SARTSE COMPLETE

17

by @legendspen

Na ɗaga kai na kalleshi, ban gane inda kalamsa suka nufa ba kwata kwata. 'Tsufa bazai min kyau ba? To ai dole na nutsu fa ko? In da rai ko ba lafiya ai sai na tsufa, kuma ni Allah Ya gani ina son ganin 'ya'yana, amma ya zanyi da shi tun da ba ya so? Me zan so bayan abinda yake so?.' 

"Shikenan, Allah Ya nuna mana lokacin." 

"Amin Nanaty, me kike shiryamana na a sabon gidan nan?" 

Na yi dariya sannan na ce. 

"Me zan shirya mana kuwa?"

"Sabuwar rayuwa mana Nana, sabuwar soyayya, sabuwar kulawa, ina ganin kamar kina rage tausayina, a da Nana kina tausayina sosai kin damu da ni da damuwata, amma yanzu sai nake ganin kamar ba haka ba ne Nana, a da abinci har abaki kike ban, amma yanzu kin barni na ci da kaina, me ya sa Nana?" 

"Bakomai wallahi, kawai kutuwar Alhaji ce har yanzu ba ta gama sakina ba, ina jin rashin sa a cikin zuciyata sosai." 

"Nana, Allan da ya bamu Alhaji yafi mu son shi kuma ya amshi abunsa, ba yadda zamu iya, Nana wasu fa uwa da uba Allah Yake ɗauke musu rana guda lokaci ɗaya, su ce me? Allah Ya ce ku kasance masu godiya ni kuma zan ƙara muku, ko gode masa da ni'imar da ya yi muku Nana, zai ƙara muku wata." 

Jawoshi na yi jikina na rungumeshi, sannan na ce. 

"Hakane, Allah Alhamdulillah, ko kai da Allah Ya bani wata ni'imace da zan gode masa akai, ina sonka, ina ƙaunarka." 

"Nima haka Nana, ina sonki! Ina ƙaunarki." 

"Allah Yabar mu tare Mijina."

"Amin matata." 

Tun daga wannan lokaci na fara rage damuwa akan rashin haihuwa, na yarda da Sardauna na kuma amince da shi, na kuma yi alƙwarin ninka tausayi da soyayyar da nake yi masa. 

Washe gari, tun asuba da na tashi na shiga haɗa ma Sardauna lafiyayen abinci, wanda rabona da na yi masa ƙayataccen abincin tun kafin rasuwar Alhaji.  Ina tsaka da aikin a cikin dabarar yi masa cupcake ta faɗomin, ba tare da wani dogon tunani ba na haɗa cake, ina wancan aikin ina wancan, wajen ƙarfe bakwai da rabi na fito na shiga ɗakinsa, yana kwance kan gado na shigo toilet na haɗa masa ruwan wanka sannan na fito, a hankali na zauna a gefen gadon sabida kar na tashe shi, na kai hannuna kan sumar kansa na fara shafawa, da sauri ya buɗe idonsa ya sauke su akaina, ya sakar min murmushi sannan ya ce. 

"Nanaty." 

"Na'am, aje ayi wanka breakfast ya zama ready." 

"Tom ɗago ni." 

Ya faɗa yana miƙamin hannunsa, na kama tare da ja amma kamar banja ba. 

"Ƙara dagewa."

Ya faɗa, na kuwa sa duka ƙarfina na ƙara ja sai da na ji hannuna ya yi ƙas amma kamar bashi na ja ba. 

"Raguwa." 

Ya faɗa yana jawoni kansa, ai kuwa kamar takarda na faɗo, ya zame ya barni kwance ya shige toilet ɗin, sif na buɗe na ɗauko masa kaya na koma kicin na ci gaba da aikina, kusan mintuna ashirin na ji maganarsa a gab da kicin ɗin.

"Baki gama breakfast ɗin ba ne?" 

"A'a na gama gashi can a dinning bara na zo na baka." 

"To me kike yi anan?" 

Fitowa na yi sannan na ce. 

"Girki nake ma." 

"Me kike dafawa, kuma me zan yi da shi?" 

"Cake ne na tafiya ofis." 

"Awwww, thank you daman rabona da cake tun kina sona, gashi na ga alamar kin dawo da sona."

