru awaje guda kowa yana sauri sauri bata saba ganin haka a london ba sam.

gashi gaba daya ta gaji gashi anyi ruwan sama waje ya jike sosaii atke taji ta rude sbd rabonta da zuwa nigeria zai iya kaiwa shekaru goma sha biyu masu kyau nd she have no damn idea how to go home frm here msmn ma da har yanxu babu wani wanda ya dauki wayarta ko ya amsa sakonta bare tace a aiko mata driver ya kaita gida.

bayan har angama clearing kayanta duka haka ta jawo karamin trolly inta ta fito waje tana neman abun hawa acikin premises na airpot din...

saidai duk wanda ta tara sai yace mata gaskiya shi bazai iya zuwa zamkora ba

duk tarasa meyasa, sai can wani mutum yazo da mashin dinsa yake gaya mata ai yarima ne yadawo daga kasar waje snn da shi da convoy dinsa dukansu ta layin zamkora suka nufa zaije ya duba yawan taron mutanen kauyukan dake wajen ne da suka fito kwansu da kwarkwatansu suke so sugansa kafin ya wuce masaurata.

lokcin ushna ta balain gajiya gashi duk a tsorace take, she dint even care abt the prince story kawai rokonsa tafara yi akan ya taimaka yakaita cikin masarautar xamkora tareda masa alkwarin ko nawa yace kudin mashin din zata biyashi..

Bai mata musu ba ya daura kayanta akan mashin din dama ba wani girma yake dashi ba, dakyar ta iya hawa machine din ta zauna akai, kirjinta sai bugawa yake da karfi bata damu da mutanen da suketa kallonta ba suka fara tafiya.

mutumin yana ta mata hirarrki ita kuma ji take kmr ta fashe masa da kuka dan ranta ya dagule da fushi matuka, she was just wondering in her mind shin meyasa agidansu aka ki daukar wayarta dan inda an dauki waya da duk wann walakanci da wahalar datake shayanxu da bazata sha shi ba...

SURAYYAHMS

***