"Wai na daina sonka." 

Na faɗa ina ƙarasawa wajen dinning ɗin, shima yazo ya zauna na fara zuba mai. 

"Wow, ni Sardauna mijin Nana, dama haka kike min kullum." 

Na yi dariya sannan na ce. 

"To me nake ma ai haka nake ma, kai dai kawai ka ci." 

Haka kuwa ya ci sosai da sosai, daidai lokacin na juye masa cake ɗin da na gama decorating ɗinsa a cikin ƙaramin box." 

Sai da na rakashi har parking space, namu yana gefe na Turaki yana gefe, lallai fa ta dole sai sunyi zumunci domin kusancin gidan ya yi yawa, ko ƙara aka yi sai anji. 

"Wannan yaron yana nan kenan?" 

Ya faɗa yana shiga mota, sai da naga ya shiga sannan na juya na koma ciki na fara ayyukan, na gyara inda nake son gyarawa na goge ko ina sannan na dawo na zauna. Waya ta na ɗauka na fara dannawa, ga wayar dai amma babu layi babu wani abu da zanyi da ita, haka na gama juyata na ajiye, ga Tv babu damar yin kallo, danma gidan babu zafi amma gaba ɗaya na ji ya isheni, kamar na yi kuka haka nake ji duk gidan ya yi min zafi. 

Ganin zaman ba zai kai min ba na tashi na fara zagaye ko ina, na leƙa can na leƙa can daga baya na dawo bakin taga ina kallon gidan tanan. Turaki na ga ya fito daga ɓangarensa cikin shirinsa na ofis bai ma kalli inda ɓangaren mu yake ba ya shiga mota shima ya fice. 

"Shikenan yanzu ni kaɗai ce a gidan, na shiga uku ni Nana." 

Ɗakina na koma na zauna, amma zaman ba daɗi, na dawo falo ba daɗi, haka na yi ta zagaye zagaye har yamma. Ina zaune a falo na ji magana da motsin abubuwa, na buɗe taga na leƙa kayan gado da kujeru ne ake shiga dasu ɓangaren Turaki a raina na ce.

"Gwanda ka yi auren, ko na sami abokiyar zama da taya hira." 

Ina tsaye ta taga suka gama shiga dasu, shi kuma yana basu umarnin inda zasu jera, har suka kammala suka tafi shima ya bisu, dambun cous-cous da miyar kaza na yi wa Sardauna, sannan na yi masa lemon abarba, tun biyar da rabi nake sa ran ganinsa amma ba shi ya shigo ba sai bayan magariba, yanayin dana ganshi kaɗai ya sani farin ciki, sabida na ganshi fuskarsa a washe. 

"Ssnnu da zuwa." 

Na faɗa ina amsar jakar hannunsa.

"Yawwa, sannu da gida matata." 

Tsugunnawa na yi na shiga cire mai takalmin ƙafarsa sannan na kwasa na shiga ciki, bayan na fito ne na ce. 

"Wanka ko abinci?" 

"Abincin dai sabida ina so na sake fita yanzu." 

"Tom muje na baka." 

Na faɗa ina nufar dinning ɗin shi kuma ya biyo ni a baya, ya yi farin ciki ganin abincin amma kuma farin cikin dake cikin wayarsa yafi yawa, ina jin kamar na tambayeshi me yake gani a wayar sai kuma na ƙyaleshi, nasan ko mene alheri ne dai. 

Ina son yi masa magana akan zaman da na yi yau ba daɗi amma bai bani damar hakan ba, har ya kammala cin abincin sannan ya ce. 

"Haɗamin ruwan wankan." 

Na tashi na shige ɗakin na haɗa masa, bayan ya fito ya shirya sosai ya yi kyau kamar ko yaushe. 

"Nana, zanje dinner ɗin abokina ne, na ga kamar kin damu." 

Na yi murmushi sannan na ce. 

"Allah Ya tsare zaka yi dare ne?" 

"Bazan wuce goma ba ina ga." 

"Tom adawo lafiya, amma dan Allah ko Tv ne zan iya kunnawa zaman ni kaɗai ba daɗi wallahi." 

Kallona ya yi baice komai ba ya fice, sai na ji kamar ban kyauta ba, na dawo na zauna kan kujera tare da haɗa uban tagumi, bayan na yi sallar isha na dawo na sake zama, tun ina sa ran ganin Sardauna ƙarfe goma har sha ɗaya shiru, ta dole na bawa baccin da yake fisgata damar ɗaukana. 

Cikin bacci na na ji ana cewa.

"Anan kika kwanta? Tashi Nana tun da ba zaki iya jirana na dawo mu yi magana ba." 

A hankali na buɗe idona na kalleshi, cikin muryar bacci na ce. 

"Ka dawo?" 

"Eyh, tashi kije ki kwanta." 

Miƙewa na yi na nufi ɗaki na kwanata, ba tare da nasan asalin daidai lokacin da Sardauna ya dawo ba. 

Washe gari ma kamar jiya haka na tashi na shiga kicin, wani abu daban nasake haɗawa Sardauna, sanna na ɗauko wasu cikin cake ɗin jiya nasake docorating ɗinsu da icing suger, yau ko da naje ɗakinsa ma ya shirya da kansa, sai da wayarsa na kare a kunnesa yana magana. 

"Breakfast ya zama ready."

Gyaɗamin kai kawai ya yi alamun ya ji, ni kuma na shiga nawa ɗakin na shirya, bayan na fito na sameshi akan dinning yana danna waya. 

"Ina kwana?" 

"lafiya ƙalau Nana." 

Zama na yi na fara zuba masa abin breakfast ɗin, bayan na zuba mai nima na zuba, sai a lokacin ya kashe wayar ya fara ci. 

"Nana!" 

Ya kira sunana a hankali, na ɗago kai tare da cewa. 

"Na'am." 

"Kince bakya jin daɗin zama ke kaɗai ko?" 

"Ba banajin daɗi ba ne, kawai bansaba da gidan ba ne." 

"Hakuri ake yi Nana, yau da gobe  zaki saba, amma tun da kina so na baki damar amfani da TV ɗin shikenan?" 

"Eyh shikenan, sai kuma zancen sabon sim ɗin da ka ce zaka bani, ina son na dinga jin lafiyar Hajiya, kuma nasan itama zata nemeni, ya kamata na sanar dasu mun canja gida." 

"Eyh, to da wannan kam." 

Ya faɗa yana cire bayan cover wayarsa, ya ciro min sabon sim card sannan ya ce. 

"Gashi, amma Nana bana son na ga lambar kowa sai ta Hajiya ita kaɗai, sai kuma tawa." 

"Tom in sha Allah, na gode." 

Daga nan ya ƙarasa abinda zai yi ya fita, bayan ya fita na sim ɗin na kira Hajiya muka gaisa nake sanar da ita muncan gida, umarni ne daga familynsu kan rashin zaman daɗi da suke da Turaki gidan ma guda ɗaya ne mu da shi. 

Daga nan muka gaisa da su Yaya Radiya da su Ra'is, daga nan muka yi sallama na kashe wayar, haka kawai na ji zuciyata na ingizani akan na je na haɗa kayan Sardauna na wanke su, ba tare da na yi wani ja'in ja da zuciyata ba na ɗauka na shiga toilet na hau wanki, tun wajen sha biyu har uku na rana ina wanki, sannan na shan ya su na dawo na ɗaura girki, gaba ɗaya har na dare na yi. Bayan na ci na yi wanka na zo na kwanta na huta gajiya. Cikin barci na ji kamar ana bugu ƙofar tawa, buɗe da idona na yi tare da faɗin. 

"Waye?" 

"Ni ce." 

Na ji muryar wata mata, tashi na yi zan nufi ƙofar sai dai idona ya kai kan waya ta na ga agogon wayar ya nuna ƙarfe 06:16, gaba na ne ya faɗi afili na ce. 

"Ya ubangiji kasa ba baƙuwa na yi ba, a daidai wannan lokacin da Sardauna zai dawo ba."

Ƙara bugu ƙofar a ka yi na fita ina faɗin. 

"ina zuwa." 

A hankali na buɗe ƙofar gabana yana faɗuwa, aikuwa baƙuwar ce sai sai bansanta ba, murmushi ta yi min sannan ta ce. 

"Sannu!" 

"Yawwa sannu, shigo mana." 

Na faɗa ina matsa mata ƙofar, ta shigo cikin falon. 

"Ina wuni."

Na faɗa ganin ta girmeni sosai ma. 

"Yawwa Sunana Bilkisu, anan baya nake, na ga an kawo amarya kuma ina yawan cewa zan shigo Allah Bai nufa ba sai yau da na zagayo gidan kisto." 

Ta faɗa tana nuna hannunta baya alamun kwatancen inda take, na yi mata wani murmushi mai wuyar fassara, domin ni kaɗai nasan irin bugun da zuciyata take, lokacin dawowar Sardauna ne yanzu, kowanne lokaci zai iya shigowa, gashi baya ƙaunar ya ga wata ƙawa ta kusa ko ta nesa ta zo wajena. 

"Zauna mana to." 

Na faɗa ina nuna mata kujera, ta yi min wani irin murmushi sannan ta ce. 

"Ai sauri ma nake, amma zan dawo." 

Ban kai ga buɗe baki ba na ji horm ɗin Sardauna, wanda yake yi daidai lokacin da zai kashe motarsa, wanda yake yinsa domin sanar dani ya dawo. 

"Mai gidan ne ya dawo?"

Ta tambaya ne, na yi murmushi sannan na ce. 

"Eyh shine." 

"Ayyah to kinga kuwa ba sai na zauna ba, amma in sha Allahu zan dawo."

Ta faɗa tana juyawa zata fita, daidai lokacin kuma shi ya shigo. Kamar ana buga ganga haka na ji zuciyata na bugawa, da sauri na runtse idona sannan na buɗe. 

"Sannu da zuwa." 

Na faɗa ina ƙarasowa inda yake, ga mamakina ya sa hannu ya komo ni tare da faɗin. 

"Nanaty baƙi ne damu?"

Ya faɗa yana shigewa ciki, na bi bayanshi ina faɗin. 

"Ina zuwa." 

"Uhmm."

Ta faɗa tare da zama, ni kuma na bishi ciki. 

"Sannu da zuwa." 

Nasake faɗa ina ajiye jakarsa a ma'ajiyinta. 

"Yawwa" 

Ya amsa yana zama kan gado, tsugunnawa na yi tare da fara cire mai takalmi ina faɗin. 

"Wallahi bansanta ba, yanzu ta shigo wai anan baya take." 

Kallona ya yi tare da kamo hannuna

"To mene a ciki? Ai hakan yana da kyau sosai da sosai, ke fa kika ce min zaman ke ɗai ba ya yi miki daɗi kuma daman ka yi ta zama a waje bakasan kowa ba? Ta shi kije ku gaisa." 

Da wani irin yanayin mamaki nake kallon Sardauna. 'Sardauna dai? yau shi ke barin wata tazo gidan nan, har da cewa ayi ta zama a waje ba asan kowa ba, Sardauna da ya tsani ganin baƙo a gidan?' 

"Ki tashi mana." 

Muryarsa ta katse min tunanin da nake, na miƙe na nufi falon. 

"Ki yi haƙuri na bar ki." 

"A'a babu komai fa, ai mai gidan ne ya dawo, bari na zo na wuce amma zan dawo." 

"Tom shi kenan na gode sosai da sosai, nima idan na samu fita zan shigo gidan naku in sha Allah."

Na faɗa ina rakata waje, a gurguje na dawo haɗa masa ruwan wanka sai na tarar yana toilet ɗin ma.

Na fito na dawo na jera masa abinci akan dinning, bayan na fito masa da jallabiyar da zai sanya na ajiye mai kan gado, nima na tafi ɗakina na gabatar da magariba na dawo falon. 

*****
"Ko ka kirani na yi serving ɗinka." 

Na faɗa ina zama kan dinning ɗin. 

"Ah bakomai, har baƙuwar ta tafi?" 

Ya tambaya, na gyaɗa masa kai sannan na ce. 

"Ta tafi wai amma zata dawo, ni ba ma so nake ta dawo ba, nasan kai baka fiya son mutane suna zuwar mana ba. Zan ma taka mata burki." 

"Nina faɗa miki? kawai dai akwai waɗanda ban yarda dasu ba ne."

Legendspen
